*🤱 MAHAIFIYATA🤱*
*_🌈 KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/Kainuwawritersassociation
_By_📚✍
*🌹 Ameena first lady🌹*
_page9⃣3⃣ to9⃣4⃣_
Sai yamma jirgin su ya sauka, lokacin Khadijah tagama gajiya saboda rashin sabo, shaheed yana lure da ita yadda duk tagaji da zama kafin su karasa.
Tuni Bashir ya daɗe da zuwa airport yana jiran saukar jirgin su,...Suna sauka Bashir ya taimaka musu suka shigar da kayan su Boot suka ɗauki hanyar gidan Alhaji Kabir..
Yanayin ƙasa ya birge Khadijah sai kalle kalle takeyi sam bata saka musu baki a hirar da sukeyi tanaji Bashir ɗin yana tsokanar ta amma bata kula shiba dai murmushi kawai tayi.
Anyi musu tarba ta mutumci sosai matar alhj Kabir ta haɗa musu liyafa, suna gama cin abinci da hutawa suka nufi bangaren da aka gyara musu dansu zauna.
A gyare part din yake sai kura daya ɗanyi,,.
Shaheed yanayin wanka ya fice shida Bashir, momma ce ta cewa Maryam (yarinyar alhj Kabir). "Maryam kije ki taya Khadijah ku Dan gyara wajan nasu"
"To momma" ta faɗa tana tashi.
Tare suka jera suna hirar har suka karasa part ɗin.Maryam sarkin surutu tuni suka saba da Khadijan, da yake itama Khadijah akwai saurin sabo saika rantse dama sun san juna..
Saida suka gama gyaran tsaf sannan suka cigaba da hirar su...
Sai 10:00 sannan su shaheed suka dawo dan lokacin Maryam hatta fara jin bacci.
Yana shigowa ta tafi part ɗinsu itama.
Ko kallon su Khadijan baiyi ba ya shige ɗakin sa kai tsaye.
Wanka yayi sannan ya nufi ɗakin daya tabbatar nan Khadijan ta shiga.
Itama hartayi wanka ta kwanta yaji shigowar shaheed ɗakin da sauri ta tashi zaune tayi kasa dakai tana wasa da yatsun hannunta.
Gefenta ya samu ya zauna sannan yayi ajiyar zuciya a hankali,.
Shiru na tsawon wasu mintuna sannan shaheed yace. "Na fahimci duk lokacin da kika ganni saikin tsorata kokuma kin daina wal wala, shi yasa zanyi nesa nesa dake har saikin saki jiki dani kin tuna waye shaheed dinki sannan zan kasance dake..."! Yana gama faɗar haka ya fice ya koma ɗakin sa.Hawaye ne suka zubo mata wanda batasan kona mene ba, "meyasa takasa yafe masa, kan wani ɗan ƙaramin dalilin ta wanda tasani shaheed bashi da laifi kan ɗan wani kuskure wanda take ganin akan gaskiyar shi yayi mata hakan takasa yafe masa kuma takasa faɗa masa gaskiya, duk da har yanzu tanajin haushin abin amma Yakamata ta hakura ta manta komai...". Haka ta dinga tunani iri iri tana kuka daga karshe dole ta hakura ta kwanta amma sam bacci yaki ɗaukar ta..
🤔🤔🤔To fa akwai abinda Khadijah tabarwa zuciyarta kenan ko..?✍🏻✍🏻✍🏻
Shima ɓangaran shaheed sam yakasa bacci, tunanin Khadijah dakuma tausayin ta yake ji, tabbas yasan duk macen da haka ta faru da ita bazata taɓa mantawa ba sannan yayi hakurin da ba kowacce mace bace zata iya yi, to amma tunda ya amsa laifin da bashi ya aikata ba Yakamata ace ta hakura ta yafe masa koda kuwa shine mai laifin...
A hankali yakai hannu ya dauko wayar shi dake kusa da shi, wata number ya kira bugu biyu aka daga.
Daga can ɓangaran naji ance "Barka da hutawa shaheed"..
Bai amsa ba saima tambaya ya mayar wa da mai maganar. "sun amsa laifin su ne"..
"A'a har yanzu basu amsa ba amma dai suna hannun mu, kuma munfara tunanin miƙa case ɗin court dama ina niyyar kiran ka akan haka"..
"No Yusuf Kar a Kaishi Court banaso Aja abin haka kuci gabada tambayar mun su kafin dawowa ta.."
"Ok karka damu inshallah"Da haka ya yanke wayar yaci gaba da tunanin shi.
Duk ranar da suka faɗi gaskiya ranar zai fadawa Khadijah may be a lokacin tagane bashida laifi amma yanzu kam bazata taɓa yarda dashi ba.Da safe a palour ta sameshi yana duba wasu books, bayan ta gaida shi ya amsa ba yabo ba fallasa, zama tayi suka shiru sai ƙarar takardun dayake budawa..
Ƙarar wayar shi yaji yana duba yaga Bashir ne sannan ya daga..
"To 2birds sai kuzo muyi breakfast ai"
Murmushi shaheed yayi sannan yace gasu nan.
Bai kalli gefenta ba yace. "kisa hijjabin ki muje" bata tambayi ina zasu ba dan tasan bayasan tambaya tabi bayan shi suka nufi bangaren su Maryam.
Bayan sun gama breakfast yace Bashir ya rakashi zai shiga school ya shigar da wasu abubuwa. Suka fice.Har dare su shaheed basu dawoba, duk hankalin ta yana kanshi hira kawai takeyi amma sam bata fahimtar komai.
Jin shirun yayi yawa ne ta kira wayar shi, saida ta kusa katsewa sannan yayi picking.
Kasa ce masa komai tayi jin shiru yasa shaheed yace "ya akayi ne"
"Amm dama naji shiru nace ko lpy"?
Murmushi yayi har saida tajiyo sautin fitar sa.
"Gamu nan kan hanya ai". Tanajin haka ta katse kiran tana murmushi itama.Suna dawowa suka wuce part ɗinsu.
Har zai shige ɗakin sa ta tsayar da shi bai jiyo ba Sannan bai tafiba.
Hakan yasa tagane ita yake sauraro.
"Gobe da safe zan fara fita ina taya momma da Maryam haɗa breakfast"
"Ok nima goben zan fara fita school ai.." yana faɗin haka ya shige ɗakin shi.Tunda ga wannan ranar da asuba Khadijah take ficewa abinta, tare suke haɗa breakfast, lunch harda dinner.
Sun saba sosai da Maryam, kuma kullum sai sun waya da zainab harma da Maryam ɗin..
Tana kiran su Abba da su mommy sosai suna gaisawa..Yanzu shaheed sam bashida wani lokacin kansa karatu ya hana shi sakat, shi yasa bai fiye zuwa gidan ba dan har sati Daya yana yi cikin school ɗin saboda yasamu isasshen karatu.
Khadijah kam hakan yayi mata daɗi yawon su suke fita ita zainab tunda yabata damar fitar..Karatun nashi yazo karshe dan dab suke da fara yin exam shiyasa ya dawo gida yanzu zuwa lokacin fara jarabawar tasu, dan watanni huɗu kawai ya rage musu yanzu.
Yau a gajiye ya shigo ya, tana zaune a palour tagaji shigowar motar shi, batayi mamaki ba daman yasaba ƙin faɗa mata.
Yana shigowa tayi masa sannu dawowa da tambayar ya makarantar.
Ya amsa mata a sake.
Kafin ya fito harya haɗa masa abinci a dining table.
Saida yaci sosai sannan tace masa "zamu fita da Maryam shopping"
"Ki shirya saina kaiku"
To tace sannan ta fara shiri.Da kanshi yayi driving ɗinsu itada Maryam yakaisu shopping Mall, waje ya samu ya zauna yana jiran su gama siya ya biya su tafi......