46

153 14 0
                                    

*🤱 MAHAIFIYATA*

_By_📚✍

*🌹 Ameena first lady🌹*

*🌈 KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION🤝🏻*

'''{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

_page 8⃣9⃣ to 9⃣0⃣_

____________________

A hankali ya matsa kusa da ita, batayi tsammani ba saiji ji tayi ya kamo hannun ta cikin nashi, da sauri ta kalle shi sai taga ko gefenta bai kalla ba yaci gaba da tafiya wajan da aka tanadar musu dan zama.

Zainab ma tayi mamakin ganin su a haka amma bata nuna saima ɗadi da taji ganin nasu a haka.

Ba ɓata lokaci aka fara gudanar da dinner, duk wani motsin ta idan shaheed na kanta.
ƴar hayaniyar da akeyi ne yasa shaheed yaji kanshi harya fara ciwo dama dariyar yaƙe kawai yakeyi, anyi shagali sosai ba'a tashi ba sai kusan 10:30pm sannan kowa ya watse..

Wannan karan shaheed da kansa ya ƙarbi key zaiyi driving, Dan dole Khadijah ta shiga front sit.
Bashir kam dama tuni ya tafi gida saboda gajiyar da dayake tareda ita.

A hankali yake tuƙin kamar wanda baison zuwa gida, ganin ya sauɗe hanya ne yasa Khadija jiyowa a razane tana kallon shi saidai takasa yimasa magana saboda tsabar tsoro da fargaba.
Shaheed kuwa ko kallon gefenta bai yi ba saima ɗaure fuska dayayi babu alamar wasa a fuskar shi, a wani shagon drinks ya tsaya amma Khadijah ko motsi ta kasa ƙadan take jira tafara kuka.
Bata ƙarasa tunani ba taga yana cire babban rigarsa, salati sosai da neman taimakon Allah kawai take, shaheed duk yana lura da ita.
Yana gama cirewa ya ajiye a back seat sannan ya fice ya nufi shagon.

Tsabar tsoro Khadijah kasa kallon inda ya nufa tayi dan ita a tunanin ta hotel ne ya shiga kama musu ɗaki..
Kukane ya kwace mata. Meyasa shaheed yake mata hakane koda yake laifin tane data yarda tashi ga motar daga ita sai shi..

Shaheed kuwa yana shiga shagon saida yayi murmushi "wato na fahimci yarinyar nan tanada tsoro". Ya faɗa yana sake bayyana murmushin sa..

Drinks da snacks ya siya sosai har Khadijan ya haɗa dan yasan itama bataci komai ba tun ranar.
Duk yadda taso ta buɗe motar takasa saboda saida ya rufe ta aciki sannan ya fita.
Hango shi tayi hannun shi rike da ledoji,.
Yana zuwa  ya shiga yaci gaba da driving dinsa hankali kwance, sai lokaci lokacin sannan itama hankalin ta ya kwanta ganin ya nufi hanyar gida.

Zainab kam ganin Mama na neman ina Khadijah ta tafi ta sanar da ita suna tareda shaheed hakan yasa hankalin su kwanciya tunda yanzu sunsan yazama mijinta.

Suna zuwa bakin gate tun kafin ya gama fitowa har tayi hanyar shigewa, dakatar da ita yayi sannan ya matso yana miƙa mata ledar dake hannun shi, ƙin karɓa tayi tana girgiza masa kai alamar bazata karba ba.
"Wannan ƴar matsala ce". Ya faɗa a ransa amma a fili saida yayi wani guntun tsaki sannan ya kamo hannun ta yasa mata ledar.
Daf da ita ya matsa har suna jiyo numfashin juna sannan yace. "yanzu haƙƙina ne na ciyar dake, ina fatan kin gane". Ya wuce yabarta nan tsaye.
Saida ya tafi sannan itama tayi tsakin kamar yana ganinta sannan ta shige gida.
Zainab na ganinta tafara dariya harda rike ciki, bata kulata ba ta ajiye ledar dake hannun ta tafara cire kaya.

Shaheed kuwa harya je gida yana tunanin Khadijah, kwarai yasani yana matukar santa saidai ya fahimci da zarar ya sakar mata fuska rainashi zatayi sosai tunda har yanzu tana ganin shine wanda ya lalata mata rayuwa a baya.

Drinks Kala kala ne shaheed ya siyo, taji daɗin su sosai dama yunwa takeji kuma batajin zata iya cin wani abu idan ba snacks ɗinba...

Har cikin dare Khadijah batayi bacci ba tunanin shaheed ne fal ranta "anya kuwa wannan shaheed ɗinta ne na baya kuwa..."?  Ta faɗa a zuciyarta lallai kuwa shaheed ya sauya a yadda ta sanshi a baya mutum mai saurin hakuri da nuna mata soyayya amma yanzu ya sauya anya kuwa shine..?  Da wannan tunanin bacci ya saceta..

Shaheed kwance akan bed idanuwan shi na kallon ceiling Sam yakasa yadda shine yanzu a matsayin mijin wajan Khadijan shi wacce yakejin a da bazai iya rayuwa babu itaba sai gashi Allah ya ƙaddara shine mijinta.
A hankali yafara tariyo irin rayuwar shi da ita a school har faɗan da suka shayi,har zuwa ranar da suka rabu..
Lallai yana san Khadijah kuma bazai taɓa daya sanin auranta dayayi ba, sam kasancewar an taɓa raping ɗinta bazai sauya soyayyarta a ranshi ba..
Tunani iri iri shaheed yayi tayi har bacci ya dauke shi dama tuni Bashir ya daɗe da baccin sa.

Da sassafe zainab da tsokanar Khadijah ta tashi.  Kallanta tayi sannan ta kuma yin dariya "Khadija jiya ina kikaje tareda shaheed ne"?
Bata amsa mata saima fita tayi daga dakin danta fahimci zainab ɗin so takeyi ta tanka mata.

Har dare bataga kiran shaheed ba kuma sam bata damu ba dama, nazeer kam yakira zainab har yafi a ƙirga.

Su Abba da abbu sun kashewa yaransu ƙudi sosai wajan kayan ɗaki, shaheed kam tun safe suka fita da Bashir dakuma nazeer.

Sai dare sannan Abba yace yakamata a fara shirin kai amaren, nasiha sosai kowa yayi musu musamman Khadijah da Abba yace idan har batayiwa shaheed biyayya ba to lallai bazai ji daɗi ba idan yasamu labari kuma saiya saɓa mata.
Sunsha kuka kamar ransu zai fita haka aka fito abin tausayi.
Wata sabuwa sam Khadijah da zainab sun kasa rabuwa da juna kuka sukayi kamar wasu waɗan da akace ɗaya mutuwa zatayi tabar ɗayar,. Har saida wasu daga cikin mutanan wajan suka zubar da hawaye tausayin su,..
Duk faɗan abbu saida ya tausaya musu da kyar aka ja Khadijah suka shigar da ita mota tana kuka mai tsuma zuciya.
Ganin Khadijah ta tafi yasa zainab ma tashiga mota tana kuka sosai ko gabanta bata gani sosai...

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now