*🤱 MAHAIFIYATA🤱*
_by_
*🌹 Ameena first lady*🌹
_page1⃣1⃣ to 1⃣2⃣_
Haka rayuwa tayi ta tafiya yau baki gobe fari, a wannan lokacin ne mahaifin Shaheed wato Alhj attahir arzikinsa ya dada karuwa duk kasashen ketare an San da zaman kasuwancinsa., hakane Yasa Shaheed yakara sangar cewa ansha kawo karar sa gun mahaifin Amma saiya ce a kyakeshi harda yarinta.
Yanzu Shaheed ya kammala karatun secondary dinsa, Alhj attahir ne yace ya zabi kasar da yakeso yayi karatu Amma Shaheed yace abashi lokaci yayi bincike tukun. Alhaji attahir yace to ba komai.
Yanzu Shaheed ya hadu da wani Dan iskan aboki Mubarak, shine yake Jan shi club duk dare tun baya yadda harya zama yanzu Shaheed babu club din dabai saniba a garin abuja.
Saidai duk iskancin Shaheed baya taba mace Saidai yayi romancing kawai shima ba sosai yakeyi ba acewar shi kazanta ce.
Yadaina maganar karatun kwata kwata alhaji attahir harya gaji dayi Masa maganar....Kudi sosai mahaifin Shaheed yake sakar Masa sosai hakan yakara bawa Shaheed damar kara iskancin sa yadda yaga dama.
Akwai ranarda ya yaje club yan hisba sukayi kame harda shi, nan kuma su alhj attahir sun kasa bacci Meera sai kuka take ita a Nemo mata yayanta.
Shiru har 12am, acan office din yan hisba kuwa kowa yabada number iyayensa ciki harda Shaheed.
Ana Kira daddy ya dauka bayan an fadamai komai, kawai ya hau fadan meyasa aka kama mai yaro,
"Alhj hakkin mune kama duk wanda muka samu da wannan barakar""Kasan dawa kake magana kuwa har kake fadamin dole kukama duk wanda kuka samu wannan barakar?" Alhaji attahir ne kuma ku tabbatar kun sakomin yaro tun kafin ku rasa aikin ku shashashai kawai, tun da sukaji sunan suke ta faman bada hakuri tareda da cewa basu sani bane shiyasa Amma yanzu zasu kawo shi har gida...
16minutes saiga Shaheed an sako shi ya shigo gida, Mamee da Daddy sukayi Masa fada sosai yace zai gyara kuma zai daina.Amma maimakon Shaheed ya gyara ai kamar an tunzura shi, acan ya hadu da wata yarinya Wai ita haneefa yar Kano ce yawon iskancin ta ya kawota Abuja, a gunta yaji labarin makarantar B.U.K babu abinda yasa shi yaji yanasan makarantar kamar da yaji akwai zafafan yammata.
Da safiya bayan sun gama breakfast yacewa daddy "daddy nasamu makarantar da nakeso" dama abinda daddy ya dade yanaso kenan aikuwa da sauri yace "Ina jinka wacce makaranta ce "?
"B.U.K" Shaheed yace
"B.u.k kuma Shaheed?". "Nayi tunani zanji kace America koma China kodai wata kasa mai makarantu masu kyau, amma kuma sainaji kace kano"
"Eh Daddy indai ba b.u.k ba na hakura da karatun duka"
"A'a Shaheed abun bakai haka ba, dama nazaci zaka zabi wata kasar mu tafi gaba dayan mu Amma tunda kano kazaba dama inada Aboki acan sunan shi Ahmad zansa ya nema min gida a can mu tafi mu duka sai Meera ta karasa school a can itama"
Mamee ce da mamaki ta kalli daddy "Amma abban Shaheed yaza'ayi saboda karatun Shaheed mu koma kano gaba dayan mu"
"Eh Maman Shaheed bazan iya nesa da Shaheed ba kema kin sani"
"To Allah ya kyauta" Mamee tace, ita Meera takaici yasa ko magana bata iyayi ba
An samu kwadedan gidan a badawa ba bata lokaci suka shirya komawa can, sunje sunyi sallama da iyayen Mamee dana daddy sannan suka koma kano ta dabo tumbin giwa...
Shaheed yasamu addmition a b.u.k.ba bata lokaci ya fara zuwa daukar lecture.
Tunda ya shiga makarantar ba karatun yakeba saidai ya Tara samari da yammata irinsa su fita yayita kashe musu kudi..
Ya damu kowa a makarantar kowa shakkar sa yakeji Dan ba komai bane yasa a kori mutum daga school din tunda babanshi yanada Yana tareda yan siyasa manya manya Kai har Malaman ma bai kyale ba hakan yasa bama akai karar sa gun Malaman tunda koka Kai a banza ma, ga kudi Yana murzawa yadda yadda dama...
A anguwar su yayi abokai Usman da Nazeer kuma tare suke b.u.k din.
Usman irinsa ne shikuma nazeer yanada hankali indai Shaheed yayi ba dai daiba saiyayi Masa magana, suyi fadan Amma basa dadewa suke shirya wa, saboda duk iskancin Shaheed yanada saukin Kai sosai saidai idan baka fahimce shiba...
Shaheed yanasan girma bayasan raini ko kadan sannan akwai San ka girmama shi kuma baya San wulanci ko kadan.....
Yana zubawa yammata wulanci yadda yaga dama....