*🤱 MAHAIFIYATA🤱*
_page 1⃣3⃣ to 1⃣4⃣_
Zamansa a b.u.k babu Wanda baisan Shaheed ba.
Khadijama bata sanshi bane saboda bata dade da fara zuwa ba..
Haka yaci gabada karatun watarana yazo watarana kuma sai yayi sati ba shiga class ba,
Amma abinda zai baka mamaki gameda Shaheed bai taba faduwa exam ba kowa Yana mamakin wannan abu Saidai ga wadanda suka sanshi sunsan yanada matukar kokari irinsu ake Kira gifted and talented a cikin aji....
Akwai watarana da wata Malama takai karar sa bayasan yin assignment kuma baya yin attendance saiya ga dama, Koda aka Kira Shaheed take ya kalli shugaban makarantar yace " doka ce ko ka'ida sai dole nayi attendance da assignment, malamin yace ya danganta da yadda tsarin malamin yake.
Kallon shi ya mayar gun malamar sannan yace "to bazanyi yiba kuma bakida da hujjar da zaki ka na fadi jarabawar ki" idan Kinga dama ki fadar Dani jarabawar ki kema ki rasa aikin ki wannan ruwanki ne" yayi gaba abinsa.
Saboda makaranta daddy yakara sakarwa Shaheed kudi hakan yasa Shaheed ya sake samun wata damar na cashewa yadda yaga dama,
Mamee harta gaji da Nasiha ta koma yi Masa fada yanzu idan yayi abu Saidai tace Allah ya shirye shi.Daddy yakan ce ta kyale shi watarana bazaiyi ba yarinta ce kawai.
Meera kam ta mayar da hankali wajan karatun ta bata biye irin Halin Shaheed. Da Yana zuwa dauko ta school tunda watarana yayiwa shugaban makarantar wulanci tace daddy ya siya mata mota ya sama mata driver ita ta gaji da halin Shaheed kullum saiyayi wa wani wulanci a school din..Daddy ya kagara Shaheed ya gama karatun nasa ya damka Masa daya daga cikin company na motocinsa dake Egypt Amma gaba daya Shaheed ya mayarda karatun wasa...
"Shaheed yakamata mubar wasa haka mu fuskanci karatu lokaci fa wucewa yakeyi ba jiran mu zaiyi ba" cewar nazeer .
Wani banzan kallo Shaheed din yayi Masa sannan ya Dora da " kaga nazeer nifa dama ba karatu nazo yiba nazone saboda haneefa tacemin akwai zafafan yammata a nan kuma da nazo bangan su ba haryanzu " saboda haka inaga barin makarantar nan zanyi gaskiya".Nazeer yace "haba Shaheed kanaso kace ba karatune ya kawo ka Kano ba"?
"Eh haka nake nufi ko kanada matsala da hakan ne"?
"A'a babu ai rayuwar ka ce sai yadda kaga dama zakayi da ita it's your time"."Yauwa daga yau karka kara yimin irin wannan maganar hope ka gane"
"Naji" kawai nazeer yace.tun daga wannan lokacin nazeer ya maida hankalin sa kan karatu duk da bai rabuda Usman da Shaheed ba.....
_cigaban labarin_
....a haka har bacci ya dauke Shaheed Wanda a cikin baccin yayi mafarkin ya dauki mataki akan khadija..
Haka Shaheed ya kagara safiya tayi yaje school.
7:30am Shaheed yagama shirya wa tafiya school sai zumudi yakeyi abinda yaba Mamee da Daddy harma da Meera mamaki.
Meera ce ta kasa hakurin shiru tace " Yaya Shaheed kodai ta samu ne yau zaka school da wuri haka"
"Bansani ba" ya fada hade da hade rai.
"Sorry Yaya Shaheed" Meera tace tana cigaba da breakfast dinta itama saboda school..Yana gama breakfast ya nufi motar shi ya shiga Yana Kiran Usman a waya " hello man kana ina"? Ina gida mana cewar Usman
"Ka fito bakin titi on my way now to school"
Da mamaki Usman yace " Shaheed yau kuma da wuri haka""Eh idan kuma bazaka ba zan iya tafiya ni kadai"
"Nooo ka karaso zan fito nima yanzu"
"Ok" Shaheed yace sannan ya katse Kiran...
8:00am dai dai Shaheed da Usman suka shiga b.u.k tun a bakin gate Shaheed ya fara baza idanun neman khadija.
Usman ya kalla yace " Usman zaka iya ganeta?"
"Wa kenan"?
Usman ya mayar Masa da tambayar.
Cikin hasala Shaheed yace "dalla malam wannane villager yarinyar mana ta jiya""Ooo" usman yace Dan harga Allah ya manta ma shi.
"Zan ganeta mana muje na tayaka dubata" Usman yace.....
Nikuwa abinda dariya ma yabani😂😂😂
Basusan khadija ta tafi kauye ba tama manta da batun su😂😂