part 12

165 12 0
                                    

🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*

'''{United we stand succeed; Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

      

*Jinjina ga Auntys Dina wato*
Hassana Musa
Usaina Musa. 

Dedicated to my brother
Shafi'u Musa.  (Shafam)

       *🤱 MAHAIFIYATA🤱*

_writing by_📚✍

        *🌹 Ameena first lady🌹*

_page 2⃣1⃣ to 2⃣2⃣_

Gudu yakeyi sosai saboda karya kuma rasata ta tafi gida.

Mintina kadan ne suka karasa dashi b.u.k ya Parker motar shi inda ya saba Kamar kullum..

Khadija kuwa suna fitowa daga lecture suka nufi inda suka saba zama itada Zainab, Zainab ce tace " wato mun saba da zama kasan bishiyar nan kullum muna nan Kamar mun saka kwai a wajan"

    Dariya khadija tayi tace.  "Wajan ne da iska sosai gashi har kowa ya gane wajan zaman mu ko neman mu akeyi nan ake zuwa"
"Aikuwa wlhy" inji Zainab.

Tunda yayi parking ya ciro tabkekiyar wayarsa kirar iPhone, Kiran Usman yayi.

"Hello kana ina ne"?
"Yanzu ina tareda nazeer, naga inda suka zauna Amma"

"Ok ka kyale nazeer wannan Dan matsala ne, kazo mu tafi Ina jiran ka"

"To gani nan"

Nazeer ne ya kalle shi yace "Ina zaku kuma"
"Baruwan ka malam Dan sa ido kawai"

"Idan tayi tsami zanji ai"     "bama zatayi ba"

Lokacin daya karasa Shaheed harya kulle motar Yana jiran sa, Yana zuwa suka wuce, zuciyar Shaheed cikeda farin ciki..

..... khadija na zaune  idonta a kasa tana duba lesson din yau da sukayi Zainab na gefenta tana danna wayarta.

Kanshin turare ne ya mamaye wajan, kyakkyawar farar kafa me sanye da bakin takalmin _vata_ dagowa tayi Dan ganin mamallakin kafar...

Idanuwan ta suka sauka fuskar Shaheed Wanda ya hade girar sama data kasa Kamar bai taba dariya ba.

"Kin ganeni ba"

"Ka koma kayi sallama, sannan na nayi tunanin na sanka koban sanka ba"

Ba Shaheed ba harta Usman yayi matukar mamaki da kalamanta, a tunanin su idan tagansu zataji tsoro tabasu hakuri ne Amma sai sukaji sabanin haka.

"Ban iyaba"

"Eh to naga alamar iyawa ce kam bakayi ba"

Zuciyar Shaheed gaba daya tagama hasala idanuwan shi sunyi jajir Kamar wuta..

"Ke yar gidan uban waye a garin kano, da alama makarantar da kike takama da ita yau zaki barta"

Khadija da ranta yafara baci ta Mike ta karasa kusa dashi face to face...

"Niba yar gidan uban kowa bace Kamar yadda kake tunani, kuma Nima bana bukatar sanin waye mahaifin ka a garin kano, abinda nasani kawai shine bai baka tarbiyar iya sallama ba, sannan kuma makaranta kam da ita na dogara Kamar yadda kafada, Amma ai naga kaima da ita ka dogara"

Usman ne ya daga hannu zai mareta, Shaheed ya dakatar dashi.

Kallon Usman tayi sama da kasa sannan tace. "baka Kai matsayin dazaka mareni ba,.  Niba sa'ar yinka bace kabari nayi da uban gidan ka,, Dan aci a rage Masa kawai,. Ta buga uban tsaki, sannan tacewa Zainab "tashi muje sis"
Dama Zainab a tsure take gaba daya khadija tabata mamaki yadda akayi ta iya mayarwa da Shaheed murtani haka, aikuwa khadija na cewa su tashi su tafi tayi bada harda su tuntube..

Bakin Shaheed har rawa yake zuciyar sa na suya ya kame a tsaye kam, saida ya dauki lokaci mai tsayi sannan ya iya taka kafarshi yabar gun.

Usman ne ya kaishi gida sakamakon zazzabi daya rufe shi kuma a halin dayake ciki bazai iya driving ba...

Har part dinsa Usman ya kaishi sannan ya wuce gida shima.

Wanka ya shiga ya sakarwa kanshi shower, Yana fitowa yasha magani ya kwanta.
Kasa baccin yayi sai tunanin maganganun da khadija ta fada Masa yakeyi.

"Ita yar gidan uban waye ne" ya fada da kakkausar murya Kamar wani Yana jinsa.

_Nidai nace Shaheed a rage zuciya, Kai bakaga irin maganganun daka fada mata ba😏😏😏_

Karar wayar shi yaji, idanuwansa a rufe ya daga muryar Mamee yaji.   "Shaheed kana school ne haryanzu"

"A'a ina dakina" muryar shi acan kasa kasa alamar bashida lafiya.

Gaban Mamee ne ya fadi tace "Shaheed lafiyarka kalau kuwa"

"Eh Mamee"

"A'a banyarda ba kazo part dina yanzu"

"To".    Yace sannan ya zura farar jallabiyar sa ya fice daga part din.
Yana shiga yaga Mamee a tsaye da alama zuwanshi take jira,
Yana shiga tayo wajan shi tana taba wuyanshi, zafi rau taji gabanta ya sake faduy.   " Shaheed kana fama da zazzabi haka kaje ka kwanta ba Wanda ka fadawa,da wani abu ya sameka fa Shaheed"?

Ganin hankalin ta a tashe yasa yayi murmushin daya bayyana fararen hakoran sa yace "Mamee da sauki fa saboda Nasha magani"

"A'a Shaheed bari na dauko key din motata muje hospital"

"Mamee kibari Meera ta dawo saita rakani lokacin nayi lunch"
" Kayimin alkawari zakaje idan kayi lunch"  "eh Mamee nayi"

"To muje na hada maka coffee kasha"

Shafa kyakkyawan sajen sa yayi Yana murmushi yace "Mamee har wani ji kike Dani Amma dazarar Daddy ya dawo kike mantawa damu"

Tagane tsokanar ta yakeyi shiyasa bata kulashi ba tace "eh naji din muje dai kasha coffee mayi zancan daga baya"

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now