🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
'''{United we stand succeed; Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation
Dedicated to my sweet brother
'''Shafi'u Musa.{shafam}'''💕💞*🤱 MAHAIFIYATA🤱*
_writing by_📚✍
*🌹Ameena first lady🌹*
#ameenafirstlady@wattpad
ameenafirstlady09@gmail.com
.Ameena Musa (first lady). Facebook_page 2⃣9⃣ to 3⃣0⃣_
........sai 3:30 suka gama lecture yau sannan kowacce ta nufi gida.
Saida ta hada kayan kowa gida sannan ta fita palour, anan taga aunty rahma tana jera abinci a dining table."Lallai aunty yau gidan sai kamshi yake Kamar za'ayi bako"
Murmushi aunty rahma tayi tace "ba bako zamuyi ba mijina nayiwa girki yaci yaji dadi"
"Eh lallai kam bakiso ayi Miki kishiya kenan, gashi gidan akwai sauran wajen zama"
"Aiban hanaku ku karo uku bayan ni ba atoh"
Dariya khadija tayi sannan tace"dawasa nake fa aidaga ke ba kari uncle ya rufe kofa"
"Atoh da kun kyauta wa kanku"
"Da mun kyauta Miki dai" khadija ta fada tana dariya."Aunty ki fadawa uncle gobe zan koma gida"
"Gobe kuma khadija?, wani abu akayi Miki ne"
"A'a aunty na yanke shawara ne"
"To Allah ya dawo dashi lafiya saina fada Masa"
A haka suka cigaba da hira har aka Kira sallar la'asar sannan suka nufi daki.
Saida akayi magrib uncle ya dawo bayan ya huta aunty rahma ta fada Masa khadija zata koma gida yace. "lafiya zata koma tun yanzu"
"Wlhy tace lafiya klau zata koma Amma yakamata ka tambaye ta kaji konice taki fadawa"
"To zan tambayeta naji"
Da dare suna dinner uncle ya tambayeta.
"Khadija antin ki ta fadamin zaki koma gida, ko""Eh uncle"
"Lafiya, ko wani abu akayi Miki a nan din"
" A''a uncle gani nayi gara na koma kusa da Mommy may be hakan yasa jituwa tsakanin mu"
Shiru yayi na wani lokaci sannan yace.
"To bakomai hakan yayi kin yi tunani, Amma ki fadawa abbanki tukun""To uncle"
Juyawa yayi gun aunty rahma yace mata. "Saiki ki shirya goben ki kaita a motar ki"
"To Allah ya kaimu"
"Ameen"
*****
Yau da safe Shaheed ya shirya cikin kananun kaya Kamar yadda ya saba yanata zuba kamshi sai ya fito Kamar larabawan sudan din sak, ya nufi sashin su daddy.
A zaune ya samesu zasu fara breakfast, daddy yace.
"Shaheed yanzu nake cewa aje a taso ka"
"Ya jikin naka"
"Alhamdulillahi Dad"Gaida su yayi sannan ya zauna domin yin breakfast din shima.
Saida suka gama sannan yace.
"Daddy""Na'am Shaheed meya faru"
Shiru Shaheed yayi na few minutes.
Daddy ya kuma tambayar shi"meya faru Shaheed ka kirani kuma kayi shiru"
"Daddy motata nakeso a canja min"
"To shine kuma kake saika bata raina, saki fuskar ka kaji,. Jiya ankawo sabbin motoci daga Spain idan kadawo daga school saika je Lagos ka duba nasan yanzu sun karaso"
"Ok Dad thanks"
"Ur welcome my son, I will do anything for you"
"Daddy Nima inaso a sauya min motar" Meera ta fada tana sauya fuska.
Shaheed ne ya kalleta up to down.
"Ke ni sa'anki ne, dazan bukaci a sauya min mota kema kice kinaso"Mamee da sai yanzu tasa musu baki tace.
"To uban yan San girma, itaba ya bace dabaza tace a sauya mata ba"
Murmushi manya daddy yayi, Dan gane Meera yan tsokanar ne akanta."Meera keda baki iya motar bama tukun kibari saikin gama makaranta saina sakaki makarantar koyan mota idan kin gama zan siya Miki mota kinji"
Shure shuren kafa tafara Kamar wata yarinya karama ita a lallai sai an siya mata itama.
A zuciye Shaheed ya taso kanta, aikuwa Kamar jira take tayi daki da gudu Kamar zata tashi sama.
Kwafa yayi yace "zan kama kine yarinya"
"Wlhy karka kuskura ka tabamin yarinya, ai gaskiya ta fada"Mamee tace.
Dariya yayi yace "idan anji haushi ai sai'a saimata mugani ko Shaheed"
"Eh daddy shine zamu San ita yarce ba"
"Zaku gani wlhy sai kunyi mamakin wacce zan siya mata"
"Eh dai munji duk tsiya sai tamu tafi tsada"inji daddy.
A haka suka gama breakfast din cikeda nishadi da annashuwa.
Khadija kuwa da abbanta ya yarda ta koma aikuwa da sassafe ta shirya tafiya school tana fitowa tacewa aunty rahma. "Aunty kishirya idan na dawo zamu wuce"
"To khadija saikin dawo"
Sannan khadija ta fice sai school.
Shaheed yana gama breakfast ya dauki keys dinshi ya fice ya nufi school, tun kafin ya karasa bakin titi ya Kira Usman da Nazeer.
"Kuna Ina ne"
"Muna titi muna jiranka fa"
"Ok gani nan"
A bakin titi ya kwashe su suka tafi makarantar.
Yana parking ya kalli Usman yace.
"Usman Ina zamu sameta""Tana wajan da suka saba zama"
Nazeer ne ya kallesu yace.
"Wa kuke magana akanta badai khadija ba""Ohhh dama sunan ta khadija, ita nake magana akanta mana"
"Shaheed wato bazaka kyale yarinyar nan ba ko? Saita gama zubar maka mutumci tukun ko"?
"Ka malam bafa wani abu bane hakuri zai bata akan abinda ya faru"
"Ok ku muje to"nazeer yace badan ya yarda da hakuri zasu bata ba.