*🤱 MAHAIFIYATA 🤱*
_By_📚✍️
*🌹Ameena first lady🌹*
Wattpad @Ameenafirstladyy
🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
'''{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_page 8️⃣3️⃣ to 8️⃣4️⃣_
....Abba Yana ajiye wayar ya kalli mommy dake gefensa yace. "ki sanar da Khadijah ta shirya zamu dubo Shaheed bashida lafiya.."
"Shikenan" Mommy tace tana nufar dakin su.Saida dabara Mommy tasa khadija tafara shiryawa itada Zainab wacce keta faman zumuɗin zuwan.
Suna gama shiryawa kiran nazeer ya shigo wayarta.
Tunda aka fara wannan rikicin basuyi waya ba sai yau saboda haka da murnar ta ta ɗaga.
Bayan sun gama gaisawa yake tambayar ta meyasa batayin picking din call idan ya kira.
Hakuri tabashi sannan ta sanar dashi abinda ke faruwa ta ƙara da "yanzu ma dubo shi zamuje bashi da lafiya"
Nazeer yayi matukar mamaki amma bai nuna ba sai tambayar ta yayi wanne asibitin ne.
Address ta bashi yace su haɗu acan hospital ɗin.Kafin suje asibitin har nazeer ya rigasu, lokacin Shaheed ya farfaɗo saidai babu wanda ya iya yiwa magana.
Yayi mamakin ganin nazeer amma daya tuna may be meerah ce ta kirashi ta faɗa masa shiyasa yayi shiru da bakinsa.
Daddy ne ya matso kusa dashi yace. "my son ka kwantar da hankalin ka nanda kwana uku kaima zaka zama big man.."
Kallon ƙarin bayani yake wa daddy, murmushi daddy yayi ya sake tabbatar masa da abinda yace.
Zumbur Shaheed ya miƙe yana faɗin "daddy ka kira doctor ya sallame ni..."
"A'a Shaheed kabari mana ka ƙara jin kwarin jikinka mana.."
"No Dad I'm feeling better now"..
Dariya sukayi su duka har nazeer dake gefensa.Wayar daddy ce tayi ƙara yana dubawa yaga abban Khadijah ne, saida ya gama amsa wayar sannan ya sanar dasu su khadija ne ya fice dan shigowa dasu.
Tunda ta shigo idanuwan shi na kanta, sam yakasa ɗauke idan shi daga kanta.
Ta kula dashi Amma saita basar ta haɗe rai, saida takaraso sannan ta saki fuska ta gaida su daddy meerah Kuma ta gaida ita cikeda murmushi.
Dan dole tayi masa sannu ganin su mommy suna wajan, sannan ta samu waje ta zauna bata sake magana ba.
Saida sukayi kusan awa daya sannan suka tashi suka tafi.
Ba haka Shaheed yaso ba yaso abar masa Khadija Saidai yana jin kunyar su Abba bazai iya magana ba.Sai dare aka sallame su tareda nazeer suka tafi dan har lokacin bai tafi ba.
Saida sukaje gida yace zai tafi daddy yace yabari sai sunyi dinner tukun.
Bai musa ba ya zauna suka fara yin dinner.
"Kaga nazeer naji daɗin zuwanka, yanzu saiku shirya abinda yakamata kuyi tunda saura kwana uku.." Mamee ta faɗa.
"To Mamee amma saidai zuwa gobe naga dare yayi yanzu.."
"Kaga ba wani dare yayi a yau zamu shirya komai guri fa ƙurewa yakeyi...". Shaheed ya haɗe rai ya faɗa.
"To shikenan naji Sarkin zumuɗi".Har suka gama dinner babu wanda ya sake magana, suna gamawa Shaheed ya ja nazeer suka tafi part dinsa.
Hira sosai sukayi har abinda yasa Shaheed yabar ƙasar batareda kowa ya sani ba da Abinda Ya haɗa shi da khadija.
Nisawa nazeer yayi yace. "kayi kuskure Shaheed, naso na nuna maka wasu daga cikin halayen Usman amma ka kasa fahimtata amma ai yanzu gashi ka gani,.."
"Nasani nazeer nayi kuskure wanda babu ta yadda khadija zata iya mantawa dashi saidai kawai bayan na aureta zan fahimtar da ita.."
"Shikenan to nizan wuce gida."
Wani kallo Shaheed yayi masa na baka isaba sannan yace "babu inda zakaje bamu gama shirya komai ba.."
Dariya nazeer yayi. "nina gama shirya mana komai ai,""Meka shirya..""?
Saida yayi murmushi sannan ya faɗa masa abubuwan daya shirya "gobe za suyi Fulani day, jibi Kuma za'ayi walima.."
Shaheed ne yace. "banji ka ambaci dinner party ba,..?
"Shima na shirya komai, na basu abinda suke buƙata saboda haka bazasu nemi komai daga wajanka ba.."
"Shikenan na gode ka kyauta"
Daga haka ya tashi zai tafi amma Shaheed yace a lallai saidai ya kwana a nan, dan dole ya hakura ya zai kwana.
Saida suka kwanta sannan nazeer yake tambayar shi ya zaiyi da karatun shi.
"Hutun 2month gareni zan koma..""Amma ita khadijan fa..."?
"Tare zamu koma, dan wlhy bazan tafi na bar matata a nan ba, amma duk hutu a nan zamuyi shi"
"Hakan ma yayi ai" nazeer yace.Da sassafe aka kawo lefen khadija dana Zainab kuma duk gidan uncle Abdulmutallib aka kawo su.
Akwatuna goma sha takwas aka kawo wa kowacce kalace ta banbanta. Sunyi kyau matuka kayan ciki kuwa abin har ba'a magana mutane har gulma sukeyi wai bazawara da kwati goma sha takwas.
Khadija kuwa Basu san ma ankawo ba suna can wajan shirya wa.Kamar yadda Zainab ta tsara tayiwa khadija kara a matsayinta na ƴar Fulani, yau suka gayyato kawayen su zasu yi Fulani,.
Tun safe mai musu gyaran jiki take aikin gyara su, 12:00 dai dai mommy tazo da mai make-up artist,.
Luccy makeover kuwa tuni tafara aikinta cikin kwarewa da iyawa,...
Ba ƙaramin kyau khadija tayi ba, dan duk wanda ya santa a baya yanzu yaganta ba lallai bane ya gane ta ta fito da asalin kyaunta na bafulatana.,.8:00pm motocin daukar su sukazo,. Taji daɗin rashin ganin Shaheed da batayiba,.
***** ***** *****
Duk yadda nazeer yaso yaja Shaheed wajan ƙin zuwa yayi, dole ya ƙyale shi ya tafi shi kaɗai, khadija taji daɗin da baizo wajan ba, saboda haka ta zage suka ci gaba da sha'anin su a sake.
Nazeer ya kira ya rike shi akan ya dauko masa hotunan ta, batareda ta san hakan ba tabari nazeer ya dinga yi musu hoto itada Zainab.Sai 10:00pm suka gama shagalin su, sannan aka kawo su gida nazeer ya wuce gun Shaheed.
Tana zaune taji saƙon Shaheed ya shigo, saida ta duba sannan tayi tsaki ta taɓa baki, dan tunda aka fara sha'anin baya kiranta saidai message.
Kashe gari da sassafe Mamee ta kama shi da faɗa "shikenan saboda an kai kaya bazaka je kaji abinda take bukata ba a ƙara mata ba, kokuma akwai abinda bai mata ba, to wlhy katashi yanzu kaje ka dawo ka faɗa min yadda kayi da ita.."
"Mamee da akwai abinda bai mata ina ganin dazata faɗamin..."
"Idan kaje kenan zata fada maka, amma tunda bakaje ba ai babu wanda zata fadawa.."
"Shikenan Mamee zanje.."
"Yanzu nakeso katashi kaje.."Badan yaso ya tashi ya fice dan shi so yayi sai bayan an daura auran sannan ya bari su haɗu..
Sau biyu yana kiran wayar ta bata ɗaga ba, daman yasan bazata daga ba, wayar Zainab ya kira ya sanar mata yana sitroom.
Khadija na ganin kiransa taki dagawa,. Kuma tanaji yakira wayar Zainab suka gama wayar ta waigo wajanta.
"Khadija kije Shaheed Yana jiranki..""Malama kima kirashi kuma ce ya tafi dan babu inda zani.."
"Shikenan bari naje na fadawa uncle.."
Da sauri ta dakatar da ita. "to zanje dan Allah karki fadawa uncle din"Tabe baki Zainab tayi tace "a toh dai"
Bata kula taba ta fice ko kwalliya batayi ba saima tsaki datayi tana hararan Zainab ɗin.Tunda ta shiga yake kallanta, fuska ta haɗe babu alamar murmushi.
Harta zauna bai daina kallonta ba,.
Gajiya tayi da kallan dayake mata, tayi tsaki can ƙasa yadda bazai jiba, sannan ta gaida shi kasa kasa.
Murmushi yayi, yadda take wani haɗe rai kamar taga dodo.
Shirun ya kawar yana tambayar ta. Abinda take bukata.
"Babu Abinda nake bukata"
"Ok, dama Mamee ce tace na tambayeki idan akwai abinda kike bukata"
Har ranta bataji daɗin abinda yace ba.
Ranta a bace tace. "aida baka wahalar da kanka ba, dan bana bukatar komai"
Tabe baki yayi "shikenan.."
Yana fadar haka ya tashi ya fice.
Kamar baƙin ciki ya kasheta haka taji.
Babu laka a jikinta ta nufi dakinsu.Shaheed kuwa murna fal cikinsa ya tafi gida koba komai dai yau tayi masa magana. Yasan dole watarana zata manta da abinda ya faru a baya......