*🤱 MAHAIFIYATA🤱*
_writing by_📚✍
*🌹 Ameena first lady🌹*
_page 2⃣3⃣ to 2⃣4⃣_
Tunda suka bar wajan Zainab takewa khadija mitar abinda tayiwa su Shaheed khadija kuwa tayi shiru da ita bata kulata ba,. Ganin khadija tayi shiru ne yakara tunzura Zainab.
Zainab ce ta tsaya ta kalli khadija.
"Wlhy na kusa yawo dake a makarantar nan idan mun fita mayi zumuncin haka kawai bazaki jamin kora Ina cikin jin dadin karatu na ba"
"Matsoraciya kawai, waya fada Miki za'a koreki, idan korar ce ai bake za'a koraba ni za'a kora naga ko"
"Kuma karyar banza ce shi wanene dazaisa a koreni a makarantar nan, kawai ya fada ne Dan na tsorata dashi"
Tsaki Zainab tayi sannan tace.
"Da alamar bakisan wanene Alhaji attahir Hashim a kasar nan ba"
"Nasan shi mana inajinsa a gidajan yada labarai da kuma jaridu mana"
Zainab tace "to Shaheed dansa ne"
Ba karamin razana khadija tayi ba har cikinta saida ya kada tsabar tsorata..
Zainab taci gabada cewa. "Kuma Yana San Shaheed fiye da tunanin ki hakan yasa Shaheed yake abinda yaga dama"
Lallai idan kuwa hakane ta debo ruwan dafa kanta,. Amma bazata taba bari hakan yayi tasirin dazai nunawa Shaheed tana tsoran shiba..
"Kwarai nayi mamakin kasancewar Shaheed da ga Alhj attahir Hashim,. Saidai wlhy hakan bazaisa na raga Masa ba ko kadan"
"To ai saikije kiyi tayi watarana ke zakiji kunya, Dan wlhy wulancin Shaheed ya wuce duk inda kike tunani"
"Naji Zainab mubar maganar haka muje mu huta Dan nagaji"
"Kyaji dashi nidai ba ruwana atoh na fada Miki kar fadanku ya shafeni"
Dariya kawai khadija tayi tasan Zainab da shegen tsoron tsiya.
Shaheed Yana gama shan coffee yafara danna computer sa,.
Mintina kadan saiga Meera ta dawo.Mamee ce tace "yauwa Meera mazaki shirya ki raka yayanki hospital"
Meera ta karaso gun yayan nata "Yaya Shaheed meyake damunka"
"Fever ne Amma naji sauki ai Mamee ce taki yarda"
"Mamee aida baku jira dawowa ta ba, da kawai kin Kira family doctor ya dubashi a gida"
"A'a Meera gyara kuje private hospital acan za'a fi dubashi sosai, zazzabin nasa ba kadan bane "
"To Mamee bari nayi wanka saimuje"
15minutes Meera tagama shirinta tsaff, ta fito.
"Yaya Shaheed nagama shiryawa"
"To jirani a motar yanzu zan fito"
Mintina2 Shaheed ya fito Yana gyara agogon hannun shi kirar Rolex mai shegen kyau da tsada.
Sunje hospital an rubuta Masa magunguna, zazzabi ne kawai ba abinda yake damunshi bayan wannan.
Mamee taji dadi sosai ganin Shaheed kafin dare harya warware, hakan yasa tace kar Wanda ya fadawa Daddy idan ya dawo Dan dukda Shaheed ya warware sai ya tashi hankalin sa sosai fiyeda na kowa ma..
Yau Shaheed bai kwanta da wuri ba, sai 10:45 sannan ya samu ya kwanta.
Yana kwanciya yafara tuna kalaman da khadija ta fada Masa masu zafi,. Harya tuna kalmar data fadawa Usman.
Lallaima wannan yarinyar taciwa Usman zarafi da yawa.Baisan lokacin da murmushi ya subuce Masa, lallai zan nuna mata waye Shaheed dama na kyaleta ne saboda karta taramin jama'a a wajan, Amma Allah yakaimu gobe zata gane kuranta.
Yana zancan zuci bacci ya samu damar awon gaba dashi...
Khadija kuwa tunda aka tashi suka rabuda Zainab ta wuce gidan aunty rahma tunda dama yanzu acan take zaune Kamar yadda abbanta yace ta zauna karta koma gida yanzu..
Tunda ta dawo tashiga dakinta tana tunanin yadda haduwar ta da Shaheed zata kasance gobe, kwarai ta tsorata dajin waye mahaifin Shaheed kuma tunda ya furta zaisa a koreta kwarai zai iya din.
Saidai bazata bari ya wulakanta ta a gaban jama'a ba saita rama duk abinda yayi mata..Bata ankara ba taji Kiran sallar magrib, bayan ta idar ta nufi palour..
Aunty rahma na zaune akan kujera tana kallon MBC Bollywood, khadija ta zauna kusada ita,." Aunty rahma ya gida" "Khadija sai yanzu kika fito, lafiyarki kuwa yau".
"Kalau nake aunty"Suna cikin hira uncle Abdulmutallib ya dawo.
"my daughter da aunty nata ba Wanda zaimin oyoyo"Dariya sukayi su duka sannan Aunty rahma ta tashi suka wuce daki sukabar khadija..
Saida sukayi dinner sannan khadija tayi dakinta ta kwanta..
Da sassafe Shaheed yaje part din su Mamee, Yana shiga yaga Mamee a palour.
"Shaheed ya jikin naka"
"Na warke"
"Mamee Ina breakfast Dina""Yau kuma da wuri zakayi breakfast din, ko wani wuri zakaje"
"Eh zanje school ne"
"To jeka gashi can a dining, Amma saika jira daddyn ka ya fito ku gaisa Dan tun jiya yake San ganinka"Ko rufe baki batayi ba daddy ya sauko daga upstairs
"Good morning Dad"
"Morning too my son""Mamee tace kanasan ganina"
"Of course saboda inasan ganin lafiyarka ne"
Mamee tace "to ai gashi ka ganshi, yanzu ma breakfast zaiyi ya wuce school"
Da mamaki daddy ya kalle shi "yaushe ka fara zuwa school on time my son"
Murmushi kawai yayi ya nufi dinning table.
Tareda Daddy sukayi breakfast din suna gamawa ya fice ya hau motar sa ya wuce school..Khadija saida tagama breakfast ta Kira abbanta ta gaida shi sannan ta wuce gidan su Zainab daga can suka karasa school...