part 6

202 11 0
                                    

*🤱 MAHAIFIYATA🤱*
          
       _by_✍✍✍

*🌹 Ameena first lady🌹*

_page9⃣ to 🔟_

......part dinsa ya nufa kai tsaye.

Mamee kam mamaki ne ya kamata dan tasan ba karamin abu bane kesa Shaheed irin wannan fushin.
Da daddare suna dinner kamar kullum  daddy ne ya kalli Mamee "Ina Shaheed fa naga duk mun hallara Amma banda shi" Mamee ce ta aje spoon dinta "wallahi nima dai bansan abinda akayi Masa ba ya shigo ranshi a bace" da sauri daddy yace "Amma meyasa baki tambaye Shiba " "na tambaye shi yace min bakomai"  daddy ne ya kalli wata yar budurwa dake gefensa wacce tunda suka fara maganar batace uffan ba "Meera jeki taho da yayanki  kice Masa jiran shi mukeyi tun dazu".     "To Daddy" ta tashi ta fita daga part din.

A kwance ta same shi idon shi na kallon sama alamun tunani yake. "Yaya Shaheed kazo inji daddy zamuyi dinner"

" Nace na koshi ko ana dole ne"    marairaice murya tayi kamar zatayi kuka " plss Yaya Shaheed kasan bazamu iya cin komai batareda Kai ba kodan haka yakamata kazo muje kaci pls" tunda ta fara maganar yake sauraran ta harta gama.
Tashi yayi yace "muje to"
Tare suka fita tana taimasa surutu, murmushi kawai yayi Dan yasan tanayi ne Dan ya saki ransa shiyasa shima ya murmusa mata Dan hankalin ta ya kwanta.

A tare suka shiga har wajan dining table din dayake shake da kayan ci kamar na mutun 30.

Saida suka gama dinner sannan daddy yayi gyaran murya "Shaheed lpy Mameen ka tacemin ka shigo ranka a bace?"

"Bakomai daddy".    "A a Shaheed akwai wani abu, zaman kanon ne bakaso? Ko kuma school dince bakaso"? Daddy ne ya jero Masa wadannan tambayoyi.

Mamee ce ta katse daddy "haba abban Shaheed wanne irin kuma bayasan zaman kano bayan ta dalilin sa muka dawo kanon" "aikuma bai isa yace bayasan zaman kano ba wallahi" saida tayi shiru sannnan daddy yace " tsakanin da da uba ake magana maman Shaheed saboda haka ke yar kallo ce" daddy ya mayar da kallon sa kan Shaheed "Ina jinka Shaheed fadamin meya faru"..
"Bakomai daddy kawai nagaji da zaman kanon ne"
"Bakasan zaman kano to ina kakeso mu koma?"
Da sauri yace "a'a daddy bawai Inaso mubar kano bane a'a sonake saina gama school tukun zan bar kasar gaba daya"

"Ok shikenan, amma idan kanason zaman kano toka daina bacin rai Dan bazamu juri ganin mood dinka haka ba"

"To Daddy"
Daga haka yayi musu saida safe ya wuce part dinsa...

Koda yakoma part dinsa bayan ya kwanta tunani yake a zuciyar sa tayaya ma zaice bayasan zaman kano bayan ba dauki mataki akan waccan villager din ba. Ina bazai yiyuba dole saiya dau mataki akanta.....

_Wanene Shaheed_

Alhaji attahir Hashim shine  mahaifin Shaheed haifaffan garin bauchi ne kuma asalin bafulatanin bauchi. Allah ne ya daukaka iyayenshi da arziki.hakan yasa suka turashi _university of Liverpool_ inda ya karanci legal and business administration..
Shekarar shi takwas, sannan ya dawi Nigeria lokacin iyayenshi suka takura da maganar yayi aure saboda yazama cikakken namiji.

A wannan shekarar suka dawo abuja shida iyayen sa. Ba jimawa kuma ya bude kamfanin motoci, lokaci guda arzikin sa ya habaka inada har kasashen waje harkallar kasuwancin sa ya daukaka..

Warana Yana office Yana cike wasu takardu, security ne ya shigo yace "sir kanada visitors a waje".  Alhaji attahir yace  "yau nagama ganin baki su bari sai gobe schedule din yau ya kare tashi zanyi"   "ok sir " haryayi hanyar fita saikuma alhj attahir yace "barsu su shigo kawai". "ok sir"
1minute yaji anyi nocking "yes come in"   mutum biyu ne wani dattijo fari tass tareda wata matashiyar budurwa kana ganin su kasan ba asalin hausawa bane..

Saida ya gama cike files din sannan ya dago.. karaff idanuwan shi akan wannan matashiyar budurwar da shekarunta bazasu wuce 23 ba...
Sungama fadar bukatansu ta sunaso a sama musu gurbin aiki a wannan kamfanin idan zasu samu.
Tsaf yagama sauraran su sannan ya karbi takardun hannunta ya duba...

Da dabara ya tambayi address dinsu, sannan yace su jira zai duba nanda wani lokaci sa dawo.

.....Baisha wahalar nemo gidan ba,Saidai tun daga kofar gidan ya gane lallai suna bukatar taimako, sun karbe shi hannu biyu2.

A ranar yaji labarinsu su larabawan sudan ne sakamakon boom din da aka saki ne yaja musu dawowa Nigeria basu da kowa ga babu da suke fama dashi sakamakon rashin tahowa da kayan su day basuyi ba,
Tundaga wannan ranar alhj attahir shiyake musu komai, ba dadewa ya nuna Yana San fateema yadda yadda suna kiranta,, ba bata lokaci duka bangare biyun suka yadda..
Ba dade ba akayi auran shekarar su 2 da auran suka haifin dansu me kama da larabawa sakk, mutane suka dinga yaba kyan yaron ranar suna ta zagayo yaro yaci suna Abdulmalik suna kiranshi da Shaheed..

Soyayyar duniyar nan sun daurawa Shaheed, hakan yasa Shaheed ya tashi a sangarce babu abinda yake tabashi tun Yana yaro bayajin magana,Yana 11yrs suka kara haihuwar ya mace kyakkyawa ana sama suna Rukayya suna ce mata Meera.
Duk da hk soyayyar su tafi akan Shaheed haka shida Meera suka taso cikin kaunar juna suda iyayen nasu..

Share nd comments pls

08112138112🤝🤝🤝🤝🤝

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now