part 30

152 11 0
                                    

🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*

'''{United we stand succeed: Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

*_🤱 MAHAIFIYATA 🤱_*

_By_📚✍

*_🌹 Ameena first lady🌹_*

_page 5⃣7⃣ to 5⃣8⃣_

.... Shiru Abdulmutallib yayi sannan ya shiga palour Yana fada musu yadda akayi.

"Zama bai kama mu ba, mutashi mubishi asibitin mu duka"

Mama ce taje ta sanar da A'i da Zainab...

Zainab ana fada ta yayibi hijjabinta ta fice daga dakin.

Abba kuma asibitin ya nufa, Yana shiga ya Kira inspector.
"Gani na shigo"

Inspector ya shiga dashi bangaren da aka nufa da khadijan...

Gadan gadan Abba ya nufi dakin da aka kwantar da khadija, inspector ya hanashi shiga.

"Calm down my friend, baza'a barka ka shiga ba sai sungama aikin su tukun"

Jagwab Abba ya zauna kan kujerar dake gefensa..

Kusan 2hours doctors suna suna zirga zirga akan khadija, Abba kan ko magana bayayi Dan yadda hankalin sa ya tashi jiyake bazai iyaba...

"Inspector a wanne hali akaga khadija, kuma a Ina"...?

"Eh to tun jiya muke bincike daga karshe dabarar bin diddigin layinta yazo Mana, a nan muka gano inda take muka je,. Lokacin da mukaje gaskiya bata ko numfashi kuma munga jini a jikinta hakan yasa na hana kowa taba ta nace muzo asibiti muji komai dakuma binciken su likitocin abinda zasuce"

Hawaye masu zafine suka zubo daga idan Abba jin ance ko numfashi batayi...

Fitowar babban doctor din tayi dai dai da zuwan su uncle Abdulmutallib, gaba daya sukayi kansa da tambayar ya khadijan....

Gumin dake fuskar shi ya goge sannan yace..
"Ku same ni a office". ya nufi office din nashi.

Abba da uncle Abdulmutallib ne sukabi bayan shi suka bar su mama da Aunty Rahma..

Saida doctor yagama nazarin sa sannan ya cire farin Glass fuskar shi..

"Alhaji meyasa kuka aurar da yarku gun Wanda bashida tausayi, shiyasa akeso ayi bincike kafin aure ta yiyu dama can Dan iska ne yaran....?

Kasa daure fadan da doctor yake yi musu sukayi, uncle Abdulmutallib ne ya kasa jurewa yace.
"Bamu gane me kake cewa ba doctor, kayi Mana bayani yadda zamu fahimta Mana"..

"Ok na fahimci bakusan abinda yasamu yarku ba, I'm sorry to say anyi raping din yarinyar ku ta hanyar yi mata   allurar gneiss...?

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" shine abinda suka furta su duka sannan hawaye ya wanke musu fuska...

**** ***** ***** *****

Shaheed hankalin sa yaki kwanciya ganin ya Kira khadija wayar a kashe,. Yakira Zainab ma ba'a daga Kiran ba.

"Meya samu khadija..? "Kodai ba lafiya ne.."?

Ganin bashida amsar tambayar shi ya nufi part din su Mamee...

A hospital kuwa Zainab najin labari ta sume tsabar kaduwa,.  Gado aka bata aka bar Mommy ita kadai a wajanta Dan Abba ya hanata zuwa wajan...

"Doctor zamu iya shiga muganta". "eh zaku iya shiga Saidai idan ta farka kar abari tayi motsi sosai sannna a kirani akwai magungunan daza'a bata"

Ko amsawa basuyi ba suka fice.

A Mike take sambal a gadan hannunta dauke da robar karin jini harta Dan rame a fuska, kuka A'i take wiwi yadda taga jikar tata, Abba kuwa kasa kallon khadija yayi yanaji zuciyar shi na zafi.
"Allah ya isa duk Wanda yasaki a wannan yanayin, an bata Mana suna an cuceki an cucu zuriyarmu baki daya...". A'i ta fada tana kuka.

Abu kamar wasa magana mutane sun fara sani sakamakon shigowar yansanda zancan tuni maganar ta fasu musamman mutane da dama sun San Alhaji Ahmad mahaifin khadija...

.... Shaheed Yana shiga part dinsu Mamee yaga Daddy zai fita...
"Shaheed ka fito kenan"
"Eh Daddy"
"To shikenan ka jirani na dawo akwai maganar da nakeso nayi dakai"
"To Daddy, Ina zakaje haka"...?

"Zanje dubiya ne yar abokina ce Alhj Ahmad aka kwantar a asibiti, wasu bata gari sunyi mata fyade"

Damm gaban Shaheed ya fadi sai tsintar kansa yayi da tambayar.  "Ya sunan ta"..? 

"Khadij....."
Tun kafin ya karasa Shaheed ya maimaita sunan a firgice Yana mikewa kamar an tsokareshi.
"Khadija....!  Ya maimaita a tsorace.
"Lafiya kuwa Shaheed naji ka tambaya kamar ka Santa"

Bai bashi amsa ba sai zama yayi jagwab kanshi na Sara mai..
Daddy bai kulada yanayin da Shaheed ya shiga ba saima hanyar fita yayi Yana cewa.  "Karkaje ko'ina fa kajirani"

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now