part 4

233 14 0
                                    

*🤱 MAHAIFIYATA🤱*

            _writing by_✍✍✍

*🌹Ameena first lady🌹*

_page 7⃣ to 8⃣_

Khadija kuwa ko a jikinta tana gamawa ta wurgar da jarkar sannan ta wuce zata tafi.

Da sauri yabi bayanta Yana zuwa ya tari gabanta, tayi saurin tsayawa ta dago kanta...
Wani wulakantaccen kallo yake mata from up to down idan shi ya kankance tsabar bacin rai, yama rasa ta ina zai fara.
Can dai yayi wani malalacin murmushi sannan yace "zaki biya ne" yayi gaba yabarta a nan.

Rike hannunta taji anyi da zafi ta waiga taga Zainab ce.
         "Zomu tafi khadija" haka Zainab tace kawai taja hannunta suka tafi.
Mutanen da suka ga abinda ya faru sun tausayawa Khadija bama da suka ji yace zata biya sun San halinsa sarai abin bazai dadi ba muddin suka sake haduwa, wasu kuma na cewa zamuga drama gobe...

_Nidai nace to koma dai menene gobe zanzo B.U.K naga karshen episode din😂😂😂_

Tunda khadija da Zainab suka fita ba Wanda yayi magana musamman khadija da haryanzu ranta a bace yake.
Zainab ce tayi magana"khadija ai yanzu gashi dole ki bini ki kwana tunda ga yamma  tayi"
"Eh dolena na kwana a wajan ki Amma ban taho da kayana ba"
"Kinji yar rainin hankali kayan na gidan mu kin daukesu ne"inji Zainab.
"Ohh wallahi na manta da kayana a gidanku shiyasa".
Har suka karasa gida ba Wanda ya kara magana...
Suna shiga ciki  suka tarar da mama a palour,da murnar ta ta taresu "twins Dina yau kuma tare kuka taho ba sammaci"
Zainab tace"wlh mama dakyar ta biyoni" "mama karya takeyi da kaina nace zanzo yau na kwanan Miki" khadija ta fada tana hararan Zainab.
"Aikuwa kin kyauta yata" cewar mama

Sallar magrib sukayi sannan suka zauna zaman cin abinci anata hira sannan suka Dora da sallar Isha, Zainab ce taketa faman shagwaba ita a lallai saita fita siyan kayan make-up a daran,mama kuma sai wani lallashinta takeyi Kamar wata karamar yarinya.

Khadija batasan lokacin da hawaye suka zubo mata ba itadai rayuwar nan tana burgeta taga uwa da yarta suna  rayuwa  Kamar wasu kawaye.
Daki ta nufa ta kwanta hawaye na zubo mata shin Wai yaushe ne mahaifiyar ta zata Sota ta damu da damuwar ta Kamar yadda kowacce uwa ta damu da yarta, kuka takeyi sosai harda shashsheka.
Kamar Zainab tasan haka ta nufi dakin a kwance ta samu khadija tana faman kuka Kamar Allah ya aikota, Nasiha ta farayi mata,

  "Haba khadija har yaushe ne zaki daina kukan nan kullum abu daya saikace kanki aka fara nuna wannan halin ko inkula da mahaifiyarta ki take nuna Miki" khadija ce ta tashi sannan ta kalli Zainab " Zainab fadamin bayan ni wa kika sani a cikin wannan halin danake ciki, abinda yafi damuna shine nakasa samun kwakwaran hujjan da yasa Mommy takemin haka, nabi duk wata hanya da zanbi nakasa samun amsa kuma duk wanda nasan zan kai karar ta yai mata magana naje Amma shiru haryanzu kowa kalma daya yake fadamin nayi hakuri watarana zata gyara,shin wannan wacce irin Rana ce haka da haryanzu  19yrs batazoba"ta sake fashewa da wani sabon kukan zuciyar ta na mata zafi.
Hankalin Zainab ya tashi tace "kiyi hakuri khadija akwai wannan ranar tana nan zuwa,ranar da zaki kasance da mahaifiyarki Kamar babu abinda ya faru tsakaninku".      "Ina jiran  wannan ranar Zainab duk da bansan a wanne irin yanayi zata zomin ba,shin ta farin ciki ce kota bakin ciki"...
" Ta farin ciki ce insha Allahu khadija ki share hawayen ki Dan Allah"

Khadija share hawayen ta tayi Amma duk da haka zuciyar ta Kamar zata kone wajan zafi.
Zainab ce ta kwanata sannan ta kalli khadija," yakamata ki kwanta kuma ki rage tunani plss" kwanciya itama khadijan tayi Amma tasan bacci bazai dauketa da wuri ba kawai takwanta ne Dan kar aminiyar tata ta fahimci bata hakura ba, sai can cikin dare sannan khadija ta tashi tashiga bathroom tayi alwala ta fito tada sallah domin ta fadawa mai duka sarki Allah bukatun ta.

Da safe Zainab ta tasheta "ki tashi karmu makara"
Khadija tace "niban gaji da baccin ba ki kyaleni"

Zainab ta tsaya sororo tana kallan khadija " ikon Allah bangane baki gaji da baccin ba 7:00 fa yanzu sai yaushe zaki tashi to"?
Khadija da bacci baigama sakinta ba tace" yau bazani ba, gida zan koma"
      Zama Zainab tayi a gefen gado "me zakiyi a gida kuma"?
Tashi Khadija tayi "zanje na shirya na tafi can kauyen su mommy na fadawa mahaifin mommy halin da nake ciki kila ta saurare shi idan ya mata magana" nagaji da zama a wannan yanayin haka.
Cikin tausayawa aminiyar tata tace "to sai yaushe zaki dawo to"?

"3days zanyi,  sai Sunday zan dawo"

Haka Zainab ta shirya ta tafi school tabar khadija, itama khadijan bayan ta shirya tayi breakfast tayiwa mama sallama bayan maman tayi mata Nasiha sosai kan tayi hkr komai zai wuce..
Gida taje ta shirya ta dauki komai ta rufe dakinta da nufi palour, acan ta samu mommy tana breakfast lokacin.
Karasawa tayi ta tsugunna "barka da safiya Mommy, bazan gaji wajan baki hakuri ba har sai ranar da kika yafemin laifin danayi Miki kika daukeni a matsayin yar da kika haifa da kanki". Nasan babu uwar da zata haifi danta kuma ta tsaneshi ba, Nima nasan da laifin Dana aikata har kika kasa yafemin Amma Ina baki hakuri Allah ya huci zuciyar ki, nazo tambayar izinin ki zanje kauye gun kaka" haka ta tashi ta fita idanta na zubda hawayen bakin ciki.....

         *************

Yanayin driving dinsa kadai ya isa mutum ya gane me motar ba lafiya yake wannan sharara gudun ba , Usman dake gefe ne ya muskuta "haba Shaheed idan ranka ya baci ka dinga control din kanka kadaina barin shedan na shiga zuciyar ka Yana dada raya maka wasu abubuwan kwarai yarinyar tayi kuskure Amma yakamata kayi hakuri ka manta da batun abinda ya faru tun dazu... Da sauri  nazeer yace "tayi kuskure kam Amma mune masu laifin tunda mune mukayi mata laifi ba itace tayi mana b.....
Wawan burkin da Shaheed ya takane sukai gaba suka dawo baya shine ya katse ragowar maganar nazeer.

"Fitar min a mota" shine abinda Shaheed ya iya fada
"Bangane abin da kake nufi ba" nazeer ya fada
"I Said get out from my car" ya fada da tsawa tsawa.

Yanayin da yaga Shaheed din ne ya bashi  tsoro hakan yasa ya bude murfin motar yace "ok akan na fadi gaskiya kake fadamin na fitar maka daga mota ko ba komai" ya fice batared bata lokaci ba, Dan tunda yaga idon Shaheed yayi ja alamun ransa yakai kololuwar baci yasan komai zai iya faruwa idan bai fita ba....
 

A haka ya sauke Usman ya cigaba da sharara uban gudu Kamar Wanda ake jira jirgin su zai tashi.
Allah ne ya Kai Shaheed gida lafiya Dan a yadda yake wannan gudun saika rantse tashi sama zaiyi..

A wani Wawakeken gate ne black colour naga yayi Horn. Ana bude gate din ya shiga da gudu yayi parking ko takan mai gadi baibi ba dayake tambayar ko lafiya.
 
Babban palourn gidan ya nufa, Yana shiga ya kalli wata yar dattijuwa dake goge a palourn, kallon ta kawai yayi Yana hucu tayi saurin nufar wani katon Fringe da yafi ragowar biyun dake palourn girma, ruwa ta dauko mai sanyi ta bashi ya balle murfin ko takan cup din baibi ba.
Saida yafi rabi sannan ya ajiye robar ruwan.
2minute tsakani ya tashi zai wuce part dinsa, karar saukowa daga saman bene shiya sa ya tsaya.
Wata Farar mace kyakkyawa sosai nagani tana saukowa sai murmushi takeyi, dattijuwa ce Amma tsabar kudi sunsa bazaka iya tantance shekarunta ba.

"My son yau kadawo da wuri kodai ba school din kaje ba" shiru yayi hakan yasa ta karaso wajan sa, "lafiya na ganka haka waya tabaka haka har ni ka kiyiwa magana "  "ba kowa Mamee" yace Yana nufar hanyar fita daga palourn "ok come and eat naga tun safe bakaci komaiba"

Ko waigowa baiyi ba yace "no need na koshi" yasa Kai ya fice......

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now