part 15

157 12 0
                                    

🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*

'''{United we stand succeed;Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

Dedicated to my sweet brother
*Shafi'u Musa. (Shafam)*🌹🌹

       *🤱 MAHAIFIYATA🤱*

    _Story and writing by_📚✍

*🌹Ameena first lady🌹*

#ameenafirstlady@wattpad

_page 2⃣7⃣ to 2⃣8⃣_

Daddy Yana zama ya dauki wayar Shaheed ya Kira Usman da Nazeer akan yanasan ganin su.

Khadija gadan su Zainab tafara zuwa, ta gaida mama a palour ta wuce dakin Zainab.

A zaune taga Zainab tana duba wani novel.    "Kedai Zainab bakya gajiya da karatun novel"

"Eh Ina ruwanki sarkin tsokanar fada"

" baruwana Amma meyasa kika baroni a school kika taho"

Wani kallo Zainab tayi mata sannan tace "me kike nufi, kina so kacemin Dana tsayaki an ganmu tare nima a koreni a makarantar kenan kome"?

"Bahaka nake nufi ba Amma dai koma menene aida kin jirani ko"
"To bazan jira din ba".  Hakuri khadija ta bata tana kunshe dariyar da taci karfinta Dan tasan tsoro ne yasa Zainab fadar maganganu.

A haka Mama ta samesu tace. "sarakan fada idan kuma mutun ya shiga yaji kunya, saiku fito kuyi lunch"

A dining ma suna cin abinci suna tsokanar juna mama dai bata kulasu ba Dan tasan kunya zasu bata idan tasaka baki..

Sai yamma sannan khadija ta wuce gida kar uncle Abdul yayi mata fada.

Sai dare sannan su nazeer sukazo wajan daddy lokacin Yana palour da jarida a hannun shi, bayan sun gaida shi yake tambayar su abinda akayiwa Shaheed tunda yaki fada Masa.

Nazeer ne yabashi labarin abinda ya faru tundaga har zuwa yau sannan ya Dora da cewa "kuma daddy ba laifin yarinyar bane laifin Shaheed ne daya kasa kyale yarinyar a matsayin ta na mace bai kamata ya biye mata ba"

Jinjina Kai daddy yayi sannan yace.  "Eh to yarinyar batada laifi laifin Shaheed ne, shiyasa ma zan kyale ita yarinyar Amma da har iyayenta bazan kyale ba Saidai yanzu naji bata laifi na kyaleta dalilin haka"

"Saikuje ka lallashi Shaheed din Dan ransa ya baci sosai"

A part dinsa suka same shi Yana bacci jin shigowar su ne ya tasheshi.
Nazeer tafiya yayi gida yabarsu Dan yasan tunda Shaheed yaki hakura karshe fada zasuyi shiyasa kawai yabar gidan gabadaya.

Tunda khadija ta koma gida bata sake tunanin wani Shaheed ba. Da dare ma haka tayi waya da abbanta sannan ta kwanta hankalin ta kwance zuciyarta wasai ba damuwa.

Shaheed kuwa a daran yaci gabada zuwa club, Usman ne yajashi akan cewar idan yaje hankalin sa zai kwanta,.  Bai dawo gida ba sai 12:00am   lokacin su daddy sun dade da bacci.

Tunda wanann lokacin Shaheed yaci gabada zuwa club da kula yammatan banza duk Dan ya manta da abinda khadija tayi masa, Amma a banza saboda Koda yaushe saiya tuna wani lokacin ransa ya baci wani lokacin kuma ya cire abin a ransa, Amma haryanzu bai hakura ba yana nan Yana shirin ramuwar gayya,kuma bai fasa zuwa makaranta ba....

Khadija ma anata bangaran hakan take Dan tamanta da batun wani Shaheed kuma tana zuwa makaranta kullum, Zainab ma tagama yajin aiki taci gabada zuwa makaranta ita khadija....

Yauma Kamar kullum Shaheed ya dawo daga club 11:39 na dare, harzai wuce part dinsa Mamee ta fito ta tareshi.

"Shaheed daga Ina kake yanzu a wanann daran"

"Daga wajan Usman"

"Karka rainamin hankali wajan Usman dinne sai yanzu ka dawo"

"Eh Mamee bansan dare yayi haka b...

"Shut up stupid" ta katse shi tun kafin ya karasa.
"Yau kusan 2weeks kenan Ina lura dakai kullum idan ka fita da yamma sai cikin dare kake dawowa,. Shaheed bazakayi wa kanka fada ba, shekarar nawa yanzu Amma ace kullum sai anyi maka fada a gaban kanwar ka"

"Ko kaga ita tana wannan shashancin ne"?

"To wlhy ka saurareni da kyau kaji, daga yau idan ka kara fita ka dawo irin wannan lokacin Saidai ka nemi wani wajan ka kwana, kuma saina saba maka fiye da yadda baka zato, idiot kawai, wuce kabani waje" ta fada da tsawa sosai..
Part dinsa ya nufa yaje ya kwanta yana tunanin maganganun Mamee  kwarai gaskiya ta fada, to waima meyasa yaci gabada zuwa club aida yadaina zuwa meya jawo Masa komawa,.  "Wannan yarinyar ce tajamin komawa" haka ya fada a fili tareda furzar da wata iska daga bakin shi.

"Lallai zanyi maganin yarinyar nan to Amma tayaya"?ya tambayi kansa.

"Idan nabita ta karfi zamu zata cigabada bani kunya sannan ajina zai zube, idan kuma nabita ta lalama mutane zasuga naji tsoro Amma zan rama abinda tayimin ta lalama"  a zuciyar shi yayita sakawa Yana kwancewa a haka harya samu mafita, idan hagu taki sai'a koma dama haka zanyi.

Sha kadai ya samu mafita kuma a daran ya Kira Usman abokin yinsa ya sanar dashi abinda ya yanke.

Usman ya goyi baya akan gyara ya hakura dama tunda yarinyar itama ba zata hakura ba karta zubar musu da aji gyara su hakuran kawai yafi.

Kashe gari su duga sun shiga school yauma suna kasan bishiyar a zaune itada Zainab Kamar kullum.

"Zainab lecture din yau tayi dadi sosai"

"Nima naji dadinta wlhy Saidai mutumin bashida mutumci"

Dariya khadija tayi sannan tace "kedai kowama saikice bashida mutumci"

"To ai gaskiya na fada kema kinsan halin sa ai"

"Nasani Amma baki fahimce shibane wlhy"
"Na fahimce shi yadda yakamata, kedama ai haka kike idan aka fada Miki magana saikin mayar da ita wata hanyar Dole"
Khadija ce tace "to naji bashida mutumci yi hakuri shikenan ko"

"Na hakura"

Haka suka cigaba da hira, a cikin hirar tasune khadija take fadawa Zainab zata koma gida.

"Abba ne yace ki koma"?
"A'a kawai naga yakamata na koma ne, nesa danayi da Mommy bazaisa mu shiryaba Saidai ma ya kuma raba tsakanin mu Amma idan na koma tana ganina watarana dole zata kulani kinsan zaman tare dole watarana tayimin magana"

"Hakane kin kawo shawara mai kyau, Amma yaushe zaki koma"?

"Jibi insha Allahu"
"Kafin ki koma ki fadawa Abba tunda Kinga tun farko shiya hanaki komawa"

"Eh dama yau nake shirin sanar dashi shawarar Dana yanke"

"To Allah yabada sa'a".     "Ameen"

_Dan Allah kiyimin afwa sakamakon banida lafiya ne kukajini shiru Amma yanzu na warke na dawo insha Allahu_

Nagode da addu'oin ku gareni da masu Kira da masu sakon waya wlhy naji dadi sosai Allah yabar zumunci🤝🤝🤝🤝

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now