part 23

143 7 0
                                    

🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*

'''{United we stand succeed; Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

       *🤱 MAHAIFIYATA 🤱*

_Writing by_📚✍

*🌹 Ameena first lady🌹*

Watsapp number
_08112138112_
For comments

Dedicated this page to
'''hauwa'u ibrahim. {baby}'''💝

_page 4⃣3⃣ to 4⃣4⃣_

Suna zuwa aka karbe su, saboda angane Shaheed din.

Ko tashi takasayi daga wajan tana jiran Kiran nazeer.
"A Ina za'a ajiye kayan"
Megadi ya tambaya.
"Ka barsu a palour kace mama uwani ta Kai dakina"
"To"
Haryanzu bataji Kiran nazeer ba saboda haka ta yanke shawara ta kirashi taji ko lafiy.
Bugu kusan hudu ana biyar ya daga.
"Hello nazeer meya same shi yaje gida lafiya"
Ta jero Masa tambayoyi a jere.
"Calm down khadija, an Dan samu matsala yayi accident Amma abinda sauki tun yanzu haka sunyi Masa allura hutawa yake"
Tunda yafara maganar gabanta ya fadi dama tasan za'ayi haka.
"Nazeer bani address din asibitin plss"
Address yabata tace yanzu zata zo ya jirata.
Kafin ta karaso Shaheed harya farka, nazeer yakira doctor ya sake dubata.
Ciwone a goshin sa an nade da bandage  sannan da wani yanka a tafin hannun sa shima an nade da bandage.
Nazeer yace.
"Barina Kira gida na sanar musu ko"
Da sauri Shaheed ya ce.
"A'a karka fadawa kowa"
"Meyasa"nazeer ya tambaya.
"Idan sun tambayi dalilin accident din mezan ce musu"
"To naji yanzu ina zakaje har ciwan ya warke yadda bazaka gani ba"
"Kiramin Usman yazo mutafi"
"To"
Nazeer yakira Usman ya sanar dashi har dakin da suke kwance.
Khadija tana shigowa asibitin takira layin nazeer, lokacin nazeer Yana gyarawa Shaheed pilloy.
Yasan khadija ce shiyasa yaki dagawa saida yagama ya fita.
Tare suka shigo da khadijan tana biye dashi a baya.
Shaheed Yana ganinta ya tashi ya cire drip din da ake kara masa, da sauri nazeer yayi kansa Yana fadin.
"Haba Shaheed meye haka kuma bakaga abinda kakeyi bane"
Ku sauraran shi baiyiba ya karasa cirewa ya fice daga dakin.
Khadija kuwa ganin haka ta tabbatar bakaramin fushi Shaheed yayi da itaba.
"Kiyi hakuri khadija zai sauko nasan halin Shaheed yanada saukin Kai karki damu"
"Bakomai nizan tafi nazeer" ta fada tana ficewa.
Lokacin da ta fita dai dai Shaheed ya shiga motar da Usman yazo da ita.
Gidansu Zainab ta wuce ta fada mata duk abinda ya faru..
Hakuri Zainab ta bata sannan da Dora da cewa.
"Kinga irin abinda nake fada miki ko, gashi nan tun yanzu kin fara shiga tension din"
"Zainab narasa Wanda zanso acikin su bansan..."
Zainab ta katse ta.
"Kinga karki yaudari kanki kawai Amma duk Wanda yake tareda me yasan soyayyar Shaheed ta dade a zuciyar ki saboda haka kicire batun Wai sabawa kukayi da Shaheed keba sanshi kikeba"
Shiru tayi tana tunani, gaskiya Zainab ta fada a yanzu idan akwai wani Wanda takejin shi a jinin jikinta bayan iyayenta bai wuce Shaheed ba, kenan gakan yana nufin sanshi ya dade a zuciyar ta.
A gidan su Zainab ta kwana har cikin dare tana Kiran Shaheed yaki picking karshe ma ya kashe wayar.
Khadija sarkin zuciya nan da nan taji haushi.
"Shaheed kokaine autan maza bazan sake nemanka ba har abada"
Ta fada hawaye na zubo mata.
Shaheed kuwa Yana ganin kiranta Saidai bazai iya daga Kiran ba, ji yakeyi kamar yanzu yaganta da wani.
Har safiya bai rintsa ba tunani iri iri.
Da safe Usman yace.
"Shaheed kardai kabari soyayyar yarinyar nan yashiga ranka, bayan kasan ba wannan a gabanka ba bakuma soyayya gaskiya ce takaika gareta ba" yafada Yana kallon Shaheed din.
"Nima ban saniba Usman Saidai ba'a iya zuciyata nakejin yarinyar ba har cikin jinina inajinta nakasa manta abinda idanuwan a suka ganemi Wai khadija da wani ba niba" yafada Yana dafe kanshi dayake sara Masa aduk lokacin daya tuna.
Usman ya lura da karamin so ne yashiga zuciyar Shaheed ba saboda haka yace.
"To Allah ya kyauta, Amma kayi kokarin cireta a ranka idan ka rama abinda tayi maka saika cigabada San nata".
Yatashi ya fice yabar Shaheed a dakin.
Gaba daya Shaheed yashiga cikin wani yanayi lura da hakan yasa Usman yafara saka Masa kwadayin komawa zuwa club Wai zai rage tunani.
Khadija ma hakan take har wani rama tayi takara haske kamar wacce tayi night fever.

Nazeer kuwa soyayyar su da Zainab tayi Nisa jira kawai take abbu ya dawo ta gabatar dashi a gida.

Sau biyu nazeer Yana zuwa wajan su Shaheed da daddare sai ace basa nan, zargi yafara kodai club Usman yake Jan Shaheed su tafi ne amma sai kawai ya cire abin a ransa....

Daddy yayiwa Shaheed magana ya dawo gida Amma saiyace Shiba yanzu ba tukun.
Zuwa yanzu zuciyar Shaheed ta sauko Yana tunanin Kiran khadija amma yakasa.
Message ya tura mata.
Lokacin khadija tana kwance luf a kangado sakon Shaheed yashigo.
Tayi mamaki Dan batayi tunanin zai sauko da wuri hakaba.
Saida tagama karantawa sannan takira Zainab cikin zumudi ta fada mata.
"Aidama nace Miki kiyi hakuri zai sauko ne"
Hira sukayi sannan sukayi sallama.
Shaheed kuwa har yanzu zuciyar shi tana harbawa duk sanda ya tuna ganin Salim tareda khadija.
Binkice yasa akayi sosai akan Salim ba bata lokaci yasamu information akan Salim din har inda yake aiki.
Nazeer ya nema ya raka shi har office din salim din.
Ko sallama baiyi ba ya shiga.
A tsorace Salim ya dago, yana ganin Shaheed ya shaida fuskar shi.
Wani wulakantaccen kallo Shaheed yake masa harya karaso kusada shi.
"Malam waye Kai zaka shigomin ko sallama babu"
"Ba zuwa nayi domin magana dakai ba zuwa nayi naja maka kunne karka kara shiga sabgar khadija"
Murmushi Salim yayi.
"Da alama kaima masoyin khadija ne kamar yadda nake masoyi a wajanta, kuma kowa yanada damar soyayya da khadija tunda ba auran ta kayiba"
"Ok haka zakace, to na kara ganinka tareda ita"
"Bazai yiyuba Saidai idan ita khadijan ce tace bayaso nakara kulata ma'ana bata Sona kenan"
"To shikenan zan baka mamaki"
Ya fice ya nufi office din shugaban ma'aikatar.
Tsaki Salim yayi yace "aikin banza kawai"
Karar wayar shi yaji, Yana dubawa yaga sunan ogan shi.
"Kazo Ina San ganinka"
"Ok sir".
Ya tashi ya fice.
A zaune ya samu Shaheed Yana faman huci da kumbura fuska.
Tabe yayi yaje ya zauna.
"Shaheed ne yakawo karar ka, meyasa kake shiga gonar sa"
Labarin komai Salim yabashi yadora da cewa.
"Kuma Nima Ina Santa kamar yadda yake Santa"
Wuff Shaheed ya tashi.
"Kaji ko to wlhy duk abinda ya samu kamfanin ku shiya yaja muku" ya fada Yana ficewa.
Sosai ogan salim yayi Masa fada sannan yabashi umarnin tafiya.
Ran Salim ya baci sosai. "zan nuna masa yayi kuskuran abinda yayimin........

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now