part 21

145 11 0
                                    

🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*

'''{United we stand succeed; Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

        *🤱 MAHAIFIYATA🤱*

_By_📚✍

*🌹Ameena first lady🌹*

Watsapp number
_08112138112_
For comments.

*Ina matukar jin dadin comments dinku sosai, nagode komai nayi domin kune. I love you very much*💞💕

_page 3⃣9⃣ to 4⃣0⃣_

Da sassafe suna gama shirin tafiya school khadija ta fara hada kayan ta.
"Tun yanzu naga kike hada kaya"
"Eh zan Kira Habu driver yazo nan ya dauka, nikuma daga school zan wuce"
"To ai shikenan"
Saida suka dau hanyar school sannan Shaheed ya kirata yace   "ki jira zanzo na daukeki"
"Ai mun tafi"
"Ok " yace Yana jiya kan motar.

Ba karamin sabo ne yashiga tsakanin khadija da Shaheed ba mutane har mamaki sukeyi ciki harda Mamee da Dad.
Gaba daya halayensa sun sauya baya zuwa club baya wulanci kamar yadda yakeyi a baya Wanda hakan ya faru ne duk ta dalilin khadija.
Zuwa yanzu ya fahimci dalilin dayake sanya ta tunani, Saboda haka kusan kullum saiya dauketa sunfita yawon shakatawa tun bata sakin jiki dashi harta sake dashi.
Yau sauri takeyi taje ta amso musu dinkinsu itada Zainab, Wanda Mama tayi musu.
Kiran wayar Zainab dinne ya dakatar da ita dayin shirin "Wai haryanzu baki tafi anso dinkin ba" Zainab ta fada.
"Uwar hanzari to yanzu zan tafi, kin bashi kudin ko"
"Eh nabashi"
"To yanzu zan tafi shiryawa nakeyi"
"To kardai kijira Shaheed Dan nasan halinki zaki iya cewa saikin jira yazo ya kaiki"
"Nikadai zan tafi yanzu ma"
Katse wayar tayi ta jefa a jaka ta fice.

Baba megadi ta tambaya Ina Habu driver, yace mata ya fita Amma yanzu zai dawo. Ganin bazata iya jiraba ta fita kawai ta tare me napep.

A bakin titi ta tare me napep ta hau.
Har taje ta amso dinkin ta fito zata wuce, wani matashin saurayi ne ya tare gabanta yanacewa.
"Haba princess duk rakiyar danayo Miki shine zaki wuce kibarni anan"
Kallon mamaki tayi mai tace "rakiya kuma, daga Ina"
"Tunda kika hau napep nake binki, kuma nayi mamakin da kikace baki ga lokacin danake biyoku a baya ba"
"Gaskiya ban gani, lafiya dai ko"
Ta tambaye shi.
"Eh lafiya kalau, Amma fa idan kin taimaka min"
Yanayin yadda yadda bata amsa yafara bata dariya sai wani marairaice murya yake.
Bai kyaleta ba har saida ya gabatar da kansa a wajanta kuma ba laifi yasamu karbuwa dataga yanayin nutsuwa a tareda shi, basu rabu ba saida yasan sunanta shima ya fada mata sunan shi Salim sukayi exchange din number.

Sosai khadija take nunawa Shaheed da Salim soyayya a cewar ta ita ba auran Shaheed zatayi ba daman.

Kwana biyu Shaheed baya zuwa makaranta ga nambobin sa duk a rufe, bakaramin tashin hankali khadija ta shiga ba, gabadaya hankalin ta Yana kan Shaheed.

Yau dai takasa jurewa ta Kira Zainab, ta fada mata halin da take ciki na rashin samun Shaheed ko a wayane.
"Ki kwantar da hankalinki khadija zai neme ki da zarar ya bude wayoyin sa".

Shaheed kuwa daddy ne ya takura Masa sai sun koma Spain tare yarinyar abokin shi Alhj kabeer zatayi murnar kammala karatun ta shine Alhj kabeer ya gayyato shi Spain.
Badan yasoba dole ya shirya suka tafi Amma hankalin sa yanakan khadija saboda bai mata sallama ba Saidai tai takiransa taji wayar a kashe.

Yau khadija takasa jurewa, ko Zainab bata fadawa ba ta shirya zuwa gidan su Shaheed tagani ko ba lafiya ba.

Tun daga bakin gate take mamakin irin dukiyar da aka narkawa gidan harta shiga a zuciyar ta tace "saikace baza'a mutu ba"
Gaida gateman tayi, da farko ya hanata shiga saida ya Kira Mamee tace yabarta ta shigo.

Kalle kalle ta dingayi kamar wata yar kauye harta zauna a kan kujera a tsorace.
Karar takalmi taji alamun saukowa daga uptairs Amma takasa juyawa.
Saida Mamee ta zauna suka gaisa tasa daya daga cikin masu aiki ya kawo mata kayan tabawa sannan tace.
"Amma yammata bangane kiba"
Sai yanzu ta kalli matar, "lallai ashe Shaheed a nan ya gaji kyau" ta saurin kawar da tunaninta.
"Eh Mamee ni yar makarantar su Shaheed ce kuma class dinmu daya, anbamu group assignment gobe ne kuma za'ayi submitting gashi nawa Yana wajan Shaheed,kuma kwana biyu baizo school ba"

Murmushin Mamee ya fadada tace.  "Allah sarki gashi kuma wlhy Shaheed shida daddyn sa sunje Spain yau 2days kenan kuma baibani komaiba yace wani zaizo ya amsaba"

"To Mamee bari naje, Allah ya dawo dasu lafiya"
Ameen, Amma ban tambayi sunanki ba,"
"Sunana khadija"
"To khadija kiyi hakuri ta Dalilin Shaheed kinyi asarar assignment"
"Bakomai Mamee"
Har farfajiyar gidan Mamee ta rakota sannan ta koma ciki cikeda tausayawa khadija na rashin makin assignment din datayi, Dan ita harga Allah ta dauka khadija da gaske take.
Khadija kuwa mamakin iya tsara karyar datayi take Dan batasan ta iya karya haka ba sai yau data kama dole.
"Wato Shaheed kasar ma yabari bai fadamin ba ko, zaidawo ya sameni ai"

A can Spain kuwa kwata kwata Shaheed fasahar Kiran khadija da layin shi nacan bai zomai ba.
Yanzu ma suna zaune shida yaron Alhj kabeer Bashir.
Bashir dinne yace.
"Shaheed katashi muje wajan taron nan"
"Bazan iya zuwaba kaje Kai kadai mana"
"Wai meyake damunka ne tunda kuka zo baka walwala"
"Bakomai  bashir kawai ina tunanin gida ne"
"Mtsw gida kuma, bakada contact din Mamee dinne ka kirata da layinka na nan"
Zumbur Shaheed ya tashi zaune yace
"Kumafa hakane banyi tunanin hakaba sai yanzu"
Wayar shi ya jawo yasaka layin, number Mamee yafara Kira.
Bayan sun gaisa tace.  "Kaikuma Shaheed haka akeyi saika tafi baka bawa yarinya assignment dinta ba kasa tayi asarar makin kenan".
"Assignment kuma Mamee, wacce yarinyar"
"Oho dai tazo karbar abinta baka nan"
"Mamee yasu nanta"
"Wai khadija"
Mamaki ne ya bayyana a fuskar shi wato hargida ma taje nemanshi yanzu ya tabbatar da kaunar da khadija take Masa ba kadan bace.
"Kayi shiru, alamun bakada gaskiya tunda Kai karatun bai dameka ba sai aka fada maka kowama irinka"
Sanin fadan Mamee baya karewa yasa yai saurin tsayar da ita. "barina kirata nabata hakuri"
"Atoh dai Dan baka kyauta ba kuwa"
Sallama sukayi ya katse Kiran........

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now