🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
'''{United we stand succeed; Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation
*_🤱 MAHAIFIYATA 🤱_*
_writing by_📚✍
'''Ameena Musa'''
*🌹 Ameena first lady🌹*Dedicated to my dear brother
'''Shafi'u Musa {shafam}'''💘💝_page 4⃣9⃣ to 5⃣0⃣_
Da wannan tunanin Shaheed yagama yanke shawara Saidai bai fadawa Usman ba yabar abin a ransa dai kawai.
Kusan kwana biyu kenan kullum saiyayi attempting din Kiran wayar khadija Saidai kuma Yana tunanin yadda zasuyi da khadijan Dan yasan ba karamin fushi tayi ba.
Itama khadija duk yadda taso ta cire tunanin Shaheed a zuciyar ta takasa wani lokacin har takanyi mamakin yadda takamu da San Shaheed haka.
Ga Shaheed kuwa har yanzu yakasa gaskata San khadija yakeyi, yauma kamar kullum ya dago wayar shi Yana daga kwance picture din da yayi mata a lokacin da ya fita da ita yawon shakatawa shi yake kallo, murmushi ya subuce Masa.
Zuciyar sa yake tambaya.
"Meyasa yakejin khadija har cikin kashi da jininsa, meyasa nakasa rama abinda tayi min kuma nakasa daukar mataki Wanda kome zanyi mata nasan babu abinda zai faru, meyasa na kasa mantawa da ita"
Rashin amsoshin tambayoyin sa ne yasa ya tashi ya nufi part din su Mamee..Yau kwanan su kusan shida basu nemi junansu dukda khadija tana cikin damuwa Amma hakan baisa taji zuciyarta ya sauko ba..
Yau gidansu Zainab ta tafi wuni, suna zaune da Zainab wacce take charting da Nazeer.
"Wai Dan Allah Zainab yaushe kika zama haka daga waya sai charting da saurayi"..
"Kinga ki barni nayi, shifa zan aura kuma muba irinku bane da muke fada ko yaushe ehe".
"Au hakama zaki ce ko".
"E mana idan kinji haushi ku shirya mana keda Shaheed"
Saida tagama tsokanar khadija sannan ta fuskance ta.
"Waima kina nufin da gaske har yanzu bakwa shiri da Shaheed"
"Eh haka nake nufi mana""Amma kedai khadija bakya daukan shawara, tun yaushe nace kiyi hakuri ki kyaleshi ku shirya mana keda kanki zaki gyara shi ai".
"Nifa gaskiya Shaheed na rabuda shi kenan bazan iya soyayya dashi ba Sam bazai taba canja Halin saba"Ran Zainab ne ya baci tace.
"Shikenan tunda baza'a gaya Miki gaskiya kiji ba, Amma wlhy wahalar da kanki zakiyi Dan nasan bazaki iya rabuwa da Shaheed ba kawai dai kina ja Masa aji ne"
Murmushi kawai khadija tayi bata kulata ba.Ganin bazata hakura ba yasa Zainab ta kyaleta Dan bazata shiga fadan masoya tazo taji kunya ba musamman fada irin na Shaheed da khadija.
Sati biyu kenan basa shiri basa neman juna, tun Shaheed Yana boye damuwar shi harya fito ya fadawa nazeer.
"Nazeer gaskiya yanzu na fahimci ba soyayyar wasa nakewa khadija ba, ji nakeyi kamar zuciya ta zata fito"
"Bangane me kake nufi ba"
Labarin fadan nasu Yana Shaheed kaf.
Shiru nazeer yayi, wato shiyasa khadija tayi zazzabi kuma yaga dukta rame tayi haske.
Kallon Shaheed yayi yace.
"Shiyasa duk ka rame kawani damu kanka, gaskiya kam khadija tayi fushi sosai Ina ganin ka ka hakura da ita kawai Dan jiya munyi maganar da ita Kai tsaye ta nunamin bazata hakura ba" ya fada Yana mazewa kamar bashi ba.Ganin Shaheed ya rike Kai jikin shi na rawa idanuwan shi sunyi ja, yasa nazeer saurin matsowa Yana rikeshi.
"Lafiya Shaheed" ganin maganar bazata fisheshi ba yasa ya kama Shaheed suka motar Shaheed din.Da farko yayi tunanin yakaishi gida saikuma ya fara kaishi hospital.
Kwantar da Shaheed akayi, allura bacci akayi masa, tsawon awa uku.
Doctor dinne yace suje office subar shi ya huta tukun.."Gaskiya ciwan kan nan Yana daf da haifar Masa da hawan jini Wanda muke kirada abnormally high blood pressure a turan ce". Sosai doctor yayi Masa bayani sannan ya fice ya bar nazeer da tunani barkatai.
Kiran Zainab yayi ya sanar da ita sannan yace karta fadawa khadijan tazo ita kadai.
Bata dai lokaci mai tsayiba ta karaso asibitin.
Bakaramin tausayawa Shaheed tayiba ganin yadda ya rame a fuska.
Har lokacin Shaheed bai farka ba.
"Yakamata a fadawa khadija tasan Halin dayake ciki kila ta hakura komai ya wuce".
"A'a karki fada mata tukun"Harta tafi gida bai tashiba.
Sai 9:50pm ya farka.
A hankali yakai duban shi gun nazeer,. "Nazeer Ina fatan baka fadawa Daddy da Mamee ba"
"Eh babu Wanda na fadawa, Amma Shaheed meyasa kasa kanka a damuwa nifa da wasa nake maka asali ma niban ga khadija ba Saidai nasan itama tana nan cikin irin Halin da kake ciki na damuwa dakai"
"Nazeer idan har khadija bata hakura ba to gaskiya bazan taba cire tunanin ta a Raina ba, bazan iya ba"
Baki nazeer yayita bashi harya ji zuciyar shi ta saitu sannan yace ya Kira doctor ya sallame su.Babu Wanda yasan abinda ya samu Shaheed dagashi sai nazeer dakuma Zainab.....
Tunda ya samu lafiya yaci gabada neman hanyar dazasu shirya da khadija, Saidai duk wata hanyar dazai bi khadija tabi ta tosheta.
Ko'a school baya samunta har Zainab din baya samu inda suka saba zama.Har gidansu yaje Amma taki fitowa.
Yau gidansu Zainab yaje ba bata lokaci ta fito, ganin Shaheed ne yasa ta saki murmushi.Shima murmushin yayi.
"Zainab kin buya kamar bakya garin"
"Ina nan Shaheed, ya jikin naka"
"Alhamdulillahi jiki da sauki, Saidai alfarma nazo nema""Wacce irin alfarma"
"Inaso ki hadani da khadija, duk wata hanya dazan ganta konaji muryar ta ta tosheta"
Jinjina Kai Zainab tayi kuma tayi matukar mamaki da haryanzu khadija ashe bata hakura ba, duk irin azabtuwa da San Shaheed da takeyi."Karka damu Shaheed inshallahu zan hadaku da ita"
"Yauwa kawar mu"
Daga haka suka danyi hirarsu sannan ya tafi....Lallai Shaheed an shiga yanayi🤣🤣🤣
____________________
Bangaran khadija itama tana cikin damuwa sosai musamman da yau kwana biyu bata hadu da Zainab ba.
Hawaye ne suka zubo mata meyasa duk abinda take so yake wahalar da itane, tunawa tayi da yadda take da mahaifiyarta, tashi tayi ta nufi palour ilai kuwa anan ta samu Mommy tana duba wani littafi..
Har kasa ta tsugunna kuma haryanzu hawayen da takeyi bai daina zubaba.
Ko motsi mommy batayi ba balle ta sa ran zata tausaya mata.
Magana tafara tana kuka sosai.
"Kowacce uwa tana nunawa yaranta so koba yayan halak bane, kowacce uwa tana Jan yayanta a jikinta musamman Yaya mata, Amma bansan wanne irin zunubi na aikata Miki da kika kasa yadda ki karbe ni a matsayin yaba, dukda nasan laifi na aikata Miki Wanda kika kasa yafemin shi, Amma Dan Allah inaso ko bazaki kalleni a matsayin ya ba ki kalleni a matsayin baiwa wacce take Miki bauta, kiyimin magana kamar yadda akewa bayi magana, kiyimin hukunci kamar yadda akewa bayi hukunci, ko iya haka nasamu daga gareki zanji dadi ko yayane" kukane yacu karfinta takasa karasa maganar ta nufi dakinta da gudu ta fada gado...***** ***** *****