part 9

177 13 0
                                    

🌈 _*KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*_
{'''United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers'''}

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

      *🤱 MAHAIFIYATA🤱*
 
_Writing by_

   *🌹 Ameena first lady🌹*

_page1⃣3⃣ to 1⃣4⃣_

Har yamma tayi basuga wacce suke nema ba gaba daya Shaheed ranshi ya gama baci.

Usman ya kalla yace "mu mutafi da alama yau batazoba kokuma tsoro ya hanata zuwa"

Yau Zainab tashigo school tana zaune inda suka saba zama da khadija, wata kawarsu ce mariya ta karaso ta zauna.

       "Zainab yau ina aminiyar taki naganki ke daya"?

"Taje kauye dangin mamanta meya faru kike tambaya ta"

Mariya ce tace "naga mutumin ta yanata nemanta harni suka tambaya nace bansanta bama"

Zainab ce tace.  "Waye kenan"?
       "Shaheed mana kin manta meya faru jiya ne"

Gaban Zainab ne ya fadi daman tasan za'ayi haka, Shaheed bazai taba yafe abinda khadija tayi Masa ba.

"Kyale shi zaima hakura ne indai khadija ce Saidai yayi ya gama Amma bazai iya da itaba,itama dai dai take dashi.

  Haka suka cigaba da hirar su ta duniya sannan Zainab tayi gida.

Khadija kuwa sai yamma ta karasa kauyen walarbe,Kai tsaye gidan kakanta malam lawan ta wuce...

Da sallama ta shiga yan tsofaffin suka amsa mata.

"Ashe yau bakin birni zamuyi shiyasa tun daga waje ake jiyo kamshi" cewar laraba kakarta.

   "Tsohuwa mai ran karfe yaushe zaki mutu kibarmin mijin ni kadai ne"

"Ai saikin rigani mutuwa ja'ira kuma miji na rikeshi gam saidai ki Nemo naki".     Gaba dayansu sukayi dariya da maganar laraba.

Haka sukayi ta hira suna tsokanar ta itama tana mayarwa...

     Sai dare bayan sungama cin abinci sannan malam lawan yayi gyaran murya yace.  

    "Khadija lafiya kuwa naganki katsam baki fadi zuwanki kamar yadda kika saba ba"?

    "A'a Kaka matsalace ta kawo ni"

"To inajin ki menene matsalar"

Khadija ta kwashe ta fada Masa komai bata rage komaiba.
Ta karashe tana kuka sosai..

"Ashsha kiyi hakuri khadija kwarai kinyi hakuri a baya kuma insha Allahu komai yazo karshe,share hawayen ki kinji"

Laraba ce tace  "Amma Maryam batada hankali yanzu ashe bata daina nuna Miki halin ko inkula da take nuna Miki tun kina yarinya ba".
  "Anyi fadan Amma ashe har yanzu bata sauya ba,kiyi hakuri kidaina kukan haka...

"Yanzu yaushe zaki koma"?. inji malam lawan.

"Jibi zan tafi saboda inada makaranta ranar litinin"

     "To idan kin koma kice inasan ganinta lallai lallai tazo inji ni"
  
"To kaka nagode Allah yakara lafiya"

"Ameen tashi kije ki kwanta Allah yayi Miki Albarka"

"Ameen" sannan ta tashi tashiga dakin laraba.

            ***************
Shaheed kuwa tunda ya koma gida daki kawai ya shiga ya kwanta ba Wanda yasan ya dawo sai gate man daya bude Masa get.

Haka yayita bakin cikin rashin samun khadija da baiyi ba a haka har bacci ya dauke shi.....

Saida ya jera 3days kullum saiya je school Amma baya samun khadija.

Yauma dayaje bai sameta ba ko takan Usman baibi ba yabar school din, tareda kudura a zuciyar shi bazai kara zuwaba sai bayan sati daya...

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now