part 3

254 15 0
                                    

*🤱MAHAIFIYATA🤱*


*🌹 Ameena first lady🌹*

_Watsapp number_
   08112138112

_page5⃣ to 6⃣_

Tunda suka koma g.r.a Khadija batajin dadin zama kwata kwata,musamman da harkar Aikin Alhaji Ahmad ya  koma Lagos, hakan yasa ta koma zuwan gidan A'i ko Aunty Rahma gidan uncle Abdulmutallib,

A haka Khadija ta kammala karatun secondary School wata biyar da gamawar credentials dinta ya fito ba bata lokaci Abbanta yasa Abdulmutallib ya nema mata B.U.K tace gaba da karatun ta..

   Khadija yammata, Wanda yanzu shekarunta sunkai goma sha tara 19yrs,ranar data fara zuwa makaranta Allah ya hadata da Zainab a wajan shiga hall din lecture a guri daya suka zauna.
Bayan sun fito ne Zainab ta nunawa Khadija tanasan suzama kawaye,inda tace

    "Sunana Zainab kabeer, kefa" "Khadija Ahmad"

"Naji dadin haduwa dake" Nima haka inji Khadija.

Tun daga shakuwa mai karfi tashiga tsakaninsu,Dan mutane da yawa suna tunanin gidansu daya, musamman da akaga kusan komai tare sukeyi......

    Itama Zainab ita kadai iyayenta suka haifa suna zaune a unguwar Dorayi gidan dakali, shiyasa wani lokacin Khadija anan take weekend dinta harsu koma makaranta...
Mahaifiyar Zainab hajiya binta tana matukar jin tausayin Khadija shiyasa ta riketa tamkar yarta Zainab.

     
      ***************

_CIGABAN LABARI_

   Lokacin da khadija ta fito daga wanka har 6   O'Clock tayi gaba daya ma tadaina jin yunwar tun safe dama ta sani tabi zainb din ta kwana can.

Khadija ce taketa Kiran me girkin su"mama uwani" har sau uku
'na'am khadija ya akayi ne kike kirana Kamar mafarauciya'

Dariya khadija tayi sannan tace "abinci na zaki zubomin yaufa banci komaiba"

"To ai saiki wuce kichiene din muyi tare"
'Mama uwani gaskiya yau nagaji bazan iya shiga kichiene ba"
    
'to ki jirani kibani minti biyar kacal'

Bayan sallar Isha khadija ta Kira Zainab.   "Hello sister"
Malama ya akayi kika tasheni da wannan tsohon daran lafiya"?

'to fah ni kike wannan wulakancin zamu hadu gobe, dama cewa zanyi karki manta da dambun Naman nan Dana ce ki tahomin dashi pls"
    "To naji saikuma me"?
Dariya khadija tayi tace   'bansani ba, saida safe' katse wayar tayi a zuciyar ta tace 'masifaffa kawai dama nasan za'ayi haka"

Yau ta kasance ranar laraba (Wednesday) khadija sunada lecture 8:30 gashi malamin bashida mutumci da sauri sauri khadija ta shirya ta fice tana Kiran Bala driver..
"Na'am hajiya harkin fito"
  "Eh na fito" "Auuu nayi mantuwa ina zuwa bani 1minute"

     "To hajiya"
Da sauri ta koma palour ta nufi dakin mommy gabanta na faduwa da sauri da sauri..
Nocking tayi sau uku shiru ba'a bude ba, hakan yasa tabude a hankali ta shiga .
"Mommy barka da asuba zan tafi school ina fatan zan dawo na sameki lafiya" bata jira amsar ta ba ta fice da sauri Dan bataso ta tashi ta ganta a wajan

Karfe 8:00am dai dai tashiga makarantar sai baza idanu take taga Zainab Amma shiru,.  Wayarta ta dauko a cikin jakarta ta Kira Zainab din.

     "Zainab kina inane nashigo ban ganki inda muka saba zamaba".      "Eh kinsan anyi ruwa wallahi bansan lokaci yaja haka ba amma gani nan shigowa yanzu"

Mutwwws khadija taja tsaki "kedai wallahi naga ranar d zaki daina makara gaki ga makarantar Amma kusan kullum saina rigaki zuwa"

"Sorry sis gani nan fa yanzu" "karma kizo nidai shiga zanyi kinsan halin malamin nan ai"
"Dan Allah ki jirani bani 5minutes plsss".       "Ok tam"

4:15pm suka gama lecture gaba daya na ranar suka fito a gajiye, tafiya suke a hankali kana ganin su kasan a gajiye suke,

     "Abin haushi ace Wai driver naki baizo ba nawa ma shiru yanzu saidai mutafi a napep"inji Zainab.
"Nidai gaskiya bazan iya tafiya a napep ba zan jirashi a waje harya zo" Khadija kenan ta fada a wahale..
Suna tafiya hanyar bakin gate sunata mita musamman Zainab sarkin mita.

Mota ce jibgegiya kirar _dodge doytona_ ta shigo cikin b.u.k din a 360, dalibai da suke kan hanyar sai matsawa sukeyi da alama sunsan mai motar..
Tafiya suke itada Zainab a bakin hanya ko gani sosai khadija batayi tsabar gajiya, Ba zato kawai taji saukar ruwan dake kwance  kan hanya a jikin kayanta gashi abin haushin kayan light pink ne,hakan yasa ruwan ya fito da kalar sa ta alamun Kamar kwata.

Khadija ce ta dago cikeda jin haushi zatayi magana, ai saita gano motar hartayi parking a wajan da aka tanadarwa motoci..

     "Zainab rikemin jakata" khadija tace tanabin wajan motar da kallo"
Zainab tace "khadija kiyi hakuri karki kulasa" khadija ce ta kalli Zainab da alama tasan mai motar tunda ta dage da bata hakuri,Amma Ina khadija bataji ba ta nufi wajan motar ranta a bace..

Tana zuwa ta leka cikin motar,

Hadaddan saurayi ne zai wuce 31yrs ba amma ya hadu iya haduwa ga kyau ga alamun kudi sun rasa shi fari tarr da fararen idanu lebensa ruwan hota Dan turanci ma iya Kiranshi da (pink lips) ya hadu karshen haduwa tako ina, saboda haka mu kirashi da (first class wajan kyau)
  
  Su uku ne shine a mazaunin driver sai wani a gefen shi saikuma wani a baya Amma duk basu kaishi kyau ba.

......Tana lekawa dai dai ya daga rubar swan zai Kai bakinsa, ta fisge a hannun shi ta zuba a inda ruwan kwatar ya samu,

Mamaki ne ya kama shi ya tsaya Kamar mutum mutumi, sannan suka fito su duka ukun daga motar da San ganin wannan wacece mai irin wannan karfin halin.......

*Kuyimin afwa yau nagaji da yawa ne shiyasa kuyi hakuri da wannan*

_Yaya Hayat jinjina da ban girma a gareka ina matukar godiya da goyon bayanka 100%_ _nagode Allah yabaka zuriya ta gari_👍👏

        🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now