47

159 12 0
                                    

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

'''{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

           *🤱MAHAIFIYATA🤱*

_By_📚✍🏻

*🌹 Ameena first lady🌹*

_page9⃣1⃣ to 9⃣2⃣_

Gidan zainab yayi kyau da tsari sosai,.
Khadijah kuwa gidan da Daddy ya mallawa shaheed aka kaita, gidan aljannar duniya kenan wajan kyau, kamar a Turai yayi tsari sosai mutane suka yaba kyaun gidan..

Da kyar suka lallashi Khadijah sannan tabari suka tafi,. Shiru gidan babu alamar motsin mutum hakan yasa tafara jin tsoro dama Khadijah sarkin tsoro ce.

Shaheed kuwa yana can su mamee da Daddy suna yi masa faɗa sosai kan yaji tsoron Allah karya cutar da yarinyar mutane wacce duk abinda yayi mata bata ƙishi ba,. Suna gama yimasa faɗan jiki a sanyaye Bashir ya ɗauke shi suka tafi zai raka shi.

Ko palourn Bashir bai shiga a compound ɗin gidan ya ajiye shi yace zaizo kafin ya su tafi yaga amarya, ledojin hannun shi ya bashi sannan yayi masa sallama ya tafi.

Ya daɗe yana kallon palourn kamar mai san ganin wani abu sannan ya nufi ɗakin cikeda farin ciki.

Tunda ya shigo Khadija taji, hakan yasa taji tsoron nata ya ragu koba komai dai taji motsin mutum, tana cikin wannan tunanin ne taji alamun turo kofar ɗakin da take ciki.

A hankali cikin natsuwa ya shigo, saida ya ƙare mata kallo sosai sannan ya zauna gefenta.
Kanta na ƙasa, hannu yakai ya ɗago kan nata idanunsa cikin nata,.
Hawaye ne suka zubo daga cikin manyan idanuwanta, da sauri ya shiga girgiza mata kai alamar bayasan kukan nan.
Goge mata hawayen ya shiga a hankali da kyar ya iya furta "ya isa haka pls". Tayi mamakin jin yayi mata magana a tausashe. 
Mikewa yayi ya nufi fita yana faɗin "kiyi alwala kafin na dawo". Yasa kai ya fice baijira amsar taba..

Kamar yadda ya umarceta hakan tayi, bayan ya dawo shima da alwalar shi suka gabatar da Sallah da addu'oi kamar yadda addini ya nuna mana.

Palourn ya koma ya ɗauko ledojin daya shigo dasu ya dawo ɗakin ya zauna kan stool ɗin dake bedside.
"Kici abinci dan nasan  kinajin yunwa"

"Na koshi" ta faɗa a takaice.
Haɗe fuska yayi yana kallon ta "bana san musu kin sani". Ya faɗa yana tura mata plate ɗin.
Badan taso ba haka ta dinga tura abinci  dan dole, tana gamawa ya fitar da kayan.
Ganin ya fita da sauri ta tashi tayi night dressing sannan ta kwanta abinta dan batayi tunanin zai sake shigowa ba.
Shikam yana palour yana aiki da computer hankali kwance,  saida ya gama sannan ya shigo daki , tuni ta daɗe dayin baccin ta.
Murmushi yayi ganin yadda take fitar da numfashi a hankali, saida ya yayi wanka ya shirya sannan ya kashe fitilar ɗakin ya kunna bed side lamp sannan ya  kwanta a gefenta.
Idanunshi a kanta, wani murmushi ya sake yi kome ya tuna oho, sannan yakai hannu ya shafa lallausan gashin daketa faman sheki da daukar ido.

A hankali yafara yafara zarcewa da salon wasa,. Firgigit ta tashi da sauri ta sauka daga bed ɗin, tuni hawaye yafara ambaliya a fuskar ta.
"Dan Allah kayi hakuri..." Kawai ta iya cewa.
Shima tashi yayi ya zagayo har inda tsaye jikin bango,. "naji dama ba wani abu zanyi miki ba ai jeki kwanta.."
Ganin alamar bata yadda dashi bane yasa shaheed janyota jikin shi. Dai dai kunnen ta yakai bakin sa a hankali ya furta. "ki kwanta idan baso kikeyi nayi miki abinda bakya soba"
Kafin ya rufe bakinsa tayi saurin hawa bed ɗin.
Murmushi yayi dan tabashi dariya ma ganin jikin ta har rawa yakeyi.
Gefenta ya koma ya kwanta ba ɓata lokaci bacci ya sace shi.
Itama jin alamar yayi bacci yasa ta juya taci gaba da baccin ta.

Da asuba ta tashi amma abin mamaki bataga shaheed a ɗakin ba harya fice, bathroom ɗin dake cikin ɗakin ta shiga tayi alwala.
Saida ta idar da Sallah sannan tafara azkar, har safiya tayi sosai sannan ta tashi ta nufi palour.

Zaune ta ganshi a palourn yana danna wayarsa, shima duk da yaji buɗe kofar bai ɗago ya kalli wajan ba yaci gaba da abinda yakeyi.

Har ƙasa ta duƙa ta gaida shi, fuskar shi a sake ya amsa harda tambayar ta ya ta tashi.
"Me zan girka maka". Ta tambaye shi.
Kallon shi ya ɗauke daga kan wayar ya mayar da kanshi gare ta..
"Ki huta kawai mamee zata aiko dashi".
Shiru tayi kamar bazata tashi ba.
Kallonta ya kumayi "nace ki barshi'..
Daga haka yaci gaba da abinda yakeyi.

Sun kusa minti goma a zaune babu wanda ya sake magana sannan sukaji nocking.
Shaheed ɗinne yaje ya buɗe, Meera ce dauke da kulolin abinci da fara'ar ta ta gaida, amsa mata yayi yana bata hanya ta wuce ciki.
A dining table ta aijye tana gaida Khadijah.
Sosai ta saki fuska suka gaisa.
Har zata tafi Khadijah tace ta tsaya mana suyi hira.
Meera sarkin surutu dama haka take so.
Bayan sun gama breakfast shaheed ya shige ɗakin sa ya barsu.

Meera ta daɗe Sam Khadija bataso tafiyar taba dan taji daɗin zuwan nata saboda ta dauke mata kewar gida da zainab.

Zainab tana can gidanta tareda mijinta nazeer, sai zuba shagwaba takeyi iya san ranta shima nazeer ɗin ya biyemata ko fita yakasa yi.
Sunyi waya da zainab ɗin
Tabata labarin yadda nazeer yake ta faman taraiyar ta.
Sosai Khadijah take dariya "kiji tsoron Allah zainab karki mayar da shi mijin tace nasan halin ki sarai..'
Itama zainab ɗin dariya tayi "kedai zauna yarinya mijin kan tace ma zai koma" suka sake shekewa da dariya.
Sun daɗe suna waya daga karshe sukayi sallama...

Ta kira su mommy da mama da aunty Rahman duk sun gaisa tareda sake yimata nasiha sosai.

Da rana ma Meera ta kawo musu abinci har dare, shaheed ne yace. "zo na kaiki gida Malama kin ishemu da surutu"
"Haba yaya nifa da anan zan kwana"
"Whattt wlhy biki isaba tashi nakai ki gida, bazaki hanamu sakewa ba". Khadijah ma ta saka baki amma daga karshe cewa. "a haka ma ganinta yasa kin manta dani inaga ta kwana bazai yiwu ba"
Mamaki ne Yaka Khadijah "lallai wannan da mace ne zai iya makirci da gulma"
"A'a kabarta mana ai kulawar dazan baka bai shafi kwanan taba"
Kallonta yayi yaga ta make babu alamar da wasa take "tab ashe har yanzu Khadijah tana nan da halinta na kome akayi mata saita rama"
Meera kam Bata gano komai ba hakan yasa tace "kyale shi aunty watarana da kanshi zaije ya ɗauko ni yace na kwana"
Bai kula suba ya fice yana faɗin ta same shi a Mota...

Kwanci tashi babu yuwa yau kusan sati biyu kenan da bikin, tuni shaheed yafara shirin kowar su Spain saboda karewar hutun sa,..

Saura kwana huɗu su tafi yafara kaita tanayo sallama, daga ƙarshe yakaita gidan zainab ana gobe tafiyar tasu.
Taji daɗi sosai ko gama parking baiyi ba ta fice da murnar ta tashige gidan.
Kamar su hadiye juna dan murna, nazeer ma yana nan hakan yasa shaheed yashigowa har akayi sallar Azhar suka fice danyin sallah.
Zainab ce taja Khadijah ɗaki tana bata magunguna saida tagama mata bayani sannan Khadijah ta taɓa baki "Ni to mezanyi dasu"
Gwalai zainab tayi tana kallon ta "Khadijah kinada hankali kuwa kodai kin samu tabuwa ne.."?
Dukan wasa khadijan takai mata "nice mai tabin hankalin"
"Ai naga alama, kardai kice min babu wani abu daya shiga tsakaninku tsawon wannan lokacin.."
"Eh haka nake nufi, zainab sonake saina yarda da soyayyar da shaheed yakemin ba.."?
Kafin takarasa zainab ta tsayar da ita. "Khadijah wlhy shaheed yana sanki karma ki yaudari kanki, soyayyar dayake miki ce tahana shi yimiki dole amma da tuni an wuce wannan maganar.."
"Saboda haka ki ajiye wannan wawancin naki ki rike shaheed idan kuwa ba haka har kika siƙe shi tofa su Abba zai fadawa kokuma ya samu wata ƙatuwar budurwar ya aura shikenan"

Gaban Khadijah ne ya fadi dan tasan zainab bazata yimata karya ba dole gaskiya take faɗa mata Yakamata kam ta ajiye shashanci koma menene yanzu shaheed mijinta ne abinda faru kuma ya gama faruwa yazama labari..

Zainab tabata shawarwari sosai sannan sukayi sallama shaheed na dawowa ya ɗauke ta suka tafi..

Da kanta ta shirya musu kayan da zasu tafi dashi, shaheed yaji daɗi amma sam bai nuna mata ba,..

Da sassafe Daddy yakaisu airport Dan jirginsu na safe ne, aikuwa ba ɓata lokaci jirginsu yatashi zuwa Spain...

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now