part 52

389 19 1
                                    

*🤱 MAHAIFIYATA 🤱*

*_🌈 KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻

'''{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

_By_📖✍

*_Ameena Musa_*

*🌹 Ameena firstlady*🌹
ameenamusa881@gmail.com

*_na sadaukar da wannan fejin ga ƙungiyar kainuwa writers association, musamman ga my daughter NEESHER, da ƴar 16 17😃😛 UMMY ON TOP, ƙanwata Maryam Ismail, aunty Fauzah  da sauran Yan KAINUWA da sunan su bazai faduba, ina matukar godiya sosai Allah yakara haɗa kanmu_*

_page1⃣0⃣1⃣ to1⃣0⃣2⃣_

______________________

Saida shaheed ya shigo sannan tayi saurin nutsuwa, ta amshi babyn a daga hannun Hafsat.

Saida tagama murnar sannan ta kalli zainab tana yi mata sannu, shaheed kuwa yanayin Barka ya hanyar fita.

Nazeer ne da Usman da kuma salim suka shigo palourn harda wata yar budurwa Black beauty, shaheed yayi mamakin ganinsu duk a tare, Khadijah kuwa ganin Salim bakaramin tsorata tayi ba.

"Ashe kuna tare" shaheed ya faɗa yana sake zama.
Usman ne yayi dariya yace ai yana faɗa min na kawo Hafsat tayi Barka shine shima salim yazo da tashi kaga gashi duk sun haɗu"
Sai yanzu Khadijah tagane shaheed ma kenan yasan salim to kodai bai gane shiba ne take ta sakawa a ranta.
Hira ce sosai ta barke tsakanin su shaheed dai bai fiye saka musu baki ba, acikin hirar tasu ne taji salim yana faɗin an saka ranar auran shi da wannan budurwar da suke tare, shima Usman yace an saka nashi kusan ma duk lokaci guda ne.
A tare suka fita harda nazeer da shaheed ɗin duk suka bar yammatan nasu a nan.
Cikin kankanin lokaci suka saba suma kamar daman can sun san juna da Rukayya budurwar Salim, Hafsat kam tun a school Ashe suke soyayya da Usman.

Sai dare sannan shaheed yazo ɗaukar ta, badan taso ba ta tashi tabi shi suka tafi,..

Kwance take a saman faffaɗan ƙirjin shi sai zuba iyayi da shagwaba takeyi, shikam sai biye mata shaheed ɗin keyi,.
"Amma da sassafe zaka kaini gidan zainab ko.."?

"A'a saida rana kinga gobe zan fara fita office"
  Cikin shagwaba tace "ba saika ajiye ni idan ka dawo saika biyo mu tafiba, nayi kewar babyn fa"
"Naga kina san yara Yakamata yau na kara dagewa muma saimu samu namu"
Tun kafin ya yakarasa zancan nasa tayi saurin niyyar barin gadon, da sauri ya riko hannun ta yana dariya dan tabashi dariya sosai "ina zaki kibarni". Ya faɗa yana makewa.
Cikin alamun shagwaba kamar zatayi kuka tace "bakaji abinda kace ba, to wlhy idan ka sake mutuwa zanyi"
Tashi zaune shima yayi, ya kamo hannun ta yana faɗin "I'm just joking fa" ya faɗa yana haɗa fuskar su waje guda.
Cikin dabara ya haɗe bakinsu yafara aika mata da wani saban salon kiss, sun daɗe a haka sannan suka lula duniyar ma'aurata.

Yauma da kanshi yakaita sannan ya wuce office ɗin da Daddy ya bashi, dan fara aiki.
Saida ya dawo sannan ya biya ya dauko ta.

Ranar suna ta zagayo aka sama yaron suna Ahmad sunan mahaifin Khadijah, wanda zainab ta dage ita shi take so tayiwa Khadijah kara,.
Har hawayen farin ciki Khadijah tayi, tagane zainab ba kawarta bace kaɗai tazama yar uwa kamar ciki daya ma suka fito.
Adil sunan da suke kiran shi dashi, yaro da mamansa sunga gata iya gata mutane har mamakin irin dukiyar da Khadijah ta kashewa yaron da zainab sukeyi.
Zainab ma har kukan farin ciki tayi.
Mommyn Khadijah ce ta dage saida nazeer ya barta suka tafi da ita gida wanka wanda gidansu Khadijan Mommy tace a Bata zainab ɗin su tafi.

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now