*🤱 MAHAIFIYATA🤱*
_writin by_
*🌹 Ameena first lady🌹*_page 1⃣9⃣ to 2⃣0⃣_
........Kai tsaye private hospital suka wuce har lokacin khadija bata farfado ba..
Emergency room aka kwantar da khadija likitoci har uku akanta ana kokarin ceto rayuwar ta.
3hours saiga wani babban mutum daya daga cikin likitocin da suke ceto rayuwar khadija ya fito, idanuwan shi sanye da farin Glass...
Harya wuce su Abba basu kula dashi ba saikuma ya dawo da baya yace. "Kune kuka kawo patient yanzu"?
Zainab ce tace "eh Dr ya take ta farfado ne"
Ta jero tambayar tareda San sanin halin da khadijan take ciki.
"Bata farfado ba Saidai munasa ran nanda 4hours ta farfado lokacin ta huta, yanzu dai inasan ganinku a office Dina". Sannan yayi gaba.
Izinin zama doctor yabasu sannan yaci gabada cike files din dake gabansa, tsawon minti biyar ya dago Yana gyara zaman glass din..
"Alhaji bansan dalilin yasa kuka bar yarinya me karancin shekaru haka takamu da hawan jini ba Wanda har yake barazanar shafar zuciyar ta"
A zabure alhj Ahmad ya Mike, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai yake maimaitawa..
Zainab kam hawaye ne yaci gabada zubo mata.Doctor ne yaba Alhj Ahmad izinin zama,sannan ya koma ya zauna zufa tana keto Masa ta ko Ina..
"Kayi hakuri Alhj da alama kaima bakada masaniya akan haka Amma yakamata idanta farka ka tambayi damuwar ta ta hakan kadai zaka iya magance matsalar, sannan ta rage tunani Dan zuciyar ta gaf take da kamuwa". Haka doctor yayita basu shawarwari daga bisani ya rubuta musu magunguna...
Kamar yadda doctor yace 4hours khadija tayi ta farka,
Da sauri Zainab ta karasa kusa da ita,
"Sannu khadija"Khadija da sai yanzu abinda ya faru yake dawo mata, hawaye ne ya zubo ta gefen idanuwan ta.
Zainab sai lallashinta takeyi Amma khadija taki daina kukan kuma takasa magana..Turo kofar dakin da aka kwantar da khadija akayi, aunty Rahma ce matar uncle Abdulmutallib ta shigo, ta ajiye kulolun hannunta sannan ta karasa gun khadija..
"Haba khadija daga farkawar ki saiki kama kuka karfa ki manta a gadon asibiti kike yakamata ki rage damuwa.
Haka aunty Rahma tayita bata baki sannan aka samu tayi shiru..
"Shikenan yanzu a haka zan karasa rayuwata ga MAHAIFIYATA a raye Amma takini ta tsaneni shikena Saidai na Kira kaina wacce batada mahaifiya"...kukane ya kuma kwace mata."Haba khadija wayace bakida mahaifiya kenan mamana ba mahaifiyarki bace ita kokuma baki dauki aunty Rahma a matsayin mahaifiyarki ba? Zainab ce take mata wannan maganar.
"A'a Zainab bahaka nake nufi ba""To indai bahaka kike nufi ba kiyi shiru kidaina fadin bayan mommy bakida wata mahaifiyar"
Girgiza Kai kawai khadija tayi.
Aunty Rahma da Zainab a nan hospital din suka kwana bayan Zainab ta Kira mama ta fada mata khadija ce ba lafiya suna asibiti zasu kwana tare,. Mama tace bakomai tayiwa khadijan sannu kafin tazo..
Ba Wanda Abba ya fadawa khadija ba lafiya sai Abdulmutallib daya fadawa shiyasa aunty Rahma ma taje Amma ko A'i ba fadawaba gudun matsala a cewar sa...
Saida safe aka sallame su Abba ya wuce dasu gidan aunty rahma, Dan bazai mayar da khadija gidan sa ba sai bayan ta warke sosai yaga ba abinda yake damunta...
Nasiha sosai Abba da Abdulmutallib sukayi mata akan ta rage tunani tunda ga abinda doctor yace,. Kuma tayi alkawari zata rage yawan tunanin Kamar yadda suka bukata.
Khadija ta warke sumul batada ragowar wani cuta yanzu kuma ta rage tunani hakan yakara ta samu lafiyar da wuri, yau a gidan su Zainab ta kwana saboda su shiga school gobe da wuri..
Abu daya take tunani, shin idan kawayenta suka tambayeta akan abinda ya faru rannan mezata ce musu,. Zainab ce tace ta kyaleta dasu zata basu amsa...
Yau Monday 8:00am dai dai tayi musu a school Kai tsaye kuma suka wuce daukar lecture .....
Shaheed kuwa Yana kwance a palour Mamee tana tambayar shi meyasa kwana biyu baya shiga school tana lure dashi..
"Nothing Mamee, just Ina hutawa ne"
"Kai Shaheed ka fita idona na rufe, kaine ka zabi wannan makarantar ba dole akayi maka ba, ta Dalilin hakan kasa muka dawo kano ,to wallahi baka isa yanzu kace bakasan makarantar ba"
Saida tagama fadan sannan Shaheed yace "Mamee bafa cewa nayi banaso ba kawai fa nagaji da zuwa ne Amma very soon zan koma ai"
"Oho dai kamace bakaso kaga yadda zanyi dakai shashasha". Tafada tana haurawa saman bene.
Ina dama zanbar makarantar bayan haryanzu ban rama abinda waccan yarinyar tayimin ba...
Karar wayar shi ce ta katse Masa ragowar tunanin..."Hello Usman ya akayi"
Daga can bangaren Usman yace.
"Albishirinka guy"
"Shaheed ne yace malam idan zaka fadamin kawai ka fada idan kuma bazaka fada sai anjima"
Har zai katse wayar yaji Usman yace mutuniyar yau tashigo school..
Ai baisan lokacin daya Mike zaune ba yace "what ta shigo fa kace"
"E tashigo wlhy yanzu naganta da wannan kawar tata""Kaga Usman duk inda zatayi ka bita a boye gani nan yanzu plss"
"Ok saika zo"
Shaheed yayi saurin hawa sama ya shiga dakin Mamee.
"Mamee zan fita"
"Ina kuma zakaje, badai daukar magana zakaje ba"
" A"a Mamee school zan shiga"
"Badai school ba, duba kaga clock what time now"?
"Mamee submitting assignment zanyi ai"
"To shikenan saika dawo"
Ai ko karasawa batayi ba ya fice da sauri..
Mota ya shiga ya figeta a 360. Kamar zai tashi sama.........
_Ina godiya sosai da kuke comment yadda yadda kamata_🤝🤝🤝🤝