40

167 9 0
                                    

*_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*

'''{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

          
          *🤱MAHAIFIYATA🤱*

_By_

*🌹Ameena first lady 🌹*

_page 7️⃣7️⃣ to 7️⃣8️⃣_

Dafe da kunci ya zauna jagwab akan kujera, zuciyar shi na mishi zafi, tashi yayi fuuu ya fice ya nufi part dinsa cikeda haushi.

Yana shiga ya fada kan gado Yana maida numfashi a hankali cikin huci.
"Inama bandawo ba nayi zamana har saina gama karatuna" ya fada a ransa.
Haka ya zauna cikin kadaici shi kadai damuwa fal ransa, gashi babu Wanda zai fadawa damuwar sa kozai samu sauki.
"Aure kuma, Wai nan da kwana shida kacal"...
"Ina bazai yiyuba, bazan taba auran wacce banaso ba...."
Jin alamun shigowa dakinsa yayi, da fushi ya ya waiga a tunanin sa Meera ce saikuma yaga Mamee tsaye jikin kofa itama da alama jikinta a sanyaye yake, karasowa tayi ta zauna kusa dashi ta kamo hannun shi tana murzawa alamun lallashi.
"Kayi hakuri Shaheed munyi maka laifi Saidai bamuda zabi da ya wuce sama maka mace tagari, kwarai dakaji labarin zaka tausaya mata sosai.."
"Amma Mamee meyasa baku sanar Dani ba tun lokacin sai yanzu da komai yazo karshe."
"Kasani bazamuyi maka mummunan zabi ba, kasan irin soyayyar da muke maka, mahaifinka Yana kokarin ganin farin cikinka har sadaukar da farin cikinmu muke saboda Kai Shaheed, meyasa bazakayi wa mahaifinka biyayya akan wannan maganar ba, nasani bamu kyauta maka ba Amma kayi hakuri kabi umarnin mu idan yaso ko nan gaba saika kara auren wacce kakeso din..."
Takarasa maganar tana kallon yadda mood dinsa yake.

Jikinsa yayi sanyi kwarai yasan irin soyayyar da suka nuna Masa Kuma sunyi hakuri dashi a lokacin da yake ganiyar rashin mutumcin sa Amma meyasa yanzu yakasa bin umarnin su Wanda yake ganin yafi komai sauki a wajansa, tuna ya rasa khadija har abada bayajin zaiso wata ya mace  a duniyar nan garama ya auri zabin iyayen nashi may be yasamu relief na rashin khadija.

"Shikenan Mamee zanyi Masa biyayya kamar yadda kikace, Kuma inshallahu zan kasance Mai biyayya a gareku akan komai"
Farin cikine ya bayya a fuskar Mamee ta rungume shi tana sa Masa Albarka.
"Yanzu ka kwanta gobe idan ka fito saimu shirya komai"
"Ok Mamee good night"
"Night too dear"
Ta fice daga dakin.

Cikin dare yakasa bacci sai juyi yake a makeken gadonsa, tunani take akan maganar auran dolen da za'ayi Masa a cewar sa.
"Shikenan gaka zanyi aure babu friends, ba nazeer ba Usman.."

Sai yanzu yafara tunani a hankali Yana tuna abinda ya faru haduwar shi da Usman na karshe, Damm gabansa ya fadi "Ina khadija yanzu, ko a wanne hali take yanzu, waye zai aureta bayan wannan mummunan abinda ya faru da ita."
Rashin amsar tambayar shi yasa ya janyo wayar shi neman layin Zainab da Nazeer.
Tsaff ya duba bai samu contact dinsu ba, sai yanzu ya tuna ya karya wancan layin nasa a daran dazai bar kasar.
Wani huci Mai zafi ya fitar daga  bakinsa Yana rikeda kansa dayayi Masa nauyi.
"Dole na nemi nazeer ko Zainab aduk inda suke kozan ji labarin khadija, idan kuwa har nasamu labarin khadija lallai saina nemi inda take Koda zan rasa rayuwa ta.   Da wannan tunanin bacci Mai nauyi ya sace shi.

Da sassafe nazeer yazo gidan uncle Abdulmutallib wajan Zainab, Dan tuni a tare a gidan taki komawa gida.

Bayan sun gaisa yake tambayar ta shirye shiryen da suke ganin lokaci Yana kurewa.
"Kasan jiya Wanda khadija zata aura ya dawo, to muna jiran zuwan shi sannan mu hadu mu tsayar da komai"
"Kina nufin baizo ba tun jiyan"
"Eh baizo ba, kasan shima baisan da auran ba,"
"Gaskiya Ina tausayawa khadija sosai..."
"Dole kaji tausayin ta ai, abokinka Shaheed yaci amanarta, ta Dalilin shi tashiga damuwa sosai, gashi hakan haryayi sanadiyyar ragujewar auranta da Wanda takeso"

"Ki daina cewa haka Zainab, na fada Miki Nima yanzu bana tareda Shaheed, tunda abin yafaru"
Murmushi kawai Zainab tayi Dan ita haryanzu bata yarda nazeer baisan komai ba.
Suna hirar khadija ta fito Kiran Mai gadi, Saida suka gaisa da Nazeer sannan yafara tsokanar ta.
"Lallai amarya kin buya, da alamu jiran ango kike yafara ganin shekin amarcin"
Murmushi tayi tace. "lallai kuwa, ango ne zai fara gani kafin kowa ya gani"
Dariya sukayi gaba dayansu har Zainab din.

Kamar yadda Mamee tace Masa da sassafe ya nufi palourn su, Mamee kawai ya samu a palour tana shirya breakfast, Yana gaida ita ya haura sama dakin daddy.

Dai dai daddy zai fito suka hadu, gaida shi yayi ya amsa kasa kasa Yana neman wajan zama ko kallon inda Shaheed din yake baiyi ba.
Shaheed zama yayi a kasan capet sannan yafara yiwa daddy magana.   "Dan Allah Dad kayi hakuri banyi tunani bane a jiyan naji maganar ne a sama shiyasa Amma yanzu na amince Allah yakaimu"

Fara'a ce ta bayyana a fuskar daddy, kamo Shaheed yayi ya zaunar dashi kusa dashi. "nasani ai bazaka taba gujewa umarnina ba Shaheed, I'm proud of you, tashi muje miyi breakfast"
A tare suka jero har palour, Mamee taji dadin ganinsu tare.
Murmushi tayi tana tabe baki. "harkun shirya kenan.."?

"Dama mun fada Miki fada muke.."? Daddy ya mayar mata da tambayar.
Meera ce tace.  "A'a daddy baku fada ba kam gaskiya ". Sukayi dariya su duka Amma banda Shaheed Wanda shi Sam hankalin sa baya wajan ma.

Saida sukagama breakfast daddy da Meera suka fita tare zai ajiye ta a school ya wuce.

Mamee ce tace. "Shaheed banji kafara maganar event din dakuyi ba fa kuma lokaci kurewa yakeyi"
Yakuna fuska yayi yace. "Mamee kinsan fa, bansan komai ba akan wannan abubuwan."
"Nasani Amma ai kamata yayi kaje ka tambayo ta ita ko ita tashirya komai"
"Lallai wannan daga gani ta kagara ayi auran..". Shaheed yafada a ranshi.  Amma a fili yace "to Mamee zanje Amma sai anjima"
"Shikenan Allah yakaimu"

Ko amsa bai bata ba ya tashi ya fice.

Zainab na kwance khadija Kuma tana zaune kusa da ita. "khadija Banga kina preparing din tarbar angon naki ba.."
Damm gaban khadija ya fadi, sai yanzu ta tuna yaune fa wacan kaddararran Wanda zata aura zaizo.
Tabe baki tayi   "to saime akwai drinks da snack ai idan yazo saiyayi amfani dasu idan Kuma bazai iya ba kanshi yayiwa"
"Kutt to wlhy baki isa ba Dole mu shirya Masa special delicious food, bari naje na samu aunty rahma idan ke baza kiyi ba mu zamuyi"

Ko kula Zainab din batayi ba taci gabada chatting dinta.

Yana zaune a dakinsa, tunaninsa bai wuce dalilin dayasa su daddy suka shirya wannan maganar lokaci guda yake. "meyasa sukayi kodai akwai wani Abu a kasa ne, Amma ai yaji lokacin da Mamee tace Masa bazawara ce, kenan bazawara zai aura"

"Kowanne cikakken namiji Yana burin auran cikakkiyar budurwa Amma shi bazawara zai aura,"
Tabe baki yayi Yana tsaki kasa kasa. "toma mene na wani damuwa nida bazan sake da itaba ballan tana har wani Abu ya shiga tsakanin mu"
Da wannan tunanin yaci gabada sabgar sa.

Saida sukayi Isha Sannan suka shigo gidan.
Mamee tayi mamakin ganin Shaheed tunda yace mata dayayi magrib zaije wajan khadijan.

"Shaheed me kake nufi, karka cemin bakaje wajan yarinyar nanba"
"E..eh Mamee banje ba inaso sai gobe na dada hutawa,Kuma ma banasan zuwa ni kadai saina samu abokin rakiya"
"Shashancin banza kenan, me kake tunanin iyayenta zasuce wato kowa yasan baka damu da itaba kenan ko..,?
Ta fada tana kallonsa cikin ido.

"Ayi Masa afwa Mana kinsan bai saba ba, Amma yanzu ku tashi saimuje mu duka Kinga sai muma muyi zumunci ai, dama biki taba zuwaba" daddy yace.

"Shikenan ALHJ barina shirya". Mamee ta nufi uptairs.

Meerah ma da murnar ta tashige daki, yau zataga auntyn ta.

Shikuwa Shaheed kamar ya daga hannun ya fasa ihu haka yakejinsa., Amma babu yanda zaiyi Dole yaje.

Cikin kankanin lokaci suka shirya suka fito su duka suka nufi gidan uncle Abdulmutallib.

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now