🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
*🤱 MAHAIFIYATA 🤱*
_writing by_📚✍
*🌹 Ameena first lady🌹*
Watsapp number
_08112138112_
For comments.*Na sadaukar da wannan page din ga yan Mrs Sardauna fans group*✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
_page 4⃣1⃣ to 4⃣2⃣_
Saida Shaheed ya kwashe wasu mintina Yana mamakin zuwan khadija gidansu Dan kwana biyu bata ganshi ba, yanzu kam ya tabbatar wa kansa ba karamin soyayyar shi ce a zuciyar khadija ba.
Tabe baki yayi yace.
"Lallai kinada aiki akwai sauran rina a kaba tsakanin mu tukun" sannan ya fara neman layinta.Lokacin khadija kuwa gama wayarta kenan da salim, a zahiri soyayya tana nunawa salim Saidai zuciyarta tana can wajan tunanin Shaheed, bayan gama wayar tasu ne ta fara tunanin yaushe Shaheed zai dawo kenan,.
Kiran wayarta da akayi ne ya katse mata ragowar tunanin ta.
International number tagani sam bata kawowa kanta Shaheed bane.
Jin muryar Shaheed bakaramin dadi tajiba Amma saita ki amsa Masa.
"Afwan nayi laifi ko"
"Aa bakayi laifi ba infact ma ka kyauta sosai"
Murmushi mai sauti yayi Dan har khadija taji sautin fitar murmushin.
"Kiyimin uzuri pls tafiyar tazomin unexpected ne shiyasa"
"Naji to, ya Spain din"
"Klau Saidai banajin dadin zama bake anan"
"Dama haka zakace mana tunda katafi ko sallama babu, kuma baka nemeni a waya ba"
"Fasahar Kiran batazomin ba sai yau ai" Amma meyasa baki nemeni ba ke ko bakiyi missing Dina bane"
"Nabanyi ba" ta fada kamar da gaske.
Dariya ma tabashi har saida ya dara.
"Nazama abin dariya kawai Dan banyi kewar kaba"
"Aa ko daya, Amma na tambayeki mana"
"Inajinka ai"
"Yaushe kika koyi karya da tsara zance haka"
"Bangane ba, kana nufin baka yarda ba kome""Nayarda Saidai kuma bansan wacce khadijan ce taje har gida nemana ba, tayiwa Mamee karyar karbar assignment dinta zatayi"
Shiru khadija tayi kamar ruwa ya cinyeta Dan tagane tsokanar yakeyi.
"Ko kingane wacce khadijan ce" yakuma maimaita mata tambayar."Nima banganeta ba ta yiyu, tayi missing dinka na kwana biyu ne"
"Kenan kinyi missing Dina"
Shiru tayi duk kunya ta gama kamata.Daga haka suka zarce da hirar soyayya har kusan awa biyu...
Daga karshe khadija ta tambayeshi. "Yaushe zaku dawo ne".
"Sai zuwa jibi saboda sai yau za'a yi taron"
"To Allah yakaimu"
"Ameen"
"Mezan zomiki dashi"
"Bakomai fatana dai Allah yadawo min dakai lafiya"
"Bayan wannan fa"
"Shine kawai"
"To shikenan saina dawo dai"Sallama sukayi suka ajiye wayar.
Tun daga wannan ranar kullum suna makale a waya kamar karsu rabu.Kamar kullum yauma Shaheed yakira khadija suna waya.
"Gobe fa zaka dawo ko"
"Eh ashe kina lissafe"
"A'a kawai dai na tuna ne"
"Yayi kyau, kinki ki fadamin me kikeso gashi zan fita shopping yanzu"
"Shopping kuma"
"Eh mana kodai karnaje naji kin fada kamar bakyasan zuwan"
"A'a a dawo lafiya"
"To saina dawo"
Sukayi sallama.Tare suke da Zainab , saida suka gama wayar itada salim sannan tacewa Zainab "inajinki naga kamar da magana a bakinki"
"Akwai sosai ma kuwa""To fadi karta kashe ki"
"Khadija meyasa kikesan saka kanki cikin tension"
"Kamar Yaya bangane ba Zainab"
"Meyasa bazaki hakura da mutum daya daga cikin su biyu ba kinsan dai dole guda daya zaki aura ko"
"Eh nasani mana".
"To Amma kinkasa tsayar da hankalin ki waje daya, kardai ki manta da mungama karatu zancan aure za'a yimana, kuma lokacin dole daya zaki zaba yayinda dayan zaiga kinci amanar sa"
"Hakane Zainab kuma zanyi tunani inshallahu akan haka"
"Atoh dai"Yau jirgin su Shaheed ya sauka, Mamee da Meera ne sukaje dauko su daga airport, tunda ya sauko daga jirgi ya tabbatar yadawo Nigeria yabar kasa mai cike da ababan more rayuwa badan khadijan shi ba baiga abinda zai dawo dashi Nigeria ba.
Tofa kunji Shaheed Wai khadijan shi😏😏, kodai yakamu ne shima🤔🤔
Mamee ce tayi driving dinsu har gida.
Kamar akan kaya yake ku hutawa baigama yiba yace zai fita.
"Yaya Shaheed zan bika" Meera tace.
"Bazaki bini ba, sai shegen San yawo"
Ya fada Yana ficewa daga palourn.
Tabe baki Meera tayi.
"Saikace shima ba yawon zai fitaba" mugu kawai."Dan Kinga yafita ba" daddy yafada.
Part dinsa ya wuce yayi wanka ya shirya cikin wata black T-shirt da bakin jins, ya fesa ture kusan kala biyar ya daura agogon sa, sak yafito da ainihin kyaunsa.
Yau khadija da murna ta tashi saboda da wowar farin cikinta Shaheed,
Yafada mata da la'asar sun sauka hakan yasa tayi wanka tayi kwalliya kamar ba itaba tayi kyau sosai sannan ta saka wata riga da skirt na materials pink bakaramin kyau tayiba.
Karar wayarta ne yasa tatashi daga gaban mirror ta nufi wajan wayar.
Sunan datayiwa Salim saving tagani a fuskar screen din.
Wani haushi ne yakamata tayi tsaki sannan ta daga wayar.
"Ina jiranki.."
Tun kafin yakara ta tsayar dashi.
"Gani nan to" ta fada kamar Yana ganinta.
Salim baiyi mamaki ba saima murmushi dayayi kawai.
"Bari naje nayina sallami wancan nataccan kafin Shaheed yakaraso, Dan nasan Yana hanya"Ado bayero Mall yashiga ya jibgi siyayya sannan ya wuce jifatu nanma ya kwashi kaya, saida yashiga mota ya dauko wayar shi zai kirata saikuma ya fasa.
"Bari nayi surprise dinta" yafada Yana tayar da motar.________________
Horn yayi mai gadi ya bude Masa yashiga, tun kafin yayi parking ya lura da motar salim Saidai baikawo bakon khadija bane yayi tunanin bako sukayi.
Gaban khadija ne yafadi ganin motar Shaheed ya shigo tasan Shaheed da shegen kishi.
Ganin hankalin ta baya tareda shi yasa Salim waigawa wajan da take kallo.
Murza idanuwan shi yayi Dan gani yake kamar idanshi gizo yake nuna Masa Wai khadija da wani.
Fitowa yayi daga motar danya tabbatar da gaskiyar abinda yagani.
Lallai khadija ce kuma da wani a zaune.Jiyayi kafafunsa sun fara rawa nan da nan idanuwan shi suka zama ja zuciyar na harbawa.
Saurin rike motar yayi sannan yayiwa mai gadi alamu da hannu yazo.
"Gani yallabai, lafiya"
Nuni yakumayi Masa da hannu ya nuna Masa butt din motar.
Megadi Butt din ya kalla yaga kayane aciki.
Budewa ya fito da kayan sannan yace.
"Ciki za'a shiga dasu yallabai"
"Eh" kawai ya fizgo daga bakinshi ya furta dakyar.
Motar ya shiga ya fice da gudu.
Duk akan idon Salim da khadija.
Yanayin yadda ya fice yaba khadija tsoro, da Sauri ta fara neman layin nazeer.
Bugu biyu ya daga.
"Hello khadija ya akayi"
"Pls nazeer ga Shaheed nan hanyar gida daga gidan mu, kabiyo bayanshi Dan ranshi a bace yake ba cikin hankalin sa yakeba". Ta fada muryar ta na rawa.
"To shikenan bari nabishi nasan hanyar dazai bi karki damu"
"To" kawai tace Amma hankalin ta yagama tashi.
Salim kuwa sai yanzu ya fahimci dalilin dayasa hankalin khadija yakoma wajan tun dazu. Saboda haka yace.
"Zan tafi tunda naga kema naga hankalin ki a tashe yake, sai munyi waya" yace Yana barin wajan cikeda kishi.Kamar yadda khadija tafadawa nazeer da hanzari ya fice palour.
"Mama pls ki bani key din motar abbu"
"Lafiya tafada"
"Eh to idan nadawo kyaji" ya fadawa mahaifiyar tashi.
Fadamai wajan key din tayi yaje ya dauko.
Harzai fice ya kalli kaninshi affan dake zaune Yana jinsu.
"Affan zo mune ka dawo da motar"
"Tam" ya fada Yana mikewa.Hanyar dayasan Shaheed zaibi nan yabi gudu shima yakeyi aikuwa ya hango motar Shaheed a gefe mutane sun kewaye wajan.
"Ya Salam" ya furta a hankali.
Parking yayi yakarasa gun.
Shaheed na cikin motar kanshi kife da akan matukin motar.
"Subhanallahi aiya suma".
Nazeer ya fada.
Dakyar mutanan wajan suka matsa yashiga motar sannan ya kwantar da Shaheed a baya.
Tareda wani Dan sanda suka nufi hospital dake kusa da wajan.