33

127 13 0
                                    

🌈 *_kainuwa Writers association_*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

 
         *_🤱 MAHAIFIYATA 🤱_*

_By_

'''🌹Ameena first lady🌹'''

I Dedicated this page to my sweet brother
'''Shafi'u Musa  {shafam}'''💐💐💐

_page 6⃣3⃣ to 6⃣4⃣_

....da dare haka Mamee ta tilas ta shi yaci abinci data shirya Masa kala kala sai daukar shi da hira sukeyi Dan ya sake Amma ko amsa baya basu Saidai eh ko a'a, dare na rabawa ya nufi part dinsa ya kwanta...

Zamu iya cewa yau khadija tayi kwanan farin ciki sakamakon yadda ta kasance da mahaifiyarta daran jiya, saboda yau bata tashi da wuri ba, Zainab ce ta tashe ta, bayan tayi salla Aunty Rahma ta shigo ta hada mata ruwan wanka, dakyar aka samu ta shiga tayi wankan, tana fitowa taga Aunty Rahma da Zainab har sun hada mata kayan ta da zata tafi dasu..

Mommy ce ta shigo dakin hannunta rike da wata bakar jaka Mai kyan gaske, har kasa su khadija suka tsugunna suka gaida ta, ta amsa tana janyo hannun Zainab Dana khadijan.
A bakin bed suka zauna ta bude jakar dake hannunta saiga dogayan riguna masu shegen tsada da kyau.
Guda uku uku taba khadija da Zainab.
"Tun zuwana Hajj nayo Miki tsarabar su saboda nasan ki dasan dogayan riguna" sannan ta fito da  Dan kit cikinsa dauke da watch da chain na gold.
"Wannan shine kyautata na murnar zagayowar ranar haihuwar ki, Wanda na kwana cikin zubar da hawayen tausaya miki dalilin halin Dana sakaki a ranar".
Daidai lokacin Aunty Rahma ta shigo dakin tana fadin "to Mommy da daughter zamu wuce yanzu"
Hawayen farin ciki ne ya zubo ma khadija tafara magana cikin rauni da rawar murya. "lokacin da nakeso na kasance tare da ke saigashi kaddara tasa dole zanyi nisa dake mommy.."
Kuka ne yaci karfin ta, Mommy ta janyo ta jikinta tana lallashinta.  "Karki damu khadija zan dinga zuwa ganinki Koda yaushe, kuma kema zaki dinga zuwa ai, saboda haka ki daina kukan ya isa haka"

A haka suka samu tayi shiru, suka fita gaba dayansu.

Uncle harya zuba kayanta a booth, itama Zainab tafara rigimar saita bisu bazata iya rabuwa da khadija ba.
Duk yadda suka so ta hakura ki tayi Saida Abba yace tayi hakuri da zarar khadija ta kara samun sauki zata dawo gidansu suci gabada zuwa makaranta tare sannan ta hakura driver ya jata suka tafi suma su uncle suka wuce.....

Kwana biyu tsakani daddy ya gama Shirin tafiyar Shaheed, Dan Shaheed din ya zame musu wani kamar mara lafiya Wanda baya magana sai Dole,. Yau ta kama tafiyar Shaheed Spain tun safe Yana part dinsa har saida Dad ya same shi yayi Masa Nasiha sosai sannan ya taimaka Masa ya shirya suka fito tare.

Mamee itama Nasiha tayi masa, Meera kam sai kuka takeyi zata rabu da yayanta bata San ranar sake haduwar suba.

Su duka suka tafi kaishi airport saboda karatowar lokaci, suna zuwa airport ya fito, wayar shi ya ciro ya bude ya cire layikan gaba daya a take ya karya su Dan a wajan shi basu da wani amfani tunda baya magana da rayuwar shi wato khadija a cewar shi.

Har lokacin tashin su ya zo sannan yayu musu sallama suna kallo ya shiga plane suna daga Masa hannu.
Yana zama yaji kansa ya fara ciwo musamman daya tuna shikenan ya rabuda dukkan farin cikinsa ya rabuda abinda bazai taba samun kamar saba, Dan yasan yanzu babu abinda zaisa khadija tayi Koda tunanin sa musamman idan ta tuna abinda yayi mata.
Su Dad suna ganin shigar Shaheed sannan suka shiga mota suka tafi.
2:55 daidai jirgin su Shaheed ya lulaka sararin samaniya.✈✈✈

Saidai muce Allah ya saukesu lafiya🤨🤨🤨🤨

Tunda sukaje khadija ta shige dakinta bata fito ba, har yamma komai a ciki take, Aunty Rahma tashigo ta sameta kwance luf, zama tayi gefenta sannan tafara yimata magana cikin nutsuwa.
"Haba khadija, Meyasa kikeso saikin tashi hankalin kowa, hakuri zakiyi ki yarda da kaddara yadda tazo Miki, duk wani hali da zaki kasance baikai Allah ya isan da mukayiwa Wanda yayi Miki ba, bafa kanki aka fara fyade ba akwai yammata da yawa wadanda nasu yafi naki muni kuma basuda gata kamar ke, Kinga kenan hakuri yazama Miki Dole Saidai muce Allah ya tonawa Dan iskan..."

Da khadija ta dakatar da ita, Dan bazata iya jin munanan kalamai akan Shaheed ba, duk da yadda takejin tsanar sa da abinda yayi mata.
"Aunty ba wannan ne yake sani kuka ba, kullum tunani na shine yadda zanga ranar da mahaifiyata zata karbe ni a matsayin yarta, addu'a ta kullum Allah ya nuna min wannan ranar dukda bansan yadda zata zomin ba, saigashi tazomin cikin bakin yanayin Wanda yayi sanadiyyar barina mahaifata..."

Sosai kukan yaci karfinta, Aunty Rahma ce ta samu tayi shiru dakyar sannan suka fito taci abinci.

Allah ya sakawa iyayenmu da Alkhairi Ameen👏👏👏👏

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now