🌈 *_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
'''{United we stand and succeed; Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation
*_🤱 MAHAIFIYATA 🤱_*
_By_📚✍
*🌹 Ameena first lady🌹*
_page 7⃣5⃣ to 7⃣6⃣_
Abba ya tausaya mata Saidai babu yadda zasuyi tunda kaddara ta riga fata, saboda haka yaci gabada bata hakuri tareda nasiha da Kuma fatan alkhairi.
A daki ma Sam khadija takijin lallashi Zainab harta gaji ta fara yimata nasiha akan tayi hakuri kila wannan auran yazama shine alkhairi a wajansu gabaki daya.
"Zainab bazaki gane irin Halin danake ciki bane, shikenan ni rayuwata a kaddara zata kare da farko halin mahaifiyata sannan na biyu na rasa abinda kowacce mace take tutiya dashi yanzu Kuma auran Dole an rabani da Wanda nake so yake Sona tsakani da Allah..". Ta sake fashewa da kuka.
Cikin sigar lallashi Zainab tace. "kiyi hakuri khadija nafi kowa sanin soyayyar da kikewa Khalid, Amma hakuri zakuyi daga ke harshi"
"Zainab wanne irin hakuri ne kuke ta famar cewa nayi bayan Wanda nayi a baya, naji zan auri waccan Wanda kukeso na aura Amma kusani bazan taba jin soyayyar shi a Raina ba hasali ma na tsaneshi sakamakon ta Dalilin kaddarar auran ta rabani da Khalid Kuma wlhy saiyayi daya sanin aure na dayayi..."
Ta fada tana goge hawayenta.
Zainab tayi mamakin jin kalaman da khadija tayi Saidai tabar hakan a matsayin bacin rai dakuma zafin rabuwa da masoyi.Abu kamar wasa saigashi Khalid ya kwana biyu a hospital cikin matsananciyar rashin lafiya, hankalin iyayenshi ya tashi sosai saboda haka ba shiri mahaifin Khalid ya nufi gidan su khadija.
Bayan yagama sanar dasu sun hakura dansu ya auri khadijan, Abba yace Sam baisan zancan ba su harsun amshi kudin wani Kuma aure yana nan daram basu sauya shi ba.
Guiwa a sale mahaifin Khalid yakoma gida ya sanar dasu, Dole suka dauki hakuri sukaci gabada jinyar Khalid din.Khadija taci kuka jin amsar da Abba yabasu, ga tausayin Khalid datake ji.
Daddy kam tunda yakoma gida ya sanar wa da Mamee komai itama taji dadin hakan dama burinta a rayuwa bai wuce taga auran yaranta ba, saigashi Allah ya kawo lokacin ta farar daya.
Suma shiri sosai sukeyi harda Meera wacce take ta faman daga kan yayanta zaiyi aure,. Duk wani shiri suma sun farayi har akwatuna Mamee tabada odar su musamman ana jibi biki za'a Kai gidansu khadijan.Gyara sosai mommy tasa akeyi musu dukda khadija da kuka take bari anayi Zainab kam sai wani murna takeyi duk tagama gayyato kawayen su, soyayya da Nazeer kam kullum sai sunyi night call har khadija ta daina jin haushin su.
Gobe Shaheed yayo waya zai dawo hutu, Dan sosai ya matsu ya dawo Nigeria, su Mamee sai shirye shiryen dawowar tashi sukeyi sosai,. Mamee da kanta ta Kira mamansu Zainab ta turo mata number khadija,
Khadija na zaune a gefen bed ta tallabe kuncin ta tana ta tunanin yadda zatayi rayuwa a gidan wani ba Khalid ba, karar wayarta taji hakan yasa ta katse tunanin nata ta dauko wayar. New contact tagani har zata ajiye saikuma ta daga hade da yin sallama.
Amsawa Mamee tayi tareda fadin. "ya hidimar biki Kuma yata.."?
Sai yanzu khadija ta gane mahaifiyar Wanda zata aura ce shiyasa tayi saurin kakalo murmushi kamar tana ganinta.
Cikeda kunya ta amsa mata. "alhamdulillahi Mamee,."
"Yauwa to dama nace gobe angon naki zai dawo, shiyasa nace bari na fada Miki tunda koni sai yau nasamu number ki"
"To Mamee Allah ya kawo lafiya Kuma Allah yakaimu"
"Ameen daughter"
Sallama Mamee tayi mata tanajin soyayyar yarinyar ta farat daya a ranta.Zama khadija takuma yi tareda tabe baki, dai dai Zainab ta shigo dakin tana fadin. "anan kika boye kika barni ni kadai a palour Ina famada A'i.. " zama tayi gefen khadijan tana tambayar. "lafiya naganki kamar bakida lafiya..?
"Babu komai Zainab, yanzu mahaifiyar Wanda zan aura takira ni Wai gobe zai dawo.."
"To shine kuma kike damuwa keda zakiyi murna mijinki zai dawo, sannan makiya zasuji kunya.."
"Hakane Amma narasa dalilin dayasa banajin Ina murna"
"To ai addu'a zakiyi Allah yasa ganin nasa yasa ku dai daita"
"Ameen to"
Sannan suka fita palour tare.Yau tun safe Mamee take cooking kala kala na tarbar Shaheed, takasa samun zama tsabar aikace aikace.
Sai yamma jirgin su Shaheed zai sauka saboda haka Daddy da kansa shida Meera suka tafi dauko shi Mamee kam bataje ba saboda ayyuka da sukayi mata yawa.5:45pm dai dai jirgin ya sauka mutane suka fara takowa a hankali suna saukowa.
Idanuwana ne suka sauka kan wani kyakkyawan matashi fari tarr har daukar ido yake, sannu a hankali yake tako matattakalar benen Yana saukowa saikace Wanda baiso fitowa ba, sanye yake cikin wani farin yadi kal, tsintsiyar hannun shi daure da wani farin agogo daya amshi fatar hannunshi wacce suma ta kwanta luff, idanuwan shi sanye da farin glass sai wani hade fuska yake kamar baiso zuwan nashi Nigeria ba.
Harya gama saukowa Yana duban motocin dake wajan kozaiga drivern dayazo daukar sa.
Rungume shi yaji anyi ta baya ana fadin. "welcome to Nigeria Yaya Shaheed.."
Tun kafin ya waigo yagane Meera ce tayi Masa irin wannan rungumar.
Fuskar shi dauke da murmushi ya waigo,. Murmushin sane ya fadada ganin harda Daddyn sa suke tare.
Rungume daddy shima yayi cikeda murna ganinsu lafiya.
Waige ya farayi neman mameen shi Amma saiya ga babu ita.
"Where's my sweet Mom..". Ya fada Yana kallon Daddy.
"Mameenka tana gida, yanzu dai shiga mu tafi hankalin ta Yana nan ta kagara taga yaronta"
Basu bata lokaci ba suka nufi gida suna ta hira a hanya.
Meera ce taketa faman zuba ita kadai shidai Shaheed Saidai kawai yayi murmushi danya fara gajiya da surutun ta.Mamaee tayi tayi murna sosai musamman yadda taga Dan nata yayi kiba yakara kyau fatar shi tayi fresh babu alamun Yana cikin damuwa haryanzu.
Saida suka gama murnar tasu sannan ya tashi ya nufi part dinsa, wanka yayi ya shirya sannan ya nufo palour su tafi masallaci.A palour kuwa Mamee ce ta kalli Alhj attahir cikin nutsuwa. "Alhj kaga yadda Shaheed ya sauya kamar bashi ba,. Ni nafara jin tsoron karya ki yadda da wannan maganar fa.."
Murmushi Alhaji attahir yayi. "Ki daina tunanin Shaheed bazai yadda ba, Saidai idan bamu muka haife shiba, Kuma a yau zan fada Masa dolen sa ya yarda ma.."
Har Mamee zata Kuma magana taji shigowar Shaheed tayi shiru.
"A'a Shaheed harka fito"
"Yes Dad"
"To shikenan jirani yanzu zan fito". Yafada Yana haurawa sama.Tare suka tafi masallacin, har Saida sukayi sallar Isha sannan suka shigo cikin gidan.
Kafin su shigo Mamee tuni tayi preparing din dinning table, suna shigowa suka fara dinner harda Meera.Har goman dare suna hira, Dad ne yayi gyaran murya ya kalli Shaheed.
"Shaheed saura shekara nawa ka kammala karatun naka ne.."?.
" 2years remaining". Ya bashi amsa a takaice.
"Ok hakan yayi, Saidai Kuma zakayi aure Kuma baka gama karatun naka ba kenan"
"Aure Kuma Daddy, ni banida ra'ayin aure yanzu Sam, Amma daddy meyasa kayimin wannan tambayar""Shaheed inaso ka bani aran hankalin ka sannan ka saurareni dakyau, Kuma kayimin alkawarin zakiyimin biyayya akan duk abinda nazo maka dashi a yanzu"
Hankalin sa ya mayar kan mahaifin nasa Yana San sanin dalilin dayasa yaga duk jikinsu yayi sanyi har Meera dake gefensu.
"Shaheed na nemaka auran yarinyar abokina, nasan bazaka taba bani kunya ba Kuma saura kwana shida bikin banaso hankalin ka ya tashine shiyasa ban fada maka ba sai nabari sai yau idan ka dawo, Ina fatan bazan samu matsala daga gareka ba.."
A zabure a Mike cikin kaduwa da tashin hankali, jijiyoyin kanshi harsun tashi jikinshi ya fara rawa.
"Aure.. Kuma Daddy nanda kwana shida"
"Kwarai kuwa Shaheed"
Mamaki ne yakama su ganin Shaheed a rike kafafun daddy Yana Masa magiya.
"Dan Allah daddy karka hukunta ni da wannan mummunan hukuncin idan laifi nayi maka, kayi hakuri nayi muku alkawarin zan koma Spain a gobe idan kuna tunanin zan jawo muku wata maganar ne.."
"Wannan ba maganar hakuri bane Shaheed, tayaya zan tunkari iyayan yarinyar nace na janye maganata."
"Kayi hakuri daddy gaskiya bazan iya auran wacce kuka zabamin ba, saboda bana Santa khadija kadaice wacce nakeso kuma idan ban aureta ba babu wata ya mace dazan iya auranta....."
Ran daddy ne ya baci jin kalaman Shaheed, a fusace ya mike, saijin saukar mari Shaheed yayi a kuncin sa.
Mamee da Meera ma a firgice suka tashi Dan basu taba tsammani daddy zai iya Marin Shaheed ba.
Daddy na huci yace. "ni kake fadawa bazaka auri yarinyar dana zaba maka ba, harkake fadamin zancan banza da wofi, to wlhy Saidai ka mutu bayan an daura auran ita Kuma ka kasheta idan an kawo maka ita banza shashasha kawai.."
Daddy ya fice cikeda taikaici da bacin rai.......