51

233 15 0
                                    

*🤱 MAHAIFIYATA 🤱*


*_🌈 KAINUWA WRITERS ✍🏻ASSOCIATION🤝🏻_*

'''{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

_By_📖✍🏻

*_Ameena Musa_*

*🌹 Ameena firstlady🌹*

_page9⃣9⃣ to 1⃣0⃣0⃣_

Da wannan tunanin ta shirya ta fice, kai tsaye gida ta nufa, mommy tayi mamakin ganinta sosai amma saita bari abbanta ya dawo tukun suji ko lpy..

A hankali yake driving cikeda tunani iri iri, meyasa Khadijah tayi masa haka meyasa ta Aure shi bata san shi sai dan ta azabtar dashi, meyasa kuma takasa faɗin gaskiya sai yanzu.
Harya ƙarasa police station, sannan yayi parking ɗin motar shi ya fito.

Few minutes later, sannan wani saurayi sanye da kayan police ya fito, Tunda ya hango shaheed yafara murmushi sannan shima ya mayar masa da murmushin suka gaisa.

"Ai da ka shigo kawai kai tsaye"
"Ok zamu iya shiga yanzu ai"
Suna shiga office ɗin, ya ɗauko masa takardar case ɗin,
"Ga takardar, hannu kawai zan saka mu miƙa case ɗin sama"
"No Yusuf ba wannan ne ya kawoni ba, nazo ne abani belin su"
"What kana nufin ka hakura kenan"
"Yes that's what I mean"
"Shikenan Ina zuwa" Yusuf ya fada yana barin office ɗin.
Bai daɗe ba sosai sai gashi biyeda su biyu a bayan shi.
Shaheed bai ɗago kai ba yace "pls kadan bamu wuri zanyi magana dasu"
"Ok" sannan ya fice.

Saida yakusa second uku sannan ya ɗago idanuwan shi ya kalle su, sun bashi tausayi sosai amma sam bai nuna a fuska ba, saima haɗe fuska ya sake yi yana kawar da kai gefe.
"Zaku iya yin hakuri, idan kuma kunga bazaku iya ba, to saiku mayar da report ya dawo kaina wannan kuma ruwan ku ne"
Ya tashi zai fice.
"Shaheed..". Usman ya kira sunan shi a tausa sashe.
Tsayawa yayi amma bai jiyo ba,.

Har gaban shi Usman yazo ya tsaya sannan yafara magana a hankali.
"Kamar yadda kace zamu iya mayar da report a kanka, kwarai kuwa gaskiya ka faɗa saidai na Ni Usman bana fatan ranar da zan kai babban abokina shaheed ƙara ba, na fahimci abokina kuma na yarda dashi saidai shaheed bai fahimci abokin sa Usman ba baikuma yarda dashi dashiba"

Sosai zuciyar shaheed ta karaya yasani bai taɓa abota da mutum kamar yadda yayi da Usman ba saidai sharrin zuciya dakuma zargi suka sa ya manta da abotar tasu.
Rungume shi yayi kamar suyi kuka, sun jima a haka sannan salim yayi gyaran Murya suka jiyo suna kallon shi..
Dauke da murmushi fuskar shi shima yace "shaheed ba laifin ka bane, *_FURUCI_* nane yajamin karshe nayi dana sani, nima soyayyar Khadijah ce ta rufemin idanu har nayi wannan furucin amma daga yau zan kiyaye gaba, Saboda haka nina hakura shaheed ko nine zanyi abin dayafi haka akan matata"

Shaheed yaji daɗi sosai dayaji duk basu rike shiba, ba bata lokaci aka bashi belin su ya dauke su a motar shi.

Salim yafara saukewa, iyayen shi har kukan murna sukayi sannan yakai Usman gida, nan ma ko kaɗan umman Usman bata nuna komai ba saima godiya tayi masa tareda nasiha sosai.

Cikin farin ciki ya nufi gida, dama wannan dalilin ne kaɗai yasa yake hukunta Khadijah da haka amma yanzu kam komai ya wuce.

Saida yayi parking sannan ya nufi main palour, ganin bata palour ya nufi ɗakin ta nan ma gani yayi bata ciki kuma da alamu bata cikin bathroom, duk mamaki yagama kama shi ina Khadijah ta tafi kodai gidan zainab daya hanata ta tafi, "wato wannan yarinyar bata jin magana ko"
Ya faɗa yana huci haushi da takaici, sannan ya sake ficewa ya nufi gidan su....

MAHAIFIYATAWhere stories live. Discover now