01...

837 37 2
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI...!*
_{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA
*Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah madaukakin sarki. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam ina ƙara godiya ga Allah madaukakin sarki da ya bani baiwa da ikon rubuta wannan littafi mai suna ZAZZAFAN KISHI sabon salo Ubangiji ya sanya 'yan uwa musulmi su amfana da faɗakarwa da ke cikinsa, kuskuren da ke ciki kuma ubangiji ya yafe mana*

*Special thanks to my one & only Aunty sis thank you so much for your love & kindness*

_Na sadaukar da wannan littafi ga Zarah Bb alkhairi Allah ya kai miki a duk inda kike na gode kwarai da ƙaunarki gareni, Allahu yabar zumunci_

01....

Cikin Sanɗa ta tura Gate ɗin shigowa gidansu sai da ta fara leƙa tsakar gida ta ga Mama bata nan tana ɗaki muradinta ta shige ɗakinta kafin Wani ido ya ganta batasan cewa Mama tana nan tsaye a jikin ƙofar ɗakinta labulle da ya kare ta ne ya hanata ganinta, tana daff da isa ƙofar ɗakinta ta jin an kira sunanta cikin tsawa da sai da gabanta yai mummunan faɗuwa "Ke! Jeeddah zo nan munafuka yarinya wato ke har abada ba za a faɗa ki ji ba?" duk abinda na faɗa miki akan ki rabuda Bilal ta bayan kunne ki yake bi ya fita to wallahi kodai ki rabuda shi ta ruwan sanyi ko kuma jikinki ne zai gaya miki sakarya kawai.
Haɗe rai Jeeddah tayi ko kaɗan bataso ta ji Mama ta ambata mata kalmar rabuwa da Bilal. Ko yanzu jin maganganun da take faɗa jin su take yi tamkar ana yayafa mata tafasasshen ruwan zafi a sassan jiki sai wani cuno baki gaba take yi gami da gunguni ƙasa-ƙasa wanda ita kaɗai ke jin abinda take faɗa.
"Da za ki ɗauke shawara ta Mama da kin daina yi wa Jeeddah rantsuwa don ni fa gani nake yi tamkar rantsuwarki ƙara zurfafa mata soyayyar Bilal shattima take yi.
Cewar Khairat wacce ta fito daga ɗaki.
Kafin Mama tai magana Jeeddah ta tasowa Khairat tamkar za ta kifa mata mari "Tou baƙar munafuka algunguma ina ruwanki zuga-zugi wutar maƙera ke kam kin shiga uku Khairat ace ba ki da sana'a sai ta zugi, da shiga abinda bai shafe ki ba kin dai ji haushi wallahi.
Jeeddah ta faɗa tana gallawa Khairat muguwar harara.
Cike da takaici Mama ta saki labulle ta nufo wajen ta gadan-gadan, gani haka yasa Jeeddah ta ɓalla da gudu ta koma bakin gate tasan ba abu mai wuya bane Mama ta rufe ta da mugun duka.
Mama tai kwafa gami da furta "ashe karyar rashin kunya ki ke yi da ki tsaya ki ga yadda zan haɗa miki majina da jini sai na gurje miki baki nan naki mai tsiwa da rashin kunyar tsiya.
Tintsirewa da dariya Khairat tayi tana faɗin "Mama ki bi ta wallahi za ta iya komawa gidansu Bilal ta kwana kisan dai halinta ba wadatatce hankali ne da ita ba.
"Mtsss.... Mama ta ja tsaki tare da nufar kitchen tana faɗin "Ta daɗe ba ta koma ba ai na fi so ta koma ɗin hakan zai ƙara tabbatar min da da bata ɗauke ni a bakin komai ba. Duk abin da take yi kar ta fasa ta ci-gaba Allah ya kawo min Ɗa nan shi kaɗai ne zai saita ta.
Sosai Khairat take kwasar dariya abinta saboda tasan karyar Jeddah ta ƙare muddin Mama ta faɗawa Ya Kabeer ta sake zuwa gidansu Bilal mai kwatar da hannunshi sai Allah saboda ko jiya sai da ya zaunar da ita ya kashe mata gargaɗi akan ta daina zuwa gidansu Bilal shattima, don ba mutuncinta bane tana budurwa ta dinga bin saurayi gidansu amma da yake kunne ƙashi ne da ita sai da taga Mama ta fita asibiti dubiya, ta fake da zuwa kitso wajen A'isha shattima ƙanwar Bilal wacce ta kasance ƙawarta.
Khairat ta juya ta koma ɗaki dama tana kallo BB naija ta ji yo faɗan mama shine ta fito kar ayi ba ita.
Da zarrar Mama ta hana Jeeddah fita zance wurin Bilal sai kawai ya tsira fushi ya ɗauke ƙafa, ita kuma rasa kunya beran toka ta ɗibi ƙafafuwa ba kunya balle tsoron Allah ta bi shi gidansu, da suna ta je wajen A'isha daga nan ta rarrashe abinta. Shekarar su shidda su na zuba soyayya ta fitar hankali kawo yanzu Bilal bai ajiye ko kwarar bulo guda ɗaya da suna gini ba. Idan kuma aka ce ya turo da magabatasa sai buge da cewa a ƙara mishi lokaci ya fara gini saboda ya fiso ya fara gina gidan da za su zauna, bayaso zama gidan haya kasancewar Jeeddah da Khairat sun kammala NCE Ya Kabeer ya samar musu da koyarwa a secondary School sau uku Jeeddah tana kwasar adashe 100k a ɓoye wanda suke yi a school ɗin da take teaching tana ba Bilal Shattima ba tare da gida an sani ba, da suna fara koda buga musu bulo ne, amma sai goga naku ya darganta ƙudin. Gaba ɗaya salary ta akanshi yake ƙarewa wani abinda zai ƙara ba ku haushi da takaici da zarrar ƙudi sun shiga hannunsa sai ka nemi su ka rasa shi kanshi Idan ka titse shi ba zai iya faɗa maka takamamin abinda yai da su ba. Sai kace mai caca ba kuma caca yake yi ba irinsa ne bahaushe yai wa laƙabi da mai rariya hannu.
Gashi dai ba aiki fari balle na baƙi barshi dai da tsalla wanka ya ji gogagu kaya ya fita zaman majalisa har kwatance sa ake yi a unguwa wajen iya wanka da gayu bashi da wani aiki da ya wuce ya koma majalisa ya zauna suna gardamar siyasa ko ta kwallon ƙafa da irin-irinsa marasa abin yi duk wani shige da fice na mutane unguwa akan idanuwansu. Duk yadda zan misalta muku lalacewa da mutuwar zuciya Bilal shattima ba za ku gane nan take ba dole sai na nusa da ku cikin ainihin tarihin rayuwarsa.
A karo na biyu da Jeeddah ta ƙara leƙowa bata ga Mama a tsakar gida ba tana kitchen tai sauri ta shige ɗakinsu tana zuwa ta jefawa Khairat jakkarta mai ɗauke da kayan kitso sai akan fuskar Khairat wacce ta shagala matuƙa da kallon da take yi akan akwatin talabijin robar man kitso da ke ciki jakkar ta bugi goshinta "ouchhh.....miye haka ba ki da hankali ne da za ki yi min irin wannan jifa da kin fasa min goshi fa?"
Khairat ta faɗa rai ɓace tana shafar goshinta.
"Ai so nayi na fasa goshin naki baƙar munafuka, wacce bata ɓoye sirri duk yanda nai sirri da ke sai kin faɗawa Mama.
Jeeddah ta faɗa tana wulgawa Khairat harara.
"Kar ki sake kirana da munafuka.
"Me za ki yi idan na ƙara?"
Jeeddah tai magana gami da tunƙarar Khairat da ke zaune akan gado.
"Sai na faɗawa Ya Kabeer yau ma kin je zance wuri Bilal Shattima.
Sosai ta tsorata da jin furucin Khairat cikin kwantar da murya ta shiga ba ta haƙuri "kar ki yi min haka Khairat kinsan Ya Kabeer ba hankali ne dashi ba zai iya karya min ƙafa ko hannu Don Allah ki rufa min asiri na tuba ba zan ƙara zuwa gidan nasu ba yau ma kitso naje kema kinsan da haka.
Dariyar mugunta Khairat tayi gami da faɗin "A'a bansan ni ba kar ki lauye ni ki ja min laifinki ya shafe ni.
"Ki ji tsoron Allah Khairat kafin na fita gidanan sai da na faɗa miki kitso zan je.
"Amma ai ba gidansu Bilal ki ka ce min za ki je ba, to ubanme ya kwashe ƙafafuwanki ya kai ki can, kafin ki zubar da mutuncin gidanan gara Ya Kabeer ya karya ki ko za ki dawo cikin hankalinki, kin ɗauki soyayyar duniya kin ɗora wa Bilal shattima sai kace shi kaɗai ne ɗa namiji, ga masu sonki da gaskiya wanda za su aure ki amma kin bi kin maƙalewa marar aiki yi
ki yi wa kanki faɗa. Wallahi na rasa me za ki tsinta a jikinsa ga muni ga uban talauci..
"Ke dallah ya isa banaso shisshigi a al'amurrana in banda munafuci da tsugudidi ina ruwanki da muni da rashin aikinsa To ni a haka nake sonsa kyawawan da masu kuɗi kuma nace akai kasuwa bana yi.
Jeeddah ta katse ta cikin tsawa da tada harshe, ita ma Khairat cikin fusata ta tasowa Jeeddah, kamar za ta ɗauke ta da mari cikin ƙonar zuciya take faɗin
"Ni Ko ke da ruwa har da tsaki banda daƙiƙanci irin naki har kin manta da rashin aiki nasa ne ya janyo min har yanzu nake zaune a gidan ubana da tuni na tsofa a ɗakin mijina, watakila ma da yanzu na haifa masa ɗa ko ɗiya haka kawai Baba ya kafe akan ba za min aure na bar ki a gida ba al'hali ke ce da kanki ki ka zaɓi zaman gidan.
"To tun da kina gani an miki ba daidai ba kuma kin matsu aure ki ke so sai ki tashi ki tafi gidan Jameel ɗin ai ana haihuwa ko ba aure kin ga shikenan sauwaƙe ramar kaza sai ki fara haifa masa 'ya'yansa.
Jeeddah ta faɗa cike da zallar sheƙiyanci.
"Kam ubanan! Lallai Jeeddah sai yau na tabbatar da bakya ƙauna ta, mu fito ciki ɗaya amma kina min fatar haihuwa ba aure.
Khairat ta faɗa fuskar ta ɗauke da zallar mamaki furucin Jeeddah akanta.
Taɓe baki Jeeddah tayi gami da yarfe hannu ta ce "Me kuma ya kawo zance rashin ƙauna, ai ƙaunar ce ma ta jawo na ba ki wannan shawarar da ki ta zama gida kina tsofewa kamar ni ba gara ki haifawa Jameel 'ya'yansa ba.
Girgiza kai Khairat tayi ta tabbata idan bata rarrashe zuciyarta ba ta kai ta nesa yanzu nan za su kaure da dambe dama sun saba da kyar su yi sati ɗaya currr ba tare da sun yi dambace ba har abin ya zame musu jiki.
"Wannan dai mummunan fata kike min kuma in-sha-Allah a kanki zai ƙar....
Kafin Khairat ta ƙarasa Jeeddah tai kukan kura ta dafe mata baki tana faɗin "shegiya yarinya haɗiye saura kalaman ki su koma cikinki don wallahi ba zan bari ki ƙarasa faɗarsu ba ki lalata min rayuwa bayan nasan wannan shegen bakin naki ɗauke yake da kambu baka.
Khairat ta shiga ƙoƙarin cire hannun Jeeddah daga bakinta yayin da Jeeddah sai ƙara danne bakinta nata take yi da dukkan ƙarfinta kokawa ta kaure a tsakaninsu Khairat ta dana mata shegen cizo ga tafin hannu babu shiri ta sake ta, tana yarfe hannu. Dariya Khairat ta kyalkyale da ita tana kallon Jeeddah da ke kallon shatin haƙorata da suka fito raɗau-raɗau ga tafin hannunta ta ce "How market 'yar uwa?"
Ta ƙarasa magana tana dariya a fusace Jeeddah tayo kanta tana faɗin "Wallahi sai na rama shegiya mayya kawai.
Khairat ta rugu da gudu ta fice daga ɗakin tana cewa "ai ke ce babbar mayya da ta maƙalewa ƙato da bai da abin aurenta.
Da gudu Jeeddah ta bi bayanta a tsakar gida suka tadda Mama tana haɗa zobo ta na sayarwa, Khairat ta nufi bayanta ta ɓoye tasan duk rashin kunyar Jeeddah ba za ta dake ta a bayan Mama ba.
"Mama wallahi ki shiga tsakanina da Khairat nagaji da wulaƙanci da take min a gidanan.
Jeeddah ta faɗa cikin marairaice murya kamar wata mutuniyar kirki.
Kallon uku saura kwabo Mama tai mata gami da taɓe baki kana ta nuna ta da ƙaton ludayin da take jujjuya zobo dashi tana faɗin "Ke arrr...ko kunya ba kya ji ace ƙanwarki, ita ce abokiyar faɗanki gaba ɗaya kin jawo ta renaki bata gani girmanki.
"Mama don taga kina goyon bayanta ne shiyasa take min abin da ta ga dama amma ba komai na rantse duk ranar da ta kaini bango sai kin yi jinyarta don dukan akawo wuƙa zan mata.
Jeeddah ta katse Mama tana matsar kwalla.
"Mtsss....!
Mama ta ja tsaki tana mai ci-gaba da jujjuya zobonta tana faɗin "Ai Khairat ba raguwa bace da za ta zauna ki yi mata dukan da za ta kwanta jinya idan ki ka sake kika kaini bango yanzu-yanzu nan sai na ware muku fili na tabbata ba za ki ɗibi komai a jikinta ba.
"Haba.... Mama miyasa ki ke min haka?" wallahi in Baba ya dawo sai na faɗa masa irin cin kashin da ake min a gidanan.
Jeeddah ta faɗa cikin sigar shagwaɓa gami da bubbuga ƙafafuwanta akan floor. Yayin da Khairat sai gwalo take mata abinda ya ƙara harzuƙa ta kenan tai kwafa gami da nuna Khairat da yatsa tana cizon leɓɓe.
Mama ta ɗago ta dube ta ta taɓe baki ta ce "uhmm....shi ma Baban naki ya gaji da zama da ke da za ki yi wa kanki ƙiyamullaili ki amince da auren Haidar da ya fi miki zaman jiran wannan gantalallen Yaro mai mugun baƙi kamar zunubi marar mafaɗi yana ɓata miki lokaci a banza sa'o'i duk su na ɗakin mazaje su, daga mai haihuwa ɗaya sai mai biyu ke ga ki zaune a gida kina zaman jiran tsammani.
Kuka Jeeddah ta fashe dashi irin mai sautin nan ta juya rai ɓace ta shige ɗakinta.
"Je ki mana ki fi ruwa gudu sakarya kawai ana nuna miki Annabi kina runtse idanuwa.
Mama tai magana cike da takaici.
Duk duniya ba abinda Jeeddah ta tsana yake kuma saurin saka ta kuka bai wuce ta ji Mama tana kushe Bilal ɗinta ba. Da ka zagi Bilal ko ka aibanta shi gara kai ta lafta mata bulala tun dare har wayewar gari saboda Ita kaɗai tasan irin sirri da ke tattare da zaɓe shi da tayi a cikin dubban maza Bilal shi ne irin mijin da take so ta aura dashi kaɗai take jin za ta iya rayuwar aure muddin aka hanata aure shi sai dai ta mutu ba ta yi aure ba.
Jeeddah tana shiga ɗaki ta faɗa bisa gado tai ruff da ciki nan take ta soma tuna ranar farko da ta fara haɗuwa da Bilal shattima. Rana ce da ba za ta taɓa mantawa da ita a cikin tarihin rayuwarta ba.
*Flash Back*
Kwana mu biyu da dawowa hutun makaranta ni da ƙanwata Khairat kasancewar boarding school muke yi, anan FGC Sokoto kuma ajinmu ɗaya saboda babu tazarar mai yawa a tsakaninmu shekara biyu kacal na bata a duniya. A wannan hutun da mu ka zo na haɗu da abin ƙaunata Bilal shattima haɗuwar da har abada ba zan manta da ita ba. Kafin na ba ku labarin zazzafar soyayyarmu bari na ba ku kaɗan daga cikin tahirin rayuwata. Sunana Jeeddah Usman maishadda na taso a gaban iyayena Baba da Mama sai kuma ƙanwata Khairat wacce ta kasance tamkar ƙawata saboda muna sharing secret wa junanmu.
Tun daga nursery har zuwa makarantar gaba da secondary class ɗinmu ɗaya sai dai kowane mu da ƙawayensa dama an ce sai hali yazo ɗaya ake ƙawance to kusan haka ce tafaru duk da uwa ɗaya uba ɗaya ne ya haife mu amma halayenmu da ɗabi'unmu sun sha bamban. Na kasancewa masifaffiya mai azababben taurin kai da tsiwa bana bari ko ta kwana balle ta tashi. A lokaci da muna secondary school nasha dambe da maza clasa ɗinmu kaɗan ne daga cikinsu da ban yi dambe dasu ba, balle kuma su mata ƙaramin alhakki kullum sai na fasa baki ɗiya.
Yayin da Khairat ta kasance mai sanyi hali shiru-shiru da ita ba ta da abokin faɗa in ba ni ba da wuya ka ji Khairat bata da kwaranniya ko kaɗan har mamaki mutane ke yi idan aka ce ƙanwata ce kuma uwa ɗaya uba ɗaya don ko kusan halayenmu ba su yi kamanceceniya ba.
Tun ina cikin tsuman goyana Ya Haidar ke sona yayin da ni kuma tun lokaci da na balaga nasan menene so na ji ba wanda na tsana a duniya irinsa. Kar ku yi tunani wani laifi ya yi min da nake nuna masa zazzafar ƙiyayya irin wannan ba wani abu bane kawai dai don ya kasance kyakkyawa ajin farko kuma ɗan masu kuɗi, sai anan gaba zan warware muku dalilina da yasa na tsani kyakkyawan namiji kuma mai kuɗi.
Mu huɗu iyayenmu suka haifa mahaifina Alhaji Usman maishadda haifaffen garin Sokoto ne kuma riƙaƙken ɗan kasuwa ya yi karatun addini da na zamani sai dai karatunsa na boko bai yi tsayi ba ya tsaya iya matakin ƙaramar diploma. Da farko ya fara karantawar a primary school kafin ya koma kasuwanci da ya taso ya iske mahaifinsa yana yi na sayar da atamfofin da shadda da leshi har ma da mayafai a kasuwa. lokaci da aka yi mishi aure yana da ƙarancin shekaru a lokaci yana da shekara goma sha takwas mahaifinsa yai mishi aure da 'yar amininsa Irin aure nan na gata da ada masu kuɗin ke yi wa 'yayansu. A lokaci Mamanmu primary school kawai ta kammala aka aurar da ita ga Babanmu, cikin yarda Allah suka haɗa kansu suna tsananin ƙaunar junansu tamkar auren soyayya suka yi ba auren haɗi ba. A yadda Mama ke ba mu labari sai da ta shekara goma sha ɗaya da aure kafin ta haifi Ya Kabeer sai da ya yi shekara goma kafin ta haifi Aunty Farida wacce ita ma sai da tayi shekara bakwai curr kafin a haife ni ina da shekara biyu kacal ta haifi Khairat wacce muka taso tamkar twins komai tare ake mana kasancewar banida girman jiki yayin da Khairat take da manyan ƙasusuwa shiyasa ta kamoni har ta zo ma tafi ni girma shiyasa wanda basu san mu ba suke tunani Khairat ce babba, yayin da duk lokaci da aka sami irin wannan akasi nake rufe idanuwa naci mutunci duk wanda ya yi mana irin wannan hasashe domin na tsani naji an kira Khairat da yayata.
Da Babanmu da mahaifiyar Ya Haidar uwa ɗaya uba ɗaya suke asalima su uku ne kacal iyayensu suka haifa babbar yayarsu mai suna Mariya tana aure a Kebbi sai Babanmu sai autarsu Hauwa wacce suke kira da Turai ita ce ta haifi Haidar, kuma sunanta ne na ci. Tun banida wayau ake kirana da suna matar Haidar shi kuma mijina a lokaci bana fahimtar abinda ake nufi da hakan har na dawo na fara fahimta, ina farkon balaga a lokaci ne wani ɓoyayyen halina ya fara bayyana na azababben kishi, banaso ko Khairat da take ƙanwata ta raɓi Haidar yanzu nan zan tsira fushi na dinga cin rai na tai cika ina batsewa har da su ƙauracewa abinci sai Ya Haidar ya sha baƙar wahala Kafin ya shawo kaina na sauko daga fushi da na hau, gashi Allah ya zuba mishi farin jini 'yan mata kasancewar shi kyakkyawa azahirin gaskiya Ya Haidar yana da matsanancin kyau da ace kyawo na yawa da nace da ku nashi har ya yi yawa a lokaci da na fahimce kyawon shi yana ɗaya daga cikin abinda ke jan hankali 'yan mata sai na fara tsanar kyawon nashi daga baya kuma na gano har da kasantuwar shi ɗan masu hannu da shuni.
Ban ƙara tabbatar da hakan ba sai wata rana da mun zo hutun makarantar boko na je gidan Aunty Farida sai mijinta ya yi baƙo Aunty Farida ta aike ni na kai masa ruwa da drinks, kafin na kai da shiga parlourn Abban Siyama na tsince firar su inda abokin nasa ke faɗi "Yusuf ya kamata ka ƙara aure ka wani maƙallewa mace ɗaya sai kace pastor.
Nan take na kasa shiga parlourn na laɓe jikin ƙofa tare da baza kunnuwa naji amsar da Abban Siyama zai bashi sai naji yana faɗin "mi zai sa na ƙara aure Habeeb bayan matata tana kyautata min wallahi ina matuƙar jin daɗi zama da Farida.
"Kana da matsalar fahimtar abubuwa masu sauƙi fahimta Yusuf an gayamaka dole sai mace tai maka laifi za ka yi mata kishiya, Ubangiji ya ba ka komai Yusuf kana da kyau ga kuma ɗibin dukiya mai yawa babu abinda Allah ya rageka dashi, wallahi da nine kai da mata huɗu curr zan yi in yi ta gurgura abina hankali kwance.
Sai kawai na ji sun kece da dariya har suna tafawa kana Abban Siyama ya ce "Allah abokina?"
"Allah kuwa abokina ka fahimci wani abu guda mata wannan zamani sun fi so namiji kyakkyawa kuma mai 'ya'ya banki, kai kuma duka biyu Allah ya haɗa maka karka biyewa ta kyautatawar da Farida take maka ka cuci kanka.
Tsabar takaici ka kasa ƙarasawa parlour nan sai komawa kitchen nayi na dire tray ɗin Allah yasa Aunty Farida tana ɗaki, ba a ɗauki lokaci ba Abban Siyama ya yi ma Aunty Farida kishiya in takaice muku labari yanzu kishiyoyinta har biyu. tun daga wannan ranar da naji wannan ɓakar firar tasu na ƙudurtawa raina bani ba namiji kyakkyawa ko mai kuɗi.
Daga sanda na fahimci da gaske kuɗi da kyau sune dalili da ke sa wa ai ma mace kishiya na ji na tsani Haidar soyayyarsa ta fita daga zuciyata tamkar an wanke min ita da sosu da omo.
saboda azababben kishina sai nake gani kamar idan na aure talaka mummuna ba zai min kishiya ba tun da mata ba son talaka mummuna suke yi ba Shiyasa na zaɓi Bilal shattima kasancewar shi mummuna baƙi wulik ga shi kuma ba shi da aiki yi zauna gari banza ne.
Bai aje ba bai kuma ba wani ajiya ba.

*Please comments and share fissibilillahi*

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now