8...

111 5 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!* _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

8...

Tafe nake ina ci-gaba da mita a zuciyata "Ka ji min shegen mutum wai har ni zai kalla ya ce bana gudun abin Kunya, tsaka ni dashi waye ne bai gudun abin kunya, shi da kullum bakinsa cikin faɗar maganganu batsa yake don tsabar reni wayau zai ce min bana gudun abin kunya sai da ya faɗawa wanda bai san halinsa ba ba dai ni Jeeddah ba, da na gama sani waye shi.
Sai da na fara leƙawa ɗakin Mama na ce mata na dawo kafin na wuce ɗakinmu, ina zuwa na cire kayan jikina na ɗaura brown towel, Khairat ce ta shigo dawowarta kenan daga wuri nata aiki jakkar hannunta ta jefa kan gado tare da cire hijabin jikinta, kasancewar makarantar da take koyarwa kusa da gida ne shiyasa take zuwa a ƙafa.
"Washhh! Allahna yau akwai rana kamar za ta fasa ƙwaƙwalwar mutum.
Khairat ta faɗa sa'ili da take ƙoƙarin cire kayan jikinta.
Na juya na kalleta kana nace "Bari kawai abin ba a cewa komai gara ma ke kina kusa da gida saɓani nida nake wata uwa duniya gaskiya idan nai aure transfer zan nema na dawo kusa da gidana da aurena ba zan iya jure tafiya mai nisa ba.
Wata dariya reni wayau Khairat ta tintsire da ita gami da faɗin "Ma-sha-Allahu! Jiddon Baba yaushe kika yi miji har dasu gida ni da nake ƙanwarki kuma aminiyarki bansani ba gaskiya ki gyara halinki zama bai ce haka ba 'yar uwata.
Yadda Khairat tai magana ya tabbatar min da gatsali take min wato ta ma mayar da ni gantalalliya ko mahaukaciya. Nan take raina yai masifar ɓaci sai kawai na juya a fusace na nufi bathroom ina ji lokaci da ta sake kece wa da dariyar sheƙiyanci tana faɗin "Ashe dai su Hajiya Jiddo ana so aure miji ne kawai babu da za ki ɗauki shawarata da nace ki jingine wannan mummunan buri naki, ki rungume Ya Haidar ɗinki har wahalar fita teaching cikin uwar rana zai raba ki dashi, amma wallahi idan ba shi kika aura ba rayuwarki tana cikin kwalekwale, wallahi ba baki nai miki ba muddin kika aure ɗan kundalo wahala duniya ce za ta zama ajalinki.
A fusace na juyo tare da hayyaƙo mata har towel ɗin jikina ya shirin zamewa amma tsabar masifa ko ta kanshi ban bi ba na ce "Ai sai ki zo ki aura min shi shegiya baƙar munafuka wacce kwata-kwata a rayuwarta bata nufi na da alkhairi. Ɗan kundalo nan da bakwa so shine dai zaɓina sai dai baƙin ciki ya wulla mutum kabari ehee.!
"A'ah! tou maida wuƙa 'yar uwa ai kowa ɗebo da zafi bakinsa kuma duk wanda rai yai wa daɗi bai yi kamar mashi ba, mu kam 'yan araka yarima ne asha kiɗa Allah ya bada sa'a dama mai rabon shan duka ba ya jin kwaɓa.
Ko kusan ban fahimci inda zaurance ta ya dosa ba saboda haka na dalla mata harara tare da jan guntun tsaki, na ce "Haka dai za a ƙare a sana'ar munafuci wacce bata da riba.
Dariya tayi haɗi da shewa tana wani jujjuya ɗuwawunta kana ta watsa min kallon banza tana yatsina ta fice tabar min ɗaki bayan tasan ta manna min hauka ai kuwa na ci-gaba da zaginta sai da nayi mai isata kafin na shiga bathroom nayi wanka sai da na gabatar da sallar la'asar kana na shirya cikin atamfar chiganvy style ɗin A-shape sosai ɗinki ya fiddo min da shape ɗin jikina duk lokaci da nasa kayan ba ƙaramin kyau suke min ba suna ɗaya daga cikin tufafina da nake bala'in so.
Ina cikin shafa turare Ya Haidar ya kunno kai ta cikin dressing mirror da nake tsaye na shiga watsa masa baƙar harara, na rasa yadda zan yi da wannan mutumin duk ya bi ya taƙurawa rayuwata, ya zame min ƙarfen ƙafa wallahi da yasan yadda na tsani ganinsa da ko biyansa aka yi da kuɗi ba zai kusanto inda nake ba.
Tun kafin ya ƙaraso na ɗauki ɗan kwalina da ke aje akan gado yana zuwa ya fizge ɗan kwali, yana min wani shegen kallo gami da murmushi ƙasa-ƙasa ya sassauta murya kamar ɓakin munafuki ya ce "iyeee...Jiddatuna mai kyau kinga yadda rigar nan ta karɓe ki tubarallah Ma-sha-Allah abubuwa sun fito gwani sha'awa ina da an zarga miki igiyoyi aurena
wallahi da ji kawai za ki yi nayi wuff dake sai tsintar kanki za ki yi a tsakiyar gadona uhmm! Bari kawai na haɗiye ɗaɗina fatana Allah ya kai damo ga harawa ko bai ci ba yai birgima abinsa.
Saboda tsabage takaici basan lokaci da na dafe goshina ina masa kallon tsana, kana na ja tsaki tare da faɗin "Ɗan iska dai bai ji daɗin zaman duniya ba kai kam a haka za ka ƙare to sai dai a mafalkinka wallahi.
Faɗaɗa murmushin kan fuskarsa ya yi tamkar bai ji zafin maganata ba ya ce "Daina faɗar haka Jeeddah kinsan abu ga Allah babu wuya gobe-gobe nan sai ki ji an shafa fatiha a tsakaninmu wallahi ina tabbatar miki a ranar tsabage zumuɗi ba zan jira sai an kawo min ke ba ko a ɗaki nan za mu iya bajewa abinmu.
"Cabdijam! Wallahi ba dai ni Jeeddah Usman maishadda ba sai dai in da wata can daban za a shafa maka fatiha ka baje da ita.
"In-sha-Allahu dake za a shafa kuma da ke ɗinan zan baje wata tara ciff Hajiya kin haifa min little Jeeddah.
Ya ƙarashe magana yana wani shegen blushing mai ban haushi tsaki kawai na ja tare da zuzzuba mishi harara
Ko a jikinsa sai ma ci-gaba da magana ya yi
"Wallahi ina sonki Jeeddah irin so da baya faɗuwa balle a misalta shi... Don Allah ki so ni nima koda rabin kwatankwacin wanda nake miki ne.
Yadda ƙarasa magana yana narkewa kamar man shanu a wuta, kana ya haɗe tazarar dake tsakaninsu, ya riƙo hannunta ya ɗora saitin da zuciyarsa take ta ji zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi "kin ji yadda zuciyata ke bugawa kou? Duk saboda sanadin sonki ne ki tausaya min ki tuna ba wadatatciyar lafiya ce dani ba, abu kaɗan zai iya tayar min da ciwona.
Ko darr kalamansa basu sa ta ji ba sai ma shegen haushinsa da ta ji ya ƙara turnuƙe ta da hanzari ta kwace hannunta gami da raɓa shi ta nufi ƙofar fita, ina gani ya biyo ni na rugu da gudu, duk da na shiga parlourn Mama bai hakan bai sa ya kyaleni ba sai da ya biyoni hatta da abinci da na ɗebo sai da ya saka hannunshi yaci, saboda shegiyar yunwa da nake ji yasa na haƙura muka ci tare.
Sai daff da magariba ya wuce sai lokaci naji kamar an gafarta min muddin Ya Haidar yana gidanmu, jina nake yi tamkar ina bisa ƙaya.
Bayan sallar isha'i muna zaune a tsakar gida muna fira saboda duk lokaci da babu wutar lantarki kuma ba a tashe gen ba anan muke zama har Baba kafin a dawo da wuta kowane mu ya koma ɗakinsa. A daidai ƙofar shiga parlourn Baba Mama ta shimfiɗa mishi carpet ya zauna yana sauraren labarai duniya a ɗan ƙaramin rediyon sa. Ni da Khairat kuma muka shimfiɗa tabarma a ƙofar parlourn Mama yayin da kowacce mu ke dannar wayarta hankali kwance.
Kiran Bilal ya shigo wayata, nayi picking gami da sassauta murya ƙasa-ƙasa "Hello... Love!
"Love gani a ƙofar gidanku.
"Okay Love just a minute ganina tafe.
"No problem Love take your time.
"Yeah!
Nai sauri tashi jikina na rawa na shiga ɗaki duk da babu wutar lantarki sai da na gyara fuskata tare da fesa turare na sako zubulele hijab yana ja a ƙasa, saboda doka ce Mama bata bari mu fita zance da gyale.
Direct kitchen na shiga na buɗe deep freezer ɗin Mama na ɗauko robar kunu aya da zobo manya guda ɗaɗɗaya na dauƙo tray da cup garin rawan jiki da nake yi, cup ɗin ya subuce ya faɗi Allah ya taimake ni unbreakable ne bai fashe ba na ɗuka in ɗauke ina kai hannuna da nufi ɗauke cup ɗin, na ji sautin muryar Mama tana faɗin "Wai waye a kitchen yake min ɓari da kaya?"
Duk da sai da gabana ya faɗi hakan bai hanani furta "Mama ni ce.
"Da kyau sarkin taɓargaza dama nasan wannan aiki sai ke to ki yi a hankali karki yi min ɓarna.
"Tou Mama.
Na faɗa da sauri, kamar jira nepa ke yi na fito daga kitchen suka dawo da wuta, tuni duhun da ke lulluɓe da tsakar gidan ya yaye zuwa wadatatce haske, Mama dake zaune kusa da Baba ta waro min idanuwanta tana min kallon tuhuma.
Na sadda kai ƙasa ina tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki.
"Wai ke ina za ki je da dare nan da kika kinkimo uban tray ga wani dogon hijab da kika baza?"
Cikin sanyi murya na furta
"Mama Bilal ne ya zo shi ne na ɗauko masa abin jiƙa maƙoshi.
Uwar harara ta fara galla min gami da daka min gigitatciyar tsawa ta fitar hankali "Ina ruwana da zuwansa yo.. Allah na tuba da zuwansa da rashinsa duk ɗaya ne a wurina, wato shine kike ta ɓar-ɓar da jiki kamar wacce wani hamshaƙin mashahurin attajiri wanda kuɗi suka gama zaunawa a jikinsa ya kawowa ziyara, nan kuwa ɗan zaman kashe wando ne.
Shiru nai ni ban fita ban kuma koma kitchen ba, yayin da furucinta ya haddasa min ɓaci rai har wani dishi-dishi nake gani.
"Ba ma wannan ba faɗamin wa ya ba ki izini buɗe min freezer hadda ɗauko min kayan sana'a? Wato ga Mama mai kayan banza kou? shine don tsabage so ki ƙarya min jari sai da kika dubi na manya-manyan robobi ki ka ɗauko masa ya zuƙe ya yada empty roba to Allah yasa na gani sai a mayar min da kayana na gaji da haihuwar 'ya'ya rana tana kashewa, nace ki mayar min da kayana kin wani tsaya kina zararr idanuwa kamar mayye ya yi baƙo.
Rai ɓace Jeeddah ta haɗiye miyagun miyau kamar za ta fashe da kuka, ta sassauta muryarta ta ce "Don Allah Mama ki yi haƙuri na kai masa wallahi Bilal yana matuƙar son zobonki da kunu aya duk lokaci da na kai masa ya dinga santi kenan yana yabawa kwarewarki, har cewa yake duk faɗin unguwar nan ba wacce take kai ki iya sarrafa kunu aya da zobo.
"Mtsss......yo ba dole ya yaba min ba kullum yana sintiri a ƙofar gidana yana ɗibar banza, ai idan bai yabamin ba sai Allah ya kwashe masa albarka.
Mama ta faɗa cike da jin haushi tana taɓe baki.
A wannan karo Baba ne ya karɓe zance saboda maganganunsu da na rediyonsa suna neman su raba mishi hankali gida biyu "Haba Fatee miyasa kike da sha'awar muzanta yarinyar nan?
"Ba wani muzanta ta da nake yi kawai da so nake ta fara yi wa kanta karatun ta natsu ina amfani baɗi ba rai.
"Ke Jeeddah wuce ki tafi in don ɗan wannan zobo ne zan biya ta ƙudinta.
Baba ya yi magana gami da kallon Mama yana murmushi saboda yasan ya kashe bakin faɗan nata.
Ina fita ta kalleshi with serious face ta ce "Gaskiya Alhaji na gaji da gafara sa banga ƙaho ba. Zaman Jeeddah a gidanan ya fara isata kana dai sane da gidansu Jameel mu suke jira su ji ta bakinmu kaine ka dakatar dasu kuma a gefe ɗaya ga Haidar sai sintiri gidanan yake yi, ko ɗazu Hajiya Turai ta kirani so take in da hali wata mai kamawa ayi bikinsu kowa ya huta, tun da shi wannan maƙale mata ba abin aure ne dashi ba ɗan banza sai afki zuwa zance kamar ɗan achaba.
Mama ta ƙarasa magana tana cika da batsewa domin gaskiya haƙurinta ya fara ƙarewa gara ayi ta ta ƙare.
Ajiyar zuciya Baba ya yi gami da kashe rediyonsa, ya fuskanci Mama da kyau ya kuma gyara zamanshi cikin natsuwa da kwantar da murya ya ce "Na ji duk abinda kika faɗa Fatee kuma zancenki akwai ƙamshin gaskiya a ciki, sai dai gaskiya ba zan ɓoye miki ba al'amari nan yana neman ya zarce wa tunanina.
"Kamar ya Alhaji?
Tai sauri katse masa hanzari.
"Game da zance aure Jeeddah da Haidar mana.
"Haba Alhaji ko ka manta kaine mai cikakken iko akan Jeeddah, sai abinda ka zantar kuma dole tabi walau tana so ko bataso.
"Na sani Fatee tabbas na isa da Jeeddah kuma ina da damar da zan aura mata koma waye balle Aliyu da ya kasance ɗan 'yar uwa ta, sai dai banaso nayi abinda zan dawo daga baya ina danasani akansa.
"Ban fahimce ka ba Alhaji shin kana nufi za ka bar Jeeddah ta aure zauna gari banza, wanda bai da madogara?"
Saida Alhaji Usman maishadda ya ja fasali kafin ya ɗora da cewa "Shakka babu idan har ta nace sai shi banida wani zaɓi da ya wuce na aura mata shi.
"Cabdijam! Gaskiya Alhaji da sake wai an yiwa mai dame ɗaya sata, bana ko tantama gantalalle yaro nan kai ma bai barka a banza ba. Wannan ai toshewar basira ne haka kawai za ka ɗauke 'yar cikinka ba ma 'yar riƙo ba balle a ce ka yi mugunta ka aurawa marar aiki yi tsakani da Allah wannan shawarar taka ko kaɗan bata karɓu ba. Tou shikenan naji a tafi a haka ka amince ta aure zauna gari banza ɗin to shi kuma Haidar ya za ka yi dashi?"
"Ya ko zan yi dashi da yawuce in zaunar dashi na bashi haƙuri haɗi da nasiha na nuna masa illar da ke tattare ga auren dole, musamman shi da bashida wadatatciyar lafiya.
"Uhmm....Tou naji ka bashi haƙuri ka kuma yi masa nasiha abin tambaya anan shin kana gani gayamasa da za ka yi ya haƙura da Jeeddah hakan ba zai taɓa lafiyar tasa da kake ƙoƙarin karewa ba?" ina mai tabbatar maka Alhaji muddin Haidar ya ji wannan mummunan labari daga lokaci ba wai iya ciwon zuciyarsa zai tashi ba rankatakaf zuciyar tasa bomb za tayi ta tarwatse gaba ɗaya sai ka faɗin me ya za ka yi a wannan lokaci?"
Shiru Alhaji Usman maishadda ya yi gami da shassafa dogon geminsa, yayin da jikinsa yai mugun sanyi maganganun Mama suka ratsa shi gani haka yasa ta ƙara ƙaimi wurin gani ta wanke masa wannan mugun tunani nasa.
"Gaskiya ka sake tunani Alhaji ina amfani ka sayar da Akuyar ka ta dawo tana cin maka danga, da irin wannan aure da kake shiri yi ma Jeeddah gara babu sau ɗari dashi zai fi alkhairi mu ta ganinta a gabanmu da kwana biyu ta dawo mana zauranci a gida ka natsu Alhaji ka saita tunaninka wuri ɗaya.
A hankali Alhaji Usman ya sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sani duk abinda Mama ta faɗa gaskiya ne sai dai shi ma yana da hujja da yasa bayaso yi wa Jeeddah auren dole, domin shi ganau ne ba jiyau ba iri masifar da 'yar amininsa Alhaji Muda ta faɗa a dalili aure dole a takaice ma yana ɗaya daga cikin mutane da suka ƙara karfafawa mahaifinta Alhaji Muda kwarin guiwa don ganin ya aura mata ɗan uwanta daga ƙarshe sai gashi wani babban al'amari marar daɗi ya faru, wanda ya zama silar mutuwar auren da rushewar zumunci Alhaji Muda da ɗan uwansa yanzu haka ko ga maciji basa yi 'yan uwan juna, uwa ɗaya uba ɗaya sun dawo maƙiyan juna to ina amfani iri wannan aure shiyasa har kawo yau ya kasa aje zuciyarsa wuri ɗaya balle ya yanke hukunci da yake gani shi ne daidai.
Gashi yana matuƙar jin kunya haɗi da takaici bayyana wa 'yar uwansa Hajiya Turai ƙudirinsa ba zai iya aurawa ɗanta Haidar Jeeddah ba a dalili bataso shi, a kuma gefe ɗaya yana cike da alhini aura mata mutumin da ba shi da madogara sai yake gani tamkar ɓatan basira ne.
To amma kuma ya iya saboda Jeeddah ta kafe kai da fata lallai ita sai shi 'ya'ya zamani kenan ka haife su ba ka haifi halinsu ba.
"Ya kayi shiru Alhaji ba kace komai ba?"
Maganar Mama ce ta dawo dashi daga duniyar dogon nazari da ya afka.
Sai da ya yi gyaran murya kamar mai shirin kiran Sallah kana ya buɗe bakinsa cikin rauni murya ya ce "Fatee inaso ki sa wa zuciyarki tawakali ki sani tun ran gini tun ran zane, hakazalika wani baya aure matar wani kamar dai yadda kika ce bahaushe yana faɗa matar mutum kabarinsa, shi aure da kike gani nufin ALLAH ne duk yadda muka kai da so haɗa aure tsakanin Haidar da Jeeddah idan ALLAH bai nufa ba mu.....
"Dakata Alhaji!
Mama tai hanzari katse shi ta hanyar ɗaga masa hannu, yayin da idanuwanta har sun fara sauya launi cikin tsanani ɓaci rai ta ci-gaba da faɗin "Kada ma ka soma wannan ɓatan basira shin Jeeddah ta fi ƙarfinmu ne da ba za mu iya tankwarata ta ba tabi abinda muke so ne, ko kuma tsoronta muke ji da za mu bi son ranta?"
"Ba ko ɗaya Fatee kawai ina duba da matsalar da za ta iya faruwa idan mu ka ɗage sai mu yi mata dole. Ni fa tun daga kan Alhaji Muda na ɗauki darasi kuma gani ga wane ya ishe wane tsoron Allah.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now