044

103 20 3
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

*Assalamu alaikum*
*Shin 'yar uwa kinada labarin shararriyar Mai sayar da kayan gyaran Nan wato hjy*
*Madina Beauty Ventures** Hmmm *matso kusa Kisha labari ,wannan kamfani ya tanadar wa Mata Kayan gyara na* *musamman Wanda suka hada da kayan Mata masu kyu da inganci , Ƙarin Ni'ima, Ƙarin sha'awa,matsi da sauran su,akwai kuma* *supplements na gyaran jiki kama daga Ƙarin hips, Ƙarin kiba,gyaran skin sa haske da sheƙin fata duka Kuma Kayan su akan farashi ne Mai sauki ku tuntubemu a* *WhatsApp direct ta wannan link wa.me/2348037444722 or Call 08037444722*
*Ig_madina_beauty_ventures*
*Location _Birnin* *Kebbi,kebbi state*🤝

044..

Har ya dasa aya a zance shi ina aikin kallonshi idanuwana ne kawai ke yawo akan fuskarshi, amma a zahiri tuni na daina fahimtar abinda yake faɗa kawai dai naga bakinshi yana motsi muryarta a dusashe na ce "Tabbas Nusaiba matarka ce Bilal halali ka ce kana da damar da za ka sadu da ita a duk lokaci da ka so, to amma abin tambaya ana miyasa ka yi min alƙawari da kasan ba za ka iya cikawa ba miyasa Bilal ka yi min alƙawarin ba za ka yi min kishiya ba?"
Kai tsaye ya kalle cikin idanuwana ya bani amsa da cewa "Saboda Ina sonki ina kuma ƙaunar duk wani abu da zai sanya ki farin ciki, amma har ga ALLAH a can ƙasan zuciyata na ɗauki alƙawari ne ba don na cika ba nayi ne domin farin cikinki.
    Girgiza kai na shiga yi ina ja da baya gami da gunji kuka jin zuciyata nake yi tamkar za ta tarwatse kafin na ce "Idan nace da kai na tsane ka Bilal Shattima babu saura digon soyayyarka a zuciyata za ka yarda?"
Murmushin gefen baki ya yi gami da maƙe ƙafaɗa ya ɗage girar ido kafin ya ce "Zan iya yarda saboda azababben kishinki zai nuna miki hakan amma a can ƙasan zuciyarki ba haka bane.
   "Wallahi da gaske nake Bilal na tsane ka banaso ko kaɗan na buɗe idanuwana naga wannan mummunar fuskar taka ka cutar dani ka ɗora ni akan hanyar da ba za ta ɓulle dani ba. Na yarda da kai a makance ashe kai ba abin yarda bane, amma ba komai nima ka saurare abinda zai biyo baya don wallahi-tallahi ba kyale ka zan yi ba. Don sai na haddasa maka bala'i da masifa sai na hana ka jin daɗi rayuwa, in-sha-Allah ba za ka more amarci nan cikin daɗin rai da kwanciyar hankali ba.  Sai ka yi danasani cin amanata.
Ta ƙarashe magana gami da yi ƙwafa daga haka ta juya ta bar mishi ɗaki kitchen ta shiga duk abinci da ta ɓata lokaci ta girka masa sai da ta zubar da su duka cikin  dusbin, tana yi tana gunji kuka ta dawo tamkar mai taɓin hankali ko aljannu. Daga bisani ta faɗin zaune akan tiles ɗin kitchen ta haɗa kai da guiwa tana risgar kuka, bayan Bilal ya fito daga wanka ya sake shirya wa cikin blue color shadda ya fito riƙe da hularsa, kitchen ya leƙa ya ga hali da Jeeddah take ciki ga kuma yadda ta zubar da abinci shiru ya yi yana kallonta wani mugun haushinta ya kama shi can kuma ya yi gyaran murya gami da cewa "Jeeddah me kika aikata haka saboda zafin kishi za ki almubbazarar da abinci, kin kuwa san irin baƙar wahala da ake sha kafin a nemo shi?"
A mugun fusace na ɗago jajaye idanuwana na kalleshi dasu cikin hargowa na ce dashi "Ni kuwa nasan wahala da ake sha kafin a nemo abinci Bilal domin shekara ta uku ina ci da ƙartin banza wanda basu da halaccin zuri'ar butulci, ka ga kuwa na fi ka sani wahala da ake sha....
    "Jeeddah!
Ya kira sunana cikin kakkausar murya jikinsa har wani rawa yake yi nima na miƙe a fusace domin na ma fi shi hasala "Ko ƙarya nai muku ne Bilal Shattima gaba ɗayanku idan aka cire A'isha Shattima raguwarku kaji ne ku ci ku goge bakinku, ina mai tabbatar maka da cewa wallahi ba ku ci banza ba duk abinda ku ka ci nawa na rantse da girman ALLAH sai kun amayar dashi guntu ba zai zauna a cikinku ba.
  Murmushin gefen baki ya yi yana kallona da girar ido ɗage kafin ya ce "Ta nan kuma kika ɓullo to shikenan ba komai ai kina da damar yi duk abinda ranki yake so ba zan hana ki ba. Amma inaso ki sani ba zan lamunci faɗar maganganu banza akan ahalina ba. Gara tun wuri ki yiwa bakinki linzami.
   "Duk tsiyarka Bilal bai wuce ka sake ni ba abinda ba kasani ba a halin yanzu na fi ƙaunar saki da zama da munafiki wanda baisan darajar alƙawari ba. Sai yanzu na fahimci abinda Ya Haidar ya daɗe yana ankarar dani na kasa ganewa.
Ban yi tsammanin sako Ya Haidar a zancena zai harzuƙa Bilal ba ashe kishi ba ni kaɗai bace shima yana taɓawa domin kuwa wani irin taso min ya yi kamar zai rufe ni da duka sai faɗar yake "Ashe ba ki da mutunci Jeeddah da aurena akanki kina kira sunan tsohon saurayinki? To wallahi ba zan lamunci wannan iskanci ba.
   Duk da ina cikin tsanani ɓacin rai hakan bai hanani fahimtar kishi ne ya lulluɓe shi saboda haka nima na ƙudurta a raina sai na ƙunsa masa bakin ciki, don haka na kalleshi a ɗage na ce "ambatar sunan Ya Haidar yanzu na fara domin shi ɗin cikakken mutum ne yasan girman alƙawari shiyasa, lokaci da na nemi yai miki alƙawari ba zai min kishiya ba yaƙi a dalili yasan irin illar da ke tattare da ƙarya alkawari, saboda haka a gaban kowa zan faɗa da babbar murya Ya Haidar ya fi ka Bilal Shattima.
   Har na dasa aya Bilal Shattima yana kallona daga yanayi da yake kallona dashi na fahimci yanda ranshi ya kai ƙololuwa wajen ɓaci. Bai taɓa jin azababben kishi akan Jeeddah irin yau saboda haka ya haɗiye ɓacin rai nashi ta hanyar cewa da ita "Ki ci-gaba da ambatar sunanshi ba zai hana ki ba domin bakinki ne amma ki sani kina ambatawa kanki wutar jahannama ne. Ni ban yi aure don na ƙuntata miki ba na karo aure ne a dalili na gaji da cin tuwo ɗaya ina da buƙatar canji kuma ni ba pastor bane da zan ƙare rayuwa ta da mace guda. Gara ma ki shafawa kanki lafiya ki raba kanki da tunani wani Haidar domin har abada daga ke har shi ɗin ba za ku taɓa mallakar juna ba. Ni kuma ko yanzu ina da chance ɗin karo wasu biyu, na haɗa ki dasu dole kuma ki zauna dasu.
Yana ƙarashe magana yai tafiyarshi ya barni da dafin maganganu shi a kahon zuciya. Tabbas Bilal Shattima ya nuna min shi ɗin cikakken namiji ne to amma nima idan na kyale shi ban yiwa kaina adalci ba. Bedroom na shige na kulle kaina na dinga bitar kalamanshi ɗaya bayan ɗaya yayin da kowacce kalma tashi nake jinta tamkar ana yayyafa min tafasasshen ruwan zafi a zuciyata, kiran sallah magariba ne yasa ni tashi daga kwance da nake na shiga bathroom nayi alwala na fito, sai da na sallace sallar isha'i sannan na koma kan gado na kwanta.
Ta ɓangare Bilal Shattima da wani irin mugun haushin Jeeddah ya fita, a duk lokaci da ya tuna da ambatar suna Haidar Ka'oje da tayi sai yaji wani sabon haushinta ya lulluɓe shi. Kira Aunty Bahijja ya yi ya ce da ita gobe ta zo gidanshi ta ɗauki kayan lefen Nusaiba ta kai mata sosai Aunty Bahijja tai farin ciki da hakan domin tun lokaci da ta ji labarin Jeeddah har asibiti ta kwanta a dalili zancen auren Bilal take neman hanya da za ta haɗa su ta mayar mata da tsohon martani dake zuciyarta.
   Kwance nake sai tufka da warwara nake yi hanyoyin da zan ƙuntata wa Bilal nake nema, can kuma wani tunani ya faɗo min na tashi zubur, daga zaune da nake na buɗe bedside drawer na ɗauko zungurarriyar farar takarda da biro na shiga rubutu tun around 9 o'clock na fara rubutu sai 10:30pm na kammala na kalle rubutu da nayi na cika back and front na takarda sai kawai na saki murmushin mugunta, na linke takarda gami da ajiye ta akan drawer ɗin sai lokaci naji ƙarfi jikina har na fahimci ina jin yunwa na tashi da ɗan kuzarina na shiga kitchen na haɗa tea mai kauri ana cikin kitchen na tsaya na shanye tea ɗin, kana na koma ɗaki nayi wanka na shirya cikin sleeping dress na cotton gown, na sake bin gado nai kwanciyar ta misali ƙarfe 11:08pm daidai Bilal ya dawo, hatta da sallamar da ya yi ban amsa mishi ba shima daga haka bai ce min uffan ba har ya yi wanka ya shirya cikin kayan baccinsa ina kallonshi a ɗage, ya zauna daidai kusa da ƙafafuwana, sai da ya fesar da iska daga bakinsa kafin ya kira sunana "Jeeddah! Ki tashi zaune za mu yi magana.
Naƙi amsawa kuma ban tashi ba ya sake maimaitawa nan ma nayi biris dashi gani haka yasa ya tafi kai tsaye ga gundarin maganar da yake so ya yi min "Ki sami lokaci zuwa gobe ki yi min List na abubuwan da kike da buƙata  in-sha-Allah next week za mu tare a sabon gida, amma banda furniture saboda Aunty Farida zan turawa kudi ta zaɓar miki a plaza ɗinsu. Zan kuma turo miki da kuɗi ta account ɗinki sai ki yi amfani dasu ki kai ɗinki.
  Taɓe baki nayi gami da kallonshi na watsar, kafin na yunƙura na tashi zaune na miƙa hannu na ɗauko takarda da na rubuta domin shi na miƙa masa a wulaƙance.
  "Takarda mecece wannan?
   "Halan ba ka yi karatu bane da ba za ka buɗe ka gani ba?"
Na faɗa a yatsine sai da ya kalle ni kafin ya warware takarda ya shiga karantawa a natse can kuma ya ɗago idanuwanshi a razane ya kalle ni sai da ya ɗauki lokaci mai tsawo yana kallona kafin cikin harɗewar lafazi ya ce "Jeeddah me kike nufi da wannan dogon List ɗin naki?"
Danƙarerriyar harara na galla masa kafin na ce "ALLAH ya wadaran degree da ka yi Bilal Shattima tun da har ka kasa fahimtar wannan 'yar ƙaramar takarda...
   "Dallah dakata Jeeddah!
Ya katse ni a fusace kana ya zarce da faɗin "lissafi fa kika buga na duk wani abu da kika taɓa yi min tun daga farkon haɗuwar mu har kawo yau, aƙalla zan biya ki Naira miliyan goma Jeeddah yaushe kika kashi min maƙudan kuɗi har haka? Dan ALLAH ki dinga aiki da hankali banaso tadda zaune tsaye.
   Har ya kammala faɗar albarkaci bakinshi ina mishi kallon haɗari kaji, kafin na ce "Wallahi-tallahi Bilal muddin kana so zaman lafiya da kwanciyar hankali sai ka biya kudin nan idan ba ka biya su ta daɗin rai ba to za ka biya ta hanyar da ba ka yi tsammanin ba domin kuwa kotu zan maka ka.
   "Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Jeeddah ba ki taɓa bani rance kuɗi ba ballantana ki kai ni kotu ko kin taɓa bani aro Kudi ne?"
   "Amma ai ka taɓa yi min sata ko ka biya ni wannan satar da ka yi min?"
Kalmar sata da ta ambata ta dake shi sosai don har sai da ya runtse idanuwanshi.
   "Karka manta ko machine ɗin da ka sayar a can baya ka biyawa Aunty Bahijja kuɗin surgery, bana ka bane bakada ko kwadala a ciki saboda haka a yanzu ina da bukatar a dawo min da dukiya ta kar fa ka manta kai yanzu mai arziki ne miliyan goma ba wata tsiya bace a wurinka.
  Zazzafar iska ya fesar yayin da gumi ya karyo masa ya shiga murza goshinsa kafin ya ɗago ya ce "Jeeddah ba ki taɓa ce min duk wahalhalu da ki ka dinga yi akaina zan biya ki ba?"
   "Kamar yadda ka faɗa alƙawari da ka yi min ba ka yi shi don ka cika ba nima kyautar ba da zuciya ɗaya na yi ta ba da manufar ba za ka yi min kishiya ba tun da haƙa ta bata cimma ruwa ba, kenan babu amfani na bar maka dukiya ta, idan ba a yi gwaɗo da yaro gara a bashi 'yar daddawar sa ya ƙara gaba. Da fatar ka fahimce inda zaurance nawa ya dosa?"
Shiru Bilal ya yi ga baki ɗaya ya zama speechless, ya ja gwaron numfashi gami da cewa "Ban taɓa gani mace mai azababben kishi irin ki ba Jeeddah amma ba komai zan biya ki kudinki sai dai yanzu banida su a dalili abubuwan da ke gabana amma in-sha-Allah idan nayi settled ba Miliyan goma ba ko duk abinda na mallaka kike so zan ba ki.
    "Mtsssss!
Na ja dogon tsaki tare da yi mishi kallo sama da ƙasa kana na taɓe baki kafin na ce "Yaushe ka yi arziki da za ka mallaka kawai ka turo min da kuɗi na shine kwanciyar hankali da zaman lafiyarka?"
     "Love ban ce ba zan ba ki kuɗinki ba amma a yanzu bani da su saboda tariya nan da za mu yi dole muna bukatar sababbin abubuwa....
   "Dallah saurara malam ni bana bukatar ko komai daga gareka kudina kawai nake so period!
"Shikenan zan ba ki.
Ya faɗa kai tsaye gami da miƙewa ya bar min ɗaki.
A washegari da sassafe ya fita don koda na falka daga bacci ya daɗe da fita, misali ƙarfe 11:00am ina kwance a parlour har zuwa lokaci zuciyata a cukushe take, na rasa abinda ke min daɗi a duniya wani irin ƙunci nake ji kamar daga sama naji ana bugun ƙofa da ƙarfi jiki ba ƙwari na miƙe na nufi ƙofar ina buɗewa nai tozali da Aunty Bahijja fuskarta cike da annuri sai fara'a take ban ce da ita uffan ba na juya na koma ciki parlour na zauna biyo ni tayi daga sama har ƙasa ta shiga ƙare min kallo kafin ta kece da dariyar mugunta. Sai da tayi mai isarta kafin ta ce "Daɗina da gobe sauri zuwa Hajiya Jeeddah sai kuma kika ji abin alkhairi da ya same mu ko?"
Ban ce da ita komai ba sai wasa nake da yatsuna yayin da zuciyata tai nisa wajen tunani wanne irin kalar rashin mutunci zan tata mata, sai kawai na tsikayi muryarta tana faɗin "Lefen Nusaiba na zo ɗauka duk nasan ba banza aka barshi ba shiyasa ya ba wa 'yar uwarki contract ɗin haɗawa Nusaiba lefe, sai dai duk tsaface-tsaface ku sun tafi a banza domin hakan bai hanawa Bilal ƙara aure ba.
    Da kyar na ɗago yayin da zuciyata ke tuƙuƙi na kalle ta da idanuwana da suka yi jajir, na miƙe tsaye jikina yana rawa cikin wata irin murya na ce "Aunty Bahijja ga lefen can ki ɗauka yanda akawo su ko kallon kirki ban mu su ba, ki yi gaggawa ki ɗauka ki barmin gidana idan ki ka sake ki ka kaini bango na rantse da ALLAH sai na sauya miki kamanu.
Na ƙarashe magana ina huci kamar zakanya da ke jin yunwa.
    Dariya reni wayau ta kwashe da ita ta kalle ni ta tofar da yawu tana faɗin "Duk abin da za ki yi min Hajiya Jeeddah ba za kai koda kwatankwacin rabin wanda ni nayi miki ba, ni fa na ri ga naci ki da yaƙi sai haƙuri ina fatar kina da labari jiya mijinki ya angwace da Nusaiba ya kwashi gara da garɗi da ba ki da irin shi...
Tun kafin ta ƙarasa rufe bakinta na miƙe tsaye a mugun fusace na ɗauke ta da gigitatcen mari, kafin ta dawo hayyacinta na rufe ta da bugu ta ko ina duka nake kai mata ina kuka irin mai masifar cin rai daga ƙarshe na falla da gudu na shiga kitchen na ɗauka wuƙa tana gani na dunfaro ta gadan-gadan da wuƙa tsirara a hannu ta kwasa da gudu ta nufi ƙofar fita....

*Dan ALLAH ku taimaka ku dinga taya ni sharing novel ɗinan, saboda ba kowanne group nake turawa ba kusan abin da yawa mutum ɗaya ba zai iya shi kaɗai ba*

Thanks one love#

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now