059

120 10 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!* _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

059.

Bahijja tana ƙyala ido ta ga mijinta har wani washe baki take yi gaba ɗaya haushinta gami da takaici ta suka lulluɓe Hajja ta maka mata uwar harara kafin ta dawo da ganinta akan malam Haruna dake tsaye ƙi ƙam yana wani muzurai nan take haushinsa ya ƙara turnuƙe ta. Domin bata ga amfani wannan zuwa da ya yi ba. Ko bai musu sallama ba, bai kuma gaidata ba. A matsayin ta na uwar matarsa balle har ya bata haƙuri akan mummunan duka da yai wa 'yarta. Bata taɓa sani malam Haruna tsinanne ne marar albarka ba sai yau. Ita kuma ba abinda zai hanata nuna mishi ita ma tsohuwar banza ce don haka ta miƙe a fusace ta ce "Haruna uban me ka zo ɗauka asibiti nan ko ka zo ne ka inda ƙarasa ta?" domin duk wanda yaga wannan kafiri dukan da ka yiwa Bahijja yasan rayuwarta kaso ɗauka ALLAH ne bai ƙare mata kwana ba da yanzu ta daɗe a kushewa.
Duk maganganu da Hajja take yi Malam Haruna yana tsaye yana mata kallon wulaƙanci, yayin da Bahijja take ƙoƙari kama hannun Hajja da ɗayan hannunta mai lafiya so take ta taka wa Hajja birki, tun da har ya zo duba ta bai kamata tai masa irin waɗannan maganganu ba. In fact ita bata ga laifinsa ba tasan magauta ne suke so ɓata tsakanin su in-sha-ALLAHU ba za ta taɓa bari su yi nasara ba. Domin har ta ƙudurta a ranta tana tashi daga jinya dole ta koma wajen boka ya yi mata aiki da irin makamancin wannan abin ba zai sake faruwa ba.
"Haba miye haka don ALLAH Hajja sai ka ce ba ki san ƙaddara da sharrin magauta ba? Ni dai ya daka ba wani ba, kuma tun-tuni nace na yafe masa domin ba hali malam bane dukan macce kuma ma ai tsakani mata da miji sai ALLAH duk wanda ya shiga tsakaninsu rabonsa kunya saboda haka ki kyale min mijina.
"Innalillahi wai'inna illahim raji'un!
Anya kuwa Bahijja Haruna bai asirce ki ba kamar yadda kema ki ka asirce shi?"
Hajja tai subul da baka domin tsabar mamakin furuncin Bahijja da ya lulluɓeta bata masan takamaiman abunda take faɗa ba.
Ƙoƙari tashi zaune Bahijja take yi duk da ƙafarta guda tana sakale a jikin ƙarfe an yi mata pop ga Kuma hannunta tun daga tsitsiyar hannunta har izuwa ga shoulder ta shima lulluɓe yake da pop amma gani Hajja tana so ta ɓallo mata ruwa ta ɓata tsakaninta da mijinta, yasa ta yunƙuri tashi zaune, sai da duk iya yunƙuri da take yi ta kasa koda ɗago kanta daga pillow balle har ta iya tashi zaune.
Malam Haruna ya zura hannunshi cikin aljihun babbar rigarsa ya ciro farar takarda ya kalli Hajja da Bahijja a wulaƙancce ya shiga faɗin
"Kin ga Hajja ba zuwa nayi don ki shuka min rashin mutunci da ki ka saba shuka wa surukanki ba. zuwa nayi na kawo wa tsananniya 'yarki takarda saki domin ba zan iya ci-gaba da zama da ita ba.
Ya ƙarashe magana tare da cilla wa Hajja takarda akan fuskarta "gashi nan na saki Bahijja saki uku, tun jiya na kwashe kayan ta na aika mata dasu can gidan ubanta, a yanzu ko tsike bata dashi a gidana. Kuma yayana dukka na karɓe abina har wacce take wurinki na karɓe abata.
Yana ƙarashe magana ya nufi ƙofar fita ya buɗe ya fita abinsa yana ji Bahijja na ihu haɗe da kwalla masa kira, wani irin gunji kuka Bahijja take yi ashe haka saki yake da ciwo ashe irin wannan raɗaɗi da zafi ake ji a yayin da aka ce an sake macce, nan take ta tuna da Jeeddah ashe lokaci da suka sa aka sake Jeeddah saki uku irin wannan baƙin ciki ta ji. Jikin Hajja ya yi sanyi ta duƙa ta ɗauki takardar tana jujjuya ta kafin ta koma ta zauna, cike da baƙin ciki take kallon Bahijja dake zabga kuka tana sambatu marasa kan gado "Hajja kin cuce ni kin rabani da mijina Wallahi-azim ko da bala'i sai na koma gidansa na rantse da ALLAH ban saku ba.
Haka dai Aunty Bahijja ta ci-gaba da koke-kokenta tana haɗawa da sambatu tare da durawa Hajja laifi.
*****************
Ban yi ƙasa da guiwa ba na kira khamis na ce ya zo yau-yau ɗinan ya gabatar da kanshi ga Baba lokaci da na faɗa masa wannan magana ina ji sanda ya saki murmushi mai sauti gaske wanda na rasa na mene ne nan take na ji ya bani mugun haushi sai kawai na datse kiran ina mai jan dogon tsaki. Ban don inaso komawa gidan Bilal Shattima ba da ba abunda zai kaini da aure wannan ɗan iskan.
Da yamma sakaliya na fito cikin shirina riga da skirt na lace ne a jikina, ban ɗura ɗan ƙwali ba sai kawai na yane kaina da ɗan ƙaramin veil, ban yi makeup ba domin ni ba ma'abociya so kwalliya bace kawai dai na gogawa fuskata powder kana na zizzarawa idanuwana kwalli, na shafawa laɓɓana man leɓe, sai wani walkiya suke yi jikina na ƙamshin designer perfume wanda yana ɗaya daga cikin tsaraba da Ya Haidar ya kawo min. Na saka flat shoes a ƙafafuwana hannuna riƙe da handbag da car key kitchen na nufa wurin Mama na tsaya a bakin ƙofa na ce "Mama na tafi saloon a wanke min kaina daga can zan biya gidan khairat na duba Airah.
Mama ta dakatar da aiki da take yi ta juyo ta kalle ni tare da faɗin "wai Jeeddah miyasa ki ke so fitar yamma?" Yanzu ke da gidanan sai isha kin kuma san Babanku bayaso yawan fita nan naki.
Cuno baki nayi ina faɗin "Mama yau dai ba zan kai isha'i ba anan magariba za tai min.
"Shikenan a dawo lafiya ki gaida min da takwara ta.
"Tohm! Amma ba za ki ba da komai akai wa takwara taki ba Mama?"
Na faɗa ina dariya.
Murmushi Mama tayi gami da faɗin "Ai nayi ƙoƙari tun da har nace ina gaidata in Kuma kun rena gaisuwa tawa sai na fasa.
Da sauri na ce "a'ah mun gode ba sai kin fasa ba.
Na ƙarashe magana tare da juya wa ina kwallawa Musa almajiri kira dake falon Mama yana yiwa Aiman gugar kayanshi, ya amsa tare da fitowa Aiman yana biye dashi a baya "Musa mu je ka buɗe min gate zan fita.
Na faɗa tare da yin gaba da gudu Aiman ya sako takalmin shi ya biyo ni yana faɗin "Mommy zan bi ki.
Ba tare da na juyo na kalle shi ba na fara korafi "kai da kace ba ka da lafiya Mama ta goyi bayan ka, ka ƙi zuwa islamiyya shi ne yanzu kana ji zance yawo ka warke ko?"
Ya ƙaraso kusa dani yana dariya cikin sangartatciyar muryarsa ya ce dani "ALLAH Mommy da gaske bani da lafiya taɓa jikina ki ji har yanzu da raguwar zafi.
"Kai rufe min baki kafin na doke ka.
Nayi magana ina maka masa harara musa ya buɗe min gate ina unlock ɗin kofufin mota, har Aiman ya ri gani shiga na kalle shi kawai na girgiza kai nayi reverse na fita da motar yayin da Musa ya rufe gate yana min fatan a dawo lafiya.
Kaitsaye Ahmadu Bello way na nufa shagon Vicky wacce ta kasance classmate ɗina dama a gun ta nake wanke kai bayan ta kammala wanke min kai, na wuce gidan khairat anan nayi sallar magarib kafin na nufo gida akan hanyar mu na zuwa gida Aiman ya adabe ni sai na siya mishi ice cream dole na tsaya a Seven stars mall ina riƙe da hannunshi muka shiga mall ɗin kaitsaye gun da ake sayar da ice cream na nufa roba biyu ƙanana na siya ni da shi ina ƙoƙari fiddo kuɗi a jakkana, na ji murya Engr Ameer dab dani yana faɗin "Hajiya Maijiddah ice cream guda biyu bai yi muku kaɗan ba?" Ai ko yarona kaɗai zan iya shanye su a ƙara musu manyan guda biyar.
Ya ƙarashe magana yana kallona kafin nai magana har an ƙara ice cream ɗin ya kama hannu Aiman dole na saki dayan hannunshi dake ciki nawa, ya ja shi suka nusa cikin mall ɗin na bishi da wani irin kallon mamaki, sai kawai nayi zugun ina tambayar kaina "miyasa wannan ɗan taliki ke so takurawa rayuwata ne?"
Da nagaji da tsayuwa na juya har ice cream ɗin anan na barshi nai tafiya ta ina ji ma'aikatan wuri suna min magana nai banza dasu, na bude mota na shiga na zauna, lokaci zuwa lokaci nake kallon agogon mota na tabbata yau faɗa a wurin Mama sai na toshe kunnuwana.
Na ƙudurta a raina sai nai masa tijara domin banga dalili da zai sa yi min irin wannan shisshigi ba. Tsabar takaici ji nake kamar na tafi na barshi da Aiman ɗagowa da zan yi sai na hango su tafe yana riƙe da hannu Aiman yayin da ma'aikatan wurin ke biye dashi da 'yan uban shopping bags niƙi-niƙi har dasu keke yara wanda ko ban tambaya ba nasan Aiman ya siyawa, sai kawai na ji raina ya ƙara ɓaci ko uba wa ya gayamishi Aiman yana bukatar keke, bayan ko wannan tafiya da Ya Haidar ya yi sai da ya siyo mishi wani keke mai charging da wutar lantarki shi ma sai nayi faɗa don banga abunda zai yi dashi ba, baya kusan keke huɗu yake da dukka uku Ya Haidar ne ya siya mishi guda ɗaya ne Ya Kabeer ya kawo mishi fisibilillahi idan ba dafa masa keke zan yi ya ci ba, me zai yi dashi.
Knocking ɗin gilashi motar da ya yi yasa ni dawowa daga duniyar tunani da na lula cikin fusata na sauke gilashi kana na buɗe ƙofar front seat na kalli Aiman da ke ta faman haɗiyar chocolate yadda yake ci choco ɗin tsakani da ALLAH sai ka ce bai taɓa ci ba, wani mugun haushi ya ƙara turnuƙe ni, a hasale na daka mishi rikitatciyar tsawa "Aiman shiga mota mu tafi kuma kafin ka shigar min mota ka tabbatar ka jefar da wannan Choco dake hannunka. Idan muka je gida wallahi sai naci ubanka ba dai na sha faɗa maka ka daina karɓa abu a hannu strangers ba? amma da yake kai ɗin kwaɗayayye ne, shi ne ka karɓi Choco a hannu wannan mutumin mai siffar mugaye.
Da sauri Aiman ya jefar da chocolate ɗin tare da furzar da na bakinshi, yana goge bakinshi da bayan hannunshi, tuni idanuwanshi suka fara tara kwalla domin yasan halina mugun duka nake masa kuskure kaɗan zai yi min na kama shi nai ta duka cikin ma Mama tana tsawata min, kwata-kwata bani da haƙuri da yara. Mama na yawan faɗar da Aiman a hannuna ya taso da tuni duka ya kashe shi. Shiyasa babu wata shaƙuwa a tsakanin mu.
Jikin Aiman yana rawa ya kama murfi mota zai shiga karaf ya riƙe mishi hannu kana ya watsa min jajaye idanuwanshi, da babu komai cikinsu sai zallar ɓaci rai nima nawa ran a ɓaci yake na kalle shi a mugun fusace ciki tsawa na ce "Dallah malam! Cika min yarona mu tafi nagaji da wannan wulaƙanci naka.
"Idan kina da ƙarfi ki zo ki karɓi shi a hannuna.
Yana ƙarashe magana ya ɗauki Aiman ya nufi motarshi dashi, yayin da na bishi da kallo baki buɗe akan idanuwana, aka saka mishi shopping bags ɗin shi har ma da keke da nake zaton na Aiman ne a motarsa.
Cikin wani irin fushi na ɓalle murfin mota na fita, tsabar raina a ɓace yake ko gabana bana gani, ina zuwa na buge gilashi motarsa da ƙarfi.
Engr Ameer ya saki murmushi dama yasan dole ta biyo ɗanta ya saukar da glass ɗin ya wani zuba min idanuwanshi, a fusace na ce "Wannan wane irin kalar hauka ne ya za ka ɗauke min yaro baya ka gama ɓata min lokaci?
"Idan kina so na ba ki yaronki ki shigo mota mu yi magana just five minutes.
"Idan naƙi fa?
"Ba zan ba ki shi ba.
"Shikenan na bar maka shi kai ta riƙo.
"Wasa ki ke yi Habibty nasan ba za ki iya tafiya ki bar shi ba yadda ki ka tafi a fusace nan haka za ki dawo.
Ya yi magana yana dariya, na juyo a wani kalar hasale na ce "Za ka ga wasa gani idonka.
Daga haka na juya na shiga motata a harzuƙe na yi reverse na halba ta kan titi da sauri shi ma ya tashe mota ya bi ta a baya, ta mirror na hango yana bina, na ƙudurta da na fita round zan tsaya na karbi yarona. Sai dai abinda yai mugun ɗaure min kai ya kusa ya sumar dani bai wuce rashin gani Engr Ameer ba. Kusan five minutes Ina zaune a mota babu shi babu labarin sa, kafin nagama mamaki ina ya tafi min da yaro wayana ya yi ringing, na buɗe jakka na ɗauka Mama ce ke kirana kasa ɗauka nayi har sai da kiran ya tsinke. Nai maza na dannawa numbershi call sai dai har wayar ta ƙarashe ringing bai ɗaga ba. A takaice sai da na jera masa kira goma jere da juna amma ɗan taliki nan yaƙi picking up. Abu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Cikin mutuwar jiki na buɗe mota na fito na gani koda ya yi parking nesa dani, kiran khamis ne ya shigo wayata tsaki na ja tare da yi disconnected duk da haka sai da ya sake kira, kusan kira biyar khamis yai min ina disconnected can kuma sai ga Baba ya kira ni anan kam ido ya rena fata don ban san sanda na fashe da kuka ba. Kira uku Baba ya yi min amma ban ɗauka ba. Na ƙudurta a raina muddin na haɗu da Ameer ya bani yarona wallahi sai nayi masa wulaƙanci da kaff a tarihin zamansa na duniya ba a taɓa yi masa makamancin sa ba. Sai naci zarafinsa sai na zagi ta uwa da ubansa. Zagin ƙare dangi zan masa.
Haka na shiga mota na sake komawa Seven stars mall, har ciki na koma na tambaye ma'aikatan wuri koda sun ga ya sake dawowa nemana, amsar da suka bani saura kaɗan zuciyata, ta buga a haka na fito na sake shiga mota sai gani na buge da bin titunan ina neman Ameer ina rera kuka ga baki ɗaya dabara ta ɓace min. Har na nufi hanyar gida sai ga Ya Haidar ya kira ni, ai kuwa da mugun sauri na saka signal na gangara gefen titi nayi parking, da azama nayi picking "Hello....Honeypie!
Ya Haidar ya faɗa cike da shaukin son sa'ili da ya ji nayi picking up, sai kawai ya ji na fashe mishi da matsanancin kuka, a firgici ya tashi tsaye daga zaune da yake "Subhanalillah! Jeeddah mene ne me ki ke yiwa kuka?"
Jin muryarsa kaɗai da nayi na ƙara ji wani irin mugun rauni a zuciyata domin shi kaɗai ne mutumin da a koda yaushe yake taimakona a duk sanda na shiga matsala ko damuwa ba tare da yaga laifina ba koda ya kasance ina da laifi ɗin.
"Ya....Hai....dar.....Ai....man...
Na faɗa cikin sarƙewar murya domin kuka da nake yi bana wasa bane ambatar sunan Aiman ya ƙara masa tashin hankali "me ya sami Aiman?
"Ya ɓata Ya Haidar wani mutum ya tafi dashi bansan inda zan ganshi ba.
"Innalillahi wai'inna illahim raji'un! Hasbunallahu wal-imal wakil! Jeeddah a gari ya ya Aiman ya ɓata?
"A Seven stars na je siya mishi ice cream shine ya ɗauke shi ya tafi dashi.
"Ke kuma kina aiki me har ya tafi dashi?"
Ya Haidar ya faɗa a tsawace alamar na bashi haushi ba kaɗan ba, gani haka sai kawai na ƙara wa kukana sauti, dama nasan abunda ya tsana kenan cikin sauri ya ce "Ya isa ki daina kuka ganina zuwa kina ina yanzu?"
"Ina kan titi sama Road.
"Okay ki jira ni anan kada ki ɗaga ko ina kina cikin wannan hali ba za ki iya driving cikin natsuwa ba.
"Uhmm!
Na faɗa tare da hanging up sai lokaci na ji zuciyata ta ɗan yi sanyi ko ba komai zan sami mai taimaka min.
Cike da tashin hankali Ya Haidar ya fito farfajiyar gidansu yana kwallawa direban Mommy kira da gudu ya zo "Rabi'u mu je ka kaini sama Road.
Haidar ya faɗa yana miƙa mishi key ɗin mota da high speed suka iso yana shiri kirana sai kawai ya hango ni tsaye jikin motata, ina juyawa naga Ya Haidar ya nufo ni da saurinsa, kasa jira nayi ya ƙaraso na kwasa da gudu na isa gare shi ina zuwa na faɗa jikinshi na ƙanƙame shi ina wani irin gunji kuka na fitar hankali. Bubbuga bayana ya shiga yi tare da faɗin "Banaso kuka nan Jeeddah ya isa in-sha-ALLAHU za a ganshi ina ji a jikina Aiman bai ɓata ba.
Sai gyaɗa kai nake yi kusan three minutes muna tsaye yana aikin rarrashina da kyar nai shiru ya cire ni daga ƙirjinshi ya riƙe min hannu muka nufi motata, sai da ya zaunar dani kana ya zauna a driving seat ba tare da ya tashi mota ba, ya kalle ni gaba ɗaya nayi wani irin zuru-zuru, idanuwana sun kumbura sutum. Cikin sanyi murya yake tambayana yadda Aiman ɗin ya ɓata gani hali da nake ciki babu saura wani ɓoye-ɓoye da zan masa, ciki sadda kai na bashi labari tun daga farko haɗuwa ta da Engr Ameer har kawo yau da zafin kai ya ɗebe ni na bar mishi Aiman tun sanda na fara magana Ya Haidar ya kafe ni da idanuwanshi bai taɓa ji haushi da takaicina irin yau ba. har baisan sanda ya finciko ƙafaɗata ya juyo dani na fuskance shi ya kifa min wani mugun mari zan iya cewa yau ne rana ta farko da hannu Ya Haidar ya sauka a jikina da sunan duka.

#Haidar Ka'oje
#Engr Ameer
#Jeeddah maishadda
#Aunty Bahijja
#Malam Haruna
#Hajja
#Team zazzafan kishi.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now