060

124 9 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!* _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

060

Ina dafe da kuncena nake kallonshi fuskarshi cike da wani irin kalar fushi wanda tsawon zamana dashi ban taɓa gani ya yi makamancin irinsa ba. Ya sake fizgo ni da ƙarfi tamkar zai ƙarya min kafaɗa cikin kakkausar murya yake faɗin. "Ashe ba ki da hankali Jeeddah?" ashe haukar naki har kai, ki saka rayuwar yaro ƙaramin cikin hatsari. Wannan wane irin daƙiƙanci ne? Halan babu ƙwaƙwalwa a kokon kanki ne Jeeddah?" Da za ki tafi ki bar ɗa da ki ka haifa da cikinki a hannu mutumin da ba ki sani ba.
Sake fashewa da kuka nayi cikin muryar kuka na ce "Wallahi Ya Haidar a lokaci raina ne yai mugun ɓaci shiyasa amma na rantse da ALLAH bana nufi....
"Rufe min baki sakarya uwa kawai. Na rasa laifin me Aiman ya yi miki da ya cancanci wannan kiyaya daga gare ki. Watakila mutumin nan ko mai garkuwa da mutane ne ko kuma mai satar yara. Kawai dai zafin kanki ya ba ki, ki tafi ki bar mishi yaronki.
"Ya Hai.....
"Nace ki rufe min shiru banaso ji kalma ko ɗaya tak! Ta sake fitowa daga bakinki.
Dole na haɗiye kalamaina sai na ci-gaba da rera kukana yayin da Ya Haidar ya ci-gaba da babbaka min faɗa abunda ba halinsa ba. "Da kinsan bakyaso Aiman salwantar da shi za ki yi ta wannan hanyar dani kin bar min shi, saboda ina sonshi tamkar yadda nake so numfashina ban taɓa kallo Aiman a matsayin ɗa Bilal Shattima ba. Face ɗan da na haifa da jinin jikina, Jeeddah Aiman yaro ne mai shiga rai, yaro ne mai wata irin bawa wacce rashin kulawar ku daga ke har wancan nusari uban nashi ku ka kasa ganewa. Ga shi nan sanadi sakarcin ki, kin jefa rayuwarsa a hatsari.
Tsabar tashin hankali da Haidar ya shiga gaba ɗaya rigar jikinsa ta jiƙe da zufa ga wani irin hawa da sauka da numfashinsa ke yi a dalili faɗa da yake yi ciwon sa na ƙoƙari tashi da sauri ya ɓalle murfin mota ya fita, yadda yake dambe da numfashinsa ya ƙara linka tashin hankali da nake ciki da sauri na fito, na tsaya gabanshi tare da ƙoƙari riƙe mishi hannu da wani irin zafin nama ya janye hannunsa gami da nuna ni da yatsa yana sauke numfashi ɗaɗɗaya ya ce "Kar kuskura ki sake yunƙuri taɓa ni.
Wannan kashedi da yai min yasa ni dole matsawa nesa dashi ina shasshekar kuka. Mun ɗauki lokaci a tsaye kafin ya samu daidaituwar numfashinsa. Ba tare da ya kalli gun da nake ba ya ce "Shiga mota mu tafi police station gara mu yi gaggawa kai musu report.
Da sauri na zagaya na shiga domin ni yanzu Ya Haidar ya dasa min tsoronsa. Mun kusa isa police station sai ga Engr Ameer ya kira wayana, jikina yana rawa gami da wani irin bugawar zuciya na kalli Ya Haidar muryarta yana cracking na ce "Ya Haidar shi ne yake kira. Da sauri ya ce "Yi maza ki yi picking kuma ki saka wayar a handsfree. Da kuwa sauri na bi umarninsa gaba ɗaya muryar Ameer ta karade cikin motar "Hello....My Habibty nasan zuwa yanzu nayi magani wannan tsiwar taki, ko ba haka ba Habibtynaaaa?"
Ya wani ƙarashe magana yana jan sabon sunan da ya laƙa min.
Wani irin kuka ya subuce min cikin muryar kuka na ce "Don girman ALLAH Ameer kada ka cutar min da yaro ka faɗa min me ka ke buƙata gare ni amma don ALLAH ka dawo min da Aiman ɗina.
Haidar ji yake kamar ya finciko wayar ya ɗuɗɗura mishi ashar amma kuma sai yake gani da zarar ya yi magana watakila zai katse kiran, shikenan sun rasa Aiman shiyasa ya shiga kokari danne fushinsa, saboda haka sai wani irin huci yake yi tare da fesar da zazzafar iskar daga bakinshi.
"Ni fa Habibty ba wani abu nake buƙata mai yawa daga gare ki ba kuma ni ban yi garkuwa da yaronki ba asalima kece ki ka yi fushi, ki ka bar min shi ni kuma tun daga kallo ɗaya da nai masa ALLAH ya dasa min ƙaunarsa a zuciyata, wallahi-azim Maijiddah ko akuya ce ta kasance mallakin ki ba zan iya cutar da ita ba balle ɗan da ki ka haifa da cikinki. Ashe idan na cutar da Aiman soyayyar da nake miki ba ta gaskiya bace.
Ɗagowa nai na kalli Ya Haidar ya maka min wata kafira harara, da sauri na kauda fuska na sake cewa "To idan abunda ka faɗa gaskiya ne Ameer ka faɗa min inda ka ke na zo na karɓe shi wallahi ina cikin tsanani tashin hankali.
'yar dariya ya yi tare da faɗin "Ai nasani dole ki shiga tashin hankali Maijiddah da gangan na tafi domin na hora ki koda gobe kin yi fushi ba za ki sake yunƙuri bari yaronki a hannun stranger. Ko ba haka ki ka kira ni dashi ba?"
Ban sanda na sake fashewa da kuka ba ina faɗin "Na tuba ba zan sake ba Ameer ka rufa min asiri ka faɗa min inda ka ke kada ka zama silar bugawar zuciyata.
"Okay...naji zan faɗa miki amma banaso na sake ji ki ambaci bugawar zuciyarki. Ki duba inbox ɗin wayarki tun ɗazu na turo miki da address ɗin gidana.
Ya ƙarashe magana yana dariya ƙasa-ƙasa da sauri na yanke kira na duba naga one new message almost one hour ago da ya turo shi, da ƙarfi Ya Haidar ya fincike wayar ya karanta address ɗin, rai ɓace ya ƙara taka mota, a maimakon mu nufi police station kamar yadda ya ƙudurta tun farko sai naga ya sauya hanya. A rikice na kalle shi da firgitattu idanuwana masu cike da zallar tsoro muryata tana rawa na ce "Ya Haidar akwai hatsari mu tunƙare shi, mu kaɗai Why not mu fara zuwa police station?"
Kafin ya amsa min sai da ya zuzzuba min harara kana cikin zallar takaicina ya ce "Ke wacce irin mahaukaciya ce? Wato kanki kawai ki ka sani bakya tunani wane irin hali Aiman yake ciki. Idan muka je police station kafin su gama daukar statement, wani ɓata lokaci ne. A shirye nake da na tunƙare wannan mutumin komai hatsari sa muradina nai ido huɗu dashi.
Gaba ɗaya jikina ya yi mugun sanyi nasani Ya Haidar yana ƙaunar Aiman sosai yana bashi kulawa ta musamman fiye da mahaifinsa Bilal Shattima da yake Bilal irin mutane nan ne da ba su damu da 'ya'ya ba. amma ban taɓa tsammani ƙaunar da yake masa tayi zurfi har haka ba.
Ikon ALLAH ne ya kawo mu ƙofar gidan da Ameer ya turo min da address sabuwar unguwa ce da babu mutane sosai, amma duk da haka Ya Haidar bai karaya ba. Kanshi tsaye ya danna horn maigadi ya buɗe mana gate Ya Haidar yana danna hanci mota a farfajiyar gidan muna hango Engr Ameer tsaye jingine jikin motarsa ga Aiman sabe a ƙafaɗarsa yana bacci. Ya Haidar ya taka wani mahaukaci brake cikin zafin nama gami da tafarfasa zuciya ya ɓalle murfin mota ya fito, kaitsaye ya dumfari Engr Ameer nima da sauri na fito na bi bayan shi, wani irin zubawa Haidar Ka'oje idanuwa Engr Ameer ya yi yayin da wani irin ƙololon takaicinsa mai haɗe da kishi suka ya tsaya masa a maƙoshi. Haidar yana zuwa abu na farko da ya fara yi, finciko Aiman da ƙarfi daga ƙafadarsa, juyowar da Engr Ameer ya yi cikin fusata Haidar bai tsaya wata-wata ba ya ɗauke fuskarshi da matsiyacin mari, har sai da ya dafe kumatunsa na hagu da ya mara yana ɗagowa a mugun fusace nima ina ɗauke shi da mari a ɓari kunce sa na dama sai kawai ya dawo da ganinshi kaina ya zuba min rinannu idanuwanshi yai wani kalar ɗage gira ni kuma ina masa kallo mai ɗauke da gundari tsana kafin na ƙyasta mishi yatsuna akan fuskarshi na shiga kashe mishi gargaɗi "Ina gargaɗinka da kakkausar murya daga yau daga rana mai kama da yau kada ka kuskure ka sake zuwa inda nake na tsaneka wallahi. Kai mugu ne baƙin azzalumi...
Kafin na ƙarashe magana Ya Haidar ya jawo ni ya miƙa min Aiman wanda tuni ya falka daga bacci da yake yi, sai rarraba idanuwa yake, kana ya maye gurbina ya tsaya gaban Ameer, ba za ka iya tantance tsakanin su biyu wanne yafi harzuƙa ba. Cikin matsanancin fushi Haidar ya kai wa Ameer nushi cikin sa'a ya same shi a hanci da yake Haidar ya fi shi tsayi wani irin mahaukaci zafi Ameer ya ji ya ziyarci shi a hanci, bai bari ya wartseke ba ya rama nushin sa, shi ma ya sami ya Haidar a chest, haba nan take ƙazamin dambe ya barke a tsakaninsu maigadin Engr Ameer ya iso da gudu ya dinga ƙoƙari raba su yayin da Jeeddah ta fashe da ihun kuka domin duk abunda yake faruwa ita ce sila, kururuwar da Jeeddah ke yi yasa mahaifiyar Ameer fitowa "subhanalillah! Waye kai da za ka shigo har cikin gidana ka kama yarona da kokawa?"
In ji Umma sa'ili da ta ƙaraso tare da ƙoƙari ɓamɓare Haidar daga jikin Ameer da kyar Umma da maigadi suka yi nasara raba su Umma ta fashe da kuka tare da ƙanƙame Ameer tasan halinsa da baƙar zuciya, zai iya aikata mummunan abu akan Haidar yayin da Haidar ya nuna shi da yatsa yana huci alamar gargaɗi "Wannan shi ne kashedi na farko kuma na ƙarshe da zan maka ka fita harka iyalina idan ba haka ba na rantse da ALLAH kotu ce za ta raba mu. Banza baƙin jahili.
Ameer ya yada ganinshi akan fuskar Haidar ga mamaki Haidar sai yaga ya sakar mishi wani ƙazamin murmushi ya ce "Sai dai ka yi haƙuri domin zuciyata ta riga ta nutse a kogin son matarka, idan duk mutane duniya za su taru akaina ba zan daina sonta ba. Ina mai tabbatar maka komai dare daɗewa sai na cika burina akan Maijiddah idan Ameer ya ce yana son abu kasani duka da zagi ba sa tasiri akansa ko na juya baya sai dai ma su daɗa ƙara min ƙaimi. Wannan duka da ka yi min ba abunda ya rage min daga cikin soyayyar da nake wa matarka, sai ma ƙara min sonta da ya yi.
Wani irin ture Ameer ummanshi tayi tare da kifa mishi mari, tsabar takaicinsa da gama lulluɓe ta kasa magana sai kawai ta zuba mishi idanuwanta da suka take fidda kwalla.
Wani irin zubura Haidar ya yi da nufi sake tunƙarar shi da sauri Jeeddah ta sauke Aiman ƙasa ta riƙe shi "Don ALLAH Ya Haidar ka yi haƙuri ka zo mu tafi in yaso gobe mu kai wa 'yan sanda report gwada ka bari hukuma ta ɗauki mataki akanshi, domin wannan da ganinsa mugun criminal ne.
Ba don Haidar yaso ba ya kyale shi sai don kukan da Aiman ya fara yana rirriƙe shi kamar yadda yaga Jeeddah tayi, duk da haka sai da ya nuna Ameer da yatsa cikin kakkausar martini ya ce "To shikenan idan har ka cika cikakken ɗan iska ka bari na sake ganinka kusa da matata na rantse da ALLAH sai dai uwarka ta sake haifar wani ba kai ba. Ya ƙarashe magana a matuƙar fusace kana ya sunkuce Aiman ya nufi mota da gudu Jeeddah ta bi su a baya da ƙarfi ya ja mota yayin da maigadi ya danna da gudunsa ya buɗe masa gate. Ameer yana cika yana batsewa ya nufi entrance ɗin gida yana wani kalar sauri kamar zai tashi sama, umma ta bishi tana kira sunan shi "Ameer! Ameer! Ameer na ce ka tsaya ka saurareni ko kuma ranka ya ɓaci.
Ameer ko waigo wa bai yi ba ballantana Umma tasa ran zai saurare ta. Yana isa cikin parlor Umma tana kama rigarsa ta baya ta jawo shi da karfi, cikin wani irin mugun fushi ya juyo tamkar zai kai mata bugu kana cikin tsawa da hargowa ya ce "Ki rabuda ni Umma ki tafi ki bani wuri bana so gani kowa kusa dani Maijiddah kaɗai nake so, dole na mallaki Maijiddah Umma koda hakan yana nufi zan kawo ƙarshen numfashin wancan ɗan iskan mijin nata.
Yana dasa aya a zance sa Umma tana sake ɗauke shi da tagwaye maruka. Sannan kuma ta fashe da matsanancin kuka, cikin sauti kuka take faɗin "Ameer ka natsu kasan irin maganganu da suke fitowa daga bakinka. Kada ka jefa rayuwarka a hatsari, wannan wane irin toshewar basira ne ya same ka na son matar aure? Haba Ameer wannan wane irin son zuciya ne? Ka bar yarinya nan ta zauna lafiya da mijinta Idan har ni na haife ka Ameer a karo na biyu ina ƙara gargaɗinka ka fita sabgar Maijiddah. Ka yi gaggawar cire ta daga zuciyarka.
Umma tana ƙarashe magana ta juya ta nufi ɗakin bacci ta zuciyarta na mata wani irin zogi, tasan duk wannan abu da Ameer yake yi ba yin kansa bane ciwo da yake ɗauke dashi ne ke sa shi aikata abubuwa da hankali ba zai ɗauka ba.
Yadda Haidar ke sharara gudu akan titi za ka zaci cewa don shi kaɗai aka shimfiɗa shi. Inaso nai masa magana nace ya rage gudu amma ina jin tsoro saboda haka sai ƙara ƙanƙame Aiman nayi koda muka iso ƙofar gidanmu 10:33pm daidai sai wani irin bugawa ƙirjina ke yi ina cike da fargaba haɗuwar da Mama da Baba baisan irin amsar da zan basu ba ina nan ina tunani har Ya Haidar ya fita ya buɗe gate ya dawo ya shigar min da motata ciki, kana ya fito ya buɗe side ɗin da nake zaune nayi zugun gaba ɗaya na dawo kalar tausayi, ya ɗauki Aiman daga jikina ya nufi cikin gida na bishi da kallo kafin na sauke naunanye numfashi, kana na fito tare da kule mota Cikin mutuwar jiki na bishi a baya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ina zuwa tsakar gida na tsaya cak! Sakamakon muryar Mama da naji tana sallati gami da tafa hannuwa "To wai a gari ya ya Aiman ya ɓata?
Sai kawai na ƙara baza kunnuwana na ji wacce amsa Ya Haidar zai bata kusan gogan naku miskili ne maganarsa can ƙasan maƙoshi yake yi ta dole sai da na cire ƙafafuwana na nufi baƙin ƙofar shiga parlorn Mama na rakube, kana na ji abunda ya faɗa "A Seven stars mall ne ta je siya mishi ice cream Mama kinsan hali Aiman da ƙiriniya sai da ya bari hankalin Jeeddah ya dauku ya sace jiki ya fita daga cikin mall ɗin.
"A'ah! Aliyu kawai dai kana ƙoƙari kare Jeeddah ne kawai amma kowa yasan halinta na sakaci da sakaryaci.
"Mama ba kare ta nake yi ba hakikanin abinda ya faru ne, na faɗa miki.
"Ni fa Aliyu duk abinda za ka faɗa ba zai sa na daina ganin laifinta ba. Babban takaicina da Jeeddah bata tsira shegen yawonta na tsiya sai taga yamma tayi liss! Sai ka gannta tafe da jakka sai kace jikar wanzamai tana wani maƙe murya tai min daɗi baki ta fita. To wallahi bari ta shigo daga yau na soke fitar yamma, ba don da ALLAH ya takaita mana wahala ba aka ga yaro nan ciki sauki da yanzu ta haifar min da hawan jini.
"Kin ga Fatee kada ki bi ki daurawa yarinya nan laifi shi fa tsautsayi idan ALLAH ya kawo shi ba wanda ya isa ya hana, kamata ya yi ki godewa ALLAH da yasa aka ganshi.
Baba ya faɗa cike da so kawo ƙarshen mita Mama.
Ƙarfaffiyar ajiyar zuciya na sauke ina ƙara godewa ALLAH tare da Ya Haidar da ya kare ni da bai faɗi takamaiman abunda ya faru ba da yau na shiga uku don mai hana Mama ta ci ƙaniyata sai ALLAH.
Ina ji Ya Haidar yai musu sallama zai wuce gida sai na ji Mama ta ce "To wai ita Jeeddah ina ta tsaya ne?
Kafin Ya Haidar ya bata amsa nai wuff na faɗa ciki parlor, ina faɗin "Gani Mama.
"Auu.... laɓe ki ka yi mana.
Na kasa magana sai kawai na sadda kai ƙasa Ya Haidar ya miƙe yana faɗin "Ni zan wuce sai da safen ku Baba.
"Sai da safe Aliyu ALLAH ya tsare ya kai ka gida lafiya.
Baba ya faɗa ina gani ya fita nai wuff na bi shi ina faɗin "Mama bari na bashi key ɗin motata saboda bai zo da mota ba.
Gudu-gudu na bishi a baya gami da kwalla masa kira "Ya Haidar! Ya Haidar tsaya ka karɓi key.
Ya tsaya ba tare da ya juyo ba na ƙaraso kusa dashi sai ina kallonsa naga yadda ya murtuƙe fuska babu annuri ko misƙara zarrati akanta, nai sauri miƙa masa key ɗin ya fizge shi da ƙarfi ni na buɗe masa gate ya fita ina kokari yi masa godiya ya ja motar da kafiri gudu ya barni tsaye da baki buɗe. Can kuma na taɓe baki a fili na furta "Can ta matse ma mai baƙar zuciya.
Na maida gate na rufe kana na wuce cikin gida kaitsaye ɗakina, na shige na cire kayan jikina nayi wanka har bacci ya fara fizgata na ji ringing ɗin wayata ina jin ringintone ɗin nasan Bilal Shattima ne mai kirana saboda special ringintone nasa masa. Cikin kasalalliyar murya nai mishi sallama a maimakon ya amsa min sallama da nai masa sai kawai na ji ya rufe ni da faɗa "wannan wane irin wulaƙanci ne Jeeddah? Ya za ki ce khamis ya zo sai da yazo kofar gidanku ya kira wayarki ki ka ƙi picking ya aika yaro a kira ki aka ce kin fita.
"Uhm! Wallahi Love kana da muguwar matsala da kasan abinda ya faru dani a yau ɗinan da sai ka tausaya min.
Jin abunda ta faɗa yasa shi sassauto wa daga fushi da ya hau ya ce "Subhanalillah! Me ya faru dake love wallahi ba ki ji yadda gabana ya yi mummunan faɗuwa ba?
Na kwashe irin karya da Ya Haidar ya shimfiɗa wa su Mama na faɗa masa ya nuna alhininsa a fili sai kuma ya sake dauko min zance khamis.
"Jeeddah ni fa so nake Baba yasan da zaman khamis kafin ya turo da iyayensa.
"Wannan ba abin damuwa bane Love zan kira shi gobe ya zo, kafin ma ya zo zan faɗawa Baba yasan da zuwan nasa.
"Shikenan Love ALLAH ya kai mu gobe.
"Amin!
"Love!
"Na'am Love!
Na amsa mishi ina narkar da murya.
Haka da tayi ya ƙara rura wutar abunda Bilal Shattima ya ke ji akanta.
"Love Please ki kunna Data mu yi video call kinsan kwana biyu nan bana gane kanki ba ki ga yadda nayi rama ba duk tumbin nan nawa da ki ke complain ya ɓace fatt!
Yana ƙarashe magana na kwashe da dariya cikin shagwaɓe murya na ce "Kai love anya kuwa wannan maganar taka gaskiya ce?
"To ki buɗe Data ki gani da idanuwanki.
Ina dariya na katse kira kana na kunna data jim kaɗan kiran shi ya shigo da alama already yana online, sai da na ƙara gyara kwanciyata kana nai picking up, idanuwana suka sauka akan mummuna fuskar nan tasa daga shi sai farar vest a jikinshi. Wani irin mushriki kallo yake min ni kuma na ɗage girar ido ina wanke shi da ƙayatatce murmushi.
"Love a kullum ƙara kyau ki ke yi kalli yadda ƙirjinki ya ƙara ci-cikowa kamar balan-balan fatar jikinki sai glowing take yi, wallahi har tsikar jikina ya fara zuba Love kin yi bala'i tayar min da hankali fa.
Bilal Shattima ya faɗa cikin wata 'yar iskar murya yana kashe min farara idanuwanshi. Ƙara faɗaɗɗa murmushin kan fuskata nayi tare da yi fari da idanuwa ina faɗin "Ba wani nan koda ma na tayar maka da hankali kana da wurin zuwa da ka ci-gaba da jin sauyi a jikin ka kashe min waya za ka yi ka je ɗakin matarka ku kashe fitila.
Na ƙarashe magana cikin azababben kishi.
"Mtssss! Don ALLAH Love idan ina maganar akanki ki daina sako min zance wancan sokuwa mata, abunda ba ki sani ba wallahi Nusaiba bata da ni'ima ko kaɗan gaban nan nata a bushe yake ƙamass! Ga ɗan banza abun nata a wage kamar ƙofar kasuwa duk da fa kullum cikin shan kayan mata take ta sha wannan ta cusa wancan, ta lashe wannan amma duk a banza, kana jefa guga sai da ka ji zudum!
Ai bansan sanda na fasa wata uwar dariya ba yana tayani sai babbaka dariya muke yi sai kace waɗanda suka shuka abin arziki.
Daga nan muka buɗe shafi hira duk rabin hirar ta mu zagin Nusaiba ne yake yi, musamman da ya fahimci hakan yana sa Jeeddah nishaɗi sai ƙara aibanta Nusaiba yake yi.
Su Bilal Shattima an shagala sosai sai suburbuɗo zance yake yi, ga wani shaƙiyi murmushi shimfiɗe akan munafukar fuskarsa.
Abunda bai sani ba tun lokaci da ya fara waya da Jeeddah Nusaiba take tsaye jingine da ƙofa kasancewar kofar a buɗe take shiyasa bai ji shigowarta ba.

#Bilal Shattima
#Haidar Ka'oje
#Jeeddah maishadda
#Nusaiba
#Aiman Shattima
#Team zazzafan kishi.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now