053

85 7 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

053..

Baƙar harara na bankawa wayata ina kallo har kira ya tsinke ya sake kira shima ya tsinke ban ɗaga ba. Sai harara nake zubawa wayar sai kace ita ce tai min laifi sai da Bilal Shattima ya jera min 21 missed call kafin na ɗauki wayar a mugun fusace nai switch off ɗin ta. Knocking ɗin ƙofa aka yi sai da na kalli wall clock naga 10:10pm kafin nai wani yunkuri naji an turo ƙofa an shigo jajaye idanuwana na sauke akan kyakkyawar fuskarshi ma'abuciya kyau da kwarjini jikinshi sanye da pyjamas sky blue in colour ba ƙaramin kyau yai cikin kayan "Ya Haidar kenan ba dai kyau ba.
Na faɗa cikin zuciyata "Assalamu alaikum!
Ya furta cikin zazzaƙar muryarsa mai daɗi da gardi ga kunne ma'abuci sauraren ta.
   Cikin sanyi murya na amsa mishi da "Wa'alaikum Salaam! Ya Haidar ashe kana ganowa?
Kyakkyawan murmushi ya saki min wanda yai bala'i ƙara masa kyau tsanani kyau da yai min har ban san lokaci da na mayar mishi da martani murmushinsa ba.
   "Jiddoh kenan ai ko zan yi wuyar gani ga kowa ban dake kawai dai na ba ki space ne banaso taƙura miki amma ba don haka ba kema kinsan ni mugun mayyenki ne. Ban ƙi na zauna a gabanki na share wuni guda daga safe har faɗuwar rana ina kallon wannan kyakkyawar fuskar taki mai daɗa ƙara jefa ni a kogin sonki.
  Ya ƙarashe magana tare da kai hannunshi kan kumatuna ya shafa da sauri na buge mishi hannu na yunƙura na tashi zaune kusa da ƙafafuwana ya zauna.
  "Ya ciwon kan naki ya daina ko za mu tafi asibiti ne?"
Ya tambaya with so much care na kauda fuskata domin a dalili tunawa da nayi da Bilal Shattima yana can yana more darenshi tare da amaryarsa ni kuma yabar ni cikin ƙunci da suyar zuciya, kafin na dawo daga zance zuci da nake yi Ya Haidar ya kafanɗuna ya dawo da fuskata izuwa kallonshi "menene hakikanin abinda yake damunki jikina ya bani ba Headache kadai bane akwai wani abu na dabam faɗa min menene shi?"
Ƙoƙari janye fuska ta nake yi amma ya hanani cikin rawar murya nace "Ba komai Ya Haidar zan kwanta bacci nake ji.
  "Ban yarda dake ba jiddoh domin a duk lokaci kina cikin damuwa koda ba ki kusa dani zuciyata tana bayyana min, saboda haka ki faɗa min damuwarki a matsayina na yayanki wanda ya damu da damuwarki.
   Maganganu shi suka ƙara karye min zuciya dama mai neman kuka an jefe shi da kashin awakai sai kawai na fashe mishi da matsanancin kuka cikin shasshekar kuka nake faɗin "Ya Haidar a yau amaryar Bilal Shattima ta tare gaba ɗaya wani irin zafi zuciyata take min na rasa me yake min daɗi, ji nake kamar na haɗiye zuciya.
Na ƙarashe magana ina mai sake rushewa da kuka.
  Shiru ya yi yana kallonta ya fahimci from the bottom of her heart take kukan nan kafin ya matsa kusa da ita ya riƙo hannunta na dama ya haɗe da nashi cikin kwantar da harshe ya shiga faɗin "Ni banga abin kuka da ɗaga hankali ba Jeeddah! Ki ɗaure ki ɗauki rabuwarku a matsayin rubutacciyar ƙaddara, ki yi ƙoƙari ki fitar dashi daga cikin zuciyarki domin tun da ki ka ga ya tare da amaryarsa to alama ce da ke nuni da cewa shi ɗin ya fara taka matakin farko na goge babinki daga cikin rayuwarsa.
  Kalaman Ya Haidar suka ƙara dagule min lissafi sai kawai na sake rushewa da wani sabon kuka, da kyar ya rarrashe ni nayi shiru da ya tambaye ni naci abinci na girgiza kai ya tashi da sauri ya fita sai gashi ya dawo yana gaba mai aiki Mommy Turai tana biye dashi ɗauke da ƙaton tray da warmers a sama ya nuna mata bedside drawer ta ajiye kana ta fice da kanshi yai min sarving ya tsare ni sai da naci abinci nan sosai raguwar wanda na rage ya ci sannan ya fita da kwanuka koda ya dawo na shiga bathroom nayi fitsari haɗe da yi brush. Na fito tare da komawa wajen zamana na zauna ya shiga yi min hira mai daɗi cikin ƙanƙani lokaci na nemi damuwa ta na rasa ni ce har da su dariya sai da ya ga ina hamma akai-akai sannan yai min sai da safe ya fice. Nayi addu'a gami da kwantawa sai dai na ƙasa bacci na lula tunani rayuwata ta nan gaba. Ni kaina nasan Ya Haidar yana matuƙar ƙaunata, ƙauna irin wacce babu algusu a cikinta zan iya cewa Ya Haidar yafi Bilal Shattima sona sai dai duk da irin tsanani ƙaunar da yake min har yanzu na kasa tsaida zuciyata akanshi

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now