058

99 11 2
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

058

Girgiza kai Nusaiba tayi cike da tausayi kanta take kallon fuskar mahaifinta da ya zaƙalƙale yana wanke mata allonta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Ita kaɗai tasan iri-iri kaloli wulaƙanci da take shanye wa a gidan Bilal Shattima. Wulaƙanci yau daban na gobe daban, matuƙar za ta faɗi wata mummunar kalma akan Jeeddah to kuwa zai ƙare mata zagi ƙare dangi wani lokaci har da su duka ya sha faɗa mata akan Jeeddah zai iya tsitsika igiyoyi aure ta. Tun jiya da ya sami matsala da Jeeddah tayi fushi dashi ya kira wayarta yafi a kirga taƙi receiving call ɗinshi, shikenan ya bi ɗaga hankalinsa. Daga karshe ya sauke haushinsa akan Nusaiba hadda su maruka ya ɓaɓɓala mata.
********
Washegari sai misali ƙarfe 10:30am na tashi daga bacci shima don Mama ta tashe ni ne da wallahi sai 11:00am zan tashi, tunawa da nayi da haukar da wancan mutumin ya yi min a wuri aikina yasa yau kwata-kwata bana ji sha'awar zuwa office saboda haka na fake da mura da nake yi. Wanka nayi tare da shiryawa ciki atamfar chiganvy pink colour mai ratsi fari da baƙi ɗinki fitted gown rigar ta ɗan kama ni sosai a dalili kwana biyu ɗinan na ƙara ƙiba ina ciki fesa turare na ji wayana ya yi ringing sai da na ja tsaki "mtsssss! A zatona Bilal Shattima ne haka jiya ya dame ni da kira kamar naci bashin sa sai da nagaji nayi switch off ɗin wayata sa'annan na sami lafiya. A fusace na nufi wayar dake aje a gefen pillow da na tashi akai sunan wancan mutumin naga yana yawo a sensor ɗin wayata, dama ina neman ya kira na ƙare masa tanadi da na tanadar masa nayi receiving call ɗin tare da kara wayar a kunnena na dama a daƙile na ce "Ya aka yi ne Malam?"
  Wata ƙarfaffiyar ajiyar zuciya na ji ya sauke kafin cikin kwantar da murya ya ce dani "Ki yi haƙuri Maijiddah nasan abunda nayi miki jiya kwata-kwata ban kyauta ba. Ki yi min uzuri kasancewa ta mutum mai sauri fushi da zafin zuciya, Ina da sauri ɗaukar zafi nan take. Maijiddah idan nayi fushi ko na fusata na kan fita hayyacina Idanuwana rufe wa suke yi sai na aikata abu na dawo ina danasani. Amma duk da zafi kaina Maijiddah wallahi ni mutumin kirki ne.
   "Ka gama ɗan reni wayau wai har ni za ka shaƙewa wuya to da an yi daidai da ajali ka kashe ni shikenan ka kashe banza ko?"
"Haba Maijiddah ta ya ma za a yi na kashe ki bayan ke ce duniyata idan babu ke me zan tsinta a wann....
"Dalla malam! Ka yi min shiru kowacce kalma dake fitowa daga bakinka ƙara min haushinka take yi.
Na ƙarashe magana a wani irin tsawace domin wannan dogon sarhi nasa ƙara harzuƙa ni ya yi, ya ƙara tula min haushinsa da tsana kuma dama idan ba ku manta ba bana bari ko ta kwana balle ta tashi muddin aka tabo ni to fa sai nayi rashin mutunci.
   "Dan ALLAH ki yi haƙuri Maijiddah kar ki yi fushi dani zan iya jure kowanne irin hukunci daga gare ki amma banda fushinki, zan iya durƙusawa a gabanki na dafa ƙafafuwanki na ba ki haƙuri ki ji Habibty?"
   Cikin kaɗuwa na zaro idanuwana domin kalmar Habibty ba ƙaramin mamaki ta haifar min ba. Rai ɓace na furta "Habibty a gidan uban wa?
Ga mamakina sai na ji ya ce "A gidan ubana Maijiddah!
Yadda ya yi magana a tausashe da kuma kalar amsar da ya bani yasa na ji wani iri, har na ɗan sassauto daga rashin mutunci da na tanadar masa ɗayan sashe na zuciyata ya ce na bashi haƙuri domin na faɗi masa kalma mai tsauri da rashin ɗa'a, a daƙile na ce "I'm sorry!
  Sai da na ji ya ja numfashi tare da sauke wa kafin ya ce dani "sorry for what?
   Cuno baki nayi gami da ya tsine fuska kafin na ce "for the insult.
   "Ohh! Nevermind dear ni ban ɗauke shi komai ba na tabbata ba halinki bane dan kawai na ɓata miki rai ne.
  "Uhmm!
Na faɗa tare da ƙosawa da zancen nasa.
   "Maijiddah inaso ganinki i really really want to see you idan ban ganki ba komi zai iya faruwa dani ki tausaya min ki zo in ganki kin ji?"
Ɗan guntun tsaki na ja "mtsssss!
Har ga ALLAH mutumin nan ya fara kaini bango sai kace wata marar mafaɗi zai wani ce na zo ya ganni ai wannan reni wayau ne. Muddin ban nuna masa true color ɗina ba zai bar ni na zauna cikin salama ba. Saboda haka na ce "Anya Engr Ameer ka kuwa san darajar aure ina matsayin matar wani da auren wani akaina za ka ce na zo ka ganni for what reason?
   "Saboda ina mugun sonki Maijiddah I can't live without you ke ce farin cikina ina miki wani irin so da fatar baki ba za ta iya faɗarsa b....
Kafin ya ƙarasa nai maza na katse kira ina mai ƙara jan tsaki tare da faɗin "wawa kawai kidahumi banza wannan duk ranar da yasan banida aure na shiga uku saboda haka zan yi gaggawa saka khamis ya tura da magabatan shi gara ayi ta ta ƙare kada wannan maye mutumin ya ruguza min plan.
Nayi switch off ɗin wayata don kada ya sake kira.
********
Tafiya mai nisan gaske Hajja da Aunty Bahijja tare da Nusaiba suka yi kafin su iso gidan wani boka da aka kwatanta musu, da ka kalli fuskokin su za ka fahimci irin wahala da suka sha kafin isowarsu kowacce su fuska ta koɗe sun yi wani zuru-zuru dasu idanuwansu sun faɗa, musanmman Hajja wacce ta ri ga ta manyanta ga jikin tsofa gashi tana fama da ciwon ƙafafu amma saboda tsabar so zuciya ko tausai kanta bata ji muradinta araba Bilal da Jeeddah.
Bayan sun gama korawa bokan buƙatar su ya jawo wata ƙwarya dake aje a gefensa wacce ke cike da ruwa ya ɗebo wani garin magani ya zuba cikin ruwan kana ya shiga kiran sunan Bilal da Jeeddah yana kiran sunaye nasu tare da surkulle akalla sai da ya ɓata mintuna fiye da goma yana abu guda kafin ya share gumin goshinsa da bayan hannunshi kana ya ɗago ya dube su da jajaye idanuwanshi ya ce "Yarinyar ba ƙaramar hatsabibiya bace za ku sha baƙar wahala kafin mu yi nasarar raba yaronku da wannan yarinya domin baƙin tsafi tai mishi da jini saboda haka dole ku ma sai kun bi hanyar da ta bi kafin samuwar biyan buƙatar ku sai kun shayar da aljanu jini dabobbi daban-daban! Domin kowanne aljani da nake aiki dashi da kalar jini dabba da yake sha aljanu huɗu ne za su yi muku aiki saboda haka idan za ku iya yau ɗinan zan fara gudanar da aikinku.
   "Kar ka ji komai matuƙar za mu sami biyan buƙata duk abinda aike buƙata a shirye muke da mu bayar.
Hajja tayi magana tana wani ƙara sadda kanta ƙasa alamar girmamawa ga bokan. Makudan kuɗaɗe bokan ya amsa daga hannun su kafin ya ba su wata ƙatuwar laya wacce aka yi da fatar auraki jaki tare da wani gari magani cikin ƙatuwar muryarsa ya shiga kwararo musu bayani kamar haka "Wannan laya da ku ke gani ku nemi tsakiyar bola ku binne ta daga lokaci Jeeddah za ta ji ta tsani koda mai sunan Bilal ne. Wannan gari magani ku bi kowacce irin hanya ku tabbata kun zubawa Bilal a ciki wani abu ya ci da zarar ya ci wannan gari magani zai ji duk duniya ba wacce ya tsana irin ta da ace akwai aure a tsakaninsu nan take zai sake ta ba saki ɗaya ko biyu ba saki uku zai mata saboda haka ku kiyaye kada a sami matsala don tsanani tasiri wannan asiri ko ba Bilal ba duk wanda yaci wannan magani zai iya kama shi, shiyasa na ce ku kiyaye domin gudun afkuwar wata matsala.
"Za mu kiyaye sosai boka.
Aunty Bahijja ta faɗa cike da zumudi.
"Shikenan aikin ku ya kammala ku tashi ku ɓace min da gani.
Boka ya ƙarashe magana a tsawace da sauri suka tashi kafin su iso gida suka nemi wata tsohuwar Bola inda mutane basu cika wucewa ba, suka binne layar, bayan sun iso gida suna sauke gajiya a falon Hajja. Aunty Bahijja ta fiddo da garin magani ta miƙawa Nusaiba gami da faɗin "Nusaiba wannan aiki ke ce za ki aiwatar dashi domin ke ce matarsa ki tabbatar abincinsa na yau kin juye masa magani nan duka.
   "Tohm! Aunty.
Cewar Nusaiba tana mai miƙa hannu ta karɓi magani daga nan kowacce su ta kama hanyar gidanta cike da burin so kawo ƙarshen Jeeddah.
Nusaiba tana komawa gida ta hau girki tuwo da miyar kuka ta yiwa Bilal domin tasan yana so tuwo da miyar kuka dukka ta juye masa magani ciki miya, da ya dawo ya tarar da tuwo nan ba ƙaramin daɗinsa ya ji ba dukka ya cinye shi.
  Bayan sati ɗaya Aunty Bahijja tana ɗakin ta tana linke wakakku kayan da ta kwaso akan igiyar shanya, mijinta malam Haruna ya shigo, dawowarsa daga kasuwa kenan ciwon haƙori ya sako shi gaba shine ya baro kasuwa ya dawo gida da nufi ya sha wani maganin gargajiya da gwaggonsa da taɓa karɓo masa a wani ƙauye a lokaci baya da ciwon ya dame shi da yai amfani da magani ya ji sauƙi tun daga lokaci ciwon bai sake tashi ba sai yau.
   "Sannu da zuwa malam! In ce dai lafiya ka dawo yanzu?"
   Sai da malam Haruna ya cire babbar rigarsa ya nemi gefen gado ya zauna kafin da kyar ya buɗe bakinsa cikin raɗaɗi da azabar ciwo ya ce "Bahijja ciwon haƙori nan ya tashi ji nake tamkar zan mutu.
   "Subhanalillah! Sannu malam.
"Yawwa Bahijja yi maza ki nemo min garin magani nan wanda gwaggo ta taɓa karɓo min a sabon birni, ai akwai raguwar sa ko?"
   "En! Malam akwai dan ko kwanaki baya idan za ka tuna na samma Hajara shi da haƙorin ta ya dame ta da ciwo {Tana nufi abokiyar zamanta}
   "Haka ne yi maza ki ɗauko min shi 'yar aljanna.
A wasu lokuta suna da yake kiranta dashi kenan ko a gaban Hajara ne ba abunda ya dame shi to, ta ya ma zai dame shi tun an riga an shanye shi.
"Tohm! Malam.
Ta ƙarashe magana tare da nufar uwar ɗaka da saurinta, ta sha wahala kafin ta ganshi cikin wata jakkar hannunta kafin ta ganshi malam Haruna ya yi mata kira da yafi goma da sauri ta fito gaba ɗaya ta jiƙe da  gumi ta miƙa masa magani tare da faɗin "Riƙe magani na ɗauko tsamiya sai na haɗa na jiƙa maka, kasan da tsamiya ake haɗa shi.
Ya gyaɗa kanshi domin babu bakin magana ƙarfi hali kawai yake yi duk sanda ya buɗe bakinsa ji yake kamar haƙori balle wa zai ya faɗo ƙasa.
A gaggauce Aunty Bahijja ta murza Tsamiya ta tace a ƙaramin kofin roba ta kawo mishi ta karɓe garin magani ta juye shi dukka cikin ruwan tsamiya ta saka yatsanta ta jujjuya magani ya gauraye ta miƙa masa ya karɓa haɗe da kafa kai ya shanye kana ya miƙa mata cup ɗin ta karba ta fita dashi waje da fitar ta Malam Haruna ya fara rawar sanyi jikinsa yana wani irin kakkarwa, idanuwanshi suka juye tun daga bakin ƙofa Aunty Bahijja ta hango hali da yake ciki a guje ta ƙaraso ta kama ƙafadarsa tana faɗin "Sannu malam! Ya naga kana rawar sanyi kodai har da zazzaɓi yana damunka?"
Kwantawa ya yi tare da taƙure kanshi wuri guda yayin da jikinsa bai fasa kakkarwa ba. Gaba ɗaya hankali Aunty Bahijja ya tashi ta dauko ƙaton bargo ta lulluɓe shi, can kuma ya shiga sambatu wanda ta rasa abinda yake faɗa, jim kaɗan bacci yai awon gaba dashi. Hakan ya ba ta damar fita ta nufi ɗakin Hajara cike da izza ta shiga kwalla mata kira "Hajara! Ke Hajara!
   "Na'am maman Abdul!
Hajara ta faɗa haɗe da fitowa zaninta a hannu jikinta har wani kalar rawar tsoro yake yi cikin girmamawa ta ce "Gani maman Abdul wani abu ki ke buƙata nayi miki?"
Sai da Aunty Bahijja ta yatsine fuska gami da galla mata uwar harara kafin ta ce "Ki je ki ɗura mana girki zan kula da Malam yanzu ya dawo daga kasuwa ciwon haƙori nan nashi ya tashi.
   "Tohm! An gama maman Abdul ki yi masa sannu kafin na shigo.
Ba tare da Aunty Bahijja ta amsa mata ba ta juya cikin taƙama tana hura hanci ta koma ɗakinta har da su rufo ƙofa don kawai ta ƙara tulawa Hajara takaici.
Hajara ita ce uwargida amma Aunty Bahijja mulkarta take yi gaba ɗaya ta mamaye gidan sai abinda ta ce shi za a yi Hajara bata da 'yanci kanta.
Almost two hours malam Haruna ya ɗauka yana bacci yayin da Aunty Bahijja ke zaune kusa dashi tana mishi fiffita kasancewar babu wutar lantarki, a hankali Malam Haruna ya shiga buɗe idanuwanshi ya watsa su akan fuskar Bahijja wani irin mugun tsanar ta ya ji yana bin jini da ɓargon jikinshi, ya yunƙura ya tashi zaune da sauri Aunty Bahijja ta ajiye hand fan ɗin hannunta ta kama shi da nufin taimaka mishi hannunta yana sauka a ƙafadarshi ya ji tamkar an watsa mishi ruwan zafi a wuri. Da sauri ya kai wa hannuwanta mugun duka sai da ta ji tamkar da ƙaton ice ne ya buga mata. "Subhanalillah! Malam meke faruwa ne da kai?"
In ji Bahijja tana mai miƙewa tsaye gami da shafar hannunta na hagu domin dukan yafi samunta sosai ga hannun. Wani irin zabura malam Haruna ya yi yana zare idanuwa.
"Malam wai duk zafin haƙora ne yasa ka zazzare idanuwa haka to ko in je in nemo adaidaita mu tafi asibit....
Saura kalaman ta suka ƙargame a maƙoshinta sakamakon kafiri mari da ya kife mata, cike da zallar mamaki Bahijja take kallonshi dafe da kumatunta "Malam mari na fa ka yi anya kuwa haƙori nan bai saka, ka zare ba haka kawai ba Laifi zaune balle na tsaye ka dubi kumatuna ka watsa min mari irin wannan?
"Ni ki ke kira da zararre to bara na nuna miki ni ɗin cikakken zararre ne.
Cewar malam Haruna yana mai nufar Bahijja a mugun fusace, da sauri ta nufi ƙofar fita sai dai ta, taki rashin sa'a domin tun shigowar ta, ta datse kofar da sakata kafin ta zare sakata ɗin har malam Haruna ya fizgota, ya rufe ta da mugun duka sai kace ba zai barta da ranta ba. Ihu take yi gami da neman taimako ALLAH sarki Hajara da gudu ta nufi ɗakin tana kiran sunan Bahijja tare da tambayarta lafiya gaba ɗaya hankalinta ya tashi sai dukan ƙofa take yi. Hannun Bahijja malam Haruna ya kama yai wani irin murɗe shi cike da zallar mugunta Bahijja ta ji lokaci da ƙashin hannunta ya ce "ƙasss"ƙassss! Azabar da ta ji ya tabbatar mata da cewa ya ƙarya mata shi, batasan lokaci da ta saki fitsari ba. Ta window ɗakin Hajara ta buɗe ta leiƙa su idanuwanta suka sauka akan malam Haruna da ke ta faman jigar Bahijja, gaba ɗaya ya yi mata jina-jina da gudu ta fita ƙofar gida ALLAH ya taimake ta, ta haɗu da wasu maza za su tafi sallar la'asar masallaci anan layi suke da taimakon su suka ƙarya ƙofa, koda kofar ta karye Bahijja na kwace tsakar ɗaki sumammiya, duk da haka malam Haruna bai fasa dukanta ba. Da kyar maza nan suka ɓamɓare shi daga jikinta domin ya raba ruwan cikin ta biyu ya haye. Sai da aka rirriƙe shi kafin aka samu aka fita da Bahijja, gaba ɗaya maƙota sun cika musu gida kowa da irin abinda yake faɗa sai dai masu tunani malam Haruna ya haukace sun fi yawa domin kowa yasan, yadda yake ririta 'yar aljanna don ko kara ta gifta bai isa ya tsalleke shi ba sai da izinin ta, sai gashi yau ya yi mata dukan mutuwa. Koda aka isa da Bahijja asibiti Hajara ta kira Hajja babu daɗe wa sai ga Hajja ta zo lokaci da taga Bahijja kwace a emergency room taga irin mugun duka da malam Haruna ya yi mata batasan lokaci da ta ɗura hannu aka ta dinga rusa kuka. Su kansu likitoci sun sha mamaki matuƙa da aka ce musu mijinta ne ya yi mata wannan ƙazamin duka domin kariya biyu da tsagewar ƙashi ta samu, ƙafa da hannunta ga kuma ƙanana raunuka daban-daban a sassan jikinta. Tun aka kawo ta asibiti har ta kwana ta yini malam Haruna ko take ko leƙe bai zo ba. Sai dai duk wannan abun da ya faru Bahijja bata ga laifi mijinta ko kaɗan ba, domin ita tana zargin Hajara ce tai musu asiri take so shiga tsakanin su. Hajara kullum tana sintiri tahowa ta kawo musu abinci, amma wulaƙancce Bahijja take kallonta dagaranar da ta cika sati ɗaya ya kama ranar juma'a ana saukowa daga masallaci, kai tsaye malam Haruna ya nufo asibiti fuskarshi a murtuƙe ya tura ƙofa ba ko sallama Hajja dake zaune akan kujerar rubber kusa da gadon Bahijja ta waiga ta kalle shi ta watsar dama tana jiraye dashi don sai ya gayamata laifi me Bahijja tai masa da ya yi mata wannan mugun dukan na fitar hayyaci.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now