014...

87 7 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

   *Ga masu buƙatar a tallata musu hajarsu cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

014...

Sunkuyar da kai ƙasa Jeeddah tayi ranta in ya yi dubu ya ɓaci, wato dama Mommy Turai ta shirya cin zarafinta ne tai mata tozarci shiyasa ta zo tarbon lefenta saboda ta ƙi auren ɗanta Ya Haidar. Babban takaicinta bai wuce yadda suke ta kushe mata lefe ba gami da tofa kalaman ɓataci ga Bilal ɗinta bata dawo daga tunani da ta nusa ba, ta ji saukar muryar Mama a kunnenta tana cewa "Dan Allah Asabe zo ki kawar min da tarkace banza nan a gabana wallahi ko ƙaunar ganinsu bana yi duk lokaci da idanuwana suka sauka akan akwatuna nan sai naji wani iri takaici da ɓaci rai ya lulluɓe ni.
Tun kafin Umma Asabe ta kwashe akwatuna nai sauri bari parlourn ina toshe bakina da tafin hannu ɗakinmu na shige, na haye gado ina rera kuka ba kakkautawa saboda maganganun Mama da mommy Turai suka faɗa akan Bilal sun yi bala'in tsaya min arai.
Bayan fitar Jeeddah daga parlourn Mommy Turai ta kalli Mama a natse kana ta ce "Fatee yanzu kina gani ƙiri-ƙiri a ɗauki 'yarki akai gidan matsiyata irin wannan?"
Sai da Mama ta ja fasali kafin ta sami damar furta "Ya na iya Turai?" faɗa da yafi karfin ka dole ka maida shi wasa, tun da ubanta ya ɗaure mata gindi ni miye nawa a ciki?
  "ALLAH ya kyauta amma tsakanin da Allah Jeeddah ta gama cutar da kanta ba kuma za ta fahimci hakan ba sai anan gaba.
Hajiya Turai ta faɗa haɗe da yatsine fuska.
Da dare bayan Baba ya dawo yaci abincinsa Mama ta matsu ya kammala domin ta nuna masa lefen Jeeddarsa tana gani ya gama ta tattare kwanuka takai kitchen.
Daga kitchen ta zarce parlournta ta jawo akwatuna a wulaƙance ta kawo gaban Baba ta ajiye "Alhaji ga kayan lefen shalelenka nan kasa albarka.
"Ma-sha-Allah! Shi kuwa Bilal me zai sa ya wahalar da kanshi da irin wannan hidima?"
   Tsaki Mama ta ja kana ta ce "Ai kuwa dai da bai wahalar da kanshi ba, domin da wannan lefen nashi na ɓanar suna  wallahi gara babu. Saboda mugun talauci daga atamfofi har lace babu na ƙirki a ciki.
Mama ta ƙarashe magana tana huci.
  "Subhanalillah...! Me kike faɗa haka Fatee?" Irin waɗannan maganganu basu kamace ki ba yaronan ba wani aiki ne dashi ba  amma don kawai ya faranta wa 'yarki rai duk da bashi da shi ya ɗage ya yi mata kaya nan amma ke kuma kina aibanta wa. Lefe ba shi bane zaman aure domin ko ba lefe idan mace tana so namiji za ta aure shi su kuma zauna lafiya,  zance na gaskiya Fatee ki gyara halinki mace nawa aka yi wa aure ba kayan lefe suka zauna ɗakunan mazajensu cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Tun da Jeeddah tana sonshi ina da yaƙini ko bai mata kayan lefe ba za ta taɓa nuna damuwarta ba. Domin gudun surutun mutane iri-irinku yasa Bilal ya ɗorawa kanshi wannan hidimar amma duk da haka bai tsira ba, ku dai mata ba a iyar muku.
Baba ya ƙarashe magana cikin faɗa-faɗa domin ba ƙaramin haushi Mama ta bashi ba.
   Yayin da furuncin Baba yai masifar ƙara harzuƙawa Mama rai sai  kallonshi take yi kafin ta ce "Duk da bakaso a faɗin laifin Bilal hakan ba zai hanani faɗa maka ka zauna ka yi nazarin gobe 'yarka kada son zuciya ya jefa ka a danasani.
  "Ke don kin tsane shi ne shiyasa duk bajintar da zai yi ba ki gani, ina kuma shawartaki da ki daina irin haka ko don albarkacin 'yarki, kuma in-sha-Allah da amincewar Ubangiji sai kin yi alfahari da goben Jeeddah.
Sosai Baba ya zage damtse ya wanke wa Mama allonta tass..daga ƙarshe baram-baram suka rabu. Washegari da Baba ya tashi dawowa daga kasuwa ya haɗowa Jeeddah tsadaddun kayan lefe na gani na faɗa set ɗaya na akwatuna irin ma na Khairat ne. Ya zuba mata laces, atamfofi, shaduddi da material gami da Abayas kusan kala hamsin da biyar haɗe da set ɗin shoes and bags designer masu tsadar gaske guda bakwai, sai veils kuma wani abin burgewa hadda ƙaramar gold necklace mai matuƙar kyau ya kawo kuɗi ɗinki 100k ya bata.
Saboda tsabagen farin ciki Jeeddah har da kuka tayi.
Lokaci da Mama ta kammala duba kayan ba ƙaramin ɓaci rai ta ji ba sai dai a wannan karon tayi ƙoƙarin danne ɓaci ranta gudun irin martani da Baba zai iya maida mata. Duk da haka sai da ta kira mommy Turai da Aunty Farida ta faɗa masu dukkansu su yabawa ƙoƙarin Baba domin suna gani yadda yayi shine daidai da bai yi wa Jeeddah kayan lefe ba da me za ta saka a lokaci biki. Sai lokaci Mama ta fahimci Baba ya yi ne domin ya fidda su kunya.
Ranar bata karya yau saura kwana uku a fara shagalin biki, zuwa lokaci Baba ya Kammala gyara musu gidan da za su zauna. Bilal Shattima sai rasa bakin godiya ya yi domin Baba ya gama mishi komai ya bashi 'ya kuma bashi muhallin zama. Ta bangaren kayan ɗaki komai iri ɗaya Baba ya siya musu kawai dai akwai banbanci colour, sai kuma Khairat da ke da four bedrooms gado huɗu aka sa mata Jeeddah kuma two bedroom ne, a maimakon gadajen da aka sakawa Khairat da ba a siyawa Jeeddah ba Baba sai da ya siya mata standard freezer da generator babba bayan already ya sai musu deep freezer, zuwa lokaci bakin Mama ya mutu mutuss...sai kawai ta zubawa sarautar Allah ido domin lamarin Baba ya fi ƙarfin ta. Sosai Baba ya kashewa 'ya'yansa miliyoyin kuɗi. Lokaci da za a kai gara gidajen angwaye Mama bata so akai yawa ɗaya ba ta so a bambanta a cewarta tuwon girma miyarsa nama tun da Bilal bai kawo lefen arziki ba babu dalili kai masa gara mai yawa ba. Sai da suka kai ruwa rana da Baba kafin ta amince aka kai 'yan uban tulin kayan abinci gidansu Bilal a matsayin gara.
A yau ne amare suka shiga lalle da yamma za a yi kamu a gidan Farida kasancewar compound ɗin gidanta yana da matuƙar girma. Kwararrun masu decoration ta yo booking tun daga Kaduna, aka tsantsara masu decoration na ji da gani.
Amare kuma sun sha gyara ciki da waje idan ka ga Jeeddah da Khairat sai ka matsa musu da kallo kafin ka yi nasarar gane su. Koda five o'clock ta buga an kammala musu makeover sun yi kyau na ban mamaki amarya Jeeddah sanye cikin wedding gown golding in colour kanta ɗauke da Royal blue turban Khairat kuma nata gown ash colour ce da turban irin na Jeeddah, kowacce su ta sanya gold necklace ɗinta. Lokaci da dangin Bilal suka zo kamu suka yi arba da amaryarsu sai da suka rena kansu, suka fara zargin anya Bilal bai yi tsaga da faɗi ba na aure mace kamar Jeeddah.
Sai daff da magariba taro ya watse yayin da Aunty Farida ba ƙaramar hidima ta yi ba domin ta raba souvenirs na gani na faɗa.
Ƙarfe 9 za a tafi dinner party wanda friends ɗin Jameel suka shirya masa shi da amaryasa Khairat amma sai gayyaci Bilal Shattima da nasa tawagar abokai, ko kaɗan Jeeddah bataso zuwa ba sai da Aunty Farida ta buɗe mata wuta sosai kana ta bari aka shirya ta.
Dinner tayi matuƙar ƙayatarwa sakamakon duk abokan angwaye da amare wayayu ne, sai around 12 o'clock kowa ya kama gabansa.
Washegari bayan an sauko daga masallaci juma'a ɗaruruwa mutane suka sheda ɗaurin aure Bilal Ibrahim Shattima da Jeeddah Usman maishadda akan sadaki naira dubu talatin sai kuma na Jameel Bello Sifawa da Ummul-khairi Usman maishadda akan sadaki naira dubu ɗari biyu. Sosai wannan sadaki da Iyayen Jameel suka bayar ya janyo ce-ce-kuce a tsakanin 'yan ɗaurin aure shi kansa ango Bilal Shattima sai da ya ji wani iri koda aka gama daurin aure ranshi a jagule sai murmushi yaƙe yake yi, wannan ita ce rana ta farko da Bilal ya ji baƙin ciki rashin aikin yi har ya sha alwashi duk inda aiki yake zai nemo sa kuma muddin ya yi kuɗi sai ya faranta wa Jeeddah fiye da tunanin duk wani mai tunani, kuma har gaba da abada ba zai so wata 'ya mace ba daga kanta ya datse ƙofar zuciyarsa.
Bayan isha'i amare har sun kammala shirinsu cikin lafayya fara sol sai ƙamshi na musamman ke fita daga jikinsu, zuwa ƙarfe takwas aka kai su part ɗin Baba nasihar zaman aure mai ratsa jiki ya yi musu kana ya ƙara tunatar dasu muhimmanci haƙuri da adana sirrikan gidajen su, daga Jeeddah har Khairat ba wanda bai zubda hawaye ba. Kana Mama ta ɗora daga inda Baba ya tsaya, lokaci da aka zo tafiya dasu Jeeddah kwacewa tayi daga hannun Mommy Turai ta faɗa jikin Mama tana rusa kuka tana faɗin "Dan Allah Mama ki ce kin yafe min ɓaci rai da na sakaki, idan ba ki ce kin yafe min ba Mama ba zan taɓa farin ciki ba a rayuwarta.
   Idanuwan Mama sai da suka ciciko da hawaye domin ba ƙaramin tausai Jeeddah ta ji ba, a hankali take ɗan bubbuga gadon bayanta "Ya isa haka Jeeddah daina kuka kada ki bata kwalliyarki, ni uwa ce mai ƙaunar farin cikin 'ya'yanta nasan illar dake tattare da fushina akanki shiyasa tun a wancan lokaci na sa wa raina na yafe miki, Allah ya yi muku albarka Allah yasa wurin zamanku ne har mutuwa, ina muku fatan alkhairi da wanzuwar farin ciki mai ɗorewa ke da 'yar uwarki. Tashi maza akai ki ɗakin mijinki dare na ƙara yi.
   Baba da Mommy Turai suka amsa da "Amin!
Kana mommy Turai ta ɓanɓare Jeeddah daga jikin Mama ta ja ta zuwa ƙofar gida yayin da Umma Asabe ke riƙe da Khairat ita ma sai faman gunji kuka take yi, Jameel ya aiko da tsadaddun motocin ɗaukar amaryasa saboda haka dasu aka yi amfani aka saka Jeeddah cikin ɗaya daga ciki, kasancewar ita ce babba sai da aka fara kai ta gidanta kafin aka wuce da Khairat zuwa nata gida.
Tun daga gate ɗin gidan Khairat za ka san naira tayi kuka, balle kuma ka shiga ainihin cikin gidan tsarin gini turawa ne sama da ƙasa a ƙasa akwai tamgamemen parlour haɗe da two bedrooms, ga kitchen da store room ga kuma dining room, a gefe ɗaya ga wurin shan iska idan kuma ka haura upstairs za ka tarar da parlourn maigida da master bedroom ɗinsa, sai kuma sashen Khairat ita ma akwai parlour da bedroom, sai kuma dining room idan ba ka buƙatar saukowa ƙasa kenan, gidan Khairat ya haɗu iya haɗuwa yayin da 'yan uban tsadaddun kayan ɗakin da aka zuba mata suka ƙara ba da gudunmuwarsu wajen ƙawata gidan.
Duk wanda yaga tsarin gidan Khairat sai ya tausaya wa Jeeddah, don gani suke kamar tana cikin akurkin kaji. Gidan da Baba ya ba su Jeeddah part haɗu ne da ka shigo gate part ɗin farko shine nasu Jeeddah, raguwar uku kuma akwai 'yan haya a ciki na kusa da Jeeddah na Jessica ne 'yar asali kwara state ce aiki ne ya kawo ta Sokoto tana aiki a access bank sai kuma mr Mahmoud da matarsa Hajara su kuma  'yan Kaduna ne shima aiki ne ya kawo su garin Sokoto, da yaransu uku, sai part ɗin ƙarshe na wani ɗan sanda ne officer Abdoul-ganiyu tare da matarsa Sharifa da ɗan su ɗaya duk mutane da ke gidan babu ɗan asali Sokoto dukkan su aiki ne ya kawo su. Kuma tun kafin Jeeddah ta zo gidan Kabeer ya gayamusu 'yar maigidan ce shiyasa kowanne su ya sha jinin jikinsa.
Kowane part yana ɗauke da ɗakunan bacci guda biyu haɗe da parlour ɗaya da kitchen sai kuma ɗan ƙaramin dining room mai ɗaukar ƙaramin dining set mai kujeru huɗu.
Tun kafin ƙawayen Jeeddah su baro gidanta wasu daga cikinsu masu gajin haƙuri suka fara keɓewa suna gulmarta Sakina Salis ce da Hafsah Bello ke tsaye a kitchen suna kallon 'yan uban kayan kitchen ɗin da ke shaƙe da kitchen cabinet, ba abinda yafi tsone musu ido irin manya-manyan warmers masu mahaukacin tsada da aka zubawa Jeeddah, hassada da baƙin ciki ya lulluɓe musu zuciya Hafsah Bello ta ja guntun tsaki tai ƙasa da murya tana cewa
  "Tirrr... wallahi an yi asarar kayan kitchen anan wuri, za su rube a banza domin wanda aka kawowa su cima zaune ne sai dai a nemo a bashi yaci.
   "Bari kawai Hafsah Bello ni kaina na kasa daina mamakin Jeeddah Usman maishadda ko uban me ta gani a jikin Bilal ɗinan, mutum sai ƙari talauci ga kuma  muni tsiya shegiyar fuskarsa kamar ta gwaggo biri.
   Dariya suka kwashe da ita har suna haɗawa da tafawa Sakina Salis ta sake cewa "Wai nan da yake cakuss dashi Jeeddah bala'in kishinsa take bata yarda ya raɓi kowacce mace ba.
  "Shi wannan mai gajeren hanci ni wallahi banga abin so a jikinsa ba dama ace yana da 'ya'yan banking sai kayi maleji saboda ƙudinsa.
Cewar Hafsah Bello tana yatsine fuska.
   "Ni ma shi na gani da yana kuɗi sai a sonshi ko don albarkacin ƙudinsa amma...
Jin takon tafiya an nufo kitchen ɗin yasa suka yi shiru tare da fitowa suna muzurai, A'isha shattima da Raliya Hassan suka gani, murmushin yaƙe suka yi da ka kalle su za ka gano basu da gaskiya, Sakina Salis ta ce dasu "har yanzu ango da abokansa basu ƙara so ba?"
   "Eh wallahi amma in-sha-Allah ko sun daɗe ba za su wuce 10 o'clock ba ku dai ƙara haƙuri dan Allah.
Cewar A'isha shattima.
Ƙarfe goma daidai Bilal da tawagar abokansa suka shigo ɗakin amaryasa Jeeddah jin sallamar su yasa tai sauri jan lafayyarta ta lulluɓe fuskarta..

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now