076

149 11 5
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

076.

Da dukkan ƙarfina na kurma ihu ina faɗin "wayyoooo na shiga uku idona wallahi Ya Haidar ka fasa min ido shikenan ka makatani. Ba sai ka yi min irin wannan baƙi mari zan fahimci baka sona ba Ya Haidar.
Yadda take gunji kuka haɗe da sambatu ya sanyayya wa Haidar Ka'oje jiki da sauri ya nufi wurinta ya zube guiwayoyinsa gabanta kana ya saka hannuwanshi ya ɗago ta, ƙoƙari take ta ture shi ya riƙe ta gam.
Cikin shasshekar kuka na ci-gaba da faɗin "Ka sake ni Ya Haidar Dan ALLAH ka kyale ni na gaji da wannan wulaƙanci naka.
Ya sauke numfashi tare da miƙe wa ya sunkunce ta ya kaita kan gado ya zaunar da ita "Mutuwa kaɗai ta kai can ta rabani dake Jeeddah ba dai mutum ɗan adam ba don haka ki daina wannan furunci idan ba so ki ke na sake ɗauke ki da wani mari ba.
Haidar ya yi magana yana jawo ta jikinsa ture shi tayi ciki tsawa ta ce "Kai mugu ne Ya Haidar tun sanda muka yi aure ka ke musguna min ka hanawa zuciyata ta zauna cikin salama wallahi sai ALLAH ya saka min cutata da ka ke yi.
Yatsu shi biyu yasa buge min baki "Ashe baki da ɗa'a Jeeddah mijinki ki ke wa ALLAH ya isa?
"Mijina a ina? Sai dai kuma mijin Zarah ni bani da miji.
Sosai ya tsare ni da manyan idanuwanshi ya wani girgiza kai da alama ya ji haushi magana ta.
"Daga yau babu ni babu kai tafiyata zan yi ba zan iya ci-gaba da zama da wanda baya sona ba.
"Wane munafiki ne ya gayamiki bana sonki? Da ki ke ta maimaita wannan kalma.
"Ai ni ba doluwa bace da zan kasa fahimtarka kuma sai na gayawa mommy mari da ka yi min wallahi ba ka mari banza ba.
"Ya Rabbi ka taimake ni akan wannan rigimammiya yarinya marar fahimta.
Ya ƙarashe magana tare da ɗago haɓata ya ce "Kalle ni da kyau Jeeddah ki dubi ciki idanuwana.
A maimakon na kalle shi ɗin sai kawai na shammace shi na ture shi da ƙarfin gaske na sakko ƙasa ina ƙoƙari bar mishi ɗaki ciki zafin nama ya cafko hannuna "Sake ni
Na faɗa cikin dusashewa murya.
"Ba zan iya ba Jeeddah.
"Na ce ka sake min hannu bana sonka bana ƙaunar ganinka.
"Hannu ma ba zan iya sakinsa ba koda bakyaso ganina ni ina son ganinki Jeeddah. Bana gajiya da ganinki.
"Bana so yaudara Ya Haidar Dan ALLAH ka kyale ni.
"Ko ina yaudara ba zan iya yaudarar ki ba Jeeddah. Da kinsan irin yadda nake bala'in sonki ba ki dinga ambatar rabuwa a tsakanin mu. Ko a ciki zuciyata soyayyarki dabam take bana tunani akwai wata halitta da na taɓa so kwatakwacin yadda nake sonki. Ni kaɗai nasan irin azabar da nake sha akan soyayyarki idan har ba so ki ke yi ki ga na daina numfashi ba. Miyasa har yau kin kasa fahimtar irin mugun so da nake miki sai na tsaya ina furta miki shi ta fatar baki ba. Remember that you're my first Love ke ce macce ta farko da zuciyata ta fara so har illa yau soyayyarki bata taɓa canzawa daga gurbin ta ba. Ko naso nayi fushi dake Jeeddah zuciyata bata bari fushi nawa ya yi tasiri.
Duk wadannan maganganu da Ya Haidar yake faɗa a maimakon su saka ni farin ciki sai kawai naji haushi ya lulluɓe ni miyasa tuntuni bai gayamin su sai yanzu da ya gama wulaƙanta ni har yana faɗin ban iya komai ba wannan kalma ta fi komai tsaya min a rai fiye da mari da yai min.
"Na haɗa ka da girman ALLAH Ya Haidar ka kyale ni.
Ina rufe baki yana sakar min hannu ba tare da na kalle shi ba na fi ce zuwa ɗayan bedroom ɗina na kwanta.
Da asuba shi ya tashe ni ta hanyar bubbuga min ƙofa na taso na buɗe yana gani na buɗe ƙofar ya juya abinsa, ina kammala sallah na koma na kwata babu jimawa bacci ya ɗauke ni sakamakon daren ban yi wani bacci kirki ba.
"Mommy ki tashi ki yi min wanka kada nayi latti.
Can tsakiyar kaina na ji muryar Aiman da kyar na buɗe idanuwana sakamakon yadda nake ji ɗayan idon nawa ya yi min wani mugun nauyi shi ne wanda Ya Haidar ya mara.
"Mommy please ki tashi manaaa!
Aiman ya faɗa kaman zai yi kuka yana ja min hannu.
"Mtss! Na ja ɗan guntun tsaki kafin na tashi zaune na kalle Aiman da kumburarri idanuwana yayin da ɗayan ma har jini ya kwanta a ciki.
"Wuce ka bani wuri!
Na faɗa wa Aiman a tsawace.
"Mommy zan je school wa zai min wanka to?"
"Ban sani ba na ce ban sani ba Aiman tun jiya nake cike da kai zo nan mai shegen surutu tsiya ga baki ɗaya Mama ta gama sangartaka bata koya maka, bari shiga abinda babu ruwan ka ba ko?
Na ƙarashe magana a mugun hasale na jawo hannunshi na kama kunnenshi na murɗa "duk ranar da na fita da kai muka dawo ka ba wa Ya Haidar labari abunda ya faru sai na yanke maka kunne. Yau ɗinan za ka bar gidanan ka koma can waje Mama ka ci-gaba da surutun ka.
Aiman ya fashe da matsananci kuka yana faɗin "Mommy Dan ALLAH ki yi haƙuri na tuba ba zan sake ba.
Ture shi nayi na sakko na nufi bathroom nayi brush na fito yana jingina jikin bangon bathroom yana shasshekar kuka yana gani na fito ya ƙara wa kukanshi sauti, ya rungume ni "Mommy I'm sorry wallahi ba zan sake ba.
A fusace na sake ture shi "Ka ma sake Aiman sai dai ba a gidanan ba.
"Mommy ina sonki ina son zama dake ki yi min duka amma Dan ALLAH ki barni na zauna dake.
Duk da maganganu Aiman sun dake ni sosai amma ban tsaya ba sai ma ficewa da nayi daga ɗakin so nake ya gane kuskure abinda ya aikata. Ya riga ya saba a wuri Mama duk abinda zai yi ko ya aikata ba duka balle kwaɓa shiyasa gaba ɗaya a sangarce yake goyon kaka ne na bugawa a lissafi. Ni kuma ba zan iya barinsa ya ci-gaba da waɗannan halaye ba saboda zuwa gaba za su iya cutar dashi.
Ina fitowa mu ka ci karo da Ya Haidar daidai Aiman yana fitowa sai faman taratsi kuka yake yana kira sunana yana faɗin nayi haƙuri da wani kalar sauri Ya Haidar ya nufe wurinsa ɗaukar sa ya yi tare da rungume shi yana bubbuga masa baya "Yi shiru Aiman bana so kuka nan naka yana taɓa min zuciya. Me ki ka yi masa da sanyi safiyar nan Jeeddah?"
Haidar ya faɗa ciki ɗaga murya saboda har na kai kofar shiga ɗakina da jiya na baro shi a ciki. Na juyo azafaffe na ce "Ka tambaye shi mana.
Na shigewa ta ɗaki tare da datse ƙofa.
Haidar ya wuce da Aiman upstairs bedroom ɗin sa sai da ya rarrashe shi  yai masa wanka ya shirya shi ciki school uniform ɗinsa, da kanshi ya shiga kitchen ya soya masa kwai ya haɗa masa tea ya sha, ya kai shi school akan hanyarsu ya tsaya a Royal city restaurant ya siya mishi abinci aka sa mishi a lunch pack ɗin shi kana ya sauke shi school. Yana dawowa daga kai Aiman ya wuce flat ɗin Zarah a kitchen ya hango ta tana haɗa breakfast "Good morning my sweetie!
Ya faɗa sa'ili da ya isa ciki kitchen ɗin ta juya ta kalle shi da fara'a akan fuskarta "Morning angon Jeeddah da Zarah da fatan kun tashi lafiya.
"Al-hamdullilah!
Ya faɗa yana mai sakar mata tattausan murmushi "me ake haɗa mana gaba ɗaya kin cika gida da ƙamshi?
Dariya tayi mai ban sha'awa tana faɗin "Nake dai haɗawa kaina.
"Kina nufi ke kaɗai za ki cinye wannan daɗi.
"Kwarai kuwa domin kaima na tabbata matarka ta tanada maka daɗi da ya fi wannan.
Ya ƙara faɗaɗɗa murmushin sa yana faɗin "Haka ne kam bari ma na tafi dama na leiƙo ne na duba lafiyar ki  naga yadda ki ka tashi.
"Lafiya ƙalau na tashi sai dai kewarka.
Sosai furuncinta yai mishi daɗi
"Same here.
Ya faɗa tare da nufar ƙofar fita da sauri Zarah Malik ta bishi ta raka shi har ƙofar fita daga flat ɗin ta kana ta koma ta ci-gaba da aikin ta.
Ina fitowa daga wanka na kira Khairat a waya tana gani kirana da sassafe sai da gabanta ya faɗi ina ji ta ɗauka na fashe mata da kuka ina kuka ina faɗa mata abinda ya faru bata katse ni ba har sai da na kai aya.
"Mtss! Khairat ta ja guntun tsaki ranta a ɓace ta shiga faɗin "Zance gaskiya Jeeddah bakida kai sai na ɗaukar kaya. Ke kam ko kaɗan baki da wayau bansan sai yaushe za ki yi hankali ki fahimci cewa yanzu kai ya waye an daina kishi hauka ke ko a ƙauye an daina irin wannan mugun kishi naki, a yanzu kishi wayewa ake Jeeddah kowa ya biya allonsa ya wanke idan ki ka yi wasa wallahi kina ji kina gani zaman gidan Ya Haidar zai gagare ki ALLAH ya ba ki miji mai masifar sonki amma kishi ya hana ki ganewa. To ki natsu kisan abinda ki ke yi kada kwaɓarki tayi ruwa tsululu. Shi namiji da ki ke gani wawa ne duk inda aka fi kyautata masa da tarairayarsa a can yake, ki yi gaggawa jinginar da wannan zafin kan naki ki rungume mijinki ki je ki bashi haƙuri ku sulwanta kanku kada ki bari abokiyar zaman ki ta farga da irin zaman da ku ke yi, iya shawara da zan iya baki kenan.
Khairat tana gama magana tai hanging up tare da switch off ɗin wayarta kaman tasan zan sake kiranta amma kuma an ce sani hali yafi sani kama Khairat tasani ciki da waje ina kira na ji switch off. Dole na haƙura na tashi jiki a macce na nufi kitchen na haɗa mishi breakfast mai rai da lafiya, da na kammala na jera akan dining table na nufi upstairs bedroom ɗin sa gabana yana dukan tara-tara na tura ƙofa kaman munafuka daidai yana fitowa daga wanka daure da towel a ƙugunshi muna haɗa ido ya sakar min miskilin murmushi "wa nake gani kaman Jiddata?"
Danƙarerriyar harara na maka mishi ina cuno baki haɗe furta "Ba ita bace wannan Jeeddah haƙuri ta zo ta ba ka tun da koda yaushe kallon mai laifi ka ke mata.
Ya ƙaraso kusa dani ya kama hannuna ya nufi gefen gado ya zauna tare da zaunar dani dab da ƙugunshi cikin tausasa kalami ya ce "Ke ma ki yi haƙuri Honeypie ban kyauta ba da na taɓa lafiyar jikinki kema kinsan ba halina bane duka furunci da ki ka yi ne yai mugun ɓata min rai amma har ciki zuciyata ban ji daɗi marinki da nayi.
"Uhm!
Na faɗa tare da matsa wa nesa dashi da sauri ya sake matsowa "Ya za ki matsa ko ba ki so na ji ɗumin jikinki?
Taɓe baki nayi cike da takaici na ce "jiki da ka gama sharara wa mari.
"To bana ce ki yi haƙuri ba.
"Na ƙi na haƙura ɗin.
Na faɗa a fusace.
"tun da ba za ki haƙura ba ki zo ki rama daga ni sai ke ne a ɗaki ba wanda za ka ga sanda ki ka mare ni amma ki tuna ALLAH yana gani ki hakazalika Mala'iku ma suna gani ki.
Cike da so tadda zaune tsaye na sake cewa
"Ni mari da ka yi min bai dame ni ba kaman cewa da ka yi wai ban iya komai ba. Wato kana nufi Zarah Malik ta fini a shimfiɗarka ko?
"Subhanalillah! Ni fa ba haka nake nufi ba.
"To idan ba haka ka ke nufi ba me ka ke nufi?
Sai da ya yi dariya gami da jawo ni cikin naked body ɗinsa dashin ruwan wanka jikinsa ya haifar min da wata kalar natsuwa ban san sanda na lafe a jikinsa ba, ina shaƙar ƙamshi shower gel ɗin da ya yi amfani dashi.
{'yan zazzafan kishi fans group ku daina shiga faɗa mata da miji rabon ku kunya to ba ga irin ta nan ba duk tadda jijjiyoyin wuya da ku ke yi akan Jeeddah gashi nan ta shige jikin oga Haidar tana samun natsuwa ku kuma ta bar ku da haɗiye takaici lol 😂}
"Jeeddah rigima 'yar Baba yanzu dai tun da mun shirya abar wani zance tone-tone amma har ga ALLAH bana nufi abinda zuciyarki ta fassara miki.
"Koma mene ne ka ke nufi ni dai ban ji daɗi wannan kalma ba.
"To ki yi haƙuri my Honeypie ko kuma ki zo ki mare ni kawai a wuce wuri.
"Sai faɗin ka ke na mare ka to bari ka ji duk fitina da rigimata lalacewa ta bata kai can ba.
"ALLAH ya huce zuciyarki Honeypie.
"Ni fa suna nan da ki ke kira na dashi anya kuwa babu zallan yaudara a cikinsa?
"Ta nan kuma ki ka dawo?
"Ba dole ba tun da naga wacce ka ke nuna maitar ka a fili akanta ita ce ta dace da wannan suna ba ni ba.
"Uhm! ALLAH kaɗai yasan karatun kurma Hajiya Jeeddah ki iya sani idan ana sallah ba a magana.
Shiru nayi ina bitar maganganunsa amma duk iya tunani na kasa fahimtar wannan zaurance nashi.
Haidar ya zame min ɗan ƙwali yana shafar kitso kaina cike da shauki ya ce "Tubarakallah Ma-sha-ALLAH! A'isha Shattima ta gama biya na saura ni na biya ta yau dai gani ga kitso nan da ake min kwalele.
Yana magana yana ta faman shasshafa kitso ni kuma hakan ba ƙaramin daɗinsa nake ji ba, saboda har lokaci ina jin zafin kitso taɓa wa da yake sai nake ji tamkar yana min tafiyar tsotsa. Musamman yadda yake bin tsagar da yatsanshi har wani lumsashe idanuwa nake yi. Can kuma ya dawo ga ƙunshi hannayena yana shafa wa "Duk ni kaɗai wannan kwalliyar?
"A'ah! Ni ba don kai nayi ba.
"Don wa ki ka yi?
"Don kaina.
"Rantse da ALLAH.
"Ban yi.
Sosai yasa dariya yana faɗin "Da ki rantse.
"Zo ki biya min karatu da na koya miki.
Sai da na zaro idanuwa kafin na ce "Yaushe ka koma malami ni kuma ɗaliba?
"Dama can ni ne malami ke kuma ɗaliba.
"Uhm! Ka dai yi amanka ka lashe Ya Haidar.
"Komai za ki faɗa ba zan musanta miki ba.
Duk yadda naso na bijirewa buƙatarsa abin ya ci tura domin sai da ya jagwalgwala ni iya son ranshi, ba ƙaramar gajiya ya jinga min ba gaba ɗaya gaɓɓan jikina ciwo suke.
"Honeypie miye sirri na ji gaba ɗaya ki sauya ba zan iya misalta adadin abinda na ji ba. Saura kiris ƙwaƙwalwata, ta buga. Gashi fatar jikinki tayi wani irin tsatsi da taushi you're completely different da yadda ki ka zo gidanan.
Murmushi nayi cike da jin daɗi yadda yake ta ƙodani yana ya ba min.
"Ai naga alama irin wannan ihu da sambatu ka dinga yi ko ranar da nai maka fyaɗe albarka.
Dariya Ya yi tare da ƙara ƙanƙame ni yana min raɗa a kunne tsakani da ALLAH Ya Haidar ya lalace abinda ya faɗa bakina ba zai iya faɗarsa ba.
Tare muka yi wanka tamkar saɓani bai taɓa shiga tsakanin mu ba. Muna kammla breakfast ya ce bacci yake ji mu je mu kwanta ban ƙara firgita da al'amarinsa ba sai da ya sake tsallaka border yana ta zuba min sambatu kaman wani zautatce. A ciki zuciyata sai ya ba wa kayan mata na kamfanin Manzil Alwafir tare da hadin gwiwar mg's skincare products domin sune kan gaba wuri gigita ƙwaƙwalwar Ya Haidar tabbas na yadda na amince da ingancin kayan Manzil Alwafir da mg's skincare products. Tun safe muna manne da juna Ya Haidar sai wani tattalina yake yana rirrita ni hatta da lunch cewa ya yi ba sai na shiga kitchen ba na bari yai mana order a royal city restaurant sai da lokaci dauko Aiman daga school ya yi sannan ya fita koda ya dawo har na sake wanka da sallar azhar na shirya ciki half gown maroon in color mai gajeren hannu ban ɗaura ɗan ƙwali ba saboda na fahimci yadda Ya Haidar yake masifar so kitso kaina na saki abina, ina ciki fesa turare suka shigo shi da Aiman cike da tsoro Aiman ya gaida ni, fuskata a haɗe na amsa a dakile.
Gani yadda na amsa mishi yasa Ya Haidar ya ja shi suka fice ɗakin da na ware masa suka shiga ya cire masa uniform tare da yi masa wanka sai da ya sake shirya shi ciki uniform ɗinsa na islamiyya, koda suka fito ina zaune a main parlor. Abinci da ya yi mana order muka ci kana ya tafi kai Aiman islamiyya yada yake ta faman ɗawainiya da Aiman tamkar shi ya haife shi ya ƙara masa wani irin girma da daraja a idanuwana na ji wata kalar soyayyarsa tana mamaye sassa jikina. Sai yau na ƙara yarda da ƙarin maganar da ake cewa kowa yaso uwa yaso ɗan ta.
Ranar kwana farin ciki muka yi manne da juna duk da ba abinda ya sake wakana washegari kafin ya koma ɓangaren Zarah Malik wai sai na bashi na bankwana ai kuwa sai da ya yi sannan hankalinsa ya kwanta. Da dare da naga na kasa bacci sai kawai na tashi na yi alwala nayi nafila.
A kwana a tashi asarar mai rai gashi har aurena da Ya Haidar ya cika watanni biyu a lokaci na fara laulayi gaba ɗaya na fita daga hayyacina domin hatta da ruwa idan nasha sai na amayar dasu duk na bi na rame. Sai da na share sati ɗaya akan gado asibiti kafin aka yi dismiss ɗina ba wai don na ji sauki ba sai don ciwo nawa ba shi da magani sai haƙuri. Wani zuwa da Mommy Turai tayi duba ni take gayamin Zarah Malik tana ɗauke da ciki uffan ban ce da mommy ba. Yanayi zaman mu da Zarah zan iya cewa kadaram kadaham saboda babu mai shiga sabga wani sai mu share sati fiye da ɗaya ba mu haɗu ba wasu lokuta mu fi haduwa a parking lot idan zan tafi wajen aiki ita kuma za ta fita da yake tana bautar ƙasa. Sai wannan ciwo da na fara ta je asibiti kusan sau uku tana duba ni da nawa gida shima ta shigo kusan sau biyu. Lokaci da ta shigo na hango tsanani tausayina kwance a ƙwayar idanunta saboda hali da nake ciki ba kishiya ba ko makiyina ya ganni sai ya tausaya min. Kullum hannuna manne da drip. Ya Haidar duk ya bi ya rame saboda hali da nake ciki.
  Kwance nake akan three seater a parlor as usual hannuna manne da drip Ya Haidar ya sauko daga upstairs, kai tsaye ya wajena ya nufo ya ɗauke kaina daga throw pillow ya zauna kana ya mayar da kan nawa akan cinyoyin shi "Sannu Honeypie!
Da hannu na nuna masa ya miƙo min robar da nake zubda yawu a ciki, da sauri ya ɗauko ya buɗe min na ɗago da kyar na tofar da wasu kalar yawu masu masifar kumfa sannan na amsa mishi.
"ALLAH ya ba ki lafiya.
"Amin.
Na amsa a takaice
"Kin ga Zarah kaman ba mai ciki ba komai ci take ɗazu ma sai da nasa aka nema mata rama ko za ki gwada ci kwaɗo rama ɗin watakila yai miki daɗi a baki?
Da sauri na girgiza kai har ina haɗawa da yatsine fuska.
Damuwa ta bayyana ƙarara akan fuskarsa "To faɗa min me ki ke so ki ci ko na ɗauko miki apple ɗinki?
Nan ma na sake girgiza kai sai da na tofar da yawu kafin na ce "Idan zan sami ɗanye mangwaro zan ci.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'um! Jeeddah ɗanye mangwaro fa ki ka ce ai sai ya ɓata miki ciki. Don ALLAH ki canza wani abu mana ga irin su goriba, yalo ga kuma agwaluma amma me za a yi da ɗanye mangwaro.
Kwaɓe fuska nayi tare da faɗin "Idan  da hali shi nake so idan kuma babu Dan ALLAH ka kyale ni.
"ALLAH ya ba ki haƙuri za a nemo mangwaro ɗin baya shi ba ki buƙatar komai?
"Shi kaɗai nake so.
Na faɗa tare da runtse idanuwana ji nake tamkar ana yayyaka naman jikina. Sallama Zarah Malik na tsikayi nai sauri buɗe idanu ta ƙaraso ta zauna kujerar da ke kusa damu "Sannu sweetie ya fama da jinya?"
Jeeddah ya jiki?

Remain few page mu zo ƙarshe maybe ba zai wuce 1-2 pages ba.

#Haidar Ka'oje
#Jeeddah maishadda
#Zarah Malik
#Team zazzafan kishi.









ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now