051

145 13 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

051..

"Ameer meke faruwa ne naga ka shigo kana zabga fara'a sai kace wanda aka yiwa bushara da gidan aljanna?"
   Kusa da ita ya nema ya zauna ya kama hannunta ya haɗe da nashi zuciyarshi fess! Ya shiga faɗin "Umma na ganta duk da tana cikin yanayi na jinya hakan bai dusashe farin ciki da nake ji na gami da ganinta da nayi ba.  Umma soyayyar maijiddah dabam ce a cikin zuciyata, a wasu lokuta har na kan ji tamkar ban taɓa so wata 'ya mace ba sai akanta. Dan ALLAH ummata ki tayani da addu'a na mallaketa domin ita ce muradina abinci ruhina.
   Har ya kawo ƙarshen zance shi umma da ƙawarta Hajiya Tambai suna kallo shi, yayin da umma ita kaɗai tasan hali da zantuka shi suka jefa ta ciki, daidaita natsuwa umma tayi gami da sauke gwaron numfashi kafin cikin fargaba ta furta "Ameer wacece Maijiddah waye ita shin yaushe ka ƙula alaƙa mai ƙarfi irin wannan da ita ni da nake matsayin mahaifiya a gareka ba ka taɓa faɗa min ba?"
   Sadda kanshi ƙasa ya yi zuciyarshi tana wani irin bugawa da ƙarfin gaske wato yana dubin ta ina zai fara sanarda umma wacece Maijiddah.
   "Ameer ka buɗe baki ka bani amsa shiru ka yana nufi abubuwa da dama banaso zuciyata ta dasa min zargi akanka.
  Cike da kunya abinda zai fito bakinsa ya ɗago idanuwanshi ya kafe umma dasu, kafin ya ce "Maijiddah ita ce yarinya da na taɓa ba ki labarinta  almost seven years ago, umma cikin hukunci Ubangiji har na fitar da rai da ƙara haɗuwa da ita sai gashi kwatsam! Kwanaki uku da suka wuce na haɗu da ita, yanzu haka tana asibiti nan a ɗakin da ke facing naki bata da lafiya a iya bincike da nayi domin ji irin ciwo da ke damunta abin mamaki umma Maijiddah tana fama da cutar hawan jini which means mijinta yana ƙuntata mata bata jin daɗi zama dashi, saboda haka na ɗaura ɗamarar kwace ta daga gare shi walau ta sauƙaƙƙiya hanya ko kuma akasin hakan. Ni dai muradina guda ɗaya ne na kasance Inuwa ɗaya da ita.
    Ya ƙarashe magana yana wani irin huci ƙofufin hancinshi yana fitar da iska mai zafi wata irin fargaba gami da tsanani tsoro suka lulluɓe umma, tasan wanene ɗanta ta kwana da sani hali naci da kafuwar sa bai iya son abu ba musamman akan soyayyar mace ta wannan fanni bashi da kyau ko kaɗan, komai zai iya aikata wa domin ya mallake abinda yake so.
  "Umma zan tafi gida nayi wanka ba zan jima ba zan dawo idan da akwai abinda kike da buƙata na taho miki dashi?
Sautin muryarshi ce ta fargar da umma daga duniyar tunanin da ta faɗa cikin sauri ta dakatar dashi domin har ya kai ƙofar fita "Ameer idan har ni na haifeka, ka sha daga gareni to ka fita sabgar matar mutane, ka yaƙi shaiɗaniyar zuciyarka da take kwaɗaita maka soyayyarta da ta haƙura da ita domin koda ta kasance batada igiyar aure wani akanta ba zan taɓa amincewa da ka ƙara yi aure a rayuwarka ba. Ina so ka gaggauta goge babinta a zuciyarka ka manta da ita koda hakan zai cutar da kai.
  Cike da zallar tashin hankali Engineer Ameer Bello Sardauna yake kallon ummarsa da ta koma ta kwanta gami da juya masa baya, da sauri ya ƙarasa buɗe ƙofa ya fita yana tafe yana haɗa hanya da kyar ya isa parking lot ya buɗe mota ya shiga yana maida numfashi wani iri yake ji a jikinsa ba ko tantama yasan ciwonshi ne yake so tashi, da sauri ya tashi mota da mugun gudu ya fita daga asibiti.
   Abbas ya juya ya kalle Bilal Shattima da ya buɗe mota ya shigo ranshi a ɓace sai sauke numfashi yake yi akai-akai sai da Abbas ya ɗauki hanya kafin ya ce "Ya aka yi ne abokina naga ka fito rai ɓace ba dai wulaƙanta ka Jeeddah ta yi ba ko?
"Huhmm! Abbas ba Jeeddah bace asalima ba taji daɗi abinda Khairat tayi min ba. Abbas wallahi na tsani Khairat da ɗan iska nan Haidar Ka'oje kana gani yadda muka tarar dashi manne da Jeeddah, Abbas idan har Haidar Ka'oje ya ci-gaba da bibbiyar matata tabbas ba zan iya sarrafa fushina ba, zai kai matakin da zan ɗauki mummunan mataki akan guy nan. A matsayin ka na abokina kuma amintatce na ka dubi hali da nake ciki ka nemo min mafita Abbas ban taɓa sani ina tsanani ƙaunar Jeeddah har ka ba sai da na rasa ta. Ka tausaya wa rayuwata abokina ka nemo min hanya da Jeeddah za ta sake kasancewa matata a karo na biyu.
  Bilal Shattima ya ƙarashe magana yana hawaye, da gaske yake yi wata irin masifaffiyar soyayyar Jeeddah yake ji tana bin jini da ɓargon jikinsa.
   Shiru Abbas ya yi na ɗan wani lokaci kafin ya riƙo hannun Bilal ya haɗe da nashi cikin kwantar da murya ya ce "Calm down abokina ka sassauta wa zuciyarka mana kalli yanda ka bi ka ɗagawa kanka hankali yau kaɗai duk ka fita hayyacinka, ka ɗaure ka bani ɗan wani lokaci ƙalilan na zauna nayi nazari ta ina za mu fara.
   "Shikenan Abbas na yarda da kai domin ba ka taɓa bani shawarar banza ba. Ka yi nazari mai kyau ni kawai so nake matata ta dawo gareni ko nawa ne zan iya kashewa domin buƙatata ta biya.
  Nusaiba tana zaune a gaban Hajja tana rera kuka kwata-kwata ta kasa gane idan Bilal Shattima ya dosa, ta kira wayarshi kira yafi a kirga bai ɗauka ba. Ta rubuta mishi messages babu adadi nan ma yaƙi responding daga ƙarshe ma sai ya dannawa numberta blacklist yanzu ko ta kira shi sai dai taga user busy, a takaice zuciyarta ta kasa ɗaukar wannan baƙon al'amari shi ne ta zo da kanta wajen Hajja domin ta ji musabbabi wannan sabon sauyi saboda bahaushe yana cewa zuwa da kai yafi saƙo gara ta zo da kanta ayi ta, ta ƙare ina amfani baɗi babu rai. Sai da ya fara lasa mata zuma a baki sai kawai ya guje ta.
Hajja tayi rarrashinta har ta gaji ta zuba mata idanu da ta ga kukan nata ba mai ƙare wa bane, babu shiri Hajja ta ɗauki wayarta ta kira Aunty Bahijja ta zo domin ita ce jagaban haɗa wannan aure. Gara ta zo watakila tana da magani magance wannan kukan na Nusaiba.
   Sosai na ji raina ya yi mugun ɓaci akan irin wulaƙanci da Khairat ta yiwa Bilal ko kaɗan ban ji daɗin hakan ba, asalima haushinta naji shiyasa ina gani ya fita rai ɓace na hayyaƙo wa Khairat cikin kakkausar murya nake faɗin "Wannan wane irin kuturun wulaƙanci ne Khairat akan wane dalili za ki faɗawa Love irin waɗannan maganganu?"
   "Excuse me! Me naji kin kira shi dashi anya kuwa Jeeddah kina da hankali?"
Khairat ta tambaya cikin kaɗuwa da al'ajabi, a fusace na ce "abinda duk kunne ki ya ji dashi na kira shi ko za ki hana ne?
   "Kai dallah ya isa haka!  Nan fa asibiti ne ba gida ba.
Aunty Farida ta faɗa cikin daka mana tsawa, yayin da Khairat ta ce "Aunty ita za ki yiwa faɗa ya kamata ta yiwa kanta karatun ta natsuwa ta fahimci yanzu babu wani abu da yai saura tsakaninta da Bilal Shattima, zance ta cigaba da kiranshi da Love gara tun wuri ta jingina shi a gefe.
   "Ina ruwanki da duk abinda zan kira dashi ni naji zan iya ke miye naki a ciki 'yar baƙin ciki kawai.
    Na faɗa ina mai galla mata harara Aunty Farida ta ƙarbe zance tana faɗin "gaskiya ne abinda Khairat ta faɗa Jeeddah inaso ki sani ci-gaba da kira Bilal da Love zai iya haifar miki da matsala domin a yanzu babu wata alaƙa da za ta sa ki kira da suna Love saboda haka wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da zan sake jin wannan suna ya fito daga bakinki.
   Kauda kaina gefe nayi zuciyata tana tafarfasa ji nake kamar na fashe da kuka. Domin ba su san irin mugun tausayi Bilal da ya darsu a zuciyata ba.
  Abbas ya ce da Bilal  "Shattima ka yi haƙuri mu je ka ji kira da Hajja ta ke maka.
   "Ko na je babu abinda zan yi mata Abbas saboda haka ba inda zan je duk bala'i da nake ciki duk ba ita ba ce silar jefa ni cikinsa ba. Jiya-jiya da rabuwa ta da Jeeddah Abbas dube ni da kyau ka  ga yadda na dawo, tamkar wanda ya shekara yana jinya ni dai wannan biyayyar da na yiwa Hajja ta cutar dani matuƙa.
  "Ka daina faɗar haka Shattima su Iyaye ba abin wasa bane muddin muna so mu ga dai-dai a rayuwarmu dole mu bi su sau da ƙafa mu yi musu biyayya, su kuma kada su yi amfani da biyayya da muke so musu su cutar da mu kamar dai yadda Hajja tai maka ta raba ka da matarka alhali kuna son junanku amma duk da haka ka yi haƙuri ka miƙawa Ubangiji lamurran ka in-sha-Allahu za ka ga haske. Yanzu ka yi haƙuri mu je duk abinda za ta faɗa ka zauna saurare ta.
   "Shikenan mu je ɗin na ji me kuma take so nayi mata.
Haidar Ka'oje ya dawo niƙe-niƙe da manya ledoji  yana miƙawa Khairat ya sake fita ya karɓo sakamakon gwaji da aka yi min yana gani negative ya saki doguwar ajiyar zuciya, gami da yin hamdallah! Fuskarshi cike da murmushi ya shigo yana zuwa ya miƙawa Aunty Farida result ɗin, dariya Aunty Farida da Khairat suka dinga yi masa yayin da ni kuma su duka suka yi bala'in bani haushi ji nake kamar na tashi na rufe su da duka.
Duk abinda suke faɗa ina jin su nai banza dasu sai da yamma Mama da Mommy Turai suka zo duk wanda ya zo duba ni yaga yanda Ya Haidar yake kula dani haɗe da tarairaya ta sai ya yaba mishi saɓani ni da yake bani haushi.
   "Hajja gaskiya Bilal ya yi mugun rena ki in banda reni tun yaushe ya ce gashi nan zuwa har yanzu bai ƙaraso ba ya wani shanya mutane sai kace kayan wanki.
   Aunty Bahijja ta faɗa tana yatsine fuska.
Kafin Hajja ta bata amsa ta ji murya Bilal ya bankaɗo curtain yana faɗin....

#Jeeddah Aliyu
#Team Haidar Ka'oje
#Team Bilal Shattima
#Team Engineer Ameer
#Zazzafan kishi.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now