019...

104 9 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA
   
   *Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku ta karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya kacal_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina 300
Da bansan asalinta ba ₦250

019...

"Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Haba Abbas wannan wacce irin magana ce miyasa za ka dinga jifar matata abin alfahina da munana kalamai irin wannan?" To gaskiya banaso ka daina.
Bilal Shattima ya faɗa da alamu ranshi ya ɓaci da furuncin da Abbas ya yi akan Jeeddah. Fahimtar hakan da Abbas ya yi yasa yai saurin gyaran zancensa ta hanyar cewa "ALLAH ya ba ka haƙuri Shattima ni ban faɗin wannan maganar don ta ɓata maka rai ba na faɗa ne domin ka yi wa tufka hanci gudun abinda zai iya faruwa anan gaba. Amma naga alamar kamar ranka ya ɓaci ka yi haƙuri mu ajiye wannan chapter a gefe mu ɗauko wata kawai.
   "Da yafi gaskiya don ba abinda ke saurin taɓa ni irin na ji ana aibanta matata duk mace da za ta amince ta aureka bakada aikin fari balle na baƙi ta kuma ɗauki responsibilities ɗin kanta da naka ai ba abar zagi bace, wallahi abokina tun daga ranar da mu kayi aure da Jeeddah ta damƙa min ATM card ɗinta da zarrar an yi salary zan fitar da kuɗin albashin nata nayi duk yarda naga dama dasu bata taɓa tambayata ya nayi da ƙudinta ba. Hakazalika ko 'yan uwanta suka bata kuɗi sisi Kwabo ba za ta taɓa a ciki ba ni nake saka su gaba nayi yadda nakeso. Yanzu yaushe rabonka da ka ji nayi maka kukan rashin kuɗi?" Saboda haka Jeeddah tana da daraja da ƙima a idanuwana tayi min hallaci da ba kowa ce mace ce za ta iya ba. Shiyasa duk abinda take yi nake ɗaga mata ƙafa, domin mugun son da  take min ne ke haddasa mata zazzafan kishina.
Wani irin kallo Abbas yake masa kafin ya ja iska daga ƙofufin hancinshi kana ya fesar yace
   "Huhmm..lallai da sauran rina a kaba bari ma na tambaye ka Shattima shin Jeeddah kake so ko kuma abin hannunta, domin ni gaba baki ɗaya ka ɗaure min kai da waɗannan dalilai naka masu ɗan karan ban haushi?"
  "Wannan Wacce irin tambaya ce Abbas? naga dai duk mutumin dake tare da ni zai iya bada gasasshiyar shaida akan irin tsintsar so da nake mata. Balle kai da kake close friend ɗina duk wani sirri nawa ka sani domin bana ɓoye maka duk abinda ya shafe ni.
   "Amma Shattima dole nai maka wannan tambaya ba ni ba kowaye yaji yadda ka taƙarƙare  gaba gaɗi kana furta wannan maganar dole zai yi hasashe irin nawa. Ni fa ina guje maka kwaɗayi abin hannu mace wallahi ba a cin dukiyar mace a kwashe ta daɗi. Shawarar da zan baka daga kai har ita Jeeddah so ne ya haɗa ku saboda haka ka dinga nusar da ita illar da ke tattare da mugun kishin nan nata, domin gujewa faruwa wata gagarumar matsala anan gaba. Sai kuma magana ta gaba Shattima ni a ganina kamar kana shiga hurumin da ba naka ba domin ba kai ke tsarawa kanka rayuwa ba. Rubuta ƙadddarar mu ba a tafin hannunmu take ba balle ka dinga alƙawantawa Jeeddah ba za ka yi  mata kishiya ba. To idan ALLAH subhanahu wata'ala ya ƙaddaro maka auren mace fiye da ɗaya shin ya za ka yi kenan?" Wannan alƙawari ba daidai bane dan Allah ka daina ɗora matarka akan gurɓatatciyar turba da bata da tabbas ka ɗaure ka cire son zuciya ka nuna mata komai muƙaddari ne daga Allah. Sannan kuma ka dinga kauda kai daga abin hannunta gudun wulaƙanci.
  "Shikenan Abbas zan yi iya ƙoƙarina na gani na lurar da ita amma kasani zuciya da yanayin imani ɗan adam shi kesa ya ɗauki alƙawari ya karya ko kuma ya cika shi, ni kan na yarda da kaina In-sha-Allahu in dai ba mutuwa Jeeddah tai ba bani ba ƙara aure. Sannan kuma da kake zance abin hannunta Jeeddah fa matata ce  duk abinda ta mallaka ina da iko akansa da kai da kaya duk mallakar wuya ne.
Kallonshi kawai Abbas ya yi tsabar takaicinshi ya hana shi sake yin magana, sai kawai ya ja bakinshi ya ɗinke.
Kuka sosai Jeeddah tayi ita kanta tanaso ta dinga sarrafa kishinta musamman da ta fahimci kishin nata shine silar da ke haddasa musu rashin jituwa ita da Love ɗinta. Sai dai ta rasa ta ya za ta fara controlling kanta. Wayarta da ke cikin handbag tai ringing ta tashi daga inda take ta nufi jakkar da ta wulgar akan tiles ta ɗaukota ta dawo ta zauna inda ta tashi ta ciro wayar, A'isha Shattima ce ke kiranta cikin sanyi murya tace "Hello A'isha!
   "Jeeddah ya haka tun ɗazu mai lalle nan ta zo tana zaman jiranki ko kin fasa taho wa ne tai tafiyarta?"
   "A'isha in zai yu ko zo tare gidana tayi min.
Yadda A'isha Shattima ta ji muryar ƙawarta ta tasan akwai matsala, saboda haka tana kashe waya ta shirya cikin sauri ta nufo gidan Jeeddah ɗin. Koda A'isha Shattima ta iso Jeeddah tana bedroom ta nunawa mai lalle wurin zama a parlour kana ta wuce bedroom zaune a gefen gado ta tarar da ita idanuwanta sun yi luhu-luhu alamun tasha kuka har ta gode ALLAH.
   "Subhanalillah.....Jiddo me ya faru ne naga idanuwanki sun jajir alamun kin yi kuka?"
Ajiyar zuciya Jeeddah tayi gami da cizon leɓenta hawaye na kara-kaini akan kumatunta cikin muryar kuka taba A'isha Shattima ainihin labari abinda ya wakana tsakaninta da Bilal Shattima. "Ni Wallahi A'isha gidanmu zan tafi na fara gajiya da halin ɗan uwanki.
Jeeddah ta ƙarashe magana sabbin hawaye ba bin kumatunta.
   Kasancewar A'isha Shattima tasan halin mutuniyarta ta da mugun kishi, shiyasa ko kaɗan bata yi mamaki abubuwan da ta aikata ba saboda ta kwana da sani fiye da hakan ma za ta iya. Cikin kwantar da murya A'isha Shattima ta shiga bata shawarwari gami da 'yar nasiha ta hanyar cewa "Haba Jeeddah yanzu da hankalinki da wayaunki za ki bari wata matsala ta kunno kai a cikin zamantakewar aurenku. Kishi halak ne domin ko matan Annabawa Allah sun yi amma ba irin wannan naki ba, idan kika ci-gaba da nuna wannan hali naki to ki sani za ki waye gari soyayyarki za ta ficewa Ya Bilal a zuciya domin kin kasa bashi kulawa da kwanciyar hankali da kowane namiji yake mafalkin samu daga wurin matarsa. wallahi-tallahi Jeeddah Ya Bilal yana sonki yana miki wani irin so da fatar baki ba za ta iya misalta shi ba kema shaida ce akan haka. Saboda haka ki daina zarginshi domin zargi yana ɓata aure. Dan Allah Jeeddah ki tattare wannan zazzafan kishin naki ki watsar dashi ki rungume mijinki kada ki bari wannan dalili ya kawo ɓaraka a tsakaninku akwai da yawan mutane da suka sa muku ido abu kaɗan suke jira ya ɓullo su yi muku dariya, kinsan dai yadda aka yi aurenku. Ki yi duba da ƙanwarki Khairat tun da aka yi aurenku kin ji wani saɓani ya shiga tsakaninta da mijinta?"
Girgiza kai Jeeddah tayi A'isha Shattima ta ci-gaba da cewa "saboda haka ki rufawa kanki asiri zance za ki tafi gidanku bai ma taso ba. ki koyi yadda za ki dinga magance matsalolinki ba tare da kin fitar da sirrin aurenki waje ba. Yanzu tashi za ki yi mu je parlour ayi miki lalle na rangaɗa miki kitsonki, koda Ya Bilal ya dawo ki nuna masa komai ya wuce ki ba wa mijinki haƙuri domin ke ce ƙasa dashi.
  Doguwar ajiyar zuciya Jeeddah tayi tare da sa bayan hannunta ta goge hawayenta, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi tabbas duk abinda A'isha Shattima ta faɗa babu ƙarya a ciki. Jikinta a mace ta tashi ta shiga bathroom ta wanke fuskarta ta fito cikin ƙanƙani lokaci aka kammala mata jan lalle hannuwa da ƙafafuwanta kana A'isha Shattima tai mata kitso sai bayan la'asar A'isha ta wuce gida kafin ta tafi sai da ta ƙara jaddadawa Jeeddah ta daina biyewa duk abinda zuciyata ta ayyana mata.
  Ko kaɗan Bilal Shattima bai yi marmari dawowa gida ba hatta da abinci gidan Abbas suka je ya cika cikinsa, kana da yamma suka taho zaman majalisa wanda ya zame musu jinin jiki. Tun zuwansu majalisar abokansu masu mata bibbiyu ke tsokanar Abbas dama haka ɗabi'arsu take idan kana da mata ɗaya sun dinga yi maka sharri kala daban-dabam kenan. Gami da zuga ka da ka ƙara aure koda kuwa bakada ra'ayi har sun cusa maka ra'ayi abin a zuciya to yau ma haka ce ta kasance daga zaman Bilal da Abbas, Rasheed ya fara cewa da Abbas "mai mata guda aminin gwaro haka kawai da ranka da lafiyarka Abbas ga kuɗi Alhaji ga wadatatce muhalli amma ka buge da zama da mace guda sai kace mai bakin uwa.
  Gaba ɗaya masu mata bibbiyu a wuri suka Kwashe da dariyar  shaƙiyanci sosai dariyar tasu ta ɓatawa Abbas rai saidai bashida yadda zai yi ya gwada neman aure yaso ya aure Asiya yana sonta tana sonshi haka kawai aka waye gari iyayenta suka kafe akan lallai sai 'yarsu tayi karatu a nursing school, shi kuma ya ce matarsa ba za tayi karatu ba. Shine suka rabu amma duk da haka kullum da irin sharrin da abokansa ke masa.
Murmushi mai cike da zallar takaici Abbas ya yi gami da faɗin "Surutunku ba zai harzuƙa ni ba naje na kwasowa kaina kara da kiyashi kamar yadda Sadik ya yi.
Abbas ya ƙarashe magana yana kallon gafen da Sadik yake zaune riƙe da mug ɗin black tea a hannunshi yana sipping, da sauri Sadik ya ajiye mug ɗin yana faɗin "A'ah yau ga iskanci banza da wofi ka rasa shegen da za ka buga misali dashi sai ni, to ba gara ni na ɗanɗani zaƙi da garɗin mata biyu ba kai fa?"
Dariya sosai suka kwashe da ita a wannan karon Bilal Shattima ne ya tanka "ka faɗi tsakani da Allah Sadik ɗañɗanawa kawai ka yi amma ba wani zaƙi da garɗi da ka ji.
   "Shattima ka rufe min bakinka idan ana irin wannan zance ka daina tofa albarkacin bakinka saboda kai har yanzu kana da sauran sani a wannan harkar.
   Cewar Sadik yana harara Bilal Shattima, Hisham ne karbi zance ta hanyar faɗin "tsakani da Allah duk mai mata guda anan wuri anbarshi tasha Alhaji bai kwashe romon dimokuraɗiyya ba. Wallahi ku je zuwa ƙara aure sannan ne za ku san kun yi aure amma mace guda kullum fa abu guda ne kacal kayi ta maimaitawa ai sai ya gundire ka.
Habawa yana dasa aya suka sake tintsirewa da mahaukaciyar dariya, sai tafawa suke yi sai kace waɗanda aka yi wa albishir da gidan aljanna.
Kiran sallar magariba ya tashe su daga firar tasu, bayan sun kammala sallar isha'i suka sake dawowa suka dasa sabuwar fira yanzu kuma chapter siyasar ƙasar nan suka buɗe musu da gardama ya kaure tsakanin magoya bayan jam'iyyar adawa sai sukar jam'iyyar da ke mulki suke yi yayin da kuma magoya bayan jam'iyyar da ke mulki, ke ƙoƙarin ƙare jam'iyyarsu. Zuwa wannan lokaci goganyar taku ido ya rena fata, tayi girki na musamman an caɓa kwalliya sai zaman jiran Love ake yi shi kuma yana can majalisar gantalallu yana gantallewa abinsa, sai around 10 o'clock ya waiwaye gida karar machine ɗinsa da ta ji yasa ta miƙewa da sauri ta nufi ƙofar fita daga parlour yana ƙoƙarin shigowa da machine ɗinsa parlour, dama anan yake ajiye shi gudun kada ɗan kande ya sulale mai dashi kallo guda yai mata ya ɗauke fuska, shi a dole fushi yake yi amma a can ƙasan zuciyarsa mugun daɗi ya ji don bai zaci za ta huce cikin sauƙi ba. Yana ƙoƙari gittawa ta gefenta ya wuce ya ji saukar muryarta ta ce "Sannu da zuwa Love.
   "Yawwa!
Amsa mata can ƙasan maƙoshi ya shigewarsa bedroom duk da haka bata yi fushi ba ta sake biyo shi a baya tana faɗin "Love na haɗa maka ruwanka da alamar yau ka kwaso gajiya?"
Bai tanka mata ba sai da ya ƙarasa shiga bedroom yana wani shan ƙamshi gami da hura bututun  hancinsa, a dakile ya ce "Ki barshi kawai nagode zan iya haɗawa da kaina.
  Shiru Jeeddah tayi yayin da Idanuwanta suka kawo ruwan hawaye, ko kallonta bai sake yi ba ya cire kayan jikinshi ya shige bathroom bata yi ƙasa da guiwa ba ta nufi jikin bango bathroom ɗin ta jingina tana jin saukar ruwan wankanshi lokaci zuwa lokaci take goge hawaye. Yana turo ƙofa ya ganta ya tsaye tana sharar hawaye abinka da so duk sai ya ji tayi bala'in bashi tausai amma azahiri bai nuna hakan ba, sai ma sake raɓa ta ya yi ya nufi gaban dressing mirror yana goge jikinshi. Tana gani yadda yake nuna mata halin ko in kula yasa ta sakin kuka mai ɗan ƙaramin sauti, tun tana yi a hankali har ta dawo yi da ƙarfi cikin sauri ya ƙarasa saka pajama ɗinshi ya fesa turare ya nufi ƙofar fita nufinsa ya bar mata ɗakin yana kai hannunshi kan handle ta rugu da gudu ta rungume shi ta baya tana kuka gami da bashi haƙuri tsananin kuka da take yi muryarta da kyar ta ke fita "Dan ALLAH Love ka yi haƙuri na tuba ba zan ƙara ba Dan ALLAH ka yi min uzuri wallahi ba yin kaina bane sonka ne ya yi min yawa shiyasa bana iya control kishina akanka.
Ta ƙarashe magana tare da wani irin gunji kuka. Da sauri ya juyo ya rungumeta gam yana bubbuga gadon bayanta yana faɗin "kukan ya isa haka Love kema kinsan banaso ɓacin ranki dole ce tasani fushi dake ba don raina yaso ba. Muradina ki rage wannan mugun kishin naki.
Ta ɗago idanuwanta ta kalleshi tana goge fuskarta da tafin hannunta, riƙo ta ya yi suka fito parlour.
  "Love mu je ka ci abinci yau favorite food ɗin ka na girka ma.
Ta faɗa cikin muryarta da ke nuni da tayi kuka.
Duk da baya jin yunwa gudun kada ranta ya ɓaci yasa ya washe baki, suka nufi dinning room haka nan ya dinga cusa abinci ba don yana jin yunwa ba sai don gudun kada ya sake tona wata sabuwar fitina.
***** **** ******
A kwana a tashi asarar mai rai gashi har auren Bilal Shattima da Jeeddah ya shigo wata na shidda, yau da daɗi gobe akasin hakan yau fari gobe ɓaki a haka suka ci-gaba da rayuwa, gaba ɗaya salary ta akanshi da mahaifiyarshi da 'yar uwanshi yake ƙarewa ta ɓangaren Babanta duk ƙarshen wata sai ya aiko Abdul yaronshi na kasuwa ya kawo mata foodstuffs, hatta da nama, kifi Baba na monthly yake siyo mata hakazalika 'yan uwanta duk ƙarshen wata sai sun turo mata da kuɗi ta account ɗinta. A dalilin mugun tausayinta suke ji a ganinsu bata tashi cikin rashi ba amma ta buge da aure marar aiki yi, duk ƙarshen wata sai Aunty Farida ta tura mata 20k ko ya Kabeer da baya son aureta 30k yake tura mata hatta da Khairat lokaci-lokaci tana tura mata da kuɗi sai dai kawai taga alert shiyasa gaba ɗaya Bilal Shattima ya tattara neman aiki ya watsar, daga shi har mahaifiyarshi da 'yar uwanshi ba abinda suka nema suka rasa in ka ganshi ya shirga uwar ƙiba yayin da ita kuma Jeeddah ta bi ta rame ta ƙanjame a dalili laulayin ciki da ya sako ta gaba hatta da ruwa indan tasha sai ta amayar dasu, ta dawo yau ciwo gobe lafiya. A gefe ɗaya Bilal Shattima sai wadaƙa da ƙudinta yake yi duniya ta dawo masa sabuwa tsabagen samun wuri hadda canzawa yaran Bahijja biyu school ya ciro su daga government school yasaka su a private.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now