047

95 15 3
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!* _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka*

*Ina masoyana wanda suka karanta littafin BIBIYATA AKEYI 🤝 WANNAN SALON SHEKARAR 2017 NE, YA KUKAJIN LABARIN? NASAN DA YAWANKU BAKU MANTASHI BA!*

*TO MASOYA GANI NAN NA KAWO MUKU WANI ZAZZAFAN LABARI MAI CIKE DA SALO KALA KALA!!! WANNAN SABON LABARI SHINE BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI).*

*WANNAN SALON 2023 NE! SABON LABARI SABON SALON LITTAFI DABAN YAKE DANA BAYA BIBIYATA AKEYI!*

*BIBIYATA YAKEYI(WAYESHI) PAID BOOK NE BA FREE BA.🤝*

*TURA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT D'IN.*

*ACCOUNT NUMBER:-0003075326 ZAINAB M BAWA*
*Jaiz bank SHAIDAR BIYA TA 08161146563.*

*KO KATIN MTN TA WANNAN LAMBAR 08161146563 TARE DA SHAIDAR BIYA.*

*SANNAN NAYI ADDING D'INKI A GROUP.. GA WACCE BATADA BUKATAR SANYATA A GROUP 400 ZAKI BIYA KULLUM ZAKINA SAMUNSA DA PC DA ZARAR ANSAKE.*

047..

Cikin tsanani tashin hankali na yada ganina akan Hajja yadda ta taƙarƙare tana rantsuwa sai Bilal ya sake ni ko ta tsine masa. Ba ƙaramin kaɗawa hanta cikina tayi ba. A kiɗime Bilal ya zo gaban Hajja ya zube gwuiwayinsa kana ya haɗe hannuwanshi yana faɗin "Ki dubi girman ALLAH Hajja ki janye wannan furunci naki Inaso matata ita ma tana sona na roƙe ki kada ki cilastani na aikata abinda zai wargaza min rayuwa...
"Rufe min baki sakarai kawai!
Hajja ta daka mishi rikitatciyar tsawa kana ta ci-gaba da faɗin "A yanda na sha alwashi sai ka saki tsananniyar yarinya nan magiyarka ba za ta canza min ƙudirina ba. kwata-kwata ma banga amfani zamanka da ita ba. Kai har yau ka kasan fahimtar ba son tsakani da ALLAH take maka ba. Tun daga ɗa ɗaya cal! Da ta haifa maka ta zarge bakin mahaifarta kuma tsabagen mugunta irin na iyayenta ƙiri-ƙiri suka raba ka da ɗanka kai dashi sai hange daga nesa.
"Hajja wannan hujjar bata kai matsayi da za ki dogara da ita ki cilastani na saki matata ba.
"Wallahi-azim sai ka sake ta matuƙar ni ce na tsuguna na haife ka sai ka saki Jeeddah a yau ɗinan.
Hajja ta katse shi cikin tsawa da hargowa gani yadda take ta shan rantsuwa yasa Bilal Shattima fashewa da kuka duk jarumta irin ta ɗa namiji da aka san shi da ita Bilal ya nemi ta shi ya rasa a hankali na dinga tafiya da baya-baya har na ƙure a jikin bango na jingina bayana domin ƙafafuwana ba zai su iya ci-gaba da ɗauka ta ba. Tsawon rayuwata ban taɓa shiga tashin hankali ba irin wannan, na dawo tamkar gumki gani dai a tsaye amma na kasa tantance wacce duniya nake ciki sai rarraba idanuwana nake yi daga kan love zuwa ga Hajja kana na dawo kan Aunty Bahijja tun ina fahimtar zantuka da suke musanya a tsakaninsu har na dawo sai dai naga bakunansu na motsi.
Duk roƙon da Bilal yake yiwa Hajja sai dawo tamkar yana ƙara zuga ta ne don sai rantsuwa take yi maimaita wa idan har bai sake ni ba za ta kwashe masa albarka, kuka Bilal Shattima yake yi haiƙan gani hali da ya shiga yasa nima durƙusawa na shiga bata haƙuri "Dan ALLAH Hajja ki yi haƙuri kada ki tarwatsa mana rayuwar aurenmu...
Tun kafin na ƙarasa magana ta katse ni ta hanyar daka min tsawa "Yi min shiru munafuka mai baƙar anniya yau ƙarshen zamanki da ɗana ya zo tsinaniya kawai.
Ba zan iya jure jin waɗannan kalamai ɓatatci ba zuciyata ba za ta iya ɗauka ba saboda haka na tashi daga durƙuso da nayi yayin da Aunty Bahijja ta bini da zagi, ban kulata ba na koma jikin bango na lafe Bilal ya daka mata tsawa yana faɗin "Ya isheki haka Aunty Bahijja karki sake na daina gani girmanki kwata-kwata.
"Bahijja sa'arka ce da za ka dinga yi mata barazana to bari ka ji matuƙar kana so albarkata ta ci-gaba da bibbiyarka ka bi umarnina.
"Hajja Dan ALLAH ki yi haƙuri wallahi ba zan iya sakin Jeeddah ba....
"Ka sake ta Bilal ko na tsine maka.
Hajja ta katse shi a fusace domin ya kai ta bango.
"Ba zan iya ba Hajja wallahi inaso matata.
"Na ce ka sake ta Bilal wannan shi ne kashedina na ƙarshe idan ba ka sake ta ba Wallahi-azim zan tsine maka.
"Hajja Dan ALLAH kada ki tsine min...
"To ka sake ta idan ba ka so tsinuwata.
Sunkuyar da kai Bilal Shattima ya yi, yayin da yake wani irin gunji kuka irin mai azabar cin rai ɗinan kafin ya ɗago idanuwanshi ya kalle Jeeddah da ke lafe ga bango tana shasshekar kuka, wani irin mugun sonta ya ji ya mamaye ciki da waje zuciyarshi, kana ya dawo da ganinshi akan Hajja ya ce "shikenan Hajja zan sake ta amma kafin sannan ina neman alfarmar da ki janye zance saki uku ɗinan domin gujewa faɗawa fushin ubangiji..
"Karka sake ka yi min wa'azi anan wuri ka bi umarnina shi ne zaman lafiyarka.
"Hajja saki uku ya yi yawa ko a addinan ce ba a so kada ki yi min umarni da abinda zan dawo ina danasani akansa. Idan na sake ta saki ɗaya daga baya idan kin huce Hajja sai in dawo da matata domin ina sonta.
"Wato ba za ka bi umarni nawa ba kou? To shikenan tun da ka zaɓi tsinuwata dama can ba kai kaɗai na haifa ba saboda haka Bilal ALLAH ya ts....
Kafin Hajja ta ƙarasa tsine masa yai sauri furta.
"Jeeddah na sake ki saki ɗaya saki biyu...
kasa ƙarasawa ya yi kuka ya ci ƙarfinsa cikin ɓacin rai Hajja ta kalle shi tare da faɗin "ka ƙarasa saki ɗayan mana na fa rantse saki uku za ka yi mata kuma a rubuce na ke buƙata ba a baki ba domin za ka iya dawowa daga baya ka ƙaryata ita kuma ba cikekken imani ne da ita ba za ta goyi bayanka ku dawo kuna zaman dadiro saboda haka rubuta mata a takarda ta kai ma iyayenta shaida.
Sulelewa nayi ƙasa na runtse idanuwana yayin da nake ji wani irin tuƙuƙin baƙin ciki yana bin zuciyata, can sama-sama nake tsikayar murya Bilal yana faɗin "Hajja banida takarda balle biro biyu ma da nayi mata ya wadatar.
"A gareka ya wadatar amma a gareni tamkar na kashe maciji ne ban sare kai ba saboda haka a shirye na zo Bahijja bashi biro da takarda da na riƙo masa.
Aunty Bahijja ta zuge jakkata tana murmushi mai cike da zallar farin ciki ta fiddo da biro da takarda ta miƙawa Hajja kana Hajja ta miƙawa Bilal, tana faɗin "Ai saboda gudun irin haka yasa na zo da shirina maza rantaɓa mata uku cur! Ka yadda kwallo mangwaro mu ma mu huta da kuda kafin ya karɓa sai da ya kalle ni zuciyarsa tana bugawa da mugun ƙarfi ya shiga rubutu yana kammalawa ya mike ya shige bedroom da sauri. Aunty Bahijja ta zo da sauri jikinta har rawa yake yi ta ɗauki takardar ta shiga karanta wa tana kammala wa ta saki ihu da shewa kana ta zarce da rangaɗa guɗa "Hajja yau ALLAH ya raba mu da alaƙaƙƙai aje can a bi wani sarki ba dai na garin mu ba karɓi nan annoba Bilal dai ya cika aiki ya rangaɗa miki saki uku, daga yau kin bi sahun zawarawa Sakkwato.
Ta ƙarashe magana tare da jefa min takardar akan fuskata.
"Aiki ya kammala zo mu tafi Bahijja.
Hajja ta faɗa tana kamo hannun Aunty Bahijja.
"A'ah! Hajja da saura dai gara mu tusa ƙeyar Bilal gaba tun da nan gidan ba nashi bane gara ya tattara abinda yake mallakinsa mu tafi gudun kada 'yan uwanta su zo su yi masa tozarci kinsan shi ɗin ba zuciya ce dashi ba.
"En! Kuma kina da gaskiya zo mu je ɗakin gara ya bar mata tsinane gidanta da take yiwa mutane gaddara akansa.
Daga haka suka nufi cikin ɗakin baccinmu bansan ya aka yi ba sai ga su sun fito tare da Bilal ko tsinke bai ɗauka ba Bilal ya nufi gun da nake a zaune ya durƙusa a gabana cikin muryar kuka ya ce "Ba don bana sonki ba na sake ki ba na saki ne a bisa cilastawar mahaifiyata, na bi umarninta ne domin gujewa tsinuwarta ina kuma ƙaunar na ci-gaba da kasancewa ɗa mai biyayya a gare ta, ina kuma son ki sa aranki sonki yanzu na fara idan mutum ya cika ya zo ya cire min. Raba aurenmu ba shi bane datse soyayyar dake tsakaninmu, lallai zan tabbatar miki da cewa ni Bilal Shattima mai ƙaunarki ne na haƙiƙa.
Daga haka ya juya ya nufi ƙofa fita da kyar na yunƙura na tashi tsaye domin gaba ɗaya jikina jin sa nake yi kamar bani da lakka, Aunty Bahijja ta kalle ni ta kwashe da dariya tana faɗin "ai na gayamiki Jeeddah ki bi ni a sannu domin ni kwalki ce daidai ƙugun kowa. Kin ga dai yanda na gama da babinki cikin sauƙi da sauƙaƙawa da fari sai da nasa mijinki ya yi miki kishiya a maimakon ki fahimci girman izzata gami da ƙarfin ikona da yake ke daƙiƙƙiya ce sai ki ka sake yi min abinda ya uzirani har sai da na daddatsa igiyar aurenki ba fa guda ɗaya ba duka uku na tsitsika su kamar ana tsika igiyar shanya.
Ta ƙarashe magana gami da yi min kallon sama da ƙasa ta watsar duk da ina cikin yanayi marar daɗi amma hakan ba yana nufi ba zan iya mayar mata da martani ba, saboda haka cikin dusashewar murya na ce "Tabbas kin zama silar rusa tubalin rayuwar aurena amma ina so ki sani Aunty Bahijja lallai sai na zame muku karan tsaye a rayuwarku muddin ina nunfashi rabani da Bilal sai ya zame muku bala'i da masifa ba kun kirani da annoba ba tabbas za ku ga annoba gani idonku, domin daga ke har wannan tsohuwar banzar sai na saka ku kuka da hawayenku.
A Hajja ta yo kaina da nufi rufe ni da duka domin ita Aunty Bahijja ta gama sani hatsari dake tattare da tunƙaro ni gaba gaɗi shiyasa ko kusa ba ta gwada yi wannan ganganci ba. A fusace kuma ciki ɗaga murya na ce "Kul! Karki soma gwada wannan ganganci idan ki ka sake hannunki ya sauka a jikina na rantse sai na nuna miki tsagoro jahilci, dama can ina girmama ki ne a dalili auren ɗa ki da yake kaina kin kuma ri ga da kin datse shi a yanzu babu komai a tsakanina dake kina gwada dukana sai na ƙarya miki hannu kuma maza ku tattara ku fi ce min daga gida tun kafin na nuna muku nawa kalar iskanci shegu matsiyata wanɗada basu gadi arziki ba. Idan har kun cika 'ya'yan shegu a ɗaurawa ɗaya daga cikinku aure da Bilal.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Jeeddah ni fa mahaifiyar Bilal ce wannan kuma yayarsa uwa ɗaya uba ɗaya don tsabar ɗibar albarka ki ke danganta mu da aurensa lallai Jeeddah ke ɗin ba ɗiyar arziki bace.
Hajja ta faɗa tana matsar idanuwa Aunty Bahijja ta kama hannu Hajja tana faɗin "rabuda ita Hajja zo mu tafi kinsan zafi da muka haɗa mata ba na wasa bane da alama nan gaba kaɗan haukacewa za tayi.
"Uwarki ga ta nan gabanki tsaye ita ce za ta haukace.
Na faɗa ina sauke numfashi da kyar ba su ƙara kula ni ba suka fi ce abinsu, ban tabbatar da ingancin maganar Aunty Bahijja ba sai da suka tafi na zube ƙasa na rushe da wani irin kuka ina yi ina duka fuskata don gani nake yi kamar a mafalki ne abubuwa nan suka wakana dukan da nake yiwa kaina ina yi ne domin na falka sai da naji zafin dukan ya ratsa fuskata sai na fahimci duk abinda ya faru a zahiri ne ba a mafalki ba. Na yi kuka tamkar hawaye idanuwana za su kafe babban tashin hankalina bai wuce furuncin Baba akaina ba. A duk lokaci da na tuna sai na ƙara gigicewa na rasa tudun dafawa har aka yi sallar Azhar ina kwance akan tiles idanuwana sun yi luhu-luhu ga baki ɗaya na fita hayyacina, da kyar na tashi na shiga bathroom na watsa ruwa kana nayi sallah nan take zazzaɓi mai zafi ya rufe ni. Na tashi na hau gado na kwanta na lulluɓe jikina da duvert fuskata kaɗai na bari a waje daga nan bacci wahala ya ɗauke ni.
Ta ɓangaren Bilal yana fita ya shiga motarsa da mugun speed ya bar unguwar kaitsaye gidan abokinsa Abbas ya nufa, a lokaci da ya yi arba da Abbas zubewa ya yi a gabansa ya fashe masa da kuka kamar ƙaramin yaro, sosai hankali Abbas ya tashi gaba ɗaya ya bi ya ruɗe shi ma durƙusawa ya yi ya riƙo kafanɗun Bilal yana girgiza shi "Subhanalillah! Shattima kuka me ka ke yi rasuwa aka yi ne waye ya mutu Please Shattima ka yi magana mana?"
Kusan a jere Abbas ya watsawa Bilal waɗannan jeri tambayoyi.
"Shikenan na rasata na rasa Jeeddah Abbas Hajja ta cilastani na saki Jeeddah saki har uku.
Ya ƙarashe magana tare da sake rushewa da sabon kuka har yana haɗawa da shassheka.
"Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Hasbunallahu wal-imaal wakeel! Amma kuwa Hajja bata kyauta ba me ya yi zafi da za ta yanke hukunci irin wannan?"
"Bari kawai Abbas Hajja ta gama da rayuwata ta rabani da matata adaidai lokaci da nake da burin kyautata mata. yanzu wani irin kallo take so mutane su dinga yi min? Na tabbata da yawa sai sun zarge ni da rashin yiwa Jeeddah adalci mace da ta zauna dani banida ko kwabo ta dinga faɗi tashi akaina, yanzu da ALLAH ya azurta ni a maimakon na saka mata sai kawai aji na ƙara aure baya nan kuma na sake ta saki har uku, wallahi Abbas duk wanda ya ji wannan labari dole ya tsine min.
Hannunshi Abbas ya riƙo ya miƙar dashi tsaye kana ya nufi cushion ya zaunar dashi, sa'anan shima ya zauna ya dafa ƙafadarshi "Ka yi haƙuri Shattima ka ɗauki wannan al'amari a matsayin ƙaddara iya adadin zaman da ALLAH ya tsara a tsakaninku kenan. Sai dai kai ma Bilal ka yi ganganci da ta kafe lallai sai ka saki Jeeddah sai ka yi saki ɗaya mana amma saki uku sai ka ce jahili ka sani babu biyayya ga Iyaye wurin saɓawa Ubangiji. Duk da ALLAH ne ya halatta saki amma ba irin wannan ba. Yanzu gashi tun ba a je ko ina ba ka fara kuka ba mu san abinda zai faru anan gaba ba. Iya abinda zan ce da kai ka yi haƙuri kuka ba zai dawo da aurenku ba. Ka rungume ƙaddara da ta Kunno muku. Jiya-jiya nan fa ka biya mata makka sai ga wannan al'amari ya faru.
"Uhmm!
Bilal ya faɗa yana mai dafe goshinsa.
Sai bayan sallar la'asar ya nufo gida ban yi tsammanin zan tarar da Jeeddah a gidan ba. Yana shiga bedroom ya yi tozali da ita tana sharar bacci daga yanayi da ya ga numfashinta yana sauka ya fahimci bacci wahala ne take yi, ƙura wa fuskarta idanuwanshi ya yi yana kallonta, tsanani tausayinta gami da soyayyarta suka lulluɓe shi kusa da ita ya nema ya zauna ya ciro hannunta daga cikin duvert ya matse cikin nashi ya ɗauki dogon lokaci yana aiki kallo hawa da saukar numfashinta kafin ya miƙe ya shiga bathroom ya yi wanka yasaka jallabiya ya fice zuwa parlour, ya kira royal cuisine restaurant ya yi mata order abinci saboda yasan throughout ba abinda taci.
Kiran wayata ya falkar dani daga bacci da ya dauke ni wani irin sarawa kaina ya yi na sauko daga gado dafe da goshi na ɗauki wayata dake aje akan mirror, wani irin mugun faɗuwa gabana ya yi a dalili Aunty Farida ce mai kiran nawa, har kira ya tsinke ban iya ɗagawa ba. Na bi agogon wayar da kallo ashe na ɗauki lokaci kwance ina bacci domin ƙarfe 5:40pm da sauri na ajiye wayar na nufi bathroom na sake watsa wa jikina ruwa ko zan ji kuzari, har na kammala sallah Aunty Farida tana kirana cike da ƙarfin hali na ɗauki kiran nata "Wai ke ina kika shiga ne ina ta kira ba ki ɗaga ba?"
"Ki yi haƙuri Aunty koda ki ka kira ina bacci bari nayi sai nayi sallah na bi kiran naki sai gashi kin sake kira ya gida da yarana?"
"Lafiya qalau suke naso ki zo yanzu mu je ki zaɓi furnitures ɗin da ki ke so.
Jin abinda ta faɗa ya ƙarya min da zuciya na fashe da kuka mai sautin gaske duk tambayar da ta ke yi min kasa faɗa mata dalili kukan nawa nayi, daga ƙarshe ma sai dantse kira nayi na kifa kaina a gefen gado na ci-gaba da kuka na. Sautin kukanta da Bilal Shattima ya ji daga parlour yasa shi nufo cikin bedroom ɗin.
"Love ki yi haƙuri ni kaina nayi kuka nan har na gaji dole na rungume ƙaddara.
Jin muryar Bilal a bayana yasani ɗagowa da sauri domin bansan cewa yana cikin gidanan ba. Aunty Farida bata haƙura ba ta sake kiran wayata ina kallo Bilal ya ɗauki wayar ya gayamata ga mu nan tafe gidanta.
"Love tashi ki shirya na kai ki gidan Aunty Farida domin hatsari da ke tattare da ci-gaba da zamanmu a gidanan.
Ban ce da shi uffan ba na miƙe tare da sake zura hijabina na sallah na fice ina mai ci-gaba da rera kuka.
Har muka iso gidan Aunty Farida Bilal yana aiki rarrashina amma kamar ƙara ingiza ni yake yi, da sauri na ɓalle murfi mota na fita na kwasa da gudu na shiga entrance ɗin gidan a parlour na tadda aunty Farida ina zuwa na faɗa bisa jikinta ina gunji kuka Bilal Shattima ya shigo da sallama yayin da hankali Aunty Farida yana kaina shiyasa bata sami damar amsa mishi ba ya nemi cushion ya zauna shi ma ya saki nashi kuka, ai kuwa hankali Aunty Farida ya ƙara tashi domin ƙato majiyi ƙarfi iri Bilal Shattima ace yana kuka har dasu shassheka lallai al'amari babba ne.
Da kyar da shudin goshi Bilal ya yi mata bayani abinda ya faru, ai kuwa ba ƙaramin kaɗuwa tayi ba cikin tashin hankali take kallonshi da Jeeddah ce ta faɗa mata Bilal ya sake ta saki har uku ba za ta yarda ba amma da yake maganar ta fito daga bakinsa ko kwakwaran motsi ta kasa yi ta ɗauki dogon lokaci a haka kafin ta ce "Shikenan Bilal ba komai su kuma iyayenka nasu hallaci kenan tun da yanzu sun ga ka yi kuɗi ka sami ƙazantar duniya shine za su sakawa Jeeddah da butulci ko butulci irin wannan mai matuƙar muni. Tashi ka tafi kawai da sannu za ku ga sakayya.
"Aunty Farida ki fahimce ni wall..
"Dan ALLAH Dan Annabi Bilal ka tashi ka fice min daga gida banaso ƙara jin wata kalma daga bakinka.
Aunty Farida ta katseshi cikin tsawa da hargowa saukowa ya yi daga kan kujera ya zube gwuiwayinsa kan tiles ya shiga roƙon Aunty Farida, gani yanda yake mata magiya yasa ta fizge hannuna muka shige bedroom ɗinta, Bilal ya gaji da zama kana miƙe ya bar gida zuciyarshi kamar za ta yi bindiga ga Nusaiba sai faman kiran wayarshi take yi shi kuma yaƙi picking tuni Aunty Bahijja ta fesa mata kyakkyawan labari ya saki Jeeddah...

*Ina daɗa ba wa makarantar wannan littafi haƙuri a bisa rashin update akai-akai Dan ALLAH ayi haƙuri dani*

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now