046

100 17 2
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

💧💥 *DA MA ACE.....!*

*TAGWAYE BIYU 2023*🔥🔥🔥

*SLIMZY*
*FEEDHOM*

*DAGA HAZIK'AN MARUBUTANKU WADANDA KE NISHADANTAR DAKU DA KAYATATTUN LABARANSU DA KUKE MARARI WATO RUD'ANI DA KUSKUREN SO*

*DAMA ACE....*

Labarin Nadiya! Nadiya...... Labari ne da aka gina bisa halin mu na yau da kullun, ba kuma gama garin labari ba! NADIYA, matar aure, yayin da ƙaddara ta afka mata to soma soyayya da wani mutun daban, wanda ta ke jin inda babu shi, ba zata taɓa rayuwa ba, gefe guda kuma Sadeek, wanda ya mutu a kan ƙaunar ta kuma ƙani ga Alaji....!
Bai taɓa haihuwa ba! Hasali ba zai haihu ba! Kwatsam sai ga ciki daga matar shi? Shin ɗan waye? Hmmm m... Soyayya, tausayi, cin amana, duka a littafin DAMA ACE..... 🔥🔥🔥🔥

Kin shirya?
Ki biya kuɗin ki domin tafiyar da ke, tafiya ce da zata jijjiga zukatan makaranta, Naira 500 ne  9994468172 Access bank fiddausi musa tare da shaidar biya ta 08036953516 ko 07042277401.

*AKWAI SPECIAL DISCOUNT DA MUKAYI DAGA YAU ZUWA RANAN DA FREE PAGES ZASU KARE GAREKU MASOYANMU DIK WANDA YAKESON SHIGA WANAN TAFIYA TO YA BIYA 400 DAN SAMUN DAMAR DA ZAA DAMA DAKU A LABARIN *DAMA ACE ....*

Kuma kin san wani abin ɗaɗin, ba zamu dakata da posting RUƊANI da KUSKUREN SO ba, ko da ace saura basu samu ba, ina tabbatar maku da waɗanda suka biya zasu samesa maza ku hanzarta

*SLIMZY*
*FEEDHOM*

*TAGWAYE BIYU 2023*🔥🔥🔥🔥🔥

046..

Kafin nai wani yunkuri Baba ya fito da bulala da ya sakade a cikin hannu kujerar da yake zaune, ko su mama basu san da zaman bulalar ba irin mai baki biyu ɗinan ce, tun lokaci da Aunty Farida ta faɗa mishi irin ta'asar da na aikata ya tanadi abarsa domin saita ni a cewar sa banida saiti. Dukkan hannuwana ya damƙe da hannunshi guda yayin da ɗayan hannunshi ke riƙe da dorina ya shiga zabga min ita da ƙarfin gaske, sai ihu da Karuruwar neman agaji nake yi ina bashi haƙuri amma wallahi kamar ina zuga shi ne da na fahimce da gaske Baba illata ni zai yi sai na koma kira suna Mama da Aunty Farida su zo su ceci ni, daga ƙarshe kowanne miƙewa ya yi ya bar mana parlour sai da Baba ya gaji don kanshi ya sake ni. Kana ya daka min tsawa tare da umartata da nayi mishi shiru babu shiri na haɗiye kukana, Baba ya koma akan kujera da yake zaune tun asali ya wani tamke fuska cikin hargowa ya shiga yi min faɗa in da yake shiga ba na yake fita ba. Tsawon lokaci ya ɗauka yana min faɗa gami da jan kunne kala-kala yana cikin faɗa nasa sai ga Mama da Aunty Farida sun dawo cikin parlour nan take zuciyata ta shiga kimtsa min su ma sun tsaneni kamar yadda Babanmu ya tsaneni domin da yana ƙaunata da ba zai min duka irin wannan ba. "Tashi ki zauna da kyau ina magana ki yi wani banza zama.
Babamu ya faɗa cikin tsawa domin tun lokaci da ya gama dukana na saki cinyoyina da suka yi raɗau-raɗau da shatin bulala, da kyar na ja rigar jikina na rufe cinyoyina kana Baba ya zarce da faɗin "Duk tarbiyya da gatan da nayi miki Jeeddah ba ki gani ba sai da ki ka aikata abinda zai taɓa ƙima da darajata saboda haka ina mai tabbatar miki da cewa muddin kika yi sanadi da aure ki ya sami tangarɗa ba zan taɓa yafe miki ba Fatee da Farida ku shaida idan har ba za ta bi umarnina ta zauna Lafiya da mijinta da 'yan uwansa ba ni ba ita kuma ki sani dangane da lissafi da kika buga wa mijinki daga yau banaso ko tashe batun nan na sake ji ki yi idan kuma naji sai ranki ya yi mummunan ɓaci. Kana kuma ki sa aranki ba ki da uba domin daga wannan ranar na tashi daga muhalli na mahaifinki sai ki je can ki nemi wani uba ba dai ni ba.
  Furunci Babamu ba ƙaramin gigita duniyata ya yi ba, na ƙara saki kuka jaye da ɗuwawu na isa gabanshi na kama ƙafafuwan shi sai kawai fatali ya yi da hannuwana ya tashi ya shige ɗakin baccinsa. Mama da Aunty Farida suka ɗora nasu faɗa daga inda Baba ya tsaya domin kuwa Mama har cewa tayi daga yau kar na sake zuwa mata gida kuma na tashi na ɓace mata da gani, dube-dube na shiga yi ina neman gun da na jefar da key ɗin mota ta, sai can na ganshi ƙarƙashin kujera da Aunty Farida take zaune ashe tsabar raɗaɗi bulalar Baba yasa na cilla key ɗin. Ko kallon gefen dasu mama suke yi ban yi ba na fita a fusace, domin har ga ALLAH na ga laifinsu matuƙa ai ko za a yi min faɗa da duka ya dace aji daga bakina a tambaye ni girman laifi da Aunty Bahijja tai min da yasa nai mata irin wannan hukunci amma haka kawai sun yi min rudugu sai kace wata marar gata. Ina tuƙi ina sharar hawaye tsabagen hankalina baya tare dani shiyasa ban fahimci hanyar fita gari na biyo ba ashe duk tafiya nan da nake yi nayi faci kasantuwar natsuwa da hankalina sun kaurace min sai da wani bawan ALLAH ya ankarar dani ta hanyar dinga yi min horn da na fahimce dani yake na sauke glass "Hajiya kin yi faci!
Abinda ya faɗa min kenan cikin ɗaga murya kafin ya ƙarawa motarsa gudu ya ƙara gaba, cikin sauri na gangara gefen titi nayi parking kana na kifa kaina ga steering, bansan adadin lokaci da na share a zaune ba kafin na fara tunani mafita domin tafiya kaɗan ya rage na shiga garin Bodinga. Koda na duba agogo jikin mota naga sha ɗaya da rabi ta gota da kyar na yunƙura na fito daga cikin mota gaba ɗaya jikina ya yi min tsami tsabar duka da nasha hannu Babanmu. Tsaye nayi gami da jinginawa ga mota na shiga rarraba idanuwa akan ababen hawa da ke wucewa cikin bala'in gudu duk motar da za ta wuce da mugun speed take wucewa bana tsammani na sami taimako su. Gashi inda nake babu mutane da ke tafiya a ƙafa ballantana na roƙi arziki ko take me home ce a saka min tun da ina da ita a boot. Da na ga tsayuwa nan ba za ta fidda ni ba na shiga tsayar da duk motar da ta zo wucewa amma kamar su ma suna goyon bayan Babanmu domin kuwa ko arziki kallo ban samu daga gare su ba.
Ga rana sai ƙara zafi take har sha biyu rana ta buga ina tsaye yayin da abubuwa masu tari yawa suka taru suka yi min yawa ga ciwo jiki da Headache dake barazana tarwatsa kokon kaina, ga rashin natsuwar zuciya uwa-uba yunwa da nake yi kamar ana yashe min hanjin cikina, ga kuma zafi rana da ke kuɗata ga rashin mataimaki da zai ɗora min taya in takaice muku abubuwa goma da ashirin kuma wai duk ni kaɗai. Gaskiya Bilal Shattima ya cuce ni domin shi ne ummul-aba'isi jefa ni cikin wannan bala'in. Nayi nisa a tunani shiyasa ban lura da wata mota baƙa wulik kirar Mercedes Benz 2020 ta da ta wuce ni da gudu baya wasu 'yan mintuna kuma sai ga ta dawo ta hanyar reverse, ma mallaki motar bai tsaya a ko ina ba sai kusa dani tsayuwar motar shi ya ankarar dani nai sauri ɗago Idanuwana na yada su akan motar, a hankali ya ziro ƙafafuwanshi farare tass! Da ke cikin black sandal kafin ya yunƙura ya fiddo da gangar jikinshi yana sanye da farar shadda ɗinki babbar riga yayin da ya kafa hular tangaran da ta dace da kayan jikinsa tun kafin ya ƙaraso guna na fara shaƙar haɗaɗɗen ƙamshi turarensa, walking majestically yake dunfaro ni duk tako sa ɗaya sai gaba na ya yanke ya faɗi.
  Idan har lissafi bai ɓace masa ba kusan shekaru bakwai kenan haɗuwar shi da ita amma daidai da second ɗaya bai taɓa gushewa a gareshi ba. Ba tare da ya tuno da kyakkyawar fuskarta ba. Duk da a wasu lokuta yana haɗuwa da ita a mabanbanta wurare sai dai tun lokaci da ya gano matar aure ce yake ƙoƙarin yakiceta daga zuciyarshi amma hakan ya gagara samuwa kullum soyayyar ta ƙara kanainaye masa zuciya take yi Engineer Ameer Bello Sardauna kenan{idan mai karatu ban manta ba shi ne mutumin da ya taɓa taimakawa Jeeddah har ya kai ta asibiti a lokaci da tana laulayi cikin Aiman}.
Sa'ili da ya iso daff dani sai ya yi min sallama
   "Assalamu alaikum!
zazzaƙar muryarshi ma'abociya sanyi da kammala ta ratsa dodon kunnena, sai da na sauke zazzafan numfashi kafin na buɗe bakina da ya yi min mugun nauyi na amsa da "Wa'alaikum Salaam!
   "Sannu maijiddah! Me ya sami motar ne?"
Suna da ya kira ni dashi ba ƙaramin girgiza min ƙwaƙwalwa ya yi ba yayin da ya jefa ni a duniyar tunani. Babanmu da Ya Haidar kaɗai ke kira na da suna maijiddah su ma ɗin sai tai yi musu daɗi, ko nayi musu abin kirki.
He looks so familiar but na kasa tuna inda nasan shi amma tabbas fuskarsa tayi min kama da wanda na taɓa sani "to amma a ina?"
Tambayar na kasa lalluɓo amsarta "Subhanalillah! Ashe faci ne ki ka yi ALLAH yasa kina da spare tire na canza miki domin nan wuri babu masu faci.
Can sama-sama na tsikayi muryarshi hakan yasa na tattara hankalina zuwa gareshi cikin mutuwar jiki da dusashewar murya na ce "Eh! Ina da take me home a boot.
   "Okay buɗe boot ɗin na canza miki.
  Haka na juya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na buɗe boot sai kawai naji numfashi mutum kusa dani da sauri na juyo na sauke mishi jajjayen kumburarri idanuwana da suka sha kuka har suka gode ALLAH, shi ma kafe ni ya yi da nashi idanuwana masu girma da jan hankali mai kallonsu gyaran murya da ya yi yasa ni sauri kauda fuskata "Ina tire ɗin yake?
Ya faɗa tare da kallon cikin boot ɗin "gashi nan a cik...
Sauran kalamai na suka ƙargame a maƙoshina a dalili ba wata tire a boot ɗin jack ne kawai a ciki tamkar zan fashe da kuka na kalleshi ina cewa "Babu tire maybe maigidana ya cire ta.
Wani irin faɗaɗɗa fuskarshi ya yi da sanyayyaye murmushi har sai da sautin murmushi nasa ya fito fili Yayin na kauda fuskata daga kanshi na mayar akan titi ina kallon motoci da ke ta faman kai da komo.
   "Tun da ba ki tire ni Kuma nayi niyar taimakawa bara na ara miki tawa amma make sure kin dawo min da abata domin aro zan ba ki ba kyauta ba.
   Da sauri na dawo da ganina akanshi still da murmushi akan fuskarshi cikin sanyi murya na ce "ALLAH zan dawo maka da abarka ni dai ka taimaka min naga kaina gida.
Na ƙarashe magana kamar zan yi kuka.
  Ba tare da ya sake magana ba ya nufi motarshi ya ɗauko take me home {irin ƙaramar taya nan} sai da ya fara cire babbar rigarsa yana dube-dube inda ya dace ya ajiye rigar karaf na miƙa masa hannuna gami da faɗin "Kawo rigar na riƙe maka"
Sai da ya ƙare min kallo yana shegen murmushi nan nasa da na rasa gane na menene, kafin ya ɗora rigar akan tafin hannuna ya sunkuya ya shiga kwance tire can Kuma ya miƙo min sifana yana faɗin "Maijiddah ungo riƙe min wannan.
Gudun kada na miƙa masa hannu hagu nayi rashin ɗa'a sai kawai na rataya rigarshi a shoulder na kana na karɓi sifana ɗin.
Sai kawai naga ya sake sakin ƙayatatcen murmushi wanda yafi duk waɗanda ya yi min a baya, kana ya dukufa canza tire ɗin cikin ƙanƙani lokaci ya canza min ya miƙe tsaye tare da ɗaukar tawa wacce ya cire ya buɗe boot ɗin motata ya saka min, ya dawo inda nake tsaye rataye da babbar rigarsa a ƙafaɗa hannuwanshi naga yana kallo sun yi dirty da sauri na buɗe mota na ɗauko robar ruwa na ɓalle murfi tare da kallonshi, shi ma kallo nawa yake yi kafin ya tara hannuwanshi na zuba mishi ruwan. Bayan ya kammala wanke hannuwan nashi na miƙa mishi rigar shi ya karɓa ba tare da yasaka ba ya ci-gaba da riƙe ta a hannu "Nagode sosai ALLAH yasaka maka da gidan aljanna firdausi.
Na faɗa ina ɗan murmushi.
  "Amin thumma Amin maijiddah!
So nake na tambaye shi a ina yasani domin daga jin yanda yake ambatar sunana gaba gaɗi, tabbas ba ƙaramin sani ya yi min ba. Sai dai kunya ba za ta barni nai masa wannan tambayar sai kawai na tsinci kaina da faɗar "Idan inaso na mayar maka da tayarka a ina zamu haɗu?"
    "Duk inda ALLAH ya sake haɗa mu sai ki bani.
Ya faɗa yana murmushi.
  "Uhmm!
Na furta kafin na sake yi masa godiya na raɓa gefenshi na buɗe ƙofa na shiga, har na yiwa mota key ya kwakwasa glass na sauke tare da jefa idanuwana cikin nashi "Maijiddah ki zama mai juriya yawan kuka baya magance matsala sai ma yaƙara liƙa damuwa na barki lafiya sai ALLAH ya sake haɗa mu amma bana fatar na sake gani idanuwanki a haka.
Daga haka ya juya ya tafi har ya ja motarsa ya ƙara gaba na kasa kwakwaran motsi sai naji kamar ya ɗaure ni da igiyoyi, jikina a sanyayye na ja mota na nufi gida ina zuwa gida kaitsaye kitchen na shiga  na dafa noodless naci kana na wuce bedroom na faɗa bisa gado na lumshe idanuwana, yayin da duk motsi da nayi sai na shaƙi ƙamshi turaren shi da ya gama bin rigar jikina, duk yanda naso na tuna da inda nasan bawan ALLAH nan ƙwaƙwalwata ta ƙasa tunowa dole na haƙura.
   AFTER SOME MINUTES
Na sauko daga saman gado na cire rigar jikina na maye ta da half gown wacce ta sauka iya gwuiwayina, tunawa da nayi da furucin Babanmu akaina yasa ni shiga kitchen na girkawa Bilal lunch irin abinci da yafi so, ta ƙarfi da yaji nakeso na gyara abinda na ɓata ba don komai ba sai don tsoron hukunci Baba. Ina kammala girki na zuba a warmers na kai dining room kana na wuce bathroom nayi wanka, duk da ban yi wata kwalliyar kirki ba domin kuwa har yanzu ina jin  takaici gami da ɓaci rai cin amanata da Bilal Shattima ya yi duk da inaso na cilaswa kaina na ci-gaba da yi masa biyayyar aure amma wallahi a can ƙasan zuciyata haushinsa yana nan damƙare.
Na dawo parlour na kunna kayan kallo ina kallo Indian movie amma hankalina yana can ga mutumin da muka haɗu ɗazu na kasa bari tunaninshi. Ƙarar rufe ƙofa ya dawo dani natsuwata na juya na kalle mai shigowa Bilal ne muna haɗa idanuwa na shiga ayyanawa yanzu haka daga wurin Nusaiba yake, nan take naji wani irin mugun kishi, nai sauri kauda fuskata ko kusa ban kawowa raina zai kula ni ba sai naga saɓani tunanina domin kuwa sallama ya yi min "Assalamu alaikum!
Jin haka yasa na amsa mishi cikin dusasshiyar murya "wa'alaikum Salaam!
Daga haka na sadda kaina ƙasa na shiga wasa da zoben yatsana wanda Ya Haidar ne ya bani shi har kawo yau na kasa cire shi a dalili ƙaunar da nake yiwa zoben.
   Kusa dani ya zo ya zauna ya leƙa fuskata yana murmushi, hakan da naga ya yi yasa ni ɗagowa tare da cuno baki "What!
Na faɗa ina hararashi ya saki murmushi mai sauti kafin ya rungume ni cikin jikinshi yana faɗin "Fushi ya isa haka matata kuma uwargidana abin alfarina, farin cikin rayuwata.
   Ture shi na shiga ina faɗin "Da ba amma banda yanzu ai ni tuni na yafewa Nusaiba kai.
Matse min baki ya yi na saki ƙara "Miye haka cire min lips za ka yi saboda ko ka rasa wannan kana da na Nusaiba ko?"
"Omg! Wai ke ba ki da zance ne sai na Nusaiba?"
Ya faɗa yana kallon cikin idanuwana. Na yatsine fuska gami da faɗin "Duk duniya ita da Aunty Bahijja ne matsalata ka ga kuwa bakina ba zai gaji wajen ambato sunan ta ba.
   "To naji mu ajiye wannan zance mu yi magana ta fahimta.
"Ba wata maganar fahimta da za mu yi da kana so maganar fahimta a tsakanimu da ba za ka kai ƙara ta wajen Babanmu ba kalle jikina ka ga irin duka da ya yi min duk jikina shatin bulalarsa ne.
Na ƙarashe magana gami da ya ye rigar jikina Bilal Shattima ya kalle yanda gadon bayanta ya yi jajir raɗau-raɗau da shatin bulala sosai ta bashi tausayi har bai san sanda ya rungumo ta ya shiga bata haƙuri tare da neman afuwarta a bisa dukkan laifukan da ya yi mata ya ci-gaba da yi mata daɗi baki tsakani mata da miji sai ALLAH sai ga Jeeddah ta sauko tare ma suka ci abinci sai nishaɗi gami annushuwa suke yi. Ta shiga kitchen ta wanke plates ɗin da suka yi amfani ta ji ringing ɗin wayarsa Nusaiba ce ta kira shi da sauri ta zo jikin ƙofa ta leɓe tana saurare magana da yake yi, tana ji lokaci da ya ɓalɓale Nusaiba da masifa har yana cewa karta sake kiranshi idan yana da ra'ayi magana da ita shi zai kira ta Raina ya ƙara yi fari tass! Saboda haka ban barshi ya fita ba sai da yamma liss! kuma ana gama sallah isha ya dawo sai da muka yi shirin kwanciya bacci ya riƙo hannuwana tare da furta "Albishinki love!
Sai da na ɗan taɓe baki kafin na ce "Goro!
Turo min kumatunsa ya yi yana faɗin sai kin fara bani hot kiss kafin na faɗa miki ina dariya na sumbace kumatunsa dama da hagu.
   "Cikin hukunci Ubangiji ya nufi ni da biya mana Makkah in-sha-Allah Hajji bana da mu za a tafi.
  "Are you serious?"
Na faɗa cikin zazzare idanuwana miƙewa ya yi ya dauko min shaidar biya gudu biyu ya miƙo min na karanta nasaki ihun fari cikin da murna kana nayi tsalle na rungume shi, sai kisses nake zuba mishi a kamatunsa da gefen wuyanshi sai dariya yake min daga bisani na shiga yi mishi godiya. Ɗauka ta ya yi cak ya ɗora akan gado kana ya zauna kusa dani gami da riƙe hannuwana ya kwantar da murya yana faɗin "Babu godiya a tsakanimu love duk abinda nai miki ban biya kwatankwacin rabi sadaukarwa da ki ka yi min ba. Kuma in-sha-Allah zan biya ki adadin kuɗaɗen da kika ce kina b....
Kafin ya ƙarasa magana nai sauri rufe mishi baki da tafin hannuna domin na tuna da kyakkyawan kashedi da Babanmu ya yi min akan zance kuɗaɗen da nace ina bin shi Baba ya ce muddin na sake cewa da Bilal ina bin shi bashi kuɗi bai yafe min ba. Shiyasa ina ji ya sako zance kuɗi na rufe mishi baki cikin sanyi murya nace "Love ka manta da zance kuɗi nan dama nayi ne domin na ɓata maka rai kuma a yanzu komai ya wuce ni na ma yafe maka kuɗin.
  Zaro idanuwa ya yi kana kuma yasa dariya tare da cewa "Eh! Lallai bulalar Baba ba ƙaramin shigar ki tayi ba.
Kuka shagwaɓa nasa mishi da sauri ya rungumeni in takaice muku labari dare ranar mun raya shi cike da so da ƙaunar juna har mantawa nayi da akwai wata aba wai ita Nusaiba. Washegari tun da muka yi sallar asuba muka koma bacci muna manne da juna tamkar an ce mana wani zai raba mu. Can cikin bacci muka ji ana mana heavy knock tamkar za a ƙarya mana ƙofa, daga ni har shi a firgici muka tashi ya kalle ni na kalle shi kowanne mu yana mamaki waye ke mana wannan mugun knocking sai ka ce mu ci bashi wani, daga shi sai boxer briefs da white vest ya sauko daga gado zai fita nayi sauri hana shi ta hanyar cewa "Love dawo ka kwanta abinka bara naje na duba waye?
Da sauri ya ce "a'ah yi zamanki bara na dubo da kaina.
  "Okay!
Na faɗa tare da maƙe ƙafaɗa ya fice ni kuma na sauko na shiga bathroom nayi brush kana na cire sleeping dress na maye gurbin su da boomshort da vest.
Rai ɓace Bilal Shattima ya buɗe ƙofa sai kawai ya yi arba da Hajja tare da Aunty Bahijja a bayanta da ɗan uban bandage ɗinta a damtse hannu, kallon mamaki yake musu yayin da zuciyarshi ta cika da tarin tambayoyi me suka zo yi mishi a gida a daidai wannan lokaci kasa haƙuri ya yi har sai da ya furta a fili "Hajja lafiya ku ke tafe yanzu?"
Ya ƙarashe magana fuskarshi tana ƙara bayyanar da mamakinsa a fili.
  "Ubanka na zo yi ɗan iska yaro shanyayye banza da wofi bani hanya na wuce yau dai zan kawo ƙarshen iskanci taƙadariyyar matarka.
Ta ƙarasa magana tare da ingije shi ta shiga cikin parlour yayin da Aunty Bahijja ta biyo ta a baya da sauri Bilal ya sha gaban Aunty Bahijja ya watsa mata mugun kallo kafin cikin ɓaci rai da fusata ya ce "Aunty Bahijja me nayi miki ne a duniya da bakyaso na zauna lafiya da iyalina wai me Jeeddah ta tare miki ne?"
  "Mtsssss! Duk ubanda ta tare min yau za ka gani don kuturun wulaƙanci matarka ta yayyaka min wuƙa a matsayina na wacce mu ka fito ciki ɗaya da kai ka kasa daukar mataki wallahi Bilal cka ji kunya.
Tana ƙarasa magana ta bi ta gefenshi ta nufi gun Hajja, ina fitowa daga bedroom nayi kicibus! Da Hajja ta nufo ɗakin baccinmu sai da ƙare min kallon sama da ƙasa kafin tace "Da kyau karuwa dama da wannan shigar ta karuwai ki ka mallake min ɗa ko?
   Wasu miyau na haɗiye domin ba ƙaramin zafin kalmar karuwa ta yi min ba, sai kawai na kafe ta da idanuwana "Shegiya tsinaniya baƙar karuwa yau ƙarshen ki ya zo la'ananniya kawai.
  Aunty Bahijja ta faɗa tana wani tadda murya sosai raina ya ɓaci zan iya haƙura Hajja ta kira ni da kowacce irin kalma da taga dama domin ɗanta nake aure kuma mahaifiyar ƙawata ce amma ba zan jure Aunty Bahijja ta ci-gaba da danganta ni da mummunar kalma ba. Saboda haka na tunkare ta a fusace ina faɗin "Ina gargaɗinki Aunty Bahijja da kada ki kuskura ki koma kirana da suna karuwa?"
    "Na faɗa karuwa, karuwa, Jeeddah ke karuw....
Kafin ta ƙarasa na ɗauke ta da mari ina faɗi "Ba dai ni ba wallahi sai dai in uwarki ce karuwa.
   "Jeeddah ni ki ke kira da karuwa?"
Hajja ta faɗa tana zarar ido cikin kaɗuwa Bilal ya ƙaraso yana faɗin "Jeeddah ki natsuwa ki san abinda daga yake fitowa daga bakinki Hajja fa mahaifiyarta ce?
   "Yadda take uwa nima haka nake uwa yadda za ka ji zafi idan an kira ta da wannan kalmar nima hakazalika ɗana zai ji zafi saboda haka muddin Aunty Bahijja ba za ta daina danganta ni da wannan suna ba nima ba zan daina cewa uwarta ce karuwa.
   "Wayyo ALLAH na shiga uku na lalace kaicona ni Hajja ashe na haifi ɗa da za a kirani da karuwa a gabanshi ya kasa daukar mataki.
Hajja ta ƙarashe magana tana gunji kukan munafuci yayin da Aunty Bahijja ke tayata.
   "Dan ALLAH Hajja ki yi haƙuri Jeeddah ba da ke ta ke ba, Aunty Bahijja ce ta ba wa amsa da za ta kira ki da wannan suna da tun farko da ki ka kira ta dashi da ta rama..
Cikin daka tsawa Hajja ta ce "Rufe min baki ɗan iska yaro wanda baisan darajar uwa ba to wallahi-azim yau sai ka zaba tsakani ni da ita.
   "Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Hajja me ya kawo zance zaɓi anan ke fa mahaifiya ta ce ita kuma matata ki sani kowanne ku matsayinsa daban?"
   "Wallahi-tallahi! Na rantse da Ubangiji sammai bakwai yau sai ka saki Jeeddah ba saki ɗaya ba saki uku za ka yi mata ko na tsine maka albarka.....

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now