067

222 16 5
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

067.

Haidar yana fita ya je ya buɗe wa su Aunty Farida ƙofa kallon sama da ƙasa Khairat take masa ta wani karkace fuska tana taɓe baki aunty Farida ta ce "Haba Haidar wannan wane irin kalar bacci ne?"
Ya ɗan sosa ƙeya yana wani sunne kai yana murmushi ƙasa-ƙasa. Khairat tai karaf ta karɓe zance ta hanyar faɗin "Ai ni wallahi Aunty na zaci babu masu rai a gidanan irin wannan uban knocking da muka dinga yi har maƙota ana jin mu.
Harararta Haidar ya yi "Ta ya za mu ji ku baya bacci muke yi in fact bai kamata ku yi mana sammako a gida ba.
Shewa Khairat tayi tana tafa hannuwa Aunty Farida ta kai mishi duka a kafaɗa tana faɗin "Da kyau rasa kunya bera toka, sai ka duba agogo ka ga karfe nawa sabon shiga kawai dallah ba mu hanya mu wuce.
Dole ya janye suka shigo sai lokaci ya lura da direban Aunty Farida dake ta faman jido akwatunan lefen Jeeddah daga mota yana kawowa bakin ƙofa yana ajiye wa. Khairat ta matsa kusa dashi tai ƙasa da murya cike da shaƙiyanci ta ce "Yadai bro da alama ka zura ƙwallo a raga naga sai wani annuri fuskarka take fitar wa?"
Sai da ya juya yaga aunty Farida tayi gaba ya wani langwaɓar da kai "Uhm! Bari kawai sis abin ba a cewa komai ni kuwa wai namiji tun farko ku ka aura wa Jeeddah ko kuma mata-maza?"
Wata irin dariya Khairat ta kwashe da ita "Bro namiji ne mana Aiman kaɗai ya isa shaidan zaman sa namiji amma miyasa ka tambaya?"
Yatsine fuska ya yi tare da juyawa zuwa ciki parlor da sauri Khairat ta biyo shi "Please bro ka bani amsa mana naji daɗin shuka wa Jeeddah tsiya.
"Uhm! Khairat gaskiya nusari namiji Jeeddah ta aura bai iya komai ba sai nusarranci gaba ɗaya ya mayar da ita ragguwa...
Tun kafin ya dasa aya Khairat ta sake kwashe da dariya har dasu dafe ciki girgiza kai Haidar ya yi tare da nufar upstairs yabar Khairat tana kyalkyala dariya.
Ta ɓangare Jeeddah tana gani Haidar ka'oje ya fita ta cire yagaggiyar rigarta ta dauki towel ɗin da ya cire ta ɗaura da kyar ta ja gajiyayyu ƙafafuwan ta, ta shiga bathroom sosai ta gaggasa jikinta. Ina fitowa naga Aunty Farida tsaye a tsakiyar bedroom ɗina hannunta riƙe da rigata tana jujjuya ta gaba da baya fuskarta shimfiɗe da zallar mamaki, yayin da Khairat ta shigo tana dariya na zo da wani kalar sauri na fizge rigar daga hannu Aunty Farida da na buɗe wardrobe na jefa "Aunty Farida wannan lace ɗin fa yana ɗaya daga ciki very expensive laces da aka sakawa Jeeddah a lefe ya aka yi ya yage har haka ko tayi dambe da zaki ne?
In ji Khairat tana wani zare idanuwa gami da ƙunshe dariya.
"Ke ma dai kya faɗa Khairat amma fa ga dukkan alama khairat ƙarfaffen zaki ne don da gani da mugun ƙarfinsa ya yaga rigar nan ko Jeeddah?"
Ina ji tambayar da Aunty Farida tai min mai cike da zallar iskanci na fashe da kuka a hasale na buɗe wardrobe na ɗauko rigar na jefa musu ina faɗin "Sai ku je ki tambaye zaki ai yana parlor kun baro shi.
Na ƙarashe magana tare da ɗurkushe ƙasa ina shasshekar kuka, ban taɓa gani siblings sisters iri nawa ba sai kawai suka girke min dariya wai har da Aunty Farida da nake yiwa kallo babba mai hankali, dama ita khairat ba a maganar ta tuntuni, ta gama rena ni. Sai da suka ci dariya mai isar su kafin Aunty Farida ta miƙar dani tsaye tare da rungume ni jikinta towel ɗin jikina saura kaɗan ya sabule khairat ta ce "Aunty ku kama towel kada ayi abin kunya ni dai banaso gani Ya Haidar's property.
Wani kafirin takaici ya ciyo ni a mugun fusace na ce "kar ki sake danganta ni da wannan mugun mutumin ni wallahi nayi danasani aurenshi dama Baba Ameer ɗina ya aura min yafi min wannan baƙi mugu da babu burbushin imani a zuciyarsa.
Aunty Farida tai sauri riƙo haɓata tana kallon cikin idanuwana "kin kuwa san abinda ki ke faɗa Jeeddah?
"Na sani mana Aunty.
"A'ah! Jeeddah da kinsan waye Ameer ba za ki faɗi haka ba. Ai ke kamata ya yi ki godewa ALLAH domin kin tsallake rijiya da baya, da Ameer ki ka aura da ba mugunta kaɗai zai miki a gado ba har sheƙe ki har lahira zai yi, mutumin da ke fama da mental disorder yaushe zai san yadda ake kula da macce bai san abu mai kyau ko akasin haka ba duk abunda zuciyarsa ta raya masa shi yake yi kuma a wurinsa shine daidai. 
Ciki kaɗuwa na zaro idanuwa "Aunty wai kina nufi Ameer yana ɗauke da lalarur tabin hankali?"
"Ya ma wuce wai.
Khairat ta faɗa tana taɓe baki aunty Farida ta ce "bara na duba Musa direba idan ya gama shigowa da akwatunan, na shigo mata dasu ɗaki.
Tayi magana tare da ficewa khairat ta kalle ni tana mai ci-gaba da faɗin "A dalili girman laifi da ki ka aikata Baba ya yanke shawarar aura miki duk wanda yaga dama sa'ilin da mama ta ji wannan magana, bata yi ƙasa da guiwa ba ta kira Mommy Turai dangane da zance ki da Ya Haidar, a lokaci da Mommy ta tuntube Ya Haidar da maganar sai ya nuna mata shi gaskiya ya haƙura dake a hali yanzu ba zai iya aure ki ba, Mama bata haƙura ba ta kira Haidar ɗin da kanta, ta roƙe shi idan Baba ya kira shi akan zance aurenku dan ALLAH ya amince a bisa ƙima da darajar Mama da yake gani yasa, amsa wa Baba zai aure ki. Ana gobe ɗauren aurenku sai Baba ya kira Ameer saboda kusan kullum sai ya je kasuwa ya sami Baba akan ya bashi aurenki, da Baba yaga naci nasa ya yi yawa shi ne ya ce dashi idan har Ya Haidar ya haƙura dake to zai bashi aurenki sai gashi Ya Haidar bai haƙura ɗin ba. Shi ne Baba ya kira shi ya bashi haƙuri tare da faɗi masa gobe za a ɗaura miki aure. Koda Ameer ya isa gida ciwon sa ya tashi a washegari ana shiri ɗaura miki aure kwatsam! sai  gashi ya zo in takaici miki labari haka ya hargitsa taro 'yan ɗauri aure, wai shi ala dole sai Baba ya bashi aurenki ya dinga baza hauka sai da Ya Kabeer ya kira masa jami'an tsaro da kyar suka iya tafiya dashi. A lokaci da mahaifiyar sa ta sami labari abunda ya faru dashi ta garzaya police station ba a bata belin shi sai da aka kira Ya Kabeer inda ta nuna masa certificate ɗin sa ta rashin lafiya da yake fama da ita saboda Ya Kabeer kotu ya so a tura su, saboda ya dinga karari cewa koda an yi nasarar aura miki wani ba zai taɓa rabuwa dake. Lokaci da mahaifiyar Ameer ta ba wa Ya kabeer labari kamanu da ki ke yi da matarsa Maijiddah da ta rasu shi ganinki yake yi tamkar ita. To kin ji yadda aka yi aure tsakanin ki da Ya Haidar ya kasance. Na taɓe baki "Duk da haka wallahi gara Ameer da Ya Haidar domin shi Ameer za a iya masa uzuri tun da yana ɗauke da lalura shi fa Ya Haidar ɗinan da ki ke gani wallahi bala'in mugu ne, ni kaɗai nasan kaloli azaba da ya dinga gana min.
"Watakila kin hana shi abunda yake halak ɗinsa ba dole ya kwata da ƙarfin damtse sa ba. Da ba ki yi masa taurin kai ba na tabbata zai bi dake in a romantic and gentle way saboda haka ke ki ka janyo yai miki mugunta.
A fusace na maka mata harara gami da faɗin "Wai ke Khairat miyasa a koda yaushe ki ke depending Ya Haidar?
"Saboda ya fi ki gaskiya.
"Mtss! Na buga tsaki magana da ita ma ƙara min ɓaci rai take yi sai kawai na nufi gaban dressing mirror na ja stool na zauna.
  "Ai gara da ya yi miki haka shekara nawa yana fama da danko sonki, kin zama mallakin sa halak-malak sai ya zuba miki ido sai kace wani waliyi, ni wallahi ina goyon bayansa ko gobe ki ka hana shi ta daɗin rai ya karɓa ta ƙarfin tsiya.
Na tsikayi muryar Khairat tana faɗa da sauri na waiga na kalle ta, tsabar haushinta da ya ke ci na ya hana ni tanka mata, sai kawai na ci-gaba da abunda nake yi. Aunty Farida ce ta shigo janye da akwati biyu a hannunta hagu da dama ta ajiye ta sake ficewa, Khairat ta tashi ta bi ta a baya. Khairat tana fita sai ga Ya Haidar ya shigo ya canza kaya ciki kaɗuwa nake kallonsa duk da kallon tsoro nake masa, amma sai naga wannan shadda da ya saka tafi ta farko yi masa kyau, yana karya hular sa yake min magana "Ke ga abinci can akan dining Mommy ta ce akawo miki dama shi ne na dawo na kawo miki, sai kuma ƙaddara ta faɗa min ki ka haiƙe min, ni zan wuce Kebbi wajen matata ayi min addu'a.
Murya can ƙasa na furta "ALLAH ya tsare.
Ya amsa ko bai amsa ba, ban sanar mishi ba naga dai ya juya gami da ficewa sai baza ƙamshi fitinanne turarensa yake yi wani irin kishi naji ya kamani.
A main parlor ya tadda su Aunty Farida suna ƙarasa shigowa da raguwar akwatuna da waɗansu kayayyakin Jeeddah da suka ɗebo mata "Aunty Farida ni zan wuce Kebbi ki kula min da matata.
Murmushi mai sauti Aunty Farida tayi tare da faɗin "Sai dai ka faɗawa Khairat don ni wucewa zan yi yanzu dama lefen ta na kawo mata.
  Ya juya wurin khairat yana murmushi "sis ai ta hannu dama ce ba ma sai na faɗa mata ba nasan za ta kula min da ita.
    "Har ka je ka dawo ina rirrita maka ita tamkar kwai a cokali.
Khairat tayi magana tana dariya shima darawa ya yi daga bisani yai musu sallama ya fi ce.
Sai da Ya Haidar yai min zance abinci na tuna da ko breakfast ban yi ba wata irin yunwa ta taso min da gaggawa na ƙarasa shirya wa na baro Aunty Farida da Khairat a bedroom ɗina suna min arranging kayana a wardrobe, na wuce dining room na ja kujera na zauna, jikina har rawa yake yi na zuba abinda raina ke so na cika cikina sai lokaci na fara ji kuzarina  yana dawowa jikina.
************
Da Ameer ya fito daga wanka bai sake tadda zance Jiddah ba hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Umma. Cike da farin ciki ta zuba mishi abinci yaci ta ɗauka maganganu shi ta bashi ya sha, yadda taga yana gudanar da al'amurra shi a natse ta fahimci ciwo nashi ya kwanta. Sai lokaci ta ji natsuwar da ta rasa tana dawo mata a hankali. Zuwan Balkisu gidan ya ƙara haifar wa da umma da farin ciki gani Ameer ya sake yana hira da 'yar uwarsa tamkar ba shi bane jiya aka sha artabo dashi. Anan parlor Umma ta barsu ta wuce ɗaki ta kwanta saboda tun jiya bata runtsa ba. Umma ta lumshe idanuwanta a maimakon tai bacci sai kawai ta nitse a kogin tunani rayuwar Ameer ta baya.
Alhaji Bello Sardauna haifaffen garin sokoto ne a ƙaramar hukumar kebbeh shahararren ɗan kasuwa babbar sana'ar sa siyar da gwala-gwalai da canji da waɗansu kanana sana'o'in. Alhaji Bello Sardauna yana da matan aure uku Hajiya Sadiya ita ce uwargida sai dai ALLAH bai bata haihuwa ba tsawon shekaru goma da aurensa a dalili haka ya aura Hafsah mahaifiyar Ameer suna zaman lafiya ita da Hajiya Sadiya kansu a haɗe yake. Akwai kyakkyawar fahimta a tsakanin su, cikin hukunci Ubangiji da iyawarsa Hafsah bata wuce shekara ɗaya a gidansa ba, ta haifi ɗa namiji ko arba'in bata yi ba ALLAH ya karɓe yaro sai ya zamana tana haihuwa amma yaran suna rasuwa. Ahaji Bello ya kai maƙura da kwaɗaituwar  so samun magaji gashi kuma kullum shekaru sa daɗa karuwa suke yi girma na ƙara kusanto shi. Sai ya yanke shawarar sake ƙaro aure a wannan karo bazawara ya auro mai suna Hadiza ita ma ba laifi suna zaman lafiya da ita. Shekara bata zagayo ba sai da Hadiza ta haifawa Alhaji Bello tagwaye dukka mata a lokaci ita ma Hafsah tana ɗauke da cikinta na biyar mai kimanin watanni shidda, wannan ciki ba ƙaramin kwallafa ranta akanshi tayi ba kullum addu'ar ALLAH ya sauke ta Lafiya, take. Ta sami rayyaye cikinta yana cika wata tara ta haifi kyakkyawar 'yarta mai kama da ita taci sunan Balkisu, daga lokaci haihuwa ta buɗe wa Hadiza sau biyu tana haifar tagwaye sai dai dukka 'ya'ya mata ALLAH ya bata sai ga Alhaji Bello da 'ya'ya shidda biyar daga wajen Hadiza ɗaya kuma wurin Hafsah sai da Balkisu ta shekara goma cif a duniya sannan Hafsah ta sami ciki Ameer. Lokaci da ta haifi Ameer ba ƙaramin farin cikin Alhaji Bello ya yi domin shi irin mutanan ne masu masifar son 'ya'ya maza, ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗaura wa Ameer. matsananciyar soyayya yake nuna masa wacce har ta kai ta kawo yana nuna bambanci a tsakaninsa da sauran 'yan uwansa. Tun abin baya damun Hadiza har ya zo ya fara dama ita Hajiya Sadiya baiwar ALLAH ce ba ruwanta macce mai riƙo da addini gata da kawaici. Tun Hadiza tana ɓoye damuwarta akan nuna bambanci da Alhaji Bello ke yi a tsakanin 'ya'yansu har ta fara bayyana ɓacin ranta. Ita kanta Hafsah ta sha nuna wa Alhaji Bello kuskure ne abunda yake yi amma sai ya yi biris da ita. Duk inda yasa ƙafa Ameer yana tare dashi lokaci da ya isa shiga makarantar boko sai da ya dubi makarantar da tafi kowacce tsada a wancan lokaci ya saka Ameer. Wasa-wasa Hadiza ta fara nuna wa Ameer tsana har ta kai kiyayya da take masa ta bayyana a fili. Duk wani zaman lafiya da suke yi ita da Hafsah ya kau. Yayin da Hajiya Sadiya kullum ciki yi musu sulhu take. Ameer yana jss 2 a lokacin shekarun sa 13 a duniya wata rana tafiya ta kama Alhaji Bello zuwa kebbeh an kira shi kawunsa bashi da lafiya sosai kuma shi kaɗai ya rage masa. Har ya shiga mota sai ga Ameer ya fito da gudu daga ciki gida. Ya ce zai bishi ba yadda Alhaji Bello bai yi dashi ba akan ya yi zaman shi amma Ameer ya kafe, dole Alhaji Bello ya tafi dashi kafin ya fita daga gida ya gayawa maigadi ya faɗa wa Hafsah Ameer yana tare dashi kada ta nemi shi bata ganshi ba hankalinta ya tashi. Kafin Alhaji Bello ya kai kebbeh ya yi ƙazamin hatsari sakamakon saniya da ta gitta mishi, koda aka isa dashi asibitin Uduth rai ya yi halinsa shi kuma Ameer yana unconscious. Shi Kuma Ameer likitoci suka dukufa  ceto rayuwarsa ya sami kariya biyu ƙafa da hannu sai kuma ƙanana raunuka. Har Alhaji Bello ya yi wata ɗaya da rasuwa Ameer yana jinya. Bayan yaji sauki aka sallame shi suka dawo gida ba tare da ɓata lokaci ba aka raba gado kowacce macce ta kama gabanta. Sannu-sannu wasu halaye Ameer suka fara canzawa daga mai sanyi hali zuwa mai zafin rai. Kusan ko yaushe a school sai ya yi dambe da classmates ɗin shi ta hanyar raunata abokin faɗa nasa ko dai ya bugawa yaro dutse ko ya karya masa hannu. Sannu a hankali Umma ta fara observing kamar Ameer yana da taɓin hankali, kuma abin kamar yana motsa mishi ne lokacin-lokaci kafin ya fara iri-irin waɗannan misbehaving sai ya yi fama da head na tsawo two to three days a duk ranar da hankalin nasa zai gushe sai ya yi noise bleeding daga nan sai ya fara wasu abubuwa na mugunta. Idan bai samu wanda ya raunata ba sai ya rauna ta kanshi. Lokaci da Umma ta fahimci wannan lalurar tattara da Ameer tayi kuka sosai kafin ta yanke shawarar kashi asibiti. Bayan anyi hoton ƙwaƙwalwarsa sai likitan ya fahimci cewa a lokaci da suka yi accident Ameer ya sami internal injury a ƙwaƙwalwarsa. Dole sai an yi masa surgery idan kuma ba haka ba abin zai yi ta ƙaruwa sai dai bai ɓoye Umma ba ya gayamata gaskiya  surgery ɗin yana da matuƙar hatsari gaske ta kan yiwa ya yi surviving ko kuma ya ransa ranshi. Umma tana ji haka taƙi amincewa tun da ciwo lokaci zuwa lokaci yake motsa mishi sai aka ɗora shi akan medications. A haka Ameer ya ci-gaba da rayuwa har ya yi degree sa a fanni engineering. Ya buɗe kamfanin sa na building materials and contractions. Wata rana ƙanwar Umma dake aure a Zamfara ta kawo wa Umma ziyara tare da 'yarta, ta uku mai suna maijiddah tun da Ameer ya ɗaura idanuwanshi akanta ALLAH ya ɗora mishi wata irin matsananciyar ƙaunarta sai aka yi dace ita ma Maijiddah tana sonsa. Wasa-wasa soyayyar su tai ƙarfi Umma bata ɓoye wa iyayen Maijiddah lalurar da Ameer yake ɗauke da ita ba. Hakan bai canza soyayyar da Maijiddah take masa ba. hakazalika iyayenta basu fasa bashi aurenta ba. Bayan aurensu wata irin kulawa haɗe da zazzafar soyayya Ameer yake nuna wa maijiddah yana sonta tamkar numfashin sa. Da ta fahimci ciwonsa yana so tashi sai ta kira abokinsa Dr Abdallah ya zo ya yi masa allurai a haka suka ci-gaba da gudanar da rayuwarsu ciki so da tattalin juna har maijiddah ta zo ta sami ciki kulawar da Ameer yake mata ta daɗa ƙaruwa cikinta yana da watanni takwas wata rana, ciwon Ameer ya motsa farat ɗaya cikin dare ba tare da Maijiddah taga waɗannan alamomin ba. Can ciki bacci Maijiddah taji ƙarar fashewa gilashi a parlornsu a gigice ta falka, hankalinta yai mugun tashi da ta duba gefenta taga Ameer baya nan da sauri ta diro daga kan gado, ta nufi parlor gabanta sai faɗuwa yake yi tashin hankalinta ya ƙaruwa sa'ilin da ta hango Ameer jina-jina gaba ɗaya ya yiwa kansa rauni abin ba kyau gani a rikice tayi kansa ta rirriƙe shi. Abinka da wanda baya ciki hayyacinsa yai bala'in ture ta daga jikinsa sai abin ya zo da tsautsayi gami da ƙaran kwana ta faɗa kan cikin jikinta, kafin kace kwabo jini ya ɓalle mata. Baya ciki hayyacinsa balle ya fahimci aika-aikar da ya yi gashi ita kuma ba za ta iya tashi ba balle ta nemi taimakon wani, sai da asuba da maigadin su ya ji ƙarar fashewa abubuwa daga ciki gidan da yake yasan Ameer yana da lalura da gudu ya nufi backyard door ya shiga parlor zuwa lokaci jini jikin Maijiddah ya gama tsiyayawa yayin da Ameer yana kitchen sai farfasa kayan kitchen yake yi. Ciki ruɗewa maigadi ya kira Umma tun kafin ta zo ta kira Dr Abdallah kusan a tare suka ƙara so da taimakon maigadi Abdallahi ya samu ya yiwa Ameer allurai nan take bacci ya dauke shi. Tun sanda Umma tai arba da Maijiddah kwace male-male cikin jini zuciyata ta tsinke ta fashe da kuka. Ita da Abdallah suka kaita asibiti babu alamun numfashi a jikinta. Abdallah ya fahimci tun a gida maijiddah ta rasu yana jin tsoron ya faɗawa Umma bai san yadda za ta dauki al'amari ba. Da yake yasan tana da hawan jini. Ai kuwa bai tsira ba domin kuwa likitan da ya duba ta yana faɗawa musu rasuwarta Umma ta yanke jiki ta faɗi. Da kyar aka samu ta farfaɗo aka yiwa Maijiddah sutura kamar yadda addini musulunci ya tanadar. Duk wannan abu da ke faruwa Ameer bai sani ba sai a washegari. Dole ciwonsa ya sake dawowa sabon fil bai taɓa zuba hauka kwatankwacin wacce ya zuba a ranar wanda har sai da aka kaishi asibiti irin ta masu lalurar sa. Sai da ya share watanni uku a asibiti kafin hankalinsa ya dawo. Daga lokaci Ameer ya ƙara shiga depression. Mutuwar Maijiddah ba ƙaramin taɓa shi tayi ba a dalili ya saka ta a ranshi a duk sanda ciwonsa ya motsa sai ta dinga yi masa gizo da taimakon addu'a i da Umma ta dinga sa wa ana masa ta samu ya manta da Maijiddah. Kwatsam! Sai gashi ya haɗu da Jeeddah wacce tai mugun kama da matarsa Maijiddah. Wata kalar ajiyar zuciya umma ta sauke tare da goge guntaye hawaye da suka saukar mata a gefen idanuwanta.
***********
"Ina shawartaki Jeeddah a matsayina na yayarki tun wuri ki sauke wannan zafin kan naki, ki rungume mijin ki idan kuma ki ka tsaya wasa kina ji kina gani Zarah za ta yi miki fitikau. Sai dai ki zama 'yar kallo.
  "Atoh faɗa mata dai Aunty Farida ta yiwa kanta karatu ta natsu domin samun maza irin su Ya Haidar yana da matuƙar wahala.
Khairat ta faɗa tana min wani kallo.
Aunty Farida ta cigaba da faɗin "Sai kuma abu na gama ki yi kokari ki koyi yadda za ki dinga sarrafa wannan mugun kishi naki, domin yanzu kai ya waye an daina kishi hauka kowacce macce kokari take, ta kafa babbar masaurata a zuciyar mijinta don haka ki koyi yadda ake taraiyar miji ake nuna masa soyayya domin yanzu ki ka yi aure ba ki da matsalar dangin miji ga kuma mijinki yana matuƙar ƙaunarki.  Kada ki bari reni ya shiga tsakaninki da Zarah ki Kama girman ki, ku zauna lafiya kin ga apartment ɗin ta daban naki da daban. Jeeddah ki kama kanki Don ALLAH. Bani da matsala dake dangane da tsafta da girki nasa ni kowanne ke gwana ce babbar matsalar ki, kawai zafin kishi, shima idan ki ka dinga addu'a kina roƙo ALLAH sai ki ga ya sassauta miki shi. Jeeddah namiji da ki ke gani ba abinda yake so irin yaga ana rirrita shi kamar wani ƙaramin yaro nan take za ki ga kin mallaki abinki kawai dai ki laƙanci likes and dislikes ɗin sh. 'yar kissa nan da 'yar shagwaɓa nan ki riƙe su da kyau. Suna ƙara ƙaimi wuri rikita ɗan namiji musamman a shimfiɗa.
T

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now