030

90 8 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

030...

Lokaci da za a tafi gidan amarya jere Jeeddah bata so zuwa ba. Amma Aunty Bahijja ta kira ta dole ta wanke hannunta tare da ɗauko mayafinta ta bi su, Aunty Bahijja tayi haka ne domin ƙara tulawa Jeeddah haushi da takaici ta nuna mata su kaɗai Bilal yake iya hidintawa ai kuwa ta yi nasarar hakan domin har suka baro gidan amarya Jeeddah bata cikin walwala, ga ɗan uban mamakin Bilal da ya lulluɓeta sai dare ta koma gida a gajiye liƙiss! Kasancewar ta kwaso gajiya yasa tana shiga gida wanka shi ne abu na farko da ta fara yi kana ta shiga kitchen ta girka farar spaghetti pasta tana da stew a fridge ta ɗumama a microwave, a gurguje ta haɗa salad ta zubawa kanta a plate anan kitchen ta tsaya ta cika cikinta. Ta dawo parlour ta zauna hannunta riƙe da glass cup mai ɗauke da pineapple juice tana sipping on, har zuwa lokaci mamakin Bilal sai daɗa ƙaruwa yake a zuciyata. Ta ɗauki lokaci mai tsawo a zaune tana tufka da warwara yayin da zuciyarta ta kaso kashi biyu a ɓangare ɗaya tana ji da ya dawo tai masa titse ta ji ina ya sami kuɗi da ya yi wannan uwar hidimar a wani sashe na zuciyarta yake kwaɓar ta da ta zuba mishi ido duk zaman da tayi ta kasa tantance wanne daga ciki za ta ɗauka. Bata ankara ba ta ji sallamar shi ta amsa mishi ba tare da ta bari ya fahimci halin da take ciki ba. Kasancewar shi ma a tsorace yake da ita domin har ya wuce ta ya shiga bedroom da addu'a ɗauke da bakinsa yana gudun tai mishi tambaya dangane da inda ya sami kuɗi domin har ya shigo gida bai tanadi amsar da zai bata ba. Shiyasa yana shigowa yai sauri shigewa bedroom ya yi wanka ya saka kayan baccinsa, kasa komawa parlour ya yi ya nemi gado ya kwanta har da su lulluɓewa da bargo gudun kar ta shigo ta sami damar yi masa magana.
Shiru-shiru ina jira Bilal ya dawo parlour domin na zazzage masa abinda ke cina a zuciya duk naso na rinjaye zuciyar tawa na haɗiye mamakina. Amma fitinaniyyar zuciyata ta kasa aminta da hakan. Gani shiru nashi ya yi yawa yasa na dire cup ɗin hannuna akan centre table, koda na shiga ɗaki ya kashe wuta saboda haka na lalluɓo switch na kunna bulb haske ya gauraye ko'ina na cikin ɗakin. Jin motsin shigowar ta yasa shi sauri lumshe idanuwanshi tamkar mai bacci al'hali ido shi biyu na ja numfashi na sauke kana na zauna kusa da cikinsa "Love nasan ba ka yi bacci ba ka tashi za mu yi magana.
Na yi tunani zai ci-gaba da pretending ne sai naga ya tashi zaune yana ya motsa fuska gami da wuƙi-wuƙi da idanu ya wani dafe forehead ɗinshi alamar da ke nuni headache ke damunshi, hakan bai sa na fasa antaya mishi tambaya dake raina ba "Love naga hidimar da ka yi wa A'isha ka burge ni matuƙa gayya ALLAH yasaka ma da alkhairi kana fa ƙoƙari akan 'yan uwanka.
Na ƙarashe magana ta da gatse ina mai ƙara aika mishi kallo mai cike da gundarin tuhuma.
  Tun zamana kusa dashi sai lokaci ya ya ɗago idanuwanshi ya kalle ni da guntun murmushinsa da bai wuce fatar bakinsa ba,  ya ce "Amin!
Duk da na fahimci ba son maganar yake yi da ni ba hakan kuma ba shi zai sa na tsuke bakina ba, sai ma ƙara zakuɗa ɗuwawuna nayi suka zauna daram! Fuskar nan tawa babu annuri ko kaɗan na ce "Love ina ka sami maƙudan kuɗaɗen da ka yi wa wannan uwar hidima dasu?"
Shiru ya biyo bayan tambayata domin shi bai tanka ba ni kuma ban ƙara furta uffan ba. Kawai dai na tsare shi da idanuwa ina jiran amsar da zai bani. Wani dogon numfashi ya ja tare da saukewa kafin ya yi ƙasa da murya ya ce "Gun Abbas na karɓo bashi....
  "Bashi fa kace Bilal to ka biya shi da me? Love kada son zuciya yasa ka jefa kanka a rikici kai da ba kada takamaiman sana'a shine za ka karɓi bashi maƙudan kuɗi irin wannan.
   Kafin ya yi magana sai da ya fara riƙo hannuwana ya matse cikin nashi ya ƙara lanƙwasa murya kamar wani munafuki ko mayaudari na ma kasa tantance farat ɗaya a mizanin da zan ɗora shi, can na tsikayi muryarshi yana faɗin "yarjejeniya mu ka yi sai na sami aiki zan dinga biyan shi da kaɗan-kaɗan har ALLAH yasa na biya duka. Kin ga ba zai yu ba saboda gado da kujeru a kuma fasa auren A'isha ga kuma furuncin da iyayen Al'ameen suka yi kuma ni ba ni da mafita da ta wuce na karɓi bashi daga wurin Abbas.
"Uhmm.... ALLAH ya ba ka ikon samun aiki ya kuma ba ka ikon biyan wannan uban bashi da hannunka, amma inaso ka sani Bilal ko ɓatatciyar dabara ma dabara ce ALLAH ya tashe mu Lafiya.
  Ban jira jin abinda zai sake faɗa ba na miƙe tare da shigewa bathroom, ya bita da kallo yayin da zuciyarsa ke ci-gaba da luguden aradu tabbas ya tsallake yau bai kuma san me gobe za ta haifar ba domin bai faɗa mata takamaimiyar gaskiya ba, ƙarya ce ya lafta mata domin kare kanshi, fargabar sa ɗaya idan ta gano gaskiya akwai ƙura ba kaɗan ba.
Ta fito daga bathroom ta sauya kayan jikinta zuwa na bacci ta raba kusa dashi ta kwanta, kasancewar akwai gajiya a jikinta shiyasa nan take tai bacci.
Washegari aka ɗaura auren A'isha da angonta Al-ameen sai fatan ALLAH ya basu zaman lafiya. A kwana a tashi asarar mai rai cikin hukunci Ubangiji Jeeddah ta kammala first semester examination, su ka sami hutun three weeks shiyasa yau tun da sassafe ta tashi da kwalemar ɗaki ta jawo wannan ta fiddo wannan yawan kwaranniyar da take yi ya hanawa gogan naku baccinsa na asara, ya tashi zaune ransa a ɓace a tunani sa ta ƙirƙiro aiki nan ne domin ta hana shi bacci, shiyasa ya sauko daga kan gado a fusace ya shiga bathroom ya yi wanka, ko breakfast bai yi ba ya bar mata gida yayin da ta bishi da murmushin mugunta.
Kai tsaye gidan Hajja ya nufa bayan sun gaisa ta kawo masa koko da ƙosai ya cika cikinsa, suna cikin fira sai ga ƙaramar 'yar Aunty Bahijja wacce tun bayan auren A'isha Aunty Bahijja ta tadawo da ita hannun Hajja domin ta dinga yi mata 'yan aikace-aikace, hannunta ɗauke da 'yar ƙaramar tukunyar laka mai murfi tana faɗin "Hajja duba ki gani yanzu nan da na zubar da ruwan wanke-wanke a bayan ɗakin Hajiya Bintu sai naga hayaƙi yana fita daga cikin ƙasa kuma fa ba wuta aka kunna ba shi ne na haƙo gun ashe wannan 'yar tukunyar ce take fidda hayaƙi, na shiga ɗakinta nayi ta sallama na nuna mata watakila ko nata ne amma ban ji ta amsa min ba shi ne na kawo miki ki ajiye.
   Daga Hajja har Bilal mutuwar zaune suka yi domin har zuwa lokaci tukunyar tana fidda baƙin hayaƙi ga mufeeda riƙe da ita hankalinta kwance {kuruci dangin hauka}
Da kyar Hajja tai ƙarfi hali furta "mi nake shirin gani haka mufeeda mi ya kai ki ɗauko mana wannan masifar da sanyi safiya?
  "Hajja ba masifa bace kalli ki gani tukunyar hayaƙi ce....
  "Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Bilal ya faɗa a mugun tsorace ya taso yana sanɗa jikinshi sai kakkarwa yake yi dama gogan naku akwai shi da mugun tsoro kamar farar kura, ya leƙa murfi tukunyar gun da hayaƙi yake fita ya zaro idanuwa kana ya ja da baya yana faɗin "kam bala'in! Hajja wallahi hayaƙi nan daga 'yar ƙaramar tukunyar nan yake fitowa abin mamaki menene ke fidda wannan baƙin hayaƙi?"
Sai lokaci Hajja ta sami damar tasowa gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi bakinta ɗauke da kalmar shahada "La'illaha inlallahu Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam! Kai jama'a yau mi nake shiri gani haka?" Mufeeda wannan ai tukunyar tsafi ce wallahi wani aka yi wa asiri kika haƙo Mufeeda.
Bilal Shattima yana ji Hajja ta ambaci kalmar asiri ya daka wani uban tsalle sai bakin ƙofar fita, yana faɗin "Amma Mufeeda ke ɗin ba ƙaramar 'yar banza yarinya bace muna zaune qalau za ki ɗauko mana masifa, don ubanki yau ɗinan sai kin koma gidan ubanki ba za ki kashe mana uwa a banza ba.
  "Kai ya isa haka banaso shashasha matsoraci wofi Mufeeda da kake zagi ta ma fika jarumta maloho kawai.
A bakin ƙofa Bilal Shattima ya ja tunga yana gunguni ƙasa-ƙasa "Haba! Hajja haka kawai saboda ganganci ina kallon maciji da rana ƙiri-ƙiri kuma na barshi ya sare ni, wannan kasadar ba da ni ba wallahi.
  "To na ji zo ka karɓi tukunyar hannun Mufeeda ka buɗe mu ga menene a ciki.
  Saboda tsanani kaɗuwa Bilal bai san sanda ya zaro idanuwa tamkar kwayar idonsa za ta faɗo ƙasa "Na buɗe fa kika ce Hajja?"
"En mana ko ba za ka iya bane?
"Gaskiya ba zan iya ba amma bara na fita ƙofar gida ya na nemo maza, su shigo su taimaka mana..
"Kai arrr! Matsoraci wofi kai ba namiji bane?
Kafin yai magana Hajja ta furta "Bismillah! Gami da karɓar tukunyar daga hannun Mufeeda ta ajiye a tsakar ɗaki kana ta karanta Ayatul-kursiyyu ta tofawa tukunyar, murfi ya yi tsalle ya faɗo ƙasa yayin da wani siriri baƙi hayaƙi ya fito ya bi ta window ya fita, jikinta Hajja ya ɗauki rawa ita kanta a yanzu a tsorata gogan naku tuni ya kai ƙofar shiga bedroom ɗin Hajja ya laɓe ciki labulle a hankali Hajja ta leƙa cikin tukunyar ta hango layoyi birjik a ciki da wani busasshe kadangare an bi jikinshi an sossoke da dogaye allurai, ga kuma wata ƙaramar laya cikin bakinshi. Ta maza Hajja tayi ta miƙa hannunta ta shiga fiddo da tarkace yayin da bakinta bai gushe da karanto Ayatul-kursiyyu ba. Ɗaya daga cikin layoyin ta ɗauka ta warware ta taga wata farar takarda mai ɗauke da zane uwa da ɗa a tsakiyar su an yi musu jan rubutu da rubutun ajami ta juya ta kira Bilal "zo ka gani Bilal da ajami aka yi rubutu nan ko za ka iya karantawa.
*** ** ****
Sosai Jeeddah ta gyara gidanta ya yi tsaf ko ina ya ɗauki ƙamshi, kana ta dawo kan closet ɗinta ta shiga fiddo kayanta tana sake arranging ɗinsu. Haka kawai na ji ina sha'awar ɗauko jewelry box ɗina na goge 'yar ƙura da tayi ina kammala gogewa har nayi niyar na maidata sai kuma na fasa na nemi gefen gado na zauna tun kafin na buɗe ta naji gabana yai mugun faɗuwa sai da na dafe saitin zuciyata, nan take jikina ya bani akwai matsala cikin sauri na ƙarasa buɗewa saura kiriss! Numfashina ya fita daga gagar jikina a dalili box ɗin gold necklace ɗina da ban gani ba. Jikina yana rawa na tashi tsaye na zazzage duka sarƙoƙina akan gado, abin mamaki babu box ɗin amma kuma ga extra earring da zobe da nake da su a ciki su ma na gold ne lokaci da Mama ta je Umrah ta siya mana su a matsayin tsaraba sai dai su ƙirar Sa'udiyya ne saɓani necklace ɗin da take ƙirar Dubai duka necklace ɗin bata wuce nine months da siya ba. Baba ne ya ba mu kyautar dubu ɗari biyar-biyar ni da su Khairat da Aunty Farida dama yana mana haka duk ƙarshe shekara yake raba mana kuɗi kafin mu yi aure sai Mama ta siya mana kitchen utensils. A wannan karo da ya ba mu sai Mama ta ce nawa Ya Kabeer ya karɓi ƙaramar necklace ɗina ya saida ya haɗa da nawa kuɗi ya siya min babba na ajiye a matsayin kaddara domin a cewar tasan ƙarshenta Bilal zan ba wa kuɗin ya cinye, a lokaci har gida Ya Kabeer ya zo ya ɗauke ni muka tafi shagon sayar da gwala-gwalai, na zaɓi wacce nake so ƙudinta ya kama 1.1 tsohuwa ta aka saye ta akan dubu ɗari huɗu da naga ƙudina bai kai kuɗin necklace ɗin ba har nace a kawo min wata dai-dai kudina Ya Kabeer ya ce na ɗauka kawai zai cika min raguwar dubu ɗari biyu. Sau ɗaya na taɓa sakata domin ni mace ce da bata cika saka necklace ba. Abu kamar wasa aka ce ƙaramar magana ta zama babban domin kuwa kaura wambai na dubu banga necklace ɗin ba. Ta ci tudu taci rafi kuma hatta da receipt duka an ɗauke domin ita ma a cikin jewelry box ɗin na ajiye kuma ban ganta ba. Yayin da na dawo tamkar mahaukaciya sabon kamu ɗaki da na ɓata lokaci ina gyarawa, gaba ɗaya na hargitsa shi a tunanina ko na sauya mata mazauni ne da na fahimci da gaske an sace min sarƙana sai kawai na ɗora hannu aka na kwatsama ihu, nayi faɗuwar 'yar bori ina gunji kuka...

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now