077

204 13 1
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

077.

Tsabar takaici Zarah Malik da ya kamani ina na runtse idanuwana ban sake marmarin buɗe su ba. Ina ji ta sai surutu take zubawa Ya Haidar har da su cewa "Sweetie ka tambaye ta idan za ta ci ɗan wanke nai mata akwai yaji mai daɗi da mommy ta aiko min dashi.
Har ga ALLAH Zarah Malik har cikin zuciyata tayi wannan magana ita fa mugun tausayin Jeeddah take ji.
A hankali Ya Haidar ya shafe hargitsatsiyar sumar kan Jeeddah wacce rabonta da gyara har ta manta ALLAH na tuba yaushe take da lokaci gyaran suma. Duk wani abu mai ƙamshi bata maharban dashi. "Honeypie za ki ce ɗan wanke sweetie tai yi miki?"
A mugun hasale na buɗe idanuwa sai da na tofar yawun bakina kafin na ce "Don ALLAH Ya Haidar ku kyaleni naji da abinda ke damuna. Ni wallahi da za ka taimake ni da ka ja matarka ku fice min daga falo har ga ALLAH surutun ku ya fara isata. Har can tsakiyar ƙwaƙwalwata nake jinsa.
A maimakon naga Zarah Malik ta ji haushin maganata sai kawai naga tayi murmushi tare da miƙe wa tsaye tana faɗin "ki yi haƙuri Jeeddah har cikin zuciyata nake ji tausayinki.
Uwar harara na maka mata na sake lumsashe idanuwana. Ina ji Ya Haidar yana bata haƙuri "Yi haƙuri sweetie kada ki koma ɗaya da ita tun da fara wannan laulayi take ta wannan ci rai kowa haushinsa take ji.
"Karka damu sweetie duk wanda ke cikin hali da take dole ai masa uzuri ALLAH ya raba lafiya ya kawo mana mai albarka.
"Amin sweetie.
"Zan je na kwanta sweetie idan taji tana sha'awar ci wani abu ka kira ni nayi mata
"Okay sweetie thank you.
"Mention not. Yiwa kaina ne.
Cewar Zarah Malik fuskarta cike da murmushi.
Ya Haidar ya bin bayan ta da kallo har ta ƙarasa fita kana ya dawo da ganinsa kan fuskata ya shiga yi min korafi "Haba Honeypie miyasa ki ke yi haka ne? Zarah tana iya kokarinta akanki amma ke koda yaushe ciki gwasale ta ki ke.
"Mtss! Na ja guntun tsaki tare da faɗin "Ni fa banaso munafuci duk wannan nuna damuwa da take akaina pretending ne ba na gaskiya bane. A ina ka taɓa gani kishiya tana tausayi kishiryarta?"
"Uhm! Jeeddah wallahi da gaske Zarah ke tausayi ki nan da ki ke ganinta ALLAH ya zuba mata tausayi. Ita bata ɗauke ki kishiya ba kallon 'yar uwa take miki
"To ka gayamata banaso ta daina ta zuwa min ni ban ɗauke ta 'yar uwa ba da ita ɗin 'yar uwata ce ai ba za ta aura min miji ba. Ta riƙe tausayinta banaso. Duk lokaci da ta zo sai ta bini ta dame ni da wari bunsurai, zuciyata tayi ta tashi a banza.
"La'illaha illallahu muhammadu Rasulullah!
"Sallallahu alaihi Wasallam!
Na kama mishi muka ƙarasa a tare.
"Jeeddah wari bunsurai ki ka ce fa? Fissibillahi Zarah ce ke wari bunsurai?
Ai koda sharri za ki yi mata kamata ya yi ki ce wari bunsuru tun da, da bunsuru guda take tu'amali wato ni kenan.
"Whatever!
Na faɗa tare da sake lumshe idanuwana.
Kallon mamaki Haidar yake wa fuskarta a haka bacci ya zo ya dauke ta sai da drip ɗin jikinta ya ƙare ya zare mata sannan ta falka ya taimaka mata tayi wanka ya barta tare da mai aikinta ya fita nemo mata ɗanye mangwaro.
***********
Tun lokaci aka yiwa Ameer surgery ya shiga coma har yau bai farfaɗo ba gaba ɗaya hankali Dr Abdallah a l tashe yake musamman da likitoci suka bashi tabbaci ko ya farfaɗo da matuƙar wahala bai rasa tunanin sa ba. Kullum ciki masa addu'a shi da Umma suke.
Bilal Shattima kuma tun sanda A'isha Shattima ta bashi labari Jeeddah tana ɗauke da ciki ya ƙara tabbatar da cewa shikenan ya rasata. Ta ƙarfi da yaji ya shiga yakice soyayyarta cikin hukunci Ubangiji ya haɗu da ƙanwar matar abokinsa Abbas ta kwata masa arai musamman da ya ji sunanta Jiddah sannu-sannu soyayyar yarinya ta fara shiga ransa. Har gashi iyaye sun shigo zance. Ta bangaren Aunty Bahijja kuma aiki da aka yi mata ya yi kyau har an yi discharged ɗinta ta dawo gida wajen Hajja tana ci-gaba da jinya har zuwa lokaci bata iya tafiya sai da taimakon sanda. Yayin da Hajja jikinta sai daɗa rikicewa yake kullum Bilal da A'isha Shattima suna hanyar asibiti da ita. Ita aunty Bahijja ba a maganar ta ko kanta ba ta taimaka ba balle wani ga baki ɗaya rayuwarta ta dawo abar tausayi.
***************
Sai yamma lis Haidar Ka'oje ya sami ɗanye mangwaro jikinsa na rawa ya nufo gida koda ya shigo Jeeddah tana zaune a main parlor, robar miyaunta tana aje gabanta lokaci zuwa lokaci take buɗe ta, ta tofar da yawu.
Kusa da ita Haidar ya zauna "Sannu Honeypie ya jikin naki?
"Da sauki ka samu min mangwaro kuwa?"
"Eh! Bari na kira zulai ta wanke miki.
"Uhm!
Ya ɗaga murya ya kira zulai ta zo ya bata ledar mangwaro irin manya-manyan ɗinan ta je ta wanko ta zuba su a wani babban bowl tare da wuƙa ta kawo masa. Tun kafin Ya Haidar ya fara yanka min mangwaro ɗin yawun bakina suka tsinke yana yankawa ya miƙo min na tofar da yawu na jifa baki ji kake "ƙumuss-ƙumusss! Nan take na cinye ya sake miƙo min wani duk girman mangwaro nan sai da na cinye shi tass har kokari nake ya ƙara yanka min wani "Ya isa haka Honeypie kada ya ɓata miki ciki anjima ko gobe ki ƙara ci guda ɗaya har cinye abinki.
Na gyaɗa kai ba don wai na gamsu da maganar sa ba. Ya tashi tare da ɗauke bowl ɗin sai da ya tabbatar da ya ɓoye shi inda ba zan ganshi ba kana ya wuce bedroom ɗin sa ya yi wanka. Kiran sallar magariba ya fitar dashi yana fita sai ga mai aikin Zarah ta kawo masa abinci, duk ranar girkina Zarah ke aiko masa da abinci saboda ko wari gas banaso balle akai da zance girki. Hatta da Aiman ita ke haɗa mishi lunch pack ɗin sa ta aiko masa. Duk wannan kirki da take nuna min bai sa na sakar mata fuska ba. Domin duk sanda muka haɗu na kalli fuskarta sai na ji wata muguwar tsanar ta na mamaye ni. Mu sha faɗa da Ya Haidar akan wannan hali da nake nuna mata ni kam kallo munafuka nake mata tun da ta fahimci ina da zafin kishi shi ne ta bijiro ta wannan hanya domin ta kara samun faɗa mai girma a wurin Ya Haidar. Shi kuma Ya Haidar abinda har yau ya kasa fahimta ni kwata-kwata bana iya ɓoye kishina duk yadda naso na gwada yi hakan sai ya bayyana ƙarara akan fuskata. Na fi so mu ci-gaba da zaman mu yadda tun farko mu ka fara kowanne mu baya shiga sabgar wani don ni ko kaɗan bana yiwa kishiya wani kallo sama da na maƙiyiyata.
Sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba a kai ba gashi har cikina ya shiga five months laulayi da nake ya ragu sosai tun da har ina iya shiga kitchen nayi girki. Ina samun lafiya Zarah Malik ta ja baya da shigowar da take ɓangarena. Sai dai lokaci zuwa lokaci idan tayi abu kwaɗayi irin na masu ciki za ta ba mai aikinta ta kawo min ko kallon kirki ba zai haɗani da warmer ta aiko balle na buɗe naga abunda ke ci kai tsaye zan kwaɗawa zulai kira ta zo ta ɗauke min shi wani lokaci ita da Aiman ke cinye wa. Ban taɓa hanawa Aiman ya ci ba saboda ina da yaƙi ni ba za ta zuba min wani abu na cutar wa ba. Kawai dai bana jin ƙaunarta a zuciyata, don haka duk abunda za ta bani ba zan iya ci ba.
A kwana a tashi cikina ya shiga watanni bakwai na Zarah kuma takwas bansan watanni cikinta ba sai da Ya Haidar ya kawo kayan baby da ya siya mana a lokaci yake faɗa next month ne EDD ta.
Tun sanda cikina ya shiga watanni bakwai na fara shiga damuwa da fargaba saboda likita ya tabbatar min ko wannan karo sai ayi min cs ba zan iya haihuwa da kaina ba. A koda yaushe Ya Haidar cikin kwatar min da hankali yake yana nuna min likita ba ALLAH bane da zan ɗauki maganarsa nasa araina.
Yau koda na tashi da ciwon baya na tashi ga ƙafafuwana da suka yi kumburi sai kyali suke da kyar ma nake iya taka su a daddafe na sallami Ya Haidar ya wuce wurin aiki da yake ni ce da girki kuma yau shi ne last day da yamma zai koma ɓangare Zarah Malik. Saboda haka ba sai na wahalar da kaina da shiga kitchen ba. Na saka zulai tayi min waina fulawa.
"Zulai manja za ki soya min bana so mangyaɗa.
Na faɗawa zulai dake ciki kitchen tana wanke plates 🍽️ ɗin da muka yi amfani dasu lokaci breakfast.
"To aunty!
Zulai ta faɗa sa'ili da na juya da kyar na ja ƙafafuwana, na ƙarasa ciki main parlor na nemi two seater na zauna. Zamana ke da wuya naji marata tayi bala'in kartawa, har cikin private part ɗina nai sauri runtse idanu ina ya mutsa fuska. Sannu-sannu ciwo sai daɗa ƙaruwa yake, tun ina yatsinar fuska har sai da na kai da zame wa daga kan kujera na sakko ƙasan centre carpet na mimmiƙe ƙafafuwana tare da dafe ƙugu. Wasa-wasa sai gashi na fara gumi ina yarfe hannaye gami da cizo lebbe da tafiya tai tafiya sai na dawo faɗar "innalillahi wa'inna illahim raji'um! Me yake shirin faruwa dani wannan zafin da nake ji yafi kama da na haihuwa na shiga uku ba dai naƙuda ce ba gashi cikina watanninsa bakwai. Watakila bankwani zan haifa na faɗa hawaye na bin kumatuna.
Fahimtar nayi zubda hawaye bai zai fidda ni ba na kwaɗawa zulai kira sai gata ta fito daga kitchen da gudunta.
"Zulai taimaka ki ɗauko min wayata a ɗaki ta nan kan bedside drawer yi maza Dan ALLAH.
Na faɗa ina runtsar ido jim kaɗan sai ga ta, ta dawo riƙe da wayar ta miƙo min da kyar na lallabo numbern Honeybun ina ji ya yi picking na ce "Ya Haidar ka zo ka kaini asibiti ina ga haihu zan yi?"
"Wane irin haihuwa Jeeddah?"
"Irin wacce kasan anayi.
"Kai ina ba dai haihuwa ba. Dukka cikin ki watannin sa bakwai fa?
"To shike nan Ya Haidar tun da cikina watannin sa bakwai kar ka zo ka bari har sai na mutu sai ka gasganta haihuwa ce.
Na faɗa a mugun fusace tare da kashe waya na wulgar da ita gefe na ci-gaba da munguli da yarfe hannaye tare da cizon lips yayin da zulai ta fahimci hali da nake ciki ta kasa komawa kitchen tai tsaye gefena tana min sannu, fuskarta ya yi kalar tausayi kamar za ta rushe da kuka. Ina ciki wannan hali sai ga Zarah Malik ta shigo hankalinta tashe da saurinta ta ƙaraso guna ta wani dafa min kafaɗa tana leiƙa fuskana "Subhanalillah! Sannu Jeeddah. Yanzu nan sweetie ya kirana ya ce na zo na zauna dake kafin ya ƙaraso wai ba ki da lafiya.
Duk da ina cikin halin ciwo da raɗaɗi hakan bai hana ni jin zafin kalma nan ta "wai" da ya Zarah Malik ta ambata wato ma ƙarya nake yi. A hasale kuma ciki hargowa na ce "Ciwo da nake ji ya wuce ki kira shi da wai Zarah koma mene ne ai gashi nan kin kunsa.
Na ƙarashe magana cike da mugun takaicin ta.
Mamaki shimfiɗe akan fuskar Zarah Malik saboda ko kaɗan bata ga abin ɗaukar zafi ba. kwance take tana hutawa abinta Haidar ya kira ta a rikice ya umarce da ta zo da ba don haka ba ta ina ma za tasan Jeeddah bata da lafiya da take kokari sauke gauni naƙuda akanta.
Zarah da ta fahimci lamarin Jeeddah har da zafin ciwo sai tai mata uzuri ta maida ganinta kan zulai ta ce "Zulai kunna mata Ac wannan gumin da take yi ya yi, yawa.
"Zulai karki kunna bana buƙata.
Nayi sauri katse wa zulai hanzari don har ta nufi switch ɗin Ac dole ta dawo watakila gani Zarah Malik da tayi yasa ta koma kitchen.
Ko kaɗan Zarah Malik bata yi fushi ba asalima sai ta nemi dab dani ta zauna sai faman sannu take min haɗe da addu'ar ALLAH ya sauke ni lafiya, ko sau ɗaya ban amsata ba amma a can cikin zuciyata ina amsawa da Amin a halin yanzu addu'ar da na fi buƙata kenan. Muna ciki haka sai ga Ya Haidar ya shigo a hankalinsa tashe, ya kamani muka fito ashe daidai entrance ɗin shiga flat ɗina ya yi picking da taimakon sa da na Zarah Malik suka shigar dani ciki mota kai tsaye Hamda clinic and maternity private hospital Ya Haidar ya nufa dani abinka da harka ta kuɗi nan take aka wuce dani labour room likita da nake gani aka kira abinda bai wuce ten minutes ba sai gashi ya zo yana zuwa ya shiga duba ni ya tabbatar da haihuwa ce kuma ko zan kai gobe ba zan iya haihuwa da kaina ba. Saboda haka za a yi min emergency operation. Dole Ya Haidar ya kira gidanmu da nasu ya sanar musu hali da ake ciki.
Mama da Ya Kabeer suka fara zuwa sai ga Mommy Turai jim kaɗan sai ga Aunty Farida da Khairat kowanne su hankalinsa tashe. Duk wanda ya zo asibiti ya tarar da Zarah Malik tana zaune zugun tayi wani kalar tausayi. Sai ya ji ta burge sa domin ga damuwa nan kwance ƙarara akan fuskarta. Sosai ta ba wa su Mama tausayi don har cewa Mama tayi Ya Haidar ya maida ta gida duba da yanayi da ita ma take ciki. Amma ta kafe ba inda za ta je har sai an fito da Jeeddah.
Kafin a fito da Jeeddah theater room har wata shaƙuwar bazata, ta shiga tsakaninta da khairat. Don Khairat har waje ta fita ta siyo mata ruwan roba mai ƙaranci sanyi ta bata tasha duba da yadda taga laɓɓan Zarah ɗin sun bushe.
Misali ƙarfe 12:30pm daidai aka fito da abinda Jeeddah ta haifa wanda yai matuƙar gigita duk wanda ke wuri ya hartsuna masu ƙwaƙwalai suka kasa yarda da cewa abin da Jeeddah ta haifa ne. Cikin kaɗuwa Ya Haidar ya zaro idanuwa.

Shin me Jeeddah ta haifa wanda ya haddasa wa iyayenta da 'yan uwata har ma da mijinta shiga irin wannan firgici? 😂 😂

Naso na ƙarasa muku labari nan a iya wannan shafi sai dai rashin charging ya kawo min cikass ga kuma headache dake damu na ku yi haƙuri mu haɗu a shafi na gaba.

#Haidar Ka'oje
#Jeeddah maishadda
#Zarah Malik
#Team zazzafan kishi.

*Abishirinku mata 'yan kwalisa masu son su faranta wa mazajensu rai, ku gamsar da su iya gamsuwa to ga dama ta same ku da za ki saka maigida ihun daɗi da haɗaɗɗun kayan mata daga kamfani Manzil Alwafir masu kyau da inganci, Hajiya za ki mallake mijinki a tafin hannunki ba Boka ba malam maza ki garzayu wurin gimbiyar haɗa mata mai bada gudunmawar gyara shimfiɗar aure Hajiya Hassana Abdullahi*

*_Muna da kaya kamar haka_*

Smoked heaven
Asta
Ashana
Yaqtur
Nashwa
3rd Avenue
Back to honeymoon
Kazar Mata
Tsumi
Dambun mata
Sanyi herbs
Helwa
Anwar
Deep sea
Vibrationzz
Wet and tight
Ashwa
Halwa
Helwa
Garden knot
After dark intense
Bomb oil
Yoni balm
Swan
Taurariya
Lazeez
Persion hot
HD tea
Mazan Arewa
Tightening honey
Jego package
Bridal package
Durot

Domin ƙari bayani sai a tuntube mu a waɗannan lambobi 08036072970 08121555525

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now