04...

165 6 1
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

_Na sadaukar da wannan littafi ga Zarah Bb_

04...

Wani shegen murmushi ya sake min wanda bashida bambanci da na 'yan iska, har wani jan iska yake daga bakinsa tamkar wanda ya ci yaji yana lumsashe idanuwa, kana cikin taushin murya ya ce "Soyayya ce kawai  Please ki daina danganta duk abinda nai miki da iskanci, wallahi tsabar so ne har ji nake kamar na cinyeki infact soyayyarki tana daff da zauta ni.
Harara na galla masa tare da jan dogon tsaki tamkar zan gutsere harshena.
    "Mtsssss....!
Kana na ɗora da faɗin "Ni dallah sake min hijabina banaso ƙarya da yaudara, da ace bansan yadda 'yan mata ke shawagi akanka ba da sai na yarda da maganganun ka masu cike da zallar yaudara, saboda haka nasan waye kai ba abinda zai fito daga bakinki na yarda dashi.
Na ƙarasa magana tare da fincike hijabina cire hijab ɗin nayi gami da  wulga shi bisa gado ya faɗa kusa da Khairat tsabar takaicin taɓa shi da ya yi yasa naji duk hijab ɗin ya fi ce min arai.
    Ƙara matsowa ya yi kusa da ni, cikin taushin murya ya ce
"Don Allah ki yarda dani Jeeddah wallahi-tallahi ban taɓa kama koda ɗan yatsan wata mace da nufi na ji daɗi ba, duk abinda zan faɗa ba lallai bane ki yarda saboda kin ri ga da kin gina zuciyarki da zargina amma inaso ki sani tabbas soyayyarki tai min illa matuƙa, ta yadda ba zan iya kallon ko wacce 'ya mace da sunan so ba.
"Kaga malam faɗawa kaji waɗannan zabi ne domin duk yadda kaso ka tsarani da yaudararrun kalaman ka ba za su taɓa tasiri akaina gara tun wuri ka adana abinka watakila ka haɗu da mai tosasshiyar ƙwaƙwalwa ka yaudare ta dasu.
Na ƙarasa magana gami da yi mishi kallon sama da ƙasa, na nufi ƙofar fita har na riƙo handle na ji sautin muryar Khairat tana faɗin
"Oh ni Ummul-khairi yau ina gani rayuwa waɗansu mutane ƙwaƙwalwarsu sam bata da bambanci da ta kifi, Don Allah Ya Haidar ka daina wahalar da kanka akan wannan matar mai ƙaramin kai kasan mutane masu ƙanana kawuna basu cika fahimtar masu sonsu da gaskiya ba bar su dai da mugun zafin kishi wanda idan basu yi hattara ba sai ya kai su ya baro.
Cikin tsanani fusata na juyo tare da sauke idanuwana akan fuskarta ina faɗin "Na rantse Khairat idan ba ki daina shiga sabgata ba sai na kwaɓar miki da haƙoran gaba.
   "Iyeee....lallai ma wai kina nufi ke ce za ki zubar min da haƙora?"
Yadda Khairat tai magana alama ce da ke nuna ba zan iya ba. Hakan ya ƙara fusata ni na tunƙarota gadan-gadan, da sauri Ya Haidar ya riƙo gefen ƙuguna ya jawo ni jikinsa sai zillewa nake yi yayin da Khairat ke ta faman tintsirar dariya cikin fusata nace "Sake ni na nuna mata tazarar shekaru biyu ba wasa bane nace ka cikani wallahi sai na zubarwa yarinyar nan da haƙora hankalina zai kwanta.
   "Yi haƙuri zakanya ai ke babba ce kina da hankalinki kada ki biyewa Khairat 'yar mitsitsiya da ita ta ɓata miki rai a banza, zo mu je waje na faɗa miki wata magana mai daɗi nasan za ta faranta miki kin ji Matar Haidar?"
Fizgewa nayi cikin tsawa nace "Dallah cikani malam ba matar Haidar ba kakar Haidar duk ka bi ka uziramin nace ka kyaleni ko ana so dole?" ke kuma Khairat za mu gauraya da ke wallahi sai kin sha mamaki abinda zan yi miki bai dai taƙamar ki shiga sharo babu shanu ba, za ki gane kuskurenki banza munafuka.
Ina gama magana na fice rai ɓace, harara Ya Haidar ya gallawa Khairat gami da faɗin "kin ganki kou Khairat so  ki ke ki kashe min aure.
Dariya sosai Khairat tasa tana rufe bakinta da tafin hannunta ɓata fuska ya yi ya ce "Zance gaskiya Khairat kin ɓatawa rabin raina da yawa ki ɗauko min aiki rarrashi da magiya ni dai tsorona ɗaya kada ki jawo min tasuɓali kamun kaza ga wutsiya ki tsinka min igiyar aurena.
Tsagaitawa tai da dariya tana faɗin
"Kwantar da hankalinka Ya Haidar kamar tsunma aranda duk duniya ba wanda ya isa ya kashe maka aure kai da aurenka da kaca aka daura shi tsinka shi sai an haɗa babbar runduna guda.
Murmushi ya yi yana shafar kwantatciyar sumar kanshi, gami da  ɗage gira "Allah kou ƙanwa?"
    "Allah kuwa babban yaya kasa wa zuciyarka salama domin har gaba da abada Jeeddah bata da wani miji bayan kai ta ka ce halak-malak, saboda haka ka sa ranka a inuwa ka daina saka damuwa akan shirmen da take maka duk ɗan banza kishi ne ke ɗawainiya da ita kasan dai hali mutuniyar taka da kafiri kishi bal-bal.
   Ajiyar zuciya ya sauke ya tako a hankali yayin da hannuwanshi ke zube cikin aljihun wandonsa ya tsaya gaban Khairat cikin yanayi na damuwa ya ce "Ba za ki gane bane Khairat ba ƙaramin tashi hankali nake ciki ba gami da wannan sauyawar da Jeeddah tayi farat ɗaya, ada dai nasan tana ƙaunata na rasa gano laifi da nai mata da yasa yanzu ta tsaneni duk lokaci da na kalleta ina hango tsanani tsanata a cikin ƙwayar idanuwanta. Khairat ina jin tsoro na rasa Jeeddah muddin hakan ta kasance Allah ƙadai yasan irin hali da zan shiga amma da matuƙar wahala idan zuciyata bata buga ba, idan kuma zuciya ta buga Khairat mutuwa ake yi wallahi so masifa ne.
  Ya ƙarasa magana hawaye na bin kumatunsa, tsananin tausayinsa ya lulluɓe Khairat, ita ɗin sheda ce akan irin mugun so da yake wa Jeeddah, tun bata mallaki hankali kanta ba, balle yanzu da ta zama ƙosasshiyar budurwa, rasata a gareshi tamkar dusashe duniyarsa ne cikin kwantar da murya ta ce "Ka fahimci wani abu guda Ya Haidar wallahi Jeeddah tana sonka kawai dai mugun kishinka ne yai mata yawa, ita fa gani take duk matan dake gari nan sonka suke yi.
    Murmushi gefen baki ya yi ya ce "Haba sai kace wani namamajo kawai dai ta daina sona ne shiyasa take fakewa da wannan labarin ƙanzo kurege.
"Koma mi take nufi ruwanta ne domin tuntuni Baba ya ri ga da ya ba ka ita jira kawai ake yi mu kammala secondary School a aura maka ita, duk wannan shirmen da kaga tana yi da zarrar kun yi aure za ka nemi shi ka rasa.
Khairat ta faɗa cike da son kwantar masa da hankali.
   Ajiyar zuciya ya sauke yayin da murmushi mai cike da zallar nishaɗi ya bayyana ƙarara akan kyakkyawar fuskarshi ma'abociya kyau da kwarjini, ba ƙaramin farin ciki maganganun Khairat suka haifar masa ba, ita kanta Khairat murmushi tayi tasa bayan hannunta ta goge masa hawaye haɗe da cewa"No more tears please she's only belong to you only you Ya Haidar.
"Thank you so very much sister ina alfahari da ke.
Tun lokaci da Jeeddah ta fice daga ɗakin bata ƙara dawowa cikinsa ba sai da taga Ya Haidar ya yi wa Mama sai da safe Sannan ta dawo ɗakin nasu, kasancewar tana ji gajiya a jikinta shi ya hana ta biyewa Khairat duk da irin tsokanata da take yi ta bi lafiyar gado ba daɗewa bacci ya yi awon gaba da ita.
Washegari kadaran-kadaham suka tashi kamar basu bane daren jiya suka dinga kwamza faɗa, bayan sun kammalawa Mama ayyukan gida da suke mata na yau da kullum suka yi wanka kowacce su ta shirya cikin riga da wando na Indian Pakistan iri ɗaya colour ne kawai banbamci na Khairat lemon green, na Jeeddah kuma red colour kowace su tayi matuƙar kyau na ban mamaki, gidansu ƙawar Jeeddah A'isha shattima za su je ta yi wa Jeeddah kitso. parlourn Mama suka leƙa Khairat ta ce "Mama mun tafi.
   "Allah ya tsare amma Don Allah Khairat karki biyewa Jeeddah ku nemi wuri ku zauna, ku barni da aiki tule a gida.
  "Tou Mama in-sha-Allah ba za mu daɗe ba.
"Shike nan sai kun dawo.
Daga haka suka fice akan hanyarsu Jeeddah ke ba wa Khairat Labarin haɗuwarta da ɗan baƙi saurayi mummuna, tana dasa aya Khairat ta dinga kwasar dariya, sai da tayi mai isarta kafin ta buge shoulder Jeeddah gami da faɗin "Kai ƙauyanci mugun abu ke yanzu Jeeddah kina nufi ba kisan idan saurayi ya yaba kyakkyawar halittar mace yana so ya nuna mata cewa babu kamarta a cikin dubbanan mata ba?"
  Zaro idanuwa Jeeddah tayi cikin kaɗuwa ta ce "Haba wai da gaske kike yi ko tsokanata kike yi?"
   "Wallahi da gaske nake miki yaba kyakkyawar halittar mace baya nufi iskanci, a takaice dai kamar so yake yace yana sonki ke kuma kwafasasshiya kika kwafsa masa wallahi ya kamata ki waye Jeeddah kullum kanki ƙara shiga duhu yake yi, banda azababben kishi da mugun hali ba abinda kika sani...
  "Dallah ya isheki banaso reni wayau.
"To kuwa wannan tauri kan naki da rashin karɓar gyara shine zai ta wahalar da ke har ƙarshen rayuwarki.
Khairat ta faɗa gami da taɓe baki.
     "Na dai ji duk abinda za ki faɗa go ahead, amma idan kika sake bakinki ya kuskure ya faɗi abinda ya sosa min rai na zage damtse naci ƙaniyarki.
Da Wannan taƙaddamar suka iso Gate ɗin gidansu A'isha shattima da kallon yanayi gate da zubin gini gida duk da sun tsofa hakan ba zai hana ka gano mamallaki gida ya yi tashe dukiya da alamu kariyar arziki ce ta same shi. Jeeddah ce ta fara tura Gate ɗin dai-dai yana fitowa daga ɗakinshi dake BQ zai fita yana sanye da boxer briefs da farar underwear vest, a jikinsa sosai muscles ɗin shi suka fito riɗa-riɗa dasu yayin da muninsa ya fito ƙarara, hanci nan nasa can sama karaf idanuwansu suka sarƙe.
Ya ɗage girar ido yana kallon Jeeddah gami da murmushin gefen baki.
Ina tozali dashi jikina yai wani tsamm...na kasa ɗauke idanuwana akansa hannuwanshi yasa ya tare min hanya cikin muryar ƙasa-ƙasa ya ce "Allah ya kama ki wato ke ga ki mai wayau kou?" kin hanani address ɗin gidanku shine ni za ki zo mana gida to ba za ki shiga ba.
   "Excuse me Please ni bansan cewa nan ne gidanku ba saboda haka bani hanya na wuce ko na ture ka don ba ƙarfi ka fini dashi ba.
   Da sauri Khairat ta ture ni gefe ɗaya ta shige gabana ta dinga ƙare masa kallo, tana ƙunshe  dariya mai kama da ta munafuci "Kaine Bilal shattima, yayan A'isha shattima kou?"
Khairat ta faɗa rass gabana ya faɗi tabbas sai yanzu naga tsananin kamanunsa da A'isha shattima musamman ɗan gajeren hancin nan nasu da alamu dai na gado ne domin kusan duk yaran gidansu haka hancinsu yake.
Ya saki ƙayatatce murmushi gami da faɗin.
   "Yeah! how do you know my name?"
   "Haba kai kuwa Ya Bilal tun da ba daƙiƙƙiya bace ni ace ina tare da A'isha shattima almost four years farat ɗaya na kasa gane blood relative ɗinta ai sai duniya tai min dariya.
   Daga jin yadda Khairat ta bashi amsa nasan da ni take "Bara mu koma gida za ki ga daƙiƙanci gani idonki kuwa dani kike zancen.
Na faɗa can ƙasan zuciyata haɗe da kwafa a bayyane kuma sai nace "Dallah malam ka ba mu hanya mu wuce ai ba wajenka muka zo ba balle ka ishe mu da karaɗi tsiya.
A ɗage ya kalle ni ya yi murmushi ya ce.
"Kafin na ba ku hanya sai na fara miƙo ƙoƙon barana babbar yaya naga wannan ƙanwar taki inaso da fatar za ki shige min gaba?"
Yadda yake magana yana kallon Khairat kana kuma ya nuna ni da yatsa take na fahimci abinda yake nufi bansan lokaci da na buga masa tsawa ba cike da takaici nace "Kai amma Allah ya wadaran girman idanuwanka da suka kasa haska maka ni ce gaba da ita ba ita bace gaba da ni.
    Yadda nai magana a hasale yasa ya janye gefe saida ya yi min wani kallo ni kuma nai masa kallo up and down na watsar na wuce abina, Khairat uwar 'yan kaudi da shisshigi tsiya ta tsaya yana zuba mata surutunsa marar kan gado.
A parlour na tadda mahaifyar su A'isha cike da ladabi na gaidata, ta amsa min ciki sakin fuska tana tamabyar lafiyar Mamanmu na amsa mata da lafiya ƙalau, A'isha ta fito daga bedroom ta tarbeni sai ga Khairat ta shigo tana dariya da sauri na banka mata harara, duk ƙoƙarina na gani bata  tasaki baki ta faɗi abinda ya wakana tsakanina da Bilal ba.
A'isha tana ciki yi min kitso yai sallama ya shigo.
Shigowarsa ke da wuya ya ce da mahaifiyarsa "Hajja ga fa surukarki nan ta kawo kanta tun kafin na kawo miki ita shiyasa nace bara na shigo na gabatar miki da ita in-sha-Allah da ita za a yi ki sa mana albarka domin ita ce Final choice ɗina.
Gaba ɗaya kunya ta dabaibaye ni na ɗauke gyalena da ke aje kusa dani da sauri na yane kaina tare da sadda kai ƙasa. Dariya Khairat da A'isha suka sa yayin da Hajja tai murmushi mai sautin gaske, da alamu abin yai mata daɗi shiyasa ta shiga faɗar "Kai Ma-sha-Allah! lallai Bilal ka iya zaɓe Allah yasa ayi damu.
    Duk sai kunya ta ƙara kamani kamar na nutse cikin ƙasa. Karaf Bilal ya amshe da "Amin ya hayyu ya ƙayyum Hajjarmu.
   Sai kuma ya ƙara da faɗin "A'isha ki tabbata kin mata kitso mai kyau sosai kinsan ita mai kyau ce dole komai nata ya kasance very special.
    "Iyeee... lallai Ya Bilal ƙawata ta ƙundume maka zuciya?"
A'isha ta faɗa tana zaro idanuwa.
    "Sosai ma kuwa A'isha saboda haka ki ci-gaba da yi min campaign har sai kin tabbatar tutar sona ta kafu cakk a zuciyarta.
    "An gama Ya Bilal ka dai ka tanadi ƙarafe campaign kasan gwamnatin ta hana aikin banza.
    "Ba ki da matsala ke dai ki tabbata naci zaɓe.
Hajja ce ta kalleshi tana dariya mai ƙaramin sauti tana faɗin "Tashi maza ka ba mu wuri duk kabi ka hanawa 'yar mutane sakewa.
   Langwaɓe kai ya yi gami da yi ƙasa da murya ya ce "Allah Hajja bangaji da kallon kyakkyawar fuskarta ba.
    "Idan kai bakada kunya ai ita tanada saboda haka sai anjima oya...ga ƙofa nan fita.
Hajja ta ƙarasa magana tare da pointing ƙofar fita da yatsanta ba don ranshi ya so ba ya nufi ƙofar yana faɗi "my final choice Hajja ta kore ni gashi ban gaji da kallon kyakkyawar fuskarki ba, amma ba komai zan koma kofar gida na jira har a kammala miki kitso mu sha firarmu ta soyayya.
   Har aka gama min kitso a takure nake na kasa sakin jikina tsakanin da Allah kunyar Hajja nake ji domin ɗanta ya yi min shi ne kalar mijin da nake mafalki mallaka.
Bayan su koma gida da dare bayan sallar isha'i almajiri ya shigo ya ce ana sallama da Jeeddah ƙofar gida, ina ɗaki amma sai da gabana ya faɗi take jikina ya bani Bilal Shattima ne mai kiran nawa. Ina jin lokaci da Mama ta ce ace nayi bacci sai duk naji ba daɗi har ji nayi tamkar nace idanuwa na biyu, amma kasancewar nasan saboda Ya Haidar yasa ta faɗi hakan dole na ƙunshe bakina nai shiru amma can ƙasan zuciyata naji zafin hakan ba kaɗan ba.
   Bilal Shattima da ke tsaye a ƙofar gidansu Jeeddah tare da abokinsa Abbas suna jiran ɗan aikensu ya dawo motar Alhaji Usman maishadda ta danno kai, wanda yaronsa na kasuwa Abdul-hadi ke driving ɗinsa parking ya yi da zimmar bude gate Alhaji Usman maishadda ya ga samari sababbin fuska tsaye a ƙofar gidansa, hakan yasa ya buɗe ƙofar mota ya fito tun kafin ya ƙarasa kusa dasu suka zube ƙasa suka kwashi gaisuwa.
     "Yawwa sannunku samari wa ku ke nema?"
"Baba wajen Jeeddah muka zo.
Abbas ya faɗa cikin kwantar da murya.
    "Uhmm....waye daga cikinku keso gani nata?"
    "Ni ne Baba sunana Bilal ɗan gidan marigayi Alhaji Ibrahim Shattima, ni ke sonta da aure in-sha-Allah.
Bilal Shattima ya tsince kanshi da faɗar haka a dalili kwarjini da Alhaji Usman maishadda yai masa.
Shiru Alhaji Usman maishadda ya yi yana nazari kafin ya ce "Ma-sha-Allah bari na turo muku da ita amma malam Bilal banaso yawan zuwa zance nan ka ji kou?"
   "Tou Baba in-sha-Allah za a kiyaye.
   "Madallah.
Alhaji Usman maishadda ya faɗa a takaice.
"Godiya nake Baba Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana.
Bilal ya faɗa cike da farin ciki irin tarbar da ya samu daga mahaifin Jeeddah.
   "Amin ya hayyu ya ƙayyum!.
Cewar Baba gami da nufar ƙofar shiga gida yana shigowa ya soma kwalla min kira "Ke Jeeddah kina ina zo maza ga baƙi can a ƙofar gida suna jiran ki.
   Kamar jira nake nai wuff na fito riƙe da hijabina a hannu.
  "Alhaji ka manta ne da Jeeddah ayi mata miji banga amfani fitarta zance da wani ba shiyasa nace ace tayi bacci.
   Mama ta faɗa tana kallon Baba da ɗaurarriyar fuskarta don ko kaɗan bataso na fita gudun kada Ya Haidar ya zo ya ganni ransa ya ɓaci.
   "Ba komai Fatee barta ta je gudun kada yaro ya ɗauka an masa wulaƙanci.
Kafin Mama ta sake magana nai sauri ficewa da mamaki ta bi bayana da kallo domin taga yadda jikina ke rawa.
Bayan mun gaisa Bilal Shattima ya gabatar min da abokinsa Abbas a matsayin Best friend ɗinsa, yayin da shi kuma Abbas ya shiga zayyane min irin yadda Bilal ya kamu da soyayyata, ba tare da wani jan aji ba na karɓi tayin soyayyar tasa muka taɓa fira kafin Abbas ya ba mu wuri ya koma nesa damu kaɗan yana dannar wayarsa. Cikin kwarewa da iya tsara zance Bilal Shattima ya shiga jaddada min irin yadda ya kamo da sona, na fito ɓaro-ɓaro ba kunya balle tsoro Allah na faɗa masa banaso kishiya na gindaya masa sharaɗina idan ya amince ba zan min kishiya ba nima na amince hundred percent zan aurenshi.
Abinka da wanda ya kamo da sabuwar soyayya bai kawowar zuciyarsa komai ba ya amince daga nan muka tsunduma tsundun cikin kogin soyayya sai around 10 suka wuce da alƙawarin idan ya isa gida zai kirani a waya, wanda kafin mu yi sallama muka yi musayar number waya.
A takaice dai tun daga wannan ranar zazzafar soyayya ta shiga tsakaninmu, tun Ya Haidar bai gano ba har ya zo ya gane a lokaci har 'yar ƙaramar jinya ya yi yayin da Mama ta bi kowacce irin hanya domin gani ta datsa mana soyayya, ni kuma na kafe kai da fata sai Bilal Shattima.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now