045

116 13 1
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

💃🏻🔥 *INA MASOYA LITTAFIN RUD'ANI?*

*SHIN KUNADA LABARIN FREE PAGES SUN KARE NA LITTAFIN*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
💥💧 *DA MA ACE...*

*SHIN KUNADA LABARIN HAZIK'AN MARUBUTAN NAN BIYU DA SUKAIWA KANSU LAK'ABI DA TAGWAYE BIYU SUNA NAN SUN YUNKURO DOMIN NISHADANTAR DAKU DA ZAZZAFAN LABARIN SU MAI SUNA👉🏼 DA MA ACE?.....LABARIN DAYA KUNSHI RAYUWAR MU TA YAU DA KULLUM LABARI MAI CIKE DA SOYAYYA DA NISHADANTARWA?LABARI MAI CIKE DA CAKWAKIYA DA SARK'AK'IYAR SOYAYYA AKAN MUTUM UKU DIK AKAN MACE D'AYA?LABARIN DA ZAI TAB'O MUKU SHARI'AR MUSULUNCI?SHIN KIN SHIRYA?KINSAN SUWAYE WAD'ANAN TAGWAYE BIYU?*

*TAGWAYE BIYU 2023*

*SLIMZY* Marubuciyar *RUD'ANI*

*FEEDHOM* marubuciyar  *ISHARA*

*MAZA HANZARTA KI SHIGA GANGAMI DA TAWAGAR WAD'ANAN HAZIKAN MARUBUTAN WAD'ANDA SUKE NISHADANTAR DAKU YANZUN HAKA DA ZAFAFAN LABARANSU MASU DADI FADAKARWA DA ILIMANTARWA DA NISHADANTARWA WATO  RUD'ANI DA KUSKUREN SO WAD'ANDA KE ZUWA MUKU A KYAUTA YANZUN HAKA*

MAZA KI HANZARTA KI BIYA KUDIN WANAN LITTAFI MAI SUNA *DA MA ACE* AKAN FARASHI 500 KACAL KISHA MADARAR SOYAYYA MAI RATSA ZUKATAN MASOYA....

DOMIN BIYAN KUDIN WANAN LITTAFIN KITURA TA WANAN ASUSUN BANKIN
👇🏻👇🏻👇🏻
9994468172
fiddausi musa
Access Bank

DOMIN TURA SHAIDAR BIYA TA WANAN NUMBER 08036953516 KO 07042276401

DOMIN TURA KATI TA WANAN NUMBER 08036953516

*TAGWAYE BIYU 2023*📢📢🔥

045..

Kafin hannunta ya sauka akan handle na danƙo wuyanta, ta baya na jawo ta da ƙarfi ina jan ta tana tirjewa, ni kuma ban fasa jan nata ba. Har mu ka dawo cikin parlour sannan na ingiza ta tai baya kamar za ta faɗi ƙafarta ta buge center table ta kwalla ihu. Dama Aunty Bahijja ba wani jikin kirki ne da ita ba irin su ne bahaushe ke ma laƙabi da ɓarna kiwo domin kuwa a bushe take jikin nan nata ƙamass yake, sai kace ƙamboli fara 'yar ƙarama da ita sai babbar azaba domin duk yanda ake azabtar da mutum matar nan ta azabtar dani ta hanani sukuni gaba ɗaya ta dungule min lissafi gami da harsuna min zaman lafiya. Saboda haka yau ALLAH ne kaɗai ya isa ya kwace ta daga hannuna batare da wani dogon tunani ba nayi kanta da wuƙa dake hannuna gani haka yasa ta shiga ja da baya wani irin mashahurin tsoro ya lulluɓe ta taga mutuwa ido biyu muraran, miyau bakinta ya kafe duk yanda ta so ta ba Jeeddah haƙuri bakinta yaƙi buɗewa balle har kalmar ban haƙuri ta fito daga cikinsa.
Sai kawai ta shiga dakatar dani ta hanyar buɗe tafukan hannuwanta, ban yi wata-wata ba na yanki tafi hannunta na dama ta kwalla mahaukaci ihu tana kururuwa neman agaji ban bari ta ƙarasa ihu da karuruwa nata ba, na sake yankar ta a damtse hannu, da ta fahimci da gaske rai da numfashinta nake farauta sai kawai ta zabura a karo na biyu ta kwasa da mugun gudu nima na dafe bayan ta, tana zuwa ta bugi ƙofar bedroom ɗina da dukkan ƙarfinta tana daff da shigewa ciki na sake yankar ta a gadon baya, duk da haka sai da ta rufa kofar inda ALLAH ya taimake ta akwai key saƙale a jikin ƙofar, sai kawai ta datse ƙofar zubewa ƙasa Aunty Bahijja tayi sai faman sauke numfashi wahala take yi kafin ta kai duba ga hannunta da ke tsiyayar jini ta ko ina raɗaɗi take ji yana ratsa ta, musanman gadon bayanta. Maraya kukan ta saki bata taɓa tsammani rashin hankali Jeeddah ya kai har haka ba.
Ina gani Aunty Bahijja ta rufu ƙofa har da murza key raina ya ƙara ɓaci na saƙale wuƙa a tsakani haƙorana na sama da ƙasa kana na shiga dukan ƙofar da dukkan ƙarfina da ALLAH subhanahu wata'ala ya albarkaci dashi, daga bisani na saki wuƙar tayi tsalle akan tiles ta bada wani irin sauti. Kafin na shiga faɗin "Aunty Bahijja ki buɗe ƙofar nan cikin lalama don ba abinda zai hanani aika ki gari da ba a dawowa kar fa ki bari na balla ƙofar nan na shigo na rantse yanda kika fitine rayuwata nima sai na datse miki taki.
   "ALLAH tsine miki albarka Jeeddah muguwa kawai baƙar 'yar ta'adda.
Cewar Aunty Bahijja cikin muryar kuka, yayin da hannunta da gadon bayanta ke fitar da jini ba na wasa ba.
   "Shikenan tun da ba za ki buɗe ba da kin buɗe da na rangwata miki kalar azabar da zan shayar dake amma yanzu nan zan nemo spare key na buɗe da kaina ina tabbatar miki a cikin ɗaki nan zan binne gawarki ko sallah ba za ki samu ba.
   Kowanne furunci da ke fitowa daga bakin Jeeddah Aunty Bahijja jin sa take ji tamkar ana ƙididdiga numfashinta ne, daga nan zaune ta saki fitsari gani ruwa yana fita daga ƙasanta yasa ta matsawa sai kawai taji ta zaune wayarta dake cikin aljihun gown ɗin ta. Hannunta yana makyarkyata ta ciro ta sau biyu tana zame wa daga hannunta tana faɗuwa kafin tai nasarar danno number Bilal inda ALLAH ya taimake ta shine last person da tayi waya dashi saboda haka kiransa ya zo mata a sauƙaƙe, tana ringing amma ba a ɗaga ba gashi Jeeddah sai bugu kofa take yi gami da furta mata razanannu kalamai.
   "Bilal Dan ALLAH ka dauka wallahi banaso na mutu a hannu wannan zautatciya matar taka.
Aunty Bahijja ta faɗa cikin sarƙewa numfashi, ci-gaba da kira Bilal tayi kusan kira haɗu tai mishi bai ɗauka ba. Ta kira wayar Hajja a kashe sai kawai ta sunne kanta tsakanin gwuiwayinta biyu ta saki kuka gaba ɗaya ta fidda rai ga rayuwa sai kawai ta ji wayar tai ringing a gigice ta ciro kanta ta kalle sensor din wayar tai tozali da suna Bilal ta rarumi wayar hannunta yana rawa ta danna kore madanni, kana takai wayar kunneta cikin fitar hayyaci take faɗin "Bilal Dan ALLAH ka zo ka taimake ni Jeeddah za ta kashe ni gaba ɗaya ta yayyanke min jiki da wuƙa jinin jikina zai iya ƙarewa a kowanne lokaci.
  Sosai Bilal ya tsorata a rikice ya baro Company ya nufo gida, tun a bakin Gate ya fara jin dukan ƙofar da Jeeddah take yi, saboda haka ya kwasa da mugun gudu ya tura ƙofar parlour. Jeeddah ya hango tsaye tana bugun ƙofa kamar zararriya sai faɗin take "Na gayamiki yau ni ce aljalinki a gidanan sai na faɗe ki da ranki ba dai kin ce Bilal ya kwashe gara da garɗi da ni ɗinan banida irinsa to kuwa in-sha-Allahu ba za ki sake ba wa wani mahaluki wannan labari ba don sai nayi gunduwa-gunduwa da naman jikinki....
  "Subhanalillah! Jeeddah kanki ɗaya kuwa kisan kai za ki yi?"
Bilal Shattima ya faɗa sa'ili da ya ƙaraso kusa dani, juyowa nayi na watsa masa idanuwana da suka yi jajir kamar mai cutar Apollo.
  "Idan har hauka ce ke saka mutum ya yi kisan kai tabbas na yarda na amince ni mahaukaciya ce, domin kuwa babu abinda nake da buri da ya wuce naga gawar Aunty Bahijja kwance cikin jini. Bilal banida maƙiyiya irin Aunty Bahijja wallahi ta zame min karan tsaye ta zama silar jefa ni cikin hali ƙaƙanikayi.
   Na faɗa a kausashe gami firfitowa da idanuwana waje.
Aunty Bahijja dake ƙargame a ɗaki jin murya Bilal yasa ta cewa "Bilal ka kira jami'an tsaro wallahi da gaske matar nan farautar raina take yi, ba ka yanda ta yayyanka ni ba sai rasa jini nake yi kira su Dan ALLAH kada jini jikina ya ƙarasa tsiyayewa.
Aunty Bahijja ta ƙarasa magana gami da ƙara rushewa da kuka.
Yanda Jeeddah ta ƙarashe magana tana zarar ido yasa Bilal Shattima birkicewa domin kuwa ba ƙaramin jefa shi cikin tsoro tayi ba. Har ya shiga wasi-wasi kodai tana da mutane ɓoye ne ko kuma da gaske ta haukace to kuwa ya zame masa dole ya lallaɓa ta don ya tsiratar da rayuwar Aunty Bahijja saboda haka ya kwantar da muryarshi a hankali kamar mai raɗa ya ce "Ki yi haƙuri Love ki yafe mata ko a haka ki ka barta taji jiki kuma na tabbata ko da kuɗi ba za ta sake shiga hurumin ki ba...
  "Ba zan haƙura ba Bilal har sai naga bayanta burina shi ne naga numfashinta ya fita daga gangar jikinta daga nan iyaso a rataye ni.
Jeeddah ta faɗa cikin hargowa a hankali Bilal ya shiga takowa har ya iso gabanta bata ankara ba yai mata kamun kazar kuku, ya cicciɓe ta da dukkan ƙarfi shi sai ihu take yi tana shusshura ƙafafuwanta "Ka sauke ni Bilal nace ka sauke ni to shikenan tun da ba za ka sauke ni ba na rantse kanka zan huce haushina.
Banza ya yi da ita sai da ya kai ta ɗayan bedroom ɗinsu ya sauke ta akan gado kafin tai wani yunkuri ya falla da gudu ya ciro key ya fita tare da saka key ɗin ya rufe ƙofar ta waje kana ya nufi ɗakin da Aunty Bahijja take wacce har ta fara gani dishi-dishi a dalili jini da ta zubar da kyar ta iya miƙewa tsaye ta buɗe ƙofa tana buɗewa ta faɗi ƙasa sumammiya. A rikice Bilal ya cicciɓe ta ya fita da ita da gudu yasa ta cikin mota ya ja ta da ƙarfi ya nufi asibiti mafi kusa, sai da aka yi mata ƙari jini a dalili ta zubar da jini ba kaɗan.
Sai da aka kammala treatment ɗinta ta sha ɗinkin kamar kwarya, kana ya nufo gida yana buɗe ƙofa Jeeddah tana zabura ta tashi da azamar ta, duk bala'i da masifa da take mishi bai kula ta ba sai da ya yi wanka ya ji shi cikin natsuwa kana ya shiga sauke mata nashi kalar rashin mutunci ya faɗi ta faɗi Saboda haka tai masifar ƙular dashi suka rabo baram-baram don har tabbatar mata ya yi da cewa idan wani abu ya sami Aunty Bahijja sai ya ɗauki mummunan mataki akanta. Yana fita kaitsaye gidan Aunty Farida ya je ya zayyane mata hali da ake ciki  lokaci da Aunty Farida ta ji iri ta'asar da Jeeddah ta aikata ba ƙaramin  gigicewa tayi ba. Saboda haka ta yanke shawara gara taje gida ta sanar da Baba abinda yake faruwa gudun kada al'amari ya yi ƙamari gara tun wuri yai wa tufkar hanci.
Har sha ɗaya dare ta gota Bilal bai dawo gida ba duk sai naji ba daɗi don na tabbata ni ce silar rashin dawowar tashi, sai kawai na shiga saƙe-saƙe idan har ba wani mummunan abu bane ya sami Aunty Bahijja, nan take na wani irin mashahurin tsoro ya lulluɓe ni, naji nadama haɗe da danasani abinda na aikata, duk da haka bana jin zan iya ɗaga waya na kira shi. Sha ɗaya da rabi tana bugawa na kashe kayan kallo na wuce bedroom na kwanta amma na ƙasa bacci.
Ta ɓangaren Bilal Shattima kuwa ƙarfe tara ya baro asibiti yayin da Hajja taci masa mutunci faɗa ta dinga yi ba na wasa ba don har cewa tayi sai ya saki Jeeddah, Bilal yana gani al'amari yana so ya ƙazanta ya baro asibiti. Kaitsaye gidan su Nusaiba ya nufa kamar dai wancan lokaci da suka sha shagalinsu a ɗakin Yayanta Sageer yau ma hakan ce ta faru a tsakaninsu, sun murji juna iya son ransu domin a wannan karo Bilal biye mata ya yi domin kafin ya taho sai da ya siye magani ƙari ƙarfi ya sha, sai da suka yi fourth round duk da haka Nusaiba bata gamsu ba so take ya ƙara mata shi kuma a lokaci ƙarfinsa ya gama ƙarewa hatta da abin nashi ya yi laushi, magani ya gama aiki duk jarabarta ba zai sake aikatuwa ba. Sai da ta jira gaba.
In takaice muku labari ranar sai ƙarfe ɗaya dare ya dawo gida, kuma har zuwa lokaci idanuwana biyu domin na kasa bacci. Yana switch on ɗin bulb haske ya gauraye ɗakin karaf idanuwanmu suka sarƙe, a hankali na bi shi da kallo yanda ya shigo min da tufafi duk squeezing a wancan rana yau ma haka ya dawo min, zan ma iya cewa na yau sun fi muni wallahi za ku zaci da kura ya yi dambe domin hatta da tazuge wandonshi ja take a ƙasa idanuwanshi sun yi masifar ja ko kaɗan ban yi tunani zai tarar dani a falke ba. Yadda ya ga ina ƙare masa kallo daga sama har ƙasa yasa shi jin wani iri ga baki ɗaya ya dabirce sai kuma ya tuna da irin ta'asar da tayi sai kawai ya haɗe rai ko kallonta bai sake yi ba
Nima tun da daga sau ɗaya da na kalleshi na kauda fuska ban kuma ce dashi uffan ba tsakanin da ALLAH ba zan ɓoye muku ba nagaji da musanya yawu da Bilal, na tabbata idan na ce zan kula shi da matuƙar wahala idan ban ɗuɗɗura masa ashar ba. Saboda haka na runtse idanuwana gam ban sake marmari kallonshi ba. Ban ma san lokaci da ya gama tsayuwar sa ya shiga bathroom sai saukar ruwa naji, don na gushewa kaina tantama abinda nake zargi sai kawai na sauko na nufi ƙofar bathroom ɗin cikin sa'a na tarar da bai rufe kofar ruff ba, na ɗan ƙara buɗe ta na leƙa ina kallonshi har ya kammala wanka sabulu kana ya fara na janaba, da sauri na baro jikin ƙofar na koma kan gado na kwanta na ja duvert na tattake cikinsa hatta da fuska ta ban barta a waje ba. Kana na shiga furzar da iska mai zafi gaske.
Bilal ya fito ɗaure da towel yayin da yake riƙe ɗan ƙaramin towel ɗin yana goge sumar kanshi, gani yanda ta lulluɓe cikin duvert yasa shi jan guntun tsaki, cikin rashin damuwa da hali da ya ganta ciki ya shirya cikin kayan baccinsa ya ɗauki pillow ya fito parlour.
Yanda naga rana haka naga dare ban runtse ba ko kaɗan, ina kammala sallar asuba har na kwanta sai naji ƙarar shigowar message a wayarshi da ya bari akan mirror, banaso duk abinda zai taƙura ni ko ya hanani bacci saboda haka na sauko na ɗauki wayar da nufi nasata silent sai idanuwana suka sauka akan message ɗin "Good morning Baby da fatar ka waye gari cikin ƙoshin lafiya ya gajiya daren jiya?" Duk da ina da tabbaci gajiya tabi jiki domin kai jarumi ne. ALLAH Baby jiya ka shayar dani daɗi marar misaltuwa ka buɗe data na turo maka da good morning pics I hope I'll enjoy it...
Kasa ƙarasa karantar message ɗin nayi a dalili wani ɗan uban jiri da ya kwashe ni, da baya-baya na dinga tafiya har sai da na kai ga gado na faɗin zaune dabass! A maimakon na ajiye baƙar waya nan sai kawai na tsinci kaina da son gani wane iri pics ne ake wa laƙabi da Good morning, already nasan code ɗin shi shiyasa kaitsaye na shiga WhatsApp ɗin shi. Bayan messages sun ta shigowa sai na ga na Nusaiba, ashe nudes pics ne ta turo mishi hannuna har wani rawa yake yi wajen buɗe hotunan na farko boobs ɗinta ne sai na biyu mai ɗauke da private parts ɗinta bansan lokaci da bakina ya furta "Wa'iyazubillah! Ashe da gaske ne akwai matan aure da ke turawa mazajensu hotunan tsiraicin su?"
Na faɗa cike da mamaki, rubutu da ke kasan video na karanta "Baby styles ɗinan irinsu nakeso mu yi anjima please don't say no.
Jikina ya yi bala'in sanyi wani irin tsoron mahalicci sammai bakwai ya shige ni, sannu a hankali na maida wayar inda na dauko ta ashe ko Baba da Babansa {lol}
Ina maida kaina jikin pillow yana shigowa abu na farko da ya fara yi shi ne daukar wayarshi, already ya shirya tsaf cikin English wears da alamu ɗayan bedroom ya shiga ya yi wanka, dama kuma muna da kayan sawa a ciki, ci kanki bai ce dani ba yana ɗaukar tsananniyar wayarshi ya fice abinsa. Zuciyata ta shiga kimtsa min yanzu can ya nufa wurinta su gwada styles ɗin da ta turo mishi, take naji wani zazzafan kishi ya lulluɓe ni, kuka nakeso yi amma na nemi hawaye na rasa ashe ko kuka rahama ne.
Zuwa yanzu gaba ɗaya naji Bilal Shattima da aurensa sun fita a kaina a yanzu banida buri da ya wuce ya rabani da ƙaddararre aurensa, domin wallahi ba zan iya zaman kishi da karuwa ba. Yoo! ALLAH na tuba miye banbamci Nusaiba da tamtagarya karuwa mai license a hannu.
Waya ta da ke karkashin pillow ringing ɗinta ya datse min tunani ni kaɗai nasan irin mugun raɗaɗi da nake ji a zuciyata shiyasa ban yi sauri ɗaukar wayar ba har ta tsinke aka sake kira jikina a mace na janye pillow na ɗauki wayar Baba ne mai kira nawa sai da gabana yai mummunar faɗuwa ina daga kira ko sallama da gaisuwata Baba bai amsa ba naji muryarshi a fusace ya ce dani "Duk abinda kike yi ki ajiye shi ki zo yanzu-yanzu nan Inaso gani ki.
Kafin nai wani yunkuri har ya katse kiran. Da na tuna danye aiki da na aikata jiya sai jikina ya ɗauki rawa, a tsorace na shiga bathroom nayi wanka wanda ba zan iya tantance ko na saka sabulu ko ban saka ba.
Ina tsoro karo da Baba domin na tabbata da wahala mu wanye lafiya, duk iskaci da iya shegena ina tsoro Babanmu tsoro kuwa ba na wasa ba.
Wallahi ko mai kasa shafawa nayi kawai dai na dauko Turkish Abaya mint green color na saka ba ko bra na yane kaina da mayafi mahadin rigar.
Tsabagen hankalina ya rabu kashi-kashi na manta inda na ajiye car key ɗina, har na haƙura da nema nayi deciding na hau adaidaita sai kawai na ganshi a parlour ajiye akan centre table, sai da na sauke zazzafar ajiyar zuciya kafin na ɗauki key ɗin. Da za ku tambaye ni yanda nayi tuƙi da wuya na iya faɗa domin kuwa ikon Rabbi ne kaɗai ya kawo ni ƙofar gidanmu.
   Ina fitowa daga mota tun kafin na maida murfi na rufe idanuwana suka yi tozali da motar Aunty Farida, nan fa na ƙara ruɗewa cikin sauri na maida murfi na rufe ashe na haɗa da rigata bansani ba, sai da na tunƙari kofar shiga gida naji anyi baya dani. A mugun tsorace na juya sam ban kawowa raina cewa rigata ce na dantse ba, sai naji kamar an shaƙe ni ne, na sake unlock ɗin motar na ciro rigar inda ALLAH ya taimake ni bata yage ba. Na sake kwasawa da sauri na shiga gida, kaitsaye parlour Babanmu nai yiwa tsinke,  turus nayi na kasa shiga parlour a dalili hango fuskar Babamu a mugun ɗaure iya sani na da Baba ban taɓa gani ya yi fuskar shanu kamar wannan ba, cikina ya yi bala'i murɗawa dama na kwana biyu ban sa mishi abinci kirki ba.
   "Shigo don ubanki ko ni na taso da kaina!
Furunci da Babanmu ya fara jifa ta dashi kenan,  ba yanda na iya dole na fara tattaki har na iso gabanshi na zube gwuiwayina ƙasa, da durƙusawa ta da saukar tafin hannun Baba akan kumatuna kusan a tare suka faru....

*Mu haɗu a shafi na gaba*

_please don't forget to share and comments on_

#Jeeddah Aliyu
#Team Zazzafan kishi.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now