032

106 10 2
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

032...

Sai dambe nake da numfashina tsawon rayuwata ban taɓa shiga tashin hankali kai har ma da takaici da zallar baƙin makamancin wannan ranar ba. Ban san sanda na ɗora hannu aka na kurma gigitatcen ihu na zube gwuiwayina kan tiles sai rizgar kuka nake yi a yanzu ba wai ina kuka ne saboda ɓata gwal ɗin ba ina kuka ne a dalili wai mijina ne zai min sata, wannan masifar da kayan takaici ya yi min yawa zuciyata ba za ta iya ɗauka ba. Mommy Turai ta dafa kafaɗarta cikin sigar so haifar min da natsuwa take faɗin "Kukan nan ya isa haka Jeeddah kada ki ja wa kanki wani ciwo na daban, mu shiga uku. in-sha-Allah duk gidan uban da ya kai miki gwal ɗinki za mu tusa ƙeyarsa gaba ya karɓo miki kayanki, ɗan iska Yaro maƙetaci tsohon azzalumi wallahi idan bai fito da sarƙa nan cikin sauƙi ba hukuma ce za ta raba mu dashi.
Ina ji maganganu da ke fitowa daga bakin Mommy Turai na sake fashewa da kuka.
Gaba ɗayansu suka saka ni a gaba sai aikin rarrashina suke yi da kyar na yi shiru amma wallahi can ƙasar zuciyata har yanzu kololo nan da nake ji yana nan ba inda ya tafi.
A gajiye likis su Bilal suka dawo gida suna shigowa a matuƙar fusace Hajja ta nufi ɓangaren Hajiya Bintu duk ƙoƙari Bilal na gani ya dakatar da ita amma abin ya ci turu tana gaba Aunty Bahijja na bin ta a baya cikin sa'a suka tadda Hajiya Bintu zaune a parlour ta Hajja tana zuwa ta soma zuba mata ruwan tijara "To baƙar munafuka algunguma wacce ƙarshenta ba zai yi kyau ba duk abinda ki ka daɗe kina shuka wa yau ALLAH ya toni asirinki wallahi Bintu da matuƙar wahala ki ji ƙamshin aljanna. Me na tare miki ni da 'ya'yana da za ki tarwatsa mana rayuwa?"
Kin shiga kin fita gidan bokaye kin yi nasarar raba tsakanina da ɗana Faruk, ki hanawa Bilal ya sami aiki yi, ki taɓa lafiyar mijin Bahijja shin wannan kishin naki wane iri kishi ne shi? Ko a tarihin jahiliyya ban taɓa cin karo da labari kishi kwatankwacin naki ba, to wallahi-azim ba zan kyale ki ba yadda kika tarwatsa mana rayuwa nima sai na tarwatsa miki taki, muguwar mata wacce babu ALLAH da Manzonsa a zuciyarta..
Jikin Hajiya Bintu ya ɗauki rawa ta miƙe tsaye ta fuskanci Hajja fuskarta babu alamar nadama, sai ma hayyaƙo wa Hajja da ta yi tana faɗin "Ke dakata Hajja! Ke har kina da baki yi min gori bin bokaye bayan a gunki na koya, ko kin manta badaƙalarki ta baya ne na tuna miki? Ke har kina tsammani na ƙauna ce ki ke da 'ya'yanki ai har gaba da abada ba zan so ku ba kuma zan so ci-gabanku ba. Ke kin manta da lokaci da Alhaji yana da rai irin mulki-mallaka da kika shimfiɗa to ai mutuwa ce kawai tai wa Alhaji sauri da wallahi ya yi jinkiri mai yawa da sai kin raina kanki sai kin gwammace ki kasancewar cikin kushewarki da zaman ki duniya.
"Amma Bintu duk mugun zama da muka yi a can baya ai yaci a ce mun manta dashi domin wanda muke kishin akanshi ya mutu baya duniya to miye amfani kishin mutumin da ke cikin kabari?" Kawai dai hasada ce ke ɗawainiya dake Kuma in-sha-Allah kin dinga gani yadda ba ki so kenan, kuma duk mugun nufinki akanki zai ƙare.
Hajiya Bintu tayi ihu gami da shewa kana ta tafa hannuwa ta kalle Hajja a wulaƙance ta ce "Ai Hajja zaman kishi yanzu muka fara ba dai kin yi nasarar haƙo wannan asiri ba to ki jira zuwan na gaba.
  A fusace Bahijja ta kalle Hajiya Bintu tana faɗin "Wallahi Hajiya kin yi asara kuma in-sha-Allah ƙarshen makirci ki ya zo wancan ma da kika yi nasara ki sa aranki bashi kika ci kowa da kike gani mugun kansa sai dai in ya so a zauna lafiya tun da kika nemi bala'i da masifa da kuɗinki to ki sani kin tara kin samu, ba dai kika ƙarshen mu a gidanan ba sai dai mu mu ga ƙarshen ki la'anana kawai.
   Aunty Bahijja ta ƙarashe magana tana huci kamar wata kububbuwa. Hajiya Bintu ta kalle gami da taɓe baki ta ce "Ke Bahijja dawo cikin hankalinki ki san da wacce kike magana ko uwarki ta buga dani ta barni balle ke ƙaramin alhaki, maza ku tattara ku ɓace min da gani tarkace banza 'yan wahala.
  "Ga ki nan muguwar 'yar wahala ma da farko naso a kashe maganar nan amma tun da kika nuna mana ke tantiriya ce ba ki gudun abin kunya to kotu ce za ta raba mu dake in-sha-Allah sai kin girbi abinda kika shuka, ku zo mu tafi Hajja za ta ga abinda zai biyo baya.
Bilal Shattima ya faɗa yana wani zare ido, daga haka suka fito kowanne su rai ɓace.
Duk yadda Jeeddah taso abi al'amari a tsanake amma su Mama sun ƙi su saurare ta, musanman Ya Kabeer da Mommy Turai sun fi kowa ɗaukar lamarin da zafi, don kuwa Ya Kabeer har rantsuwa ya yi ba inda zai tafi har sai Bilal ya dawo ya same shi a gidan, har aka yi sallar azhar yana gidan.
Da taimakon Aunty Farida da Khairat suka gyarawa Jeeddah ɗakinta da ta wargaza.
Bilal ya kalle Hajja yana faɗin "Hajja ki kwantar da hankalinki in-sha-Allah kamar yadda Malam ya faɗa kwana nan za ki ga Ya Faruk ya zo kuma Dan ALLAH kada ki sake kula wancan jakar matar ki jira har mu ga Ya Faruk ya dawo ainihin natsuwarsa sai mu ɗauki duk mataki da ya dace. Ke kuma Aunty Bahijja ki ɗage da ba Haruna maganganu da Malam ya ba ki shima da yarda ubangiji zai sami sauƙi. Ni zan wuce gida don wallahi wata muguwar yunwa nake ji.
Ya ƙarashe magana tare da miƙewa tsaye Hajja ta kalle shi tana faɗin "Gara ka tafi gida ka sami abin taɓa wa domin gidanan tashin hankali bar barmu mun girka komai ba.
"ALLAH yasa gantalalliyar matarsa ta girka dashi naga yanzu taƙamar rashin mutumci take duk da Malam Alti ya ce ita ma an shiga tsakaninta da Bilal. Amma wallahi rashin mutumci Jeeddah a jini jikinta yake asiri kwabai sa kawai yasa.
Aunty Bahijja ta faɗa tana wani yatsine fuska.
Haɗe fuska Bilal Shattima ya yi domin sosai ya ji zafin maganar da Bahijja tai akan Jeeddarsa "bana jin daɗi irin yadda kike faɗar kowacce magana ta fito daga bakinki akan matata Aunty Bahijja Dan ALLAH ki daina wallahi yana ɗaya cikin dalillai da yasa Jeeddah bata girmama ki.
Bilal ya ƙarashe magana yana mai ƙara tanke fuskarshi.
   Kallon uku saura Kwabo Aunty Bahijja ta watsa mishi gami da taɓe baki tana faɗi "Ai kai Jeeddar nan ta ri ga ta wanke ta ba ka ka shanye shiyasa sam ba ka gani aibunta.
Ba tare da ya tanka mata ba ya juye a fusace ya fita, ta ƙara bi shi da zafafan maganganu duk akan Jeeddah, yana fita ya tare adaidaita ya nufo gida yana tafe yana zabga addu'a a zuciyarshi ALLAH yasa girkin da Jeeddah tayi ta musu farfesu kaji domin jiya ya ga lokaci da Baba ya aiko yaronshi na kasuwa Abdul ya kawo mata figaggu kaji aƙalla za su kai biyar zuwa bakwai, da kwaɗayi su ya tashi ɓata mishi rai da tayi shi ya hana ya faɗa mata ta zaɓarɓaka mishi su. Shiyasa yanzu yake ta faman zuba addu'a. Suna shigowa layin gidansa ya ji wani mugun faɗuwar gaba, har sai da ya furta "innalillahi wa'inna illahim raji'un! Tun daga nesa ya hango motoci 'yan gidansu Jeeddah ai kuwa faɗuwar gabansa ya tsananta ko kusa bai kawowa zuciyarsa gwal ɗin da ya sata ne ya kawo su ba domin yana da yaƙini akan Jeeddah bata so saka necklace, kafin ta ankara da ɓanar da yai mata an ɗauki dogon lokaci. Sai kawai ya shiga wasi-wasi meke faruwa da 'yan uwan Jeeddah da za su cika masa gida, musanman da ya ga hadda motar Ya Kabeer da motar Mommy Turai, wata zuciya ta ce dashi ko Jeeddah ce ba lafiya har adaidaita ya sauke shi gabanshi bai fasa faɗuwa ba. Ko canji shi bai tsaya amsa ba ya kwasa da mugun sauri ko gabanshi baya gani garin sauri yaci ɗan uban tuntube da dutse saura kaɗan ya faɗin sai da ya gurje da ɗan yatsan shi har da jini ya yi amma hakan bai dame shi ba muradinsa ya isa cikin gida, jikinsa yana rawa ya tura ƙofar parlour. Suna zaune jigun-jigun kowanne su fuska ba annuri kamar waɗanda ke zaman makoki. A lokaci ɗaya suka kallo shi, kowanne su da yana yi mugun kallo da yake aika masa, nan take ya ji wani iri tsoro ya lulluɓe shi musamman da yai arba da Jeeddah yaga yadda idanuwanta suka koma alamar tasha kuka ta ƙoshi. "Shin meke faruwa a wannan gidan ga dai Jeeddah na ganta cikin ƙoshin lafiya ga kuma Aiman yana wasar shi da Ball?"
Bilal ya faɗa a zuciyarshi ashe bai san cewa tambayar tashi ta fito fili ba sai da ya ga Ya Kabeer ya taso a mugun fusace ya nufo shi yana faɗin "Idonka kenan tsohon ɓarawo to ai tsayuwa za ka yi ba kana tambayar kanka da kanka mune ya dace ka tambaya mu ba ka amsa, ai sai ka shigo domin tsayuwa bata gano ka ba ka fayyace mana ina ka kai wa Jeeddah gold necklace ɗinta da ka sata.
  Saura kiriss numfashin Bilal Shattima ya fita daga gangar jikinsa maganar ta zo masa a bazata ba a yanzu ya shiryawa zuwan ta ba. Sai gashi ta zo mishi a kwatsam! Babu shiri.
Ya haɗiye wasu busassu miyau marasa ɗanɗano a maƙogwaro. Cikin firgici da fitar hankali ya shiga ja da baya-baya a nufinshi ya cikawa wandon shi iska, sai dai kafin ya kai ga cimma manufarsa Ya Kabeer ya daka tsalle ya damƙe hannunshi, kamar makaho da ɗan jagora haka Ya Kabeer ya jawo shi izuwa tsakiyar parlour, Mommy Turai tai zubur ta miƙe tsaye ta shiga yi mishi ƙasƙantatce kallo kafin ta shiga tafa hannuwa tana faɗin "Sannu da zuwa ɓarawo tun ɗazu muke tsumaye zuwanka, finally sai ga shi ka zo. Sai ka samu damar ɗauko wa baiwar ALLAH nan sarƙata tun kafin mu yi maka yekuwa duk da bana tunani hakan zai taɓa ka tun da dama can an saba da 'yan dauke-dauke.
Gani yadda mommy take gaggaya wa Love maganganu marasa daɗi yasa ni miƙewa da sauri na nufo gunta, cikin kwantar murya nake faɗin.
"Mommy Dan ALLAH ku yi masa a hankali wallahi Love ba ɓarawo bane ni har yanzu ban gamsu da da hujjojin da Ya Kabeer ya faɗa ba wallahi love ba zai min sata ba ni fa matarsa ce abin ikonsa...
Tun kafin na ƙarashe magana Mommy Turai ta daka min gigitatciyar tsawa, har na zaci gwaɗa min mari za ta yi.
"Rufe mana baki Dan ubanki Jeeddah, ka ji min sakarci banza da wofi, mutumin da ya raba ki da kaddararki ya saka ki kuka tun safe zuwa Yanzu shine don tsabagen lalacewa you still call him love kai kuma wai har kina ƙoƙari kare shi wannan dakarci da yawa yake, wai Dan ALLAH Dan Annabi Bilal ka faɗa min gaskiya ba ka yi wa 'yar nan asiri ba?"
Tun sanda Bilal ya sadda kai ƙasa, bai sake ɗagowa ba, wata irin mashahuriyar kunya da danasani ne suka lulluɓe shi a lokaci guda. Da za ki tambaye shi a lokaci tabbas da zai iya cewa yau ce rana mafi muni a rayuwarshi. Kuma duk maganganu da iyayen Jeeddah da 'yan uwanta suka faɗa akanshi bai ji zafi ba bai kuma ga laifinsu ba. Ya cancanci fiye da hakan domin son zuciyarshi ne ya kai shi da hakan.
Duk da ni Bilal ya yi wa katoton laifi amma na rasa dalili da yasa nake jin zafi cin mutuncin ake masa, nake kuma ƙoƙari na kare shi na kasa jure zagin da ake masa sai kawai nasa kuka Aunty Farida ta taso cikin fusata ta rizgo ni tamkar za ta ƙarya min hannu, tana faɗin "Idan ba ki rufe mana baki ba sai nayi ƙassa-ƙassa dake a nan wuri.
"Kyaleta kawai Farida tun bata so a kwata mata hakkinta ga ta nan ga shi ba dai Bilal ba wallahi sai ya sa ki kukan da za ki rasa hawaye zubarwa.
Mama ta faɗa cike da takaincina.
Ya Kabeer ya ƙarbe zance yana faɗin "Bata isa ba wallahi Mama tun da ta kiramu dolensa sai ya fito da gwal ɗinan walau ta daɗin rai ko akasin haka, saboda haka Jeeddah ki ja bakinki ki tsuke idan kika kuskura ki ka ƙara sa mana baki a magana na rantse da ALLAH sai na tattaka ki.
Ina jin yadda Ya Kabeer ya ƙarashe magana na koma wurin zamana na faɗa bisa kujera gami da kifa kaina a hannu kujera na buɗe sabon babi kuka, duk irin zagi da cin mutuncin da suke wa Bilal ko kwakwaran motsi ya kasa yi balle na sa ran zai kara kanshi. Hakan ya ƙara tunzira Ya Kabeer ya ce "A karo na ƙarshe Bilal ina mai gargaɗinka da ka faɗa min ina gwal ɗin ƙanwata idan ba ka buɗe baki ka bani gamsasshiyar amsa ba wallahi-tallahi zan haɗa ka da hukuma.
Bilal Shattima yana jin Ya Kabeer ya ambaci hukuma ya ciro kanshi da sauri ya kalle shi da idanuwanshi da tuni suka sauya colour, tamkar zai fashe da kuka yake faɗin "Dan ALLAH Dan sonka da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam Ya Kabeer ka rufa min asiri kada maganar nan tafita, domin ita ta fita wallahi mutumcina da ƙima ta za su zube a idon jama'a.
  "Ai ni na fi so duniya ta gama sani kai mugun miji ne azzalumi, ban da zalunci miyasa za ka ɗauke mata gwal ba tare da saninta ba, ko kuma kana nufi ka ce dani bakasan cewa ɗaukar kayan mutum ba tare da sani mai shi ba sata ne koda kuwa kana kyakkyawan kusanci dashi?"
Zuwa lokaci Bilal Shattima ido ya rena fata ba don ya kasance namiji mai taurin zuciya ba da tuni ya fara ambaliyar hawaye, cikin kwantar da murya ya sake cewa.
"Na sani Ya Kabeer amma wallahi banida mafita a lokaci kuma ina tunani idan na faɗa mata ba lallai ta amince da buƙata ta ba. Kuma na ɗauki gwal ɗin ne da zimmar aro idan ALLAH yasa na sami aiki sai na biya ta wallahi bana nufi na cuce ta ALLAH shi ne shaida ta akan hakan.
Ya ƙarashe magana kamar zai fashe da kuka.
  Mama ta ja guntun tsaki cike da takaici ta ce "kana nufi ka sayar da gwal ɗin to me ka yi da kuɗin?"
Tirya-tirya ya zayyane masu yadda ya sayar da gwal ɗin da yadda ya yi da kuɗin. Gaba ɗaya suka ɗauki salati, ban da ni domin tuni na gano abinda ya yi da kuɗin da kuma tun farko nasan shi ya ɗauki gwal ɗin da ba zan sanar a gidanmu ba. Zan ja bakina nayi shiru gudun kada mutumcin mijina ya zube amma aikin gama ya gama masu iya magana suka ce rashin sani yafi dare duhu, takaicina ɗaya miyasa da ba zai tambaye ni ba ai ko don albarkaci ƙauna da ke tsananina da A'isha Shattima zan iya bashi gwal ɗin.
Wulaƙanci da ƙasƙanci ba irin wanda ba su yi masa ba zagi kala daban daban, hatta da Khairat da ke matsayin ƙanwata ina ji ina gani tana yaɓawa mijina maganar banza sai dai banida yadda zan yi domin shi janyo wa kansa. Duk yadda ake wulaƙanta ɗan adam a tozarta shi Bilal Shattima ya yi min naji kunya naji baƙin ciki, na kuma ji takaici da ya kasance shine mijin da nake aure. A takaice ba zan iya misalta muku irin baƙin ciki da na shiga ba sai dai kawai nace da ku kwatanta kanku a matsayina shin ya za ku ji idan aka ce mijinki shine ɓarawo ki wanne mataki za ki iya ɗauka?" Ba zan ɓoye muku ba wallahi sai na ji duk na tsani ganinsa, hakan yasa na tashi a mugun fusace na shiga ɗaki na ɗauko hijabina da wayata na fito, na kalle Khairat cikin ɗusasshiyar muryata nace "Khairat tashi mu tafi banaso na ƙara daidai da second ɗaya ina kallon fuskar mutumin nan wallahi zuciyata za ta iya bugawa.
Kafin Khairat ta miƙe Bilal ya riƙo hannuna cikin zallar tashin hankali yake faɗin "Dan girman ALLAH Love ki yi haƙuri kada ki guje ni saboda wannan abun, wallahi-tallahi zan shiga na fita koda zan rasa raina na dawo miki da gwal ɗinki ki bani dama dan ALLAH.
A fusace na fizge hannuna cikin muryar kuka nake faɗin "miyasa Bilal miyasa ba za ka tambaye ni a lokaci da ka shiga matsala na ba ka gwal ɗin da hannuna shin kana gani ba zan bane shiyasa ka sata?
"Saboda ina tunani ba za ki bani ba Jeeddah shiyasa na ara ba sata nayi ba m amma wallahi zan dawo miki dashi.
"Ka ri ga da ka makaro Bilal domin na bar ka bari na har abada ba wai don saboda gwal ɗina ba. Zan bar ka ne a dalili sata da kayi saboda haka ka sa aranka ka rasa ni domin ba zan iya ci-gaba da zama da ɓarawo ba.
Ina ƙarasa faɗa haka na juya da sauri Khairat ta biyo ni a baya Bilal yana ƙoƙarin ya bita Ya Kabeer ya cafko shi ya dawo dashi ya fito da waya daga aljihunshi ya kira Asp Saddam wanda ya kasance classmate ɗinshi ne, duk haƙuri da Bilal Shattima yake bashi hakan bai hana shi haɗa shi da jami'an tsaro ba. Yayin da house neighbours ɗinshi suka firfito daga apartment ɗinsu suna kallo tare da kus-kus a tsakaninsu...

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now