11...

80 10 0
                                    

*💥 ZAZZAFAN KISHI...!*
       _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

011...

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajarsu cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

Naceba🙋‍♀️
Kina bukatan jikinki yazama so fresh ba kwarzane ko daya ballantana kuraje ko tabo, sunburn,acne, ko knuckles? Kije kigwada products na mg's insha Allah zakiga ynd fatarki zedawo fiye da tsammaninki zakigyara jikinki naturally batare da kinbata fatarki ba jikinki yayi fresh kiyi smooth kizama kalar Madara kirar models kiringa walwali kina haskawa duk inda kikayi😍
Kidena kokonto cewa kingwada baki Dace ba insha Allah kijaraba products dinsu bi'iznillah zakiji dadinshi🙏 kayansu akwai kamshi especially sabulun kamshin yakama jikinki ko kindade da wanka jikinki zaidinga fidda ni'imtaccen kamshi bayinki ma zakiji kamshin dazai Kama😍sunada kit special domin amare Wanda indai kinyi using kit dinnan Baki bukatar kikara Kai kudinki gurin dilke domin ainihin yanda fatarki zehaska yagoge kidinga shining abun sewanda yagani😍

Mai bukatar kayan mg's chat:08062991549,07046881166,07067210195
Call:08064532391
Hausawa nacewa adade anayi sai gaskiya Kuma siyan nagari maida kudi gida🤝
💯 tested nd trusted
Natural/organic🥰
Akwai discount a medium kit

Medium kit
Normal price 17k
Now 15k

Babban kit 20k
Now 18k

Valid for only 2days


Yadda yaga Daddy yana huci idan har bai yi gaggawa taka mishi birki ba, to kuwa gaba ɗaya komai za ƙara dagule wa, dauriya yasa ta hanyar faɗin "Daddy Dan Allah ka yi shiru ya isa haka koda Baba ya tilastawa Jeeddah ta aureni kasani bai isa ya tilasta mata ta so ni ba. Daddy duk aure da za a yi shi babu soyayya haƙiƙa ɓaci rai ne zai biyo baya a hali yanzu koda Baba ya amince da aura min ita a dole ni ba zan aure ta ba domin ko na aureta gangar jikinta kawai na aura zuciyarta na can ga wani. Saboda haka daga yau mai kama da rana ta yau na haƙura da Jeeddah kuma duk wani mai ƙaunata kada ya ƙunlaceta ko kuma Baba kawai inaso ku tayani da addu'a Allah ya cire min sonta a zuciya.
Ya ƙarashe magana cikin rauni murya da karaya zuciya ga kuma idanuwanshi da suka ciciko da hawaye, duk wanda ke ciki parlour sai da jikinshi yai sanyi babu kamar Baba da yake ji a can ƙasan zuciyarshi kamar bai yi wa Haidar adalci ba, wani ɓangare na zuciyarsa kuma ya ke gani hakan da ka yi shine daidai.
  A fusace Daddy ya kama hannu Haidar ya ɗaga shi ya tashi kana ya juya gefen da su Alhaji Bashir suke ya ce "Ku tashi mu tafi Alhaji Bashir don banga amfani ci-gaba zaman mu a parlour nan ba.
   Yana gama magana ya ja Haidar suka nufi ƙofar fita Alhaji Bashir da Alhaji Ahmed suka mara masa baya yayin da Alhaji Usman maishadda bai yi yunkurin hana su tafiya ba. Saboda yasan ko ya tsayar da su ba lallai bane su tsaya su  fahimci juna ba. Hajiya Turai ta kalli Baba tana kuka ta ce "Haba Yaya yanzu shikenan ka hanawa Haidar auren Jeeddah kana gani hakan da ka yi ka kyauta kenan?"
"Ki yi haƙuri Hauwa domin duk abinda zan faɗa a yanzu ba za ki fahimta ba saboda ranki a ɓace yake, idan kun huce ke da mijinki zan zo har gida na same ku.
   "Huhmm...ni kan ban taɓa gani idan gida bai ƙoshi ba aka kai dawa, ba amma ba komai Allah na nan.
Daga haka ta juya ta nufi ƙofar fita tana sharar hawaye da gefen mayafinta. Mama ta biyo ta har gate tana ƙara bata haƙuri.
Kasa komawa bacci Bilal Shattima ya yi yasaka farar jallabiya ya nufi ɓangaren Hajja, zaune a parlour ya tarar da ita tana jan casbi ransa a jagule ya zauna kusa da ita yana so ya faɗa mata abinda ya kawo shi sai dai ya rasa ta ina zai fara, sai nushin tafin hannunshi yake yi gami fesar da iska daga bakinsa. Hajja ta kalli shi gami da faɗin "Ya aka yi ne Bilalu naga sai faman nushin tafin hannu ka ke yi da matsala ne?"
"Huhmm... matsaloli za ki ce Hajja domin ba guda ɗaya bace.
Bilal ya faɗa tamkar zai fashe da kuka duk ya dawo wani abin tausayi.
  "Tou.....ina jinka faɗa min menene matsalolin naka Allah dai yasa ba zance interview ɗin ne aka soke ba?"
   Sai da ya sauke ƙarfaffiyar ajiyar zuciya kafin ya shiga zayyane mata yadda ya yi da Jeeddah hatta da kuɗi adashe da ta ce za ta bashi bai ɓoye mata ba.
Har ya dasa aya Hajja ba ta katseshi ba, ba ta kuma furta uffan ba sai jinjina kai kawai take yi. Bilal yana gani Hajja ta ɗauki lokaci bata yi magana ba ya sake cewa "Hajja kin yi shiru ba ki ce komai ba?"
Sauke numfashi Hajja tayi gami da aje casbinta akan hannu kujerar da take zaune akai, kana ta tattara dukkanin natsuwa da hankalinta ga Bilal ta ce "Dole ka ji nayi shiru Bilal al'amari ne ya zo min wani iri azahirin gaskiya ni kaina ina da buƙatar naga ka yi aure, sai dai bani da yadda zan yi saboda ba ka da aiki yi aure kuma ko a Addinan ce ba zai yu ba sai da ci da sha da saura buƙatotin rayuwa. Shiyasa ka ga tsawon wannan lokaci ban taɓa tuntubar ka akan zance aure ba. Sai kuma gashi yau ka zo min da wannan zance, Bilal nasan kana so Jeeddah matuƙar so hakazalika ita ma tana sonka duk mace da za ta so ka ba za kai ta ba. Ni kaina ina sonka da ita burina ta zama uwar jikokina, sai dai ina fargabar iri wannan zance da ka zo min dashi.
Sassauta murya Bilal ya yi duk ya bi ya narkewa Hajja ya dawo abin tausayi "Hajja Dan Allah kada ki ce a'a domin ƙi amincewarki yana nufin na rasa Jeeddah tun da har kika ga mahaifinta ya zo da wannan tsari to haƙiƙa ya gaji da jirana so yake ya aurar da 'yarsa. Kuma wallahi Hajja Jeeddah tana da ɗimbin masoya kawai dai Allah ne ya zuba mata ƙaunata, yanzu haka akwai ɗa ƙanwar Babanta da ke mahaukacin sonta gashi kyakkyawar ajin farko ga kuma dukiya mai tari yawa amma ta nace sai ni ɗin take so. Ko don wannan hallaci da tai min bai kamata na barta ba goyon bayanki haɗi da addu'ar ki kawai nakeso Hajja.
Hatta da alƙawarin kuɗi da tai mishi ya faɗawa Hajja bai ɓoye mata komai ba.
   Shiru Hajja tayi sai jinjina kai take yi bayan dogon nazari da tayi taga babu wata mafita da ta wuce ta amince domin ko ba komai Jeeddah tai musu hallaci ba kaɗan ba, ko a watanni baya da tai rashin lafiya da kuɗinta aka yi jinyarta a asibiti duk wasu hidindimo ita ce ta dinga yi kama daga kuɗin gado har zuwa kuɗin magunguna har aka yi discharge ɗinta.
"Shikenan Bilal na amince sai ka yi ƙoƙari ka je ka sanarda Baffanka Rabi'u sai ya sanarda saura ,'yan uwansa ranar juma'a sai su je gidansu Jeeddah ɗin Allah ya sanya alkhairi Allah ya ba ka ikon riƙe ta da gaskiya da amana. Sai ka yi ƙoƙari ka kira kawunka Dauda ya kama ɗaya daga cikin shanu uku da suka yi min saura ya siyar raguwar biyu abarma A'isha idan lokaci aureta ya yi sai ayi mata amfani dasu.
Ka ga sai mu ganganɗa a haɗa maka lefe daidai na talaka mai ƙaramin ƙarfi, ba zai yu ba ace ko ɗan lefe mu kasa yi mata tun da ba a kanmu babu ta yanke cibi ba.
  Sosai Bilal ya cika da murna sai godiya yake zubawa Hajja.
Tun lokaci da Haidar suka baro gidansu Jeeddah Daddy da mommy suka zaunar dashi su na rarrashiinsa a zahiri ya nuna masu ba komai amma a baɗili shi kaɗai yasan yadda yake ji   kafin ya miƙe ya wuce ɗakinshi ya ci kuka tamkar wanda ya rasa uwa da uba a lokaci guda  sai da yaci kukanshi ya ƙoshi kana ya hau gado ya kwanta sai faman juyi yake yi alamun ciwonshi naso tashi da kyar ya ja jikinsa ya buɗe bedside drawer inda magungunanshi suke ɗauka ya sha amma bai fasa jin nauyi da zafi a zuciyarsa ba. So yake ya yakice son Jeeddah ko ta ƙarfin tsiya ne. Bayaso ko kaɗan ciwonshi ya tashi saboda ita shiyasa yake ƙoƙari ya danne abinda yake ji musanman yadda ya ga iyayenshi sun ɗaga hankalinsu. Duk lokaci ya tuna da shikenan ya rasa Jeeddah sai ya ji ciwon da yake ji a zuciyarsa ya daɗa ƙaruwa ashe haka rabuwa da masoyi yake da zafi da ciwo da ya fahimci damuwa ba inda za ta kai shi face ta ƙara jefa shi ciki mayuwaci hali, ya tashi da kyar jiri na ɗibar shi ya shiga bathroom ya yi wanka koda ya fito ana kiran sallar Azhar ya shirya cikin ƙanana kaya cike da ƙarfin hali da so ɓoye hali da yake ciki ya ɗauki key ɗin motarsa sai da ya tsaya a masallaci da ke kofar gidansu ya yi sallah kana wuce ma'aikatar su abokinsa Shariff Yusuf Barade shi kaɗai ne aboki da yake iya gayawa  damuwarsa, ya kuma ba shi shawara.
  Kamar yadda Bilal Shattima ya saba zuwa picking ɗin Jeeddah yana zaune a inda ya saba zaman jira fitowarta tun daga nesa ta hango shi ta shiga zuba murmushi.
Akan hanyarsu ta zuwa gida yake bata labari yanda ya yi da Hajja sosai Jeeddah ta shiga murna farin cikinta ya kasa ɓoyuwa, cike da nishaɗi da walwala ta shigo gida as usual ta fara leƙawa parlourn Mama tai mata barka da gida ta amsa ba yabo ba fallasa kana ta wuce ɗakinsu, ɗauke da sallama Khairat da ke tsaye gaban dressing mirror tana gyara gashinta ta amsa mata adaƙile, ta kalleta sau ɗaya ta watsar gami da taɓe baki. Sosai hakan ya ɓatawa Jeeddah rai kasancewar tasan haushinta Khairat ke ji shiyasa bata kula ta ba infact tana cikin farin ciki ba za ta yi sake a gauraya mata shi da ɓaci rai ba.
   Kayan jikinta ta cire ta ɗora towel ta nufi bathroom, tana shiga taga babu ruwa a famfo mamaki ya kamata ta fito tana faɗin "Khairat ya aka yi yau babu ruwa a bathroom ɗinmu?"
  Ba tare da Khairat ta kalleta ba ta amsa da cewa "uhmm! Ta nufi wardrobe ɗinsu ta dubin kayan da za ta saka, ran Jeeddah ya sosu cikin fusata ta ce "kamar ya uhmm ba ki da bakinki ne da ba za ki buɗe baki ki amsa min ba ko asarar yi min magana kike yi?"
   "Tabbas ba ki faɗi ƙarya ba Jeeddah asarar yi miki magana nake yi, ba amfani magana da ke sai ma tarin takaici da abin haushi, ai ke yanzu ba wanda ya isa ya faɗa miki ki ji duk abinda ranki ke so shi kike yi Mama tana cikin ɓacin rai abinda kika yi wa Haidar amma ke ko a jikinki, na rasa kalar zuciyar da ke darshe a ƙirjinki?"
    "Duk abinda za ki faɗa wallahi ko a jikina, ni dai ke zaman aure nan ba wani ba saboda haka abarni da zaɓina mana.
   "Ka ji sakarci kou? Ke nan har alfahari kike yi da zaɓen wanda bai da sana'ar yi, to bari ki ji ba za ki san kin tafka gundumemen kuskure ba sai an zarga miki igiyar aure Bilal wallahi a lokaci za ki gano shayi ruwa ne.
  "Mugun fata kike yi min to a kanki zai ƙare ni da Bilal Shattima mutu karaba takalmin kaza, sai dai mahassada su rungume sorry.
Jeeddah ta ƙarashe magana tana gallawa Khairat muguwar harara.
Girgiza kai Khairat tayi tana taɓe baki, ba ta sake kulata ba domin ta fahimci al-amarinta sai du'a'i ta ri ga da tayi nisa bata jin kira, saboda haka tasaka kayanta ta bar mata ɗakin yayin da Jeeddah ta ci-gaba da faɗar baƙaƙen maganganunta.
  Tun shigowarsa Office ɗin SY Barade ya kifa kansa a kan desk ya kasa furta kalma ko ɗaya daga bakinsa sai faman sauke ajiyar zuciya yake, yanayi da SY Barade ya gansa a ciki ya tabbatar mishi da babu lafiya domin tsawon zamanshi dashi bai taɓa ganinsa a cikin mugu tashin hankali iri wannan ba. Gashi tun shigowarsa yake fama dashi da ya faɗa masa damuwarsa amma yaƙi magana, sosai hakan ya tashi hankali SY Barade.
  "Please Ka'oje ka yi min magana mana infact miye amfani zuwanka Office ɗina indan kasa ba za ka faɗa min damuwarka ba?"
  Da kyar ya ciro kanshi ya watsa rinannu idanuwanshi akan fuskar SY Barade da ke tsaye a gefen hagunsa, cikin raunin murya ya ce "SY na rasa ta shikenan wani za ta aura ba ni ba dan Allah ka faɗa min mi zan yi da zai cire min sonta kwata-kwata daga zuciyata?"
Cike da firgici SY Barade ya dafa shoulder Haidar Ka'oje muryarsa tana rawa ya furta
  "Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Ba dai kana nufin Jeeddah ba?"
  "Ita ce SY na bi kowace hanya da za ta aminta ta aure ni amma ta ƙi a takaice dai yau mahaifinta ya fito fili ya faɗa min na haƙura da ita domin wanda take so zai aura mata.
Ya ƙarashe magana muryarsa na rawa tamkar zai fashe da kuka.
"Calm down abokina duk abinda ya yi zafi maganinsa Allah, dama nasan hakan sai ta faru da kai shiyasa tuntuni nake ba ka shawara ka rabuda ita tun da ta nuna bata sonka amma ka kafe sai kace ita kaɗai ce mace da tai saura a duniya.
  "Ba kasan yadda son yake ba shiyasa kake gani rabuwa da Jeeddah zai zo min da sauƙi.
Muguwar harara SY Barade ya watsa masa tare da jan guntun tsaki "mtsss...kai ba ka isa kace bansan so ba kawai dai nawa da naka akwai banbanci, domin ni inaso ana sona saɓani kai ke so ba a sonka kuma ka bi ka maƙale mata ai dole ta wulaƙanta ka.
   "Haka ma za ka faɗa SY a maimakon ka tausaya min sai ƙara gasa min maganganu masu zafi kake yi, domin ina da yaƙini za ka kwantar min da hankali shiyasa na zo gunka.
  Ajiyar zuciya SY Barade ya yi kana zauna akan kujerar da ke kallon Haidar ya sassauta murya ya ce "Ban san me yasa ba za ka goge babin Jeeddah a zuciyarka ba?" Ga mata nan wanda suka fi ta birjik kamar jamfa a jos sai ka zaɓa ka darje na rasa me ka gani a jikin Jeeddah da yasa ka maƙale mata har haka sai kwara kanka take yi kamar kwallo a raga?"
   "Ba za ka gane ba ko na faɗa SY saboda tun farko ba ka sonta.
Haidar ya yi magana yana kwantar da murya.
Girgiza kai SY Barade ya yi cike da jin mugun haushin Haidar ya ce "Ba sonta bane ba na yo Ka'oje tsanar da take nuna maka yasa na ji ta fice min a rai, duk mutumin da zai wulaƙanta ka Haidar koma waye shi ba za mu taɓa shan Inuwa ɗaya dashi ba.
   "I know my friend kawai ni yanzu shawara nakeso ka bani yanda zan cire ta a zuciyata na manta da na taɓa sonta so nake nayi rayuwa farin ciki kamar kowa, domin ba abinda na tsinta a cikin soyayya face baƙin ciki da ƙunar zuciya.
   "Gaskiya kam abokina gara ka yi gaggawa fitar da ita daga zuciyarka, saboda nan da ɗan wani lokaci ta zama mallakin wani. Yanzu shawara ɗaya ce da nake gani za ta sa ka manta da Jeeddah duk da mantawa da ita faratt ɗaya ba abu bane mai sauƙi kawai ka shirya kafin aurenta ka bar ƙasar nan ina gani hakan zai sa ka shafe babinta.
   "Na bar ƙasa kuma SY ina kake tunani na tafi?"
"Canada mana kaga za ka jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya za ka yi Masters ɗinka kana za ka ci-gaba da aiki da ZENN MOTORS COMPANY ya ka ga wannan shawarar tawa?"
Jim.... Haidar ya yi yana nazari maganar SY Barade kafin ya ce "Uhmm...shikenan zan yi tunani akai.
  "Wane iri tunani Ka'oje?"  Idan har da gaske kana so ka manta da Jeeddah Please ka amince kawai da wannan shawarar tawa.
  Haidar ya sauke ƙarfaffiyar ajiyar zuciya kana ya ce "Shikenan zan nemi visa gara nayi nesa da ita don gaskiya ban zan iya jure gani an ɗaurawa Jeeddah aure da wani ba. Na tabbata duk juriyar da na nuna za ta tafi a banza yanzu ma daga nan hospital zan wuce ayi min check up saboda ina jin canji a jikina.
  "Tashi na raka ka nima banaso ciwo nan naka ya tashi saboda ni kaɗai nasan iri hali da nake shiga a duk lokaci da naga kana sha wuya.
Haidar ya yi murmushin gefen baki yana ƙara jinjina girman ƙaunar dake tsakaninshi da SY Barade abota ce wacce aka gina bisa yarda da amince tun yarinta suke tare yayin da  abotarsu ta rikide ta zama 'yan uwan taka.
Jeeddah tana kwance waya take da Bilal sai kace ba ɗazu-ɗazu nan suka rabu ba. Khairat ta shigo fuskarta a murtuƙe ta ce "Ki zo inji Ya Kabeer?"
Sai da gaban Jeeddah ya yi mummunan faɗuwa tai sauri katse kira tana kalli Khairat cikin kaɗuwa ta ce "Ya Kabeer kuma me zan masa?"
  "Shi ya dace ki yi wa wannan tambaya ba ni ba.
Khairat ta faɗa kamar bataso magana kana ta fice daga ɗakin.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now