037

86 13 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

*AHAYYE NANAYE SHIN KINADA LABARIN SHAHARARRIYAR MARUBUCIYAR NAN MAI NISHADANTAR DAKU TARE DA FADAKAR DAKU WATO AMINA SLIMZY BAA KAN RUBUTU KAD'AI TA TSAYA BA?KO KUNSAN CEWA IN MATSALARKI NIIMAH CE KO INFECTION KO MALLAKA TA HANYAR ZAFAFAN MAGUNGUNAN MATA ITADIN GWANA CE?*

*HMMM KAR IN CIKAKU DA LABARI MAZA KI HANZARTA KI NEMI SLIMZY DAN BIYAN BUKATARKI TARE DA SAMUN MAI GIDANKI A TAFI HANNUNKI,DIK KARANCIN NIIMARKI DIK RASHIN DAD'INKI INSHA ALLAH KIKAJE WAJEN SLIMZY DA BUKATARKI TO MATSALARKI TAZO KARSHE.....*

*KAD'AN DAGA CIKIN SAHIHAN MAGUNGUNANTA WADANDA TAFIYAYYU NE DAGA KASAT NIJAR SUNE KAMAR HAKA:*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*ZUMAR RAKUMI DA AKALA*
*GARIN DAKA B'ATA GABAN KISHIYA*
*TSUMI DAN AGADAZ*
*MAN LALLE INGANTACCE*

*DA SAURANSU,MAZA HANZARTA KI NEMETA A WANAN LAYIN DAN SAMUN CIKAKKEN BAYANI DAGA GARETA TANA TURA KAYA KO INA A FAD'IN NIGERIA*

07042277401

*HAZIK'A KUMA FASIHIHAR MARUBUCIYARKU SLIMZY*✍🏻

037...

Akan Centre table da ke girke a tsakiyar parlourna na nufa na ɗauki kyautar da na tanadarwa da Ya Haidar, da farko ban yi niyyar bashi kyautar komai ba. Sai da Khairat ta kira ni a waya take tambayana wacce kyuta zan bashi nace babu sai take faɗa min ita da Aunty Farida kowacce su ta tanadi iri kyautar da za ta bashi dole nima naje da tawa kyauta ba don raina ya so ba na fita zuwa neman abinda zan bashi a matsayin tawa kyauta da ke nuna nayi farin ciki da dawowarshi.
Madaidaci kwali ne anyi wrapping ɗinshi na ɗauka kana na fito tare da rufe ƙofa na nufi gun motar Bilal wacce a yanzu ta zama mallakina. Kasancewar motar automatic ce shiyasa ban daɗe ina koyo ba. Kaitsaye gidan Mommy Turai na nufa maigadi yana tsaye wangale da Gate sakamakon mutane da ke ta shigowa da ababen hawan su, nima na bi ayari na nemi wuri nayi parking na fito a natse nayi using remote ɗin da ke saƙale a jikin key motar nayi lock ɗin ƙofufi, na rungume gift ɗin a ƙirjina yayin da ɗayan hannuna ke riƙe da handbag. Sosai aka ƙawata compound ɗin gidan da decoration table aka ajiye an zagaye shi da four chairs jama'a na zaune ana serving ɗinsu da haɗaɗɗun dishes, yayin da slow music ke tashi a hankali.
Tun da na nufo wuri nake ji matsanancin faɗuwar gaba, wanda na rasa na menene.
Inda na hango su Aunty Farida a zaune na nufa ina saki murmushi ba don ina jin daɗin yi sa ba.
  "Halau dai kin zo a makare.
Khairat ta faɗa sa'ili da na kai zaune taɓe baki nayi gami da faɗin "Ki ma godewa ALLAH da na zo don wallahi ban yi niyyar zuwa wannan dinner ba.
   "Cab! Ai duk wanda bai zo dinner ɗinan ba sai Mommy ta saka shi a blacklist.
Aunty Farida ta faɗa tana 'yar dariya daga nan suka ci-gaba da fira duk akan Ya Haidar yayin da na tsinci kaina da kasa furta uffan sai saurare su nake yi.
Mc ya shiga sanarwar fitowar Ya Haidar, tun Kafin ya ƙaraso cikin filin jama'a suka miƙe tsaye suna masa tafi da sowa, sai da Khairat ta zungure ƙafata da ƙafarta tai min signal sannan na yunƙura na tashi tsaye a kasalance nake tafa hannuwana, a hankali idanuwana suka sauka akan kyakkyawar fuskarshi ma'abociya kwarjini da cikar kamala Ya Haidar ya ƙara kyau na ban mamaki fiyye da yanda nasanshi a baya skin ɗinshi kamar ka taɓa jini ya fito, bashi da bambanci da balarabe ƙasar Labanon ban taɓa gani mutumin da kyau yai masa yawa irin Ya Haidar ba, sanda ya tunƙaro cikin taro sai ji ka ke yi jama'a na yaba matsanancin kyawon shi musamman 'yan mata da na ga sun fara tururuwa daukar hoto dashi. Ban san miyasa na ji wani irin mugun ɓaci rai yai min zuwan bazata ba. Duk sai na ji na tsani zama wuri ji nake yi tamkar ina zaune akan ƙaya. Muryar Aunty Farida na tsikaya tana faɗin "ku tashi mu je mu yi hoto da Haidar.
Khairat da matar Ya Kabeer suka yi sauri tashi yayin da ni kam nayi Kamar ban ji abinda Aunty Farida ta faɗa ba sai da ta sake maimaita maganarta sannan na ɗago na kalleta ina ya mutsa fuska na ce "Ku je kawai Aunty bana jin daɗi headache ke damuna.
  "ALLAH ya sauƙawa amma ya kamata idan kin koma gida ki nemi koda Panadol ne ki sha nasanki da rashin so magani kin gwammace ki ta zama da ciwo, ku zo mu tafi.
Aunty Farida ta ƙarashe magana tare da kama hannu Khairat da sauri na ɗauki kyautar da na kawo masa na danƙa wa Khairat ina faɗin "Khairat Dan ALLAH ki ba Ya Haidar ki isar min da sakon taya murna kafin headache ɗin ya lafa na zo da kaina.
Khairat bata ce komai ba ta karɓi gift din na bi su da kallo har suka isa wuri Ya Haidar ina kallonsu, yana ganinsu ya ƙara faɗaɗɗa murmushin sa ba ƙaramin ƙara masa kyau murmushi ya yi ba. Daga nesa nake kallonshi amma sai naji ba zan iya jure ci-gaba da kallo nashi ba, a dalili wani iri bugawa da ƙirjina ke yi sai kawai na kauda fuska ta na ɗan wani lokaci kafin nasake ɗagowa na kalle su sai  hotuna suke ɗauka idan ci-gaba da kallonsu na tabbata zuciyata tarwatse wa za tayi sai kawai na miƙe na bar wuri na nufi entrance ɗin gidan.
Na kutse cikin parlour Mommy Turai na tarar da wasu daga cikin ƙawaye ta suna cin abinci, da kyar na buɗe bakina nai musu sallama, na wuce cikin ɗaya daga cikin bedrooms ɗin Mommy ina zuwa na faɗa kan gado rabin jikina yana bisa gadon yayin da na sauko da ƙafafuwana ƙasa.
Bayan su Aunty Farida sun gama ɗaukar hoto kowacce ta miƙa shi kyautar ta tare da taya shi murna, daga bisani Khairat ta miƙa mishi kyautar Jeeddah ta kai bakinta daff da kunnenshi ta raɗa masa "Wannan daga Jeeddah ta ce a madadin ta na miƙa mata saƙon gaisuwa.
Ta ƙarashe magana tana blushing, shi ma murmushi ya yi ya ƙara dafe kyautar kamar yadda tai mishi raɗa shi ma haka yai mata "Kina nufi kyauta da gaisuwa kaɗai za ta aiko min ita ba za ta zo ba?"
"Tare muke da ita kanta ke ciwo ga ma ta can zaune.
Ta ƙarashe magana tare da pointing gun da suka baro Jeeddah zaune, Haidar Ka'oje ya bi yatsa ta da kallo, sai da Jeeddah bata wuri da sauri Khairat ta ce "Ba ta wuri watakila headache ɗin ya matsa mata ta shiga cikin gida bara na dubo ta.
Da sauri Khairat ta nufi cikin gida, ta duba parlour bata ganta ba sai kawai ta shiga nemanta a bedrooms ƙarar buɗe ƙofa yasa ni buɗe idanuwana, na kalle Khairat da ta nufo ni da sauri tana faɗin "Jeeddah ba dai ciwo kan bane?"
Sai da na ya mutsa fuska kafin na ce "shi ne Khairat gida zan tafi.
Da taimakon Khairat na miƙe tsaye muna fitowa muka ci karo da Mommy Turai na tayata murna kana nayi sallama da ita a bisa uzuri da na kawo mata, tai min fatan samun sauƙi. Khairat ta kira Aunty Farida a waya ta sanar mata na wuce gida, tun kafin na ƙarasa waje da nayi parking motata na hango Ya Haidar shi da Zarah 'yar abokin Daddynshi ce sun jinginar da jikinsu ga motata.
Tun ba yau ba nasan irin matsananciya ƙaunar da Zarah take masa, sai surutu take zuba mishi yayin da shi kuma sai zabga murmushi yake yi sosai naji ɓaci raina ya ƙara linkuwa, kamar daga sama naji Khairat tana faɗin "ashe dawowar nan da Ya Haidar ya yi aure zai yi ga ma shi can tare da amarya tashi wallahi sun yi matuƙar dacewa da juna.
Kamar saukar aradu haka naji maganar Khairat ta saukar min a kunne, har wani dishi-dishi nake gani hakan yasa naci wani ɗan uban tuntube saura kiriss! Na kife ƙasa Khairat tai sauri taro ni "Sannu Jeeddah halan  jiri ki ke ji?"
Na ƙasa amsa mata sai motsa laɓɓana nake yi kamar zai yi magana amma kalma ɗaya ta ƙasa fitowa daga bakina.
  "Anya kuwa za ki iya driving ko za ki bar motar ki anan na maida ki gida?"
Shiru nayi na ɗan lokaci kafin na amsa mata da cewa "Ki bar shi kawai zan lallaɓa da kaina.
"Kin tabbata?
Na gyaɗa kai Kamar an ce da Haidar Ka'oje ya ɗago idanuwanshi sai kawai yai tozali da Jeeddah, kasa janye idanuwanshi ya yi daga kanta gaba ɗaya ya tattara dukkan natsuwa da hankalinsa akanta, a hankali Zarah ta bi gun da yake kallo, tana gani Jeeddah ta tunƙaro su ta haɗe fuska domin bata manta da wacece Jeeddah da matsayinta a wurin Haidar Ka'oje. Bata kuma manta da artabo da suka yi ba don har dambe sai da suka yi ita da Jeeddah duk akan Haidar. Tun daga lokaci gaba mai tsanani ta shiga tsakaninsu ko sau dubu suka haɗu ba za su yi wa junansu magana ba.
Muna isowa nayi kamar ban gane su ba na raɓa gefen su na buɗe murfin mota na shiga, Khairat ce ta tsaya iya yinta ina ji lokaci da take faɗin "Iyeee Love birds! Ashe nan ku ka ɓoya abinku kuna zuba soyayya to ALLAH ya toni asirinku na kama ku.
Ta ƙarasa magana tana dariya su ma darawa suka yi haushinsu haɗe da takaici ya turnuƙe ni kafin su kai ga bata amsa nayi reverse da ƙarfi dama Ya Haidar hankalinsa yana kaina ya ga abinda nake shirin yi cikin zafin nama ya janye Zarah yayin da Khairat ta daka tsalle ta koma gefe, da ƙarfi na ƙarasa reverse da mugun speed na nufi gate, suka bini da kallon mamaki.
Haidar ya dawo da ganinshi akan Khairat kafin ya ce "ƙanwa yaushe Jeeddah ta zare har haka ai ni na zaci aure ya gyara ta tayi hankali?"
Dariya Khairat tasa, gami da cewa "Ta nan yadda ka san ta ba abinda ya sauya.
  "Uhmm! Ai kuwa ga alama nan na gani.
Haidar Ka'oje ya faɗa yana murmushi yayin da Zarah ta ja guntun tsaki gami da faɗin "Ya kamata a kaita asibitin kwararru a duba ƙwaƙwalwarta don gaskiya bata da cikakken hankali.
Kallon sama da ƙasa Khairat tai mata kafin ta ce "Ni kam 'yar uwata lafitarta qalau duk mutum mai hankali ba zai kalleta ya danganta ta da rashin hankali. Karki ji Ya Haidar ya faɗa ki zaci abinda ya faɗa gaskiya ne abokin wasanta ne.
  "Uhm!
Zarah ta faɗa a hasale murmushi Khairat tayi tare da maƙe ƙafaɗa alamar wannan ruwanki zuwan SY Barade wuri ya kawo ƙarshen taƙaddama tasu yayin da Haidar Ka'oje ya yi kamar baya jin su sai faman danar wayarsa ya ke yi.
Da taimakon Ubangiji ta iso gida lafiya rai ɓace ta wuce bedroom ko kayan jikinta bata cire ba ta bi lafiyar gado, sosai nake mamakin kaina domin wannan yanayi tun ina 'yar ƙanƙanu nake ji makamancinsa akan Ya Haidar kuma har yau na kasa tantance dalili da yasa nake ji hakan.
Bilal Shattima yana bisa hanyar zuwa gida kiran Nusaiba ya shigo wayarshi yai biris da ita ya rasa dalili da yasa Nusaiba take so taƙura wa rayuwarshi tana so ta haddasa masa fitina tsakaninsa da Jeeddah.
Nusaiba tayi aure shekaru haɗu da suka gabata sai dai bata haihuwa ba duka bai fi watani shidda da aure nata ya mutu, tun lokaci da ta kammala iddarta ta shiga bibbiyar Bilal Shattima gani yadda ya yi kuɗi yasa ta fara kai masa hari yayin da Aunty Bahijja ke ƙara ƙarfafa mata guiwa, ta bi ta takurawa Bilal ta hana shi sakatt saboda tsananin nacinta tun baya kulata har ya dawo yana amsa wayarta, shi ne yau ya je gidansu duka bai wuce 15 minutes da rabuwar su ba shi ne don naci za ta sake kiranshi gudun kada ta tsokana masa masifa da dare nan ya yi switch off ɗin wayarsa.
Jin an turo ƙofa yasa ni buɗe idanuwana Bilal ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama na amsa mishi can ƙasan maƙoshi kusa da ƙafafuwana ya zauna yana faɗin "Love ashe kin dawo ai ni na zaci sai na bi bayanki?
Na tashi zaune tare da ya mutsa fuska cikin yana yi marar daɗi na ce dashi "Headache ya taƙura ni shi ne na dawo tun ba a kammala ba.
  Cike da kulawa ya hayo gado ya jawo ni cikin jikinshi yana tattaɓa gefen wuyana "Sannu Love amma ban ji jikinki da zafi ba kodai stress ne yai miki yawa? Tashi ki yi wanka da hot water za ki ji karfe jikinki bara na je kitchen na haɗa miki coffee.
  Ƙara yatsine fuska nayi kafin na ce "Me ya haɗa Headache da zafi jiki?" Ba wani stress da yake damuna.
Na ƙarashe magana ina turo baki murmushi kawai ya yi tare da miƙewa ya shiga bathroom ya haɗa min ruwan wanka sai da ya ga na shiga wanka sannan ya wuce kitchen koda na fito, ya rage kayan jikinshi daga shi sai boxer briefs ya ɗora plate ɗin kilishi akan stool yana ci, ina tozali da tumbin sa ya yi wargajeje na ji wani shegen haushin sa. A hasale na ce "Wai kai Love wane irin mutum ne da baya kula da fitness maintenance ɗinshi?" Dallah kalli yadda ka dawo wani narkeke da kai kullum weight ɗinka ƙara hauhawa yake yi kai kenan cikin cin nama sai kace wanda kura ta yaye mtsss...na gaji da wannan mummunar ɗabi'a taka.
Na ƙarashe magana tare da ɗauke plate din kilishin na ɗamƙwarar akan mirror, har na shirya cikin sleeping dress ina balbala faɗa ina cikin fesa turare ya taso ya kama kafanɗuna ya juyo dani muna facing juna cikin tausassa murya ya ce "Love waya ɓata miki rai domin da gani yadda kike faɗa nan akwai wanda ya yi miki wani abu na ɓaci rai?""

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now