027

97 9 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

027...

Bilal Shattima har ya tari adaidaita sai ya tuna da ya manta da wayarshi dake charging a parlour. Sai haƙuri ya ba mai adaidaita ya juyo gida. Yana shigowa yaci karo da boxes ɗin kayan Jeeddah a tsakiyar parlour, idanuwanshi ya firfito dasu gabanshi yai mugun faɗuwa "ba dai Jeeddah tafiya za tai ba?"
Ya faɗa a bayyane daidai tana fitowa daga bedroom tana ƙoƙarin sanya hijabinta, ta ganshi  tsaye sake da baki a fusace ta zo ta gitta shi za ta wuce da sauri ya riƙo damtse hannunta ya jawo ta a hankali ta dawo gabanshi, ya tsare ta da kallo da yaudararin idanuwanshi cikin tausassa lafazi ya ce "Love ina za ki je da akwatuna haka ba dai yaji za ki yi ba?"
"Kwarai ma kuwa yaji zan yi don banga amfani zama na da kai ba gara na koma gaban Iyayena tun da nima ina dasu.
"Na shiga uku!
Ya faɗa har da wani dafe ƙirji ya ƙara firfitowa da idanuwanshi da sauri ta kauda idanuwanta daga kanshi nan take ya marairaice ya yi kalar tausayi, cikin kwantar da murya ya ce "mi ya yi zafi Love da za ki yi yaji dukka yaushe muka yi aure da har haka za ta ɓullo a tsakaninmu, ko so kike maƙiya su yi mana dariya?"
Da mugun sauri ta juyo ta kalleshi tsabagen takaicinsa bai barta ta jure kallon nashi ba sai kawai ta ja dogon tsaki, ta nufi cushion ta zauna, saboda nauyin cikinta ba zai barta ta daɗe a tsaye ba.
Gani haka yasa ya biyo ta ya durƙusa gabanta ya riƙo dukkan hannuwanta ya haɗe da nashi ya ƙara marairaicewa fiye da farko, tare da ƙarya murya yake faɗin "ban taɓa tsammanin bayan aure soyayyarmu za ta rikiɗe ta koma ƙiyayya ba Jeeddah. kwata-kwata a yanzu kin daina sona, na kuma rasa dalili ko laifi da nai miki da kika tsaneni har haka....
   "Dallah dakata Bilal!
Ta katse shi da sauri kuma a fusace kana ta ɗora da cewa "Kai yanzu har kana da bakin furta kalmar na daina sonka?" Bayan duk irin wulaƙanci da cin kashi da kake min kai da 'yan uwanka duk yadda ake nuna ƙololuwa ƙauna da sadaukarwa Bilal nayi maka, amma duk da haka kai da 'yan uwanka ba ku gani ba balle ku yabamin kullum cikin gani aibu na suke a takaice ma so su ke su liƙa ma 'yar uwarka Nusaiba to wallahi-tallahi muddin idan ka bari zugi da ingiza maikantu da Aunty Bahijja take maka yai tasiri akanka ka gauraya soyayya ta da ta Nusaiba ni da kai hayatan-hayatan mu rabu kenan rabuwa kuma ta har abada koda kuwa so da nake maka zai zama ajalina.
   "Subhanalillah! Dan ALLAH Love ki daina faɗar kalmar rabuwa a tsakaninmu ni dake tamkar hanta da jini ne ɗaya bayayi sai tare da ɗaya. Ban taɓa kallon Nusaiba da wata manufa face ta 'yan uwantaka ba.
   "Look Bilal ni fa banaso yaudara idan ma ba ka sonta ai Aunty Bahijja ta ce kai ɗin mijin mace huɗu ne. Sannan kuma rashin kulawar da kake nuna min ni da abinda ke cikina ya isheni gara na bar maka gida na tafi inda za a nuna min cikakkiyar ƙauna da kulawa. Gara na ba ka space ka ji daɗin nunawa Aunty Bahijja ita ce jininka tun da ni ba ka haɗa komai dani ba.
  "Haba....Haba! Love wannan wacce irin magana ce Dan ALLAH kada ɓacin rai yasa ki min sharri?"
Sai da na saki masa baƙar harara kafin na ce "Sharri ko wato sharri ma nake maka Bilal?" To shikenan mu tafi a haka nayi maka sharri dama kasan aikina ne...
Da sauri ya rufe min baki da tafin hannunshi ya daɗa lankwasa murya yana ci-gaba da rarrashina gami da sabunta alƙawari da yai min a can baya na ba zai taɓa yi min kishiya ba. Nan take na nemi fushina na rasa da kanshi ya jide akwatuna na ya mayar ɗaki, fitar da zai yi fasawa ma ya yi ranar hatta da girki shi yai mana wata irin kulawa ta musamman yake nuna min. Sai da yamma lis sannan ya fita kuma ƙarfe tara daidai ya dawo gida har da tsarabar kilishi ya riƙo min ranar kwana muka yi muna faranta wa junanmu tamkar mu dauwama a haka kada wani saɓani ko rashin jituwa ya sake shiga tsakanimu.
Washegari ya nemi na shirya mu je asibiti na duba Aunty Bahijja nan take annurin kan fuskata ya gushe dama muna karya kumallo ne yai min magana, duk sai na bi na haɗe rai ina shirin fara zazzaga masa tijara yai sauri katse ni ta hanyar cewa "ba sai kin ce komai ba Love na fahimci ki zan jira har ki huci ko bayan an sallame ta ne sai mu je gidanta ki dubata kin ji?"
Tsabar takaici kasa cewa komai nayi sai faman jujjuya mug ɗin hannuna nake.
_*AFTER THREE WEEKS*_
*{BAYAN SATI UKU}*
Tun da sassafe Aunty Farida ta kira ni da albishir ɗin Khairat ta haihu ta sami Baby girl, tsabagen farin ciki kwance nake ina fama da zazzaɓi amma bansan sanda na miƙe zaune ba. Duk ciwo da nake ji na nemi shi na rasa nan take na tashi na shirya ko Love ban kira ba sai da na isa asibiti da take sannan na kira shi. Da yake ita ta haihu da kanta daga ita har Babynta suna cikin ƙoshin lafiya, shiyasa tana gama hutawa aka yi discharge ɗinta, kaitsaye gidan Mama aka yo da ita domin wanka jego har dare ina gida sai da Love ya gama zaman majalisa ya biyo min muka dawo gida. Washegari ma gidanmu na yini sai ya kasance kullum gida nake wuni muna shirya yadda bikin suna zai guduna. Ranar suna Baby taci sunan khadijatul-iman.
Da yamma aka gudanar da walima mai jego da Babynta tsabar kyau da suka yi kamar ka sace su ka gudu sutura mai tsada ta kece suka sa, domin lace ɗin da Khairat tasaka kaɗai kuɗin sa kimanin dubu ɗari biyu yake. Ni kaina Khairat da 'yarta sun yi matuƙar burge ni sai dai ko kusa ba zan kwatata kaina da ita ba. Bayan sati biyu da haihuwar Khairat cikin dare na tashi da matsanancin ciwon mara abu kamar wasa sai gashi na kasa ɗaurewa dole na tashi Love daga bacci, duk ya bi ya ruɗe da gudunsa ya fita ya nufi apartment ɗin officer Abdul-ganiyu domin neman taimako kasancewar officer yana da mota da taimakon matarsa aka sanya ni mota sai asibiti tun abin ƙarfe biyu dare Jeeddah ta fara labour har garin ALLAH waye ba alama za ta haihu, gani haka yasa matar officer Abdul-ganiyu ta shawarci Bilal da ya kira gidansu Jeeddah ya sanar musu haihuwa ce tana asibiti. Ya kira Aunty Farida ko five minutes ban yi da kiran nata ba sai ga ta, ta zo tun kafin ta iso asibiti ta kira Mama da mommy Turai ta faɗa musu, cikin ɗan ƙanƙani lokaci danginta suka cika asibitin. Har ƙarfe 11 safe tayi ba ta haihu ba, gaba ɗaya hankalinsu Mama ya tashi. Sai baƙar wahala take sha gaba ɗaya ƙarfinta ya ƙare fahimtar da likitoci suka yi ba za ta iya haihuwa da kanta ba yasa suka faɗawa Bilal cs za a yi mata nan da 20 minutes kuma da gaggawa saboda ta jigata matuƙa ana buƙatar su gaggauta siyo kayan da za a yi theatre dasu sai kuma jini da za a yi amfani da shi.
Nurse ta kawo musu takarda mai ɗauke da jerin abubuwan da likita ya buƙata, har Aunty Farida ta karɓa Bilal Shattima ya ce ta kawo zai je ya siyo kafin tai magana ya kwace takardar al'hali ko kwabo ba shi dashi ya yi haka ne gudun kada dangin Jeeddah su rena shi gara ya je ko bashi ne ya karɓo, yana fita daga asibiti ya hau adaidaita ya kira Hajja da Aunty Bahijja ya gayamusu hali da ake ciki, kaitsaye shagon abokinsa Abbas ya nufa.
Aunty Farida ta kira Ya Kabeer ya zo ya bada jini saboda blood group ɗinsa ɗaya da Jeeddah, cikin abinda bai fi five minutes ba sai gashi ya zo aka ɗibi jini nasa duk wani shiri da likita zai yi kafin gudanar da cs ɗin ya kammala Bilal Shattima kaɗai ake jira, shiru-shiru gogan naku bai dawo ba har lokaci da za a shiga da ita ya yi babu Bilal Shattima babu labarinsa, Mama da Mommy Turai sai uban faɗa suke zabgawa suna kwashe masa albarka dole aka sake rubuta musu wani prescription yayin da likita sai masifa yake musu su na bashi haƙuri da mugun sauri Ya Kabeer ya je ya siyo yana dawowa aka shiga da ita.
Cike da zallar masifa Mama take faɗin "Tsawon rayuwata ban taɓa gani gantalalle matsiyaci irin miji nan na Jeeddah ba. Wallahi tun farko banso Farida ki bashi takarda nan ba domin nasan da wuya ya iya tabuƙa abin kirki.
   "Wallahi nima Mama ba a son raina na bashi ba ai kina gani kwata ya yi daga hannuna nurse tana miƙo min ya karɓe da ƙarfi.
Mommy Turai ce ta karɓe zance ta hanyar faɗin "Ku bar ni da ɗan Iska yaro muddin ya dawo ina cikin asibiti nan sai naci mutuncinsa daga sama har ƙasa mu rena wa hankali wato nufinsa ko Jeeddah ta mutu ko tayi rai ba abinda ya dame shi.
"Bari kawai Turai ni kaina wannan karo ba zan kyale Bilal ba da shikenan mu ma irinsa ne matsiyata da muna kallo rayuwar Jeeddah za ta salwanta kou?"
Mama ta faɗa cike da takaici hatta da Ya Kabeer ya fusata babban laifi Bilal da ya gani ya kuma bashi mugun haushi don me da zai karɓi prescription al'hali yasan a gaggauce ake so a shiga da ita theater zai je ya yi zamanshi sai ya danganta hakan a matsayin sakaci da wulaƙanci jira kawai suke ya dawo kowanne ya sauke masa haushi da takaicinsa da yake ji. Ana ciki haka sai ga Hajja tare da Aunty Bahijja da Hajiya Bintu sun zo a cikin reception suka tadda su Mama tsatsaye sun yi jigun-jigun kowanne su ka kalleshi za ka hango tsantsan damuwar da yake ciki, ko sallama da suka yi Aunty Farida ce tai ƙarfi hali amsa musu. Da suka tambaye jikin Jeeddah anan kan ba wanda ya amsa musu, sai kawai suka bi ayarin tsayuwa. Suna cikin wannan hali sai ga Bilal Shattima ya dawo tare da abokinsa Abbas, tun kafin ya ƙaraso wajensu gabansa ya shiga faɗuwa da mugun sauri kuma rai ɓace Ya Kabeer ya tarɓe shi yana faɗin "Kai don buhun wulaƙanci sai yanzu ka ga damar dawowa ai da karka dawo ka yi zamanka domin yanzu banga amfani da kaya da ke hannunka za su yi mana ba.
Kafin Bilal Shattima ya sami damar magana Mommy Turai ta karɓe zance tana faɗin "Ai ni Kabeer ban so ka fara masa ta kalaman fatar baki ba kamata ya yi ka fara tsinke baƙi munafuki da mari, in yaso daga bisani ka kora masa da jawabi.
Bilal Shattima ya sadda kanshi ƙasa sosai ya ji ya yi muguwa musanta, saboda daga Mommy Turai har Ya Kabeer kowanne su cikin ɗaga murya ya yi masa magana hakan ya jawo hankali wasu tsirarun mutane kansu.
Mommy Turai ta dawo da ganinta kanshi tana masa kallo mai cike da zallar wulaƙanci kana ta ce "Ikon ALLAH! wato kai Bilal dirka ciki kawai ka kware dashi ba ka san yadda ake ɗaukar wahalhalu sa ba kou?" To bari ka ji wallahi-tallahi idan wani abu ya sami Jeeddah ko da ɗa cikinta sai mu yi shari'a da kai baƙin matsiyaci marar imani kawai.
   "Wallahi Bilal ka bani mamaki tun farko kasan bakada kuɗi miyasa za ka karɓi prescription daga hannuna da sai ka bar mana mu masu kan ɗauka mu ɗauka, amma ina amfani baɗi babu rai wannan kayan takaici da yawa yake mtsss.... ALLAH ya wandam! Naka ya lalace.
Aunty Farida ta faɗa gami da jan guntun tsaki tsabar takaicin Bilal Shattima da take ji yasa tana gama magana bar wajen ta nufi bakin theater room ta tsaya don ji take kamar ta kifa mishi mugun mari.
Sosai Hajja ta kaɗu da jin irin maganganu da iyayen Jeeddah da 'yan uwanta suke faɗa akan ɗanta, yayin da Aunty Bahijja ta hasale jira take su sauke nasu ta ɗora nata, Hajiya Bintu kuwa farin ciki ne ya cika mata zuciya ji take kamar ta daka tsalle ta taka rawa. Hajja tai ƙoƙarin haɗiye duk wani abu da take ji cikin muryar lalama ta ce "Haba bayin ALLAH mi ya yi zafi haka da za ku dinga tozarta min yaro cikin bainar jama'a?" Yadda ku ke taƙama kuna da ikon akan Jeeddah shi ma yana da ikon akanta asalima ya fi ku iko da ita don kuwa shi matarsa ce, wannan hali da ku ke nuna masa zai iya jawo zubewar mutuncinku a idanuwansa.
A fusace Mama tayo kan Hajja tamkar za ta rufe ta da duka tana faɗin.
   "Eh! Ba shakka Hajja ai dole ki faɗi haka saboda ba 'yarki bace aka wofitar tana gaɓar mutuwa ba. Da yasan bai da kuɗi akwai uban da yai masa dole ai sai bar mana takarda magani amma ba ya karɓe ya tafi tsawon lokaci bai dawo ba, ko so yake likita ya dauwama yana jiransa ko kuma nufinsa sai ta mutu sannan ya dawo?"
   Zuwa lokaci hankula mutane da dama ya dawo kansu don sai kallonsu ake yi, yayin da Bilal Shattima ya cika ya yi tambatsa! Sai huci yake tun sanda ya sadda kanshi ƙasa bai sake ɗagowa ba.
Aunty Bahijja ta hayyaƙo tana faɗin "Gaskiya an zo gaɓar da ba mu ci-gaba da jure iri-iri waɗannan wulaƙanci ba. Wanda aka yi muna a baya muka jure ya isa haka sai wulaƙanta mu ake yi ana ci mana zarafi akan wata banza sai kace wata 'yar gwal....
Kafin Aunty Bahijja ta dasa aya Mommy Turai ta falla mata kafiri mari. Sai da ji da ganinta suka kaura gareta na ɗan lokaci kafin ta ɗago dafe da kunce fuskarta shimfiɗe da mamaki, tana kallon Mommy Turai wacce ta ke jira ta sake furta wata mummunan kalma akan Jeeddah ta ƙara ɗauke ta da wani mari "Ki ka mare ni?"
Aunty Bahijja ta furta da mugun mamaki.
   Sai da mommy Turai ta gagalla mata baƙar harara kafin ta ce "Ki godewa ALLAH da marin ya tsaya kanki bai faɗa kan uwarki ba wacce bata koya miki tarbiyya sarrafa harshe ba.
Da sauri Bilal Shattima ya ciro kanshi ya kalle Mommy Turai da fusatattun idanuwanshi, tsabar harzuƙa da ya yi jikinsa har rawa yake yi kamar wanda yaci tauri..

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now