057

106 7 0
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

057

Kalma tana da aure da ta ambata ba ƙaramin girgiza duniyar sa ya yi ba. wani irin mashahurin kishi ya lulluɓe shi ya haɗiye wasu yawu adams apple ɗin shi suka yi wani kalar motsawa da ƙarfi. Ina gani ya nusa a duniyar tunani na ce "Yallabai ni zan wuce sai gani na gaba ka gaida Umma.
Na faɗa tare da yiwa motata, key a manufa ta taso ya fita min daga mota nasan inda dare ya yi min amma sai yai wani ƙara gyara zamanshi cikin sanyi murya ya furta "Sauri me ki ke yi haka?"
   "Gida ake jira na Yallabai.
Na faɗa cike da ƙosawa a zahiri gaskiya ya gundare ni na matso ya fita min daga mota.
  "Shikenan Maijiddah sai yaushe za mu sake haɗuwa?"
Yatsine fuska nayi gami da furta "Duk sanda ALLAH ya sake haɗa mu.
   "Haka ne amma ki taimake ni da number wayarki.
"Yallabai number wayana fa?"
Na tambaya cike da maɗaukakiyar mamaki.
"En! Ko ba za ki bani bane?"
"En! To ba wai ba zan ba ka bane ba kawai ina tunani amfani me za tai maka.
    "Idan za ki bani Maijiddah ki ba ni kawai duk amfani da za tai min wannan ba damuwarki bane.
"Hmm!
Na faɗa gami da miƙa masa tafin hannuna karaf na ji ya riƙe min hannu har yana haɗawa da wata irin shassheka kamar wanda ya yi tserar gudu ya zo na ɗaya, cikin sauri na fincike hannuna ina faɗin "Yallabai wayarka za ka bani ba hannuna za ka riƙe ba.
   "Oh! I'm sorry.
Ya yi magana tare da ciro wayarshi daga gaban aljihun rigar jikinsa ya miƙo min na saka mishi numberna tsabagen rashin yarda sai da ya kira wayana ya ji ya yi ringing kana ya buɗe ƙofa ya fita ya dafa ƙofar mota gami da tura kanshi cikin motar cikin wani irin salo ya ce "haƙorin makkahn nan ya yi miki kyau ban taɓa gani mace da haƙorin makkahn ya yiwa kyau kamar ke ba, komai na ki na musamman ne Maijiddah.
Yana ƙarashe magana ya juya da sauri ya nufi gun da ya yi parking motarsa na bishi da kallo baki buɗe kafin na taɓe baki na ja motana na halba kan titi da high speed na iso gidan Mommy domin nasan na ɓata mata lokaci sosai ina zuwa na tarar da ita a kitchen tare muka ƙarasa aiki. Muna kammala wa ta bar min arranging dining table ita kuma ta wuce bedroom tai wanka.
   Ina tsaye a dinning room Ina ƙara ƙarewa table ɗin kallo koda da akwai abunda ban ɗauko ba. Na ji sallamar direban da yaje ɗaukar Ya Haidar ya shigo janye da luggage ɗin shi yayin da Ya Haidar yake biye dashi a baya cikin salon tafiyar nan tashi ta izza da ƙasaita tsintar kaina nayi da wani irin faɗuwar gaba bansan miyasa a yanzu ko muryar Ya Haidar na ji sai gabana ya faɗi ba, alhali ada can baya bana ji hakan akansa. Na shaƙi sanyayye ƙamshi turarensa mai haifar min da natsuwa a hankali na fara tafiya na nufo cikin falon cikin wata kalar kasalalliyar murya na ce "Ya Haidar oyoyo!
Saukar muryata a dodon kunne shi yasa shi tsayawa kana ya dawo da ganinshi ta inda nake ya wani zuba min manyan farare idanuwanshi masu kama da na mai jin bacci, ya wani ɗage girar ido fuskarshi a haɗe ya ce "Ke me ki ke yi a gidanmu?"
Murmushi ne mai ɗan karan sauti ya sumbace min domin idan ban manta ba dare da zai yi wannan tafiya muka yi faɗa har na ce dashi idan har yana da zuciya a ƙirjin shi kar ya sake zuwa mana gida wato bai manta da abunda ya faru ba shi ne ya rama.
Rausayar da kai gefe ɗaya nayi tare da faɗin "Ranka ya dade abinda ka ke zuwa yi a gidanmu nima shi na zo yi a  gidanku.
  "Oh really?"
Ya faɗa yana ƙara ɗage gira jinjina masa kai nayi tare da nufar gun da direban yake tsaye na karbi luggage ɗin ina faɗin "Malam Rabi'u kawo na kai mishi ciki.
  "Tohm! Ranki yadade.
Cewar malam Rabi'u yana mai hanita min luggage ɗin. Ya Haidar yana gani Malam Rabi'u ya fice ya kai hannunshi zai karɓe akwatin sa nai sauri janye wa ina dariya ɗan guntun tsaki ya ja gami da nufar bedroom ɗin Mommy ni Kuma na ja akwatin na nufi corridor da zai sada ni da part ɗin sa.
Har bedroom ɗinsa na kai masa akwati ina buɗe ƙofa zan fito yana sako kai muka tsaya cirko-cirko! Gaba ɗaya ya zuba min narkakkun idanuwanshi numfashi da yake saukewa akai-akai iskar tana sauka akan fuska ta hakan ya haifar min da  shiga wani sabon yanayi mai wuyar fassara wa, gashi ya tare ƙofar fita ballantana na fice da kyar na iya buɗe bakina na ce "Aliyu lazy ka bani hanya na wuce ko duk laziness ɗin ne yasa ba ka san ka tare ƙofa ba?"
  Dan kawai na harzuƙa shi na kira shi da wannan sunan tun yana primary school wani schoolteacher ɗin shi ya sa mishi wannan sunan a dalili ciwo zuciyar da yake ɗauke dashi yasa a class ba shi da kama jiki duk lokaci da aka yi musu note sai kowa ya ri ga shi gamawa sai teacher ɗin yake kira shi da Aliyu lazy sam bayaso sunan ni kuma a duk lokaci da nake so ɓata mishi rai nake kiran shi dashi. a maimakon ya ɓata rai kamar yadda ya saba sai kawai ya saki shaƙiyi murmushi tuni nayi observing ɗin Ya Haidar muddin ya yi irin wannan miskilin murmushi zai furta maganar da ta girmi tunanina saboda haka nai sauri toshe kunnuwana ina faɗin "Dan ALLAH ka rufa min asiri ka haɗiye maganarka ta koma cikin ka.
Dariya mai ƙaramin sauti ya yi tare da sa hannunsa ya ture ni ya wuce cikin ɗakinsa, yana faɗin "Da ki bari na faɗa miki hakikanin gaskiya amma duk da haka ina fatar ALLAH ya kai damo ga harawa a lokaci za ki fahimci koda ni lazy ne amma ban da wannan fanni ba.
   "Mtsssss! Ɗan iska kawai dama ba abunda ka kware dashi da ya wuce wannan.
Na faɗa ƙasa-ƙasa ina gani ya juyo na kwasa da gudu na fice.
Jim kaɗan sai gashi ya dawo sanye da farar armless da black colour three quarter crazy jeans farare ƙafafuwan shi ɗauke da flip flops, sai uban ƙamshi yake zuba wa na ɗago daga danna wayata da nake yi na sauke idanuwana akan fuskarshi ba ƙaramin kyau ya yi min ba har sai da na yaba kyau nashi a zuciyata.
Yana zuwa ya saki min ɗan ƙaramin rankwashi aka yana faɗin "Daina kallona karki cinye ni mayya.
   Dafe kaina nayi tare da furta "Ouchhhhh! Wannan zalunci fa?"
"In kin girma ki rama.
Ya faɗa yana murmushi nai sauri ajiye wayana na tashi zubur ina faɗin
"Tun da ka faɗi haka zan nuna maka na girma dan wallahi sai na rama.
Na ƙarashe magana tare da yin tsalle da nufi na rankwashi kansa kafin hannuna ya sauka akanshi ya riƙe ni kasancewar yafi ni tsayi nesa ba kusa ba.
   "Daga dawowarka ko hutawa ba ka yi ba za ku fara hali naku.
Mu ka ji muryar mommy daga bayan mu duk da yaga mommy bai sake min hannuwana ba yasa dariya ya ce "ALLAH mommy ba laifina bane ita ce ta fara gaba ɗaya yarinya nan ta gama rena ni idan har ba aura min ita ku ka yi ba reni da take min ba zai kau ba.
Jin abunda ya faɗa yasa naji Kunya ta lulluɓe ni nai sauri sadda kaina ƙasa mommy ta ƙaraso tare da zare min hannuwana daga cikin nashi tana faɗin "To naji cikamin yarinyata kar ka ji mata ciwo sarkin marasa kunya duk duniya.
Yana dariya ya sake ni Mommy ta ja ni zuwa dining room shi ma ya biyo mu a baya tare muka ci abinci, daidai da second ɗaya bai ɗauke idanuwanshi daga kaina ba. Sai dare na baro gidan shi ma da kyar Ya Haidar ya bar ni dan har rokata ya yi na kwana na ƙi saboda gobe ranar aiki ce zan je office.
Washegari sai around 11:30am na iso office yau nayi latti sosai, tun kafin na ƙarasa parking space da aka tana da domin ma'aikata, na hango shi tsaye jikin motarsa fuskarshi a haɗe babu annuri ko kaɗan akanta sai faman danna wayarsa yake yi, ko ban tambaya ba ina da tabbaci ni ce yake kira domin tun rabuwar ta dashi jiya na danna numbershi a blacklist, nima na ɗaure tawa fuska na fito daga mota ina ƙoƙari rufe ƙofa ya hango ni cikin zafin nama ya iso wurina yana zuwa ya damƙe damtse hannuna da ƙarfin gaske sam bai yi la'akari da public place muke ba ya manna ni jikin mota yana wani irin huci kafin ya ce dani "Miyasa ki ka yi blocking ɗina?"
Sosai na tsorata dashi domin yanayi sa kwata-kwata bai yi min kama da na mai cikakken hankali ba jikina ya ɗauki mugun rawa dama can bakin ne kawai dani amma tsoro kamar farar kura, cikin rawar murya na ce "Dan ALLAH ka sake ni mutane su na kallon mu zan gayamaka dalili.
   "Ba zan sake ba har sai kin gayamin.
Yayi magana cikin loud voice na ja dogon numfashi cikin sarƙewa lafazi na ce "Banaso ka kira mijina ya ji wallahi zan iya shiga matsala.
    "Mijinki.....mijinki I hate this name I absolutely hate this name idan bakinki ya sake furta wannan suna a gabana komai zai iya faruwa idan na ce komai Maijiddah ina nufi komai ma.
   Wani irin mugun tsoro shi ya ƙara lulluɓe ni da kyar na aro jarumta na yafawa kaina cikin dakakkiyar Zuciya nace "waye kai me ka ke nema a gurina don na gaji da bibbiya ta da ka ke yi?
     "Waye ni me nake nema a gurin ki wannan duk ba damuwarki bane tun da ni nasan wacece ke na kuma san abunda nake nema a gurinki abu guda nake so a gare ki if I call your phone just pick up koda ba za ki yi min magana ba ki ɗauki kiran kawai.
   "Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Wannan wane irin hauka ne?" Haba bawan ALLAH yanzu da aure nawa zan dinga picking call ɗinka hakikanin gaskiya ba ka yiwa rayuwata adalci ba da kuma nasan za ka zame wa rayuwata matsala da a wancan ranar ban amince da taimakon ka ba.
   Sai kuma naga jikinshi ya yi sanyi har ya sassauta riƙo da ya yi min cikin sanyayya murya ya ce "Ba za ki iya gane irin muhimmanci da ki ke dashi a gareni ba Maijiddah koda zan iya cutar da kowa ke ba zan cutar dake ba. Ki yi haƙuri da abunda nai miki ina da wani hali idan raina ya ɓaci hankalina gushewa yake yi amma ni ba mugun bane ki yafe min kin ji?"
Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya na sauke har zuwa lokaci tsoro shi bai gama saki jikina ba.
   "Shikenan.
Na faɗa a takaice.
  "Ke haƙura kenan za ki cire ni a blacklist?"
Na gyaɗa kai.
"To ki cire a gabana shi ne zai bani tabbaci kin yafe min.
Ba tare da nace komai ba na ciro wayana a handbag na cire security code na miƙa mishi da sauri ya karɓa ya cire da kanshi kana dawo min da ita yana mai ƙara bani haƙuri ban ce dashi uffan ba nai tafiyata ko juyowa ban yi ba. a can ƙasan zuciyata fargaba nake kada ya gano cewa bani da aure saboda wannan mahaukaci muddin yasan cewa bani da aure na shiga uku lallai dole na gaggauta sanar da khamis ya turo magabata sa domin ban ga dalili ɓata lokaci ba tun da aure wuci gadi ne za mu yi ba na soyayya ba ballantana a ce ana bukatar fahimtar juna. Ban san adadin lokaci da ya ɗauka tsaye a guri ba kamar an dasa shi kafin ya yi ƙwafa gami da shiga motarsa ya bar wuri yayin da zuciyarsa cike da muradin mallakarta ko ta hali ya ya
********
"Ban taɓa sani ke mutuniyar banza bace ba marar wayau sai yau Nusaiba. ke kenan kullum cikin yaji sai kace kanki aka fara aure.
  Cewar Baffa mahaifin Nusaiba wacce yau da sassafe ta dako yaji kullum bata da korafi da wuce Bilal yana tare da Jeeddah burinta su rabu har abada sun yi yawon gidan je bokaye da na tsibu ita da Aunty Bahijja har sun gaji sun ka sa nasarar raba tsakanin su.
Kuka Nusaiba ta fashe dashi tana faɗin "wallahi Baffa na gaji da aure nan gara araba shi kowa ya huta, tun da muka yi aure nan ban san mijina ya zauna tare dani ko na hour ɗaya ba. Hatta da hakkina na aure sai in na saka mishi magani tadda sha'awa a cikin abin sha zai nemi ni...
   "Innalillahi wai'inna illahim raji'un! Nusaiba yaushe ki ka lalace har haka? Yanzu ke ko kunya bakyaji da ki ka kalli tsabar idona ina matsayin mahaifinki ki ka dinga zaro min waɗannan manya-manyan maganganu.

#Haidar ka'oje
#Bilal Shattima
#Egnr Ameer
#Jeeddah maishadda
#Team zazzafan kishi
  

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now