048

105 15 1
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

Taɓa ka lashe..

   *ZAMANIN MU AYAU*

NA
  JEEDDAH ALIYU
      & NANA DISO

A Wannan zamanin namu ku yaran nan baku ɗauki ruwan ɗumi da mahimmaci ba, saboda Allah maryama ke ba yarinya ba da shekarunki kidinga shan ƙanƙara haka? Ki duba fa kiga babu ruwanki da tsarkin nan da ruwan dumi, wai kuma ƙin babbake ɗuk Duniya Abah ke yafiso yafi kyau na! " Wani ƙallo tayiwa mahaifiyarta tace "Anty wa zai so idan bani ba? Duk cikin family ɗin ƙinga mai kyau na? Nifa a duniya zan iya rantse miki abah yafi sona akan mahaifiyar nan tasa!  Banida diri ne ko kuma ni mummuna ce? Kuma ƙanƙara anty me zatayi min, hmm bari dai nayi shiru Amma idan kinga yadda abah yake bina a daƙi wallahi ko maye sai haka! "Lallai maryama zamani kenan ni mahaifiyarki kike gayawa wannan ƙalmar? To bazan miki baki ba Amma ina tabbatar miki ranar da abah yaga mata zakisan ke bakomai bace ba!  Kuma banda abunki ai ita macce ƴar dumi ce, wannan shanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita macce da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta da ƙanta sai sanyi ya kamaki kizo kisani agaba, haka naje na haɗomiki sassaken nan na ɓaure da ƙanin fari da minnas da zuma da citta da kirfa, nazauna nadafa miki amma kika kalleni kikace ƙwayoyin cutane wai ke ƴar boko nima mahaifiyar taki ƙallon baƙauyiya kikemin maryama kibi duniyar nan a sannu!" Hajiya anty Kenan! Basai nayi miki wani dogon bayani ba Amma nice zuciyar aba babu wata macce bayana!!!....

https://t.me/+RDbX-vD-HWdlNWE0

048..

Bilal Shattima yana fitowa daga gidan Aunty Farida kaitsaye gida ya wuce ya tattara  kayayyaki shi ko allura bai bari ba, ya rurrufe ƙofofi kasa tafiya ya yi yai tsaye yana yiwa gidan kallo na ƙarshe yana tuna irin rayuwa da suka yi shi da Jeeddah. Ji yake kamar ya dawo da baya sai dai abinda ya wuce ba zai taɓa dawowa ba. Wasu hawaye masu mugun zafi suka zubo masa a kumatu bai damu da ya goge su ba ya juya da sassarfa ya shiga motarsa kana ya yi reverse ya nufi gidan Hajja a tsohon ɗakinshi dake BQ ya saka kayanshi duk ƙura da ke ciki bai dame shi ba ya zauna gefen tsohuwar katifarsa gani komai yake yi tamkar al-mara.
Sosai Jeeddah ke ta rusar kuka Aunty Farida ke rarrashinta "Aunty ki barni nayi kuka abin kuka ne ya sami ni adaidai lokaci da muka sami daidaito tsakanina da Bilal muka fahimci junanmu kana muka tsara rayuwarmu ta gaba sai gashi kwatsam! An raba mu Aunty na kasa yarda Love ne ya saki ni kuma wai har saki uku da wane ido zan kalle Babanmu na gayamishi Love ya sake ni bayan na kwana da sani furuncinsa akaina.
   "Jeeddah Baba ba zai ga laifin ki ba domin ba ke kika ce ya sake ki ba shi kanshi Bilal cilasta shi aka yi amma duk da haka bai dace ace lokaci ɗaya ya yi miki saki har uku ba saki irin na jahilai farko, sai kace ba shi da ilimin addini.
   Girgiza kai nayi ina faɗin "Aunty titse shi tayi har ma da guzuri biro da takarda ta taho dasu, ba shi da yanda zai yi domin  tayi rantsuwa ta sake maida rantsuwa idan har bai sake ni ba tsine mishi za tayi.
Tsaki Aunty Farida ta ja gami da cewa "Mtsssss! Tsinannu mutane kawai butulu. Tun da ya yi kuɗi ai yanzu dole su tsane ki sun manta da lokaci da ɗansu yake taka rawa da bazarki. in-sha-Allahu sai sun girbi abinda suka shuka. Tun farko abinda muka yi miki gudu kenan ga ɗan uwanki me sonki tsakani da ALLAH domin tun kafin ki zama cikakkiyar mace Haidar yake danko sonki amma ki ka daka tsalle ki ka ce sai ɗan gidan gantalallu mutane wanda basu gadi mutumci ba. To ai ga irin sakayya da suka yi miki nan yanzu kan ai dole ki ɗauki darasi ki gano cewa ba inda kafuwa da naci zai kai mutum face ga wahala.
Duk abinda Aunty Farida take faɗin nasan gaskiya ne amma abu ɗaya na kasa gasganta wa shine laifin Bilal da take gani domin ni ko kaɗan ban ga laifinsa ba. Ni dai na dogara ne da cewa Hajja da Aunty Bahijja ne suka raba mana aure.
   Sai bayan sallar isha'i Aunty Farida ta tattara ni muka yo gida har Aunty Farida ta gama yiwa Baba jawabi ba abinda nake yi sai shasshekar kuka da alama ba ƙaramin girgiza Babanmu ya yi ba. Domin tallaɓe kumatu ya yi sai "innalillahi wa'inna illahim raji'un! Yake ta maimaita wa daga bisani ya yi shiru sai Mama ce ke ta zuba faɗa inda take shiga ba ta nan take fita ba domin kuwa har cewa tayi duk kudaden da na lissafa sai Bilal ya biya ni abina domin kuwa bai yi min adalci ba. Sai da Baba ya taka mata birki ya ce ko cikin fira bayaso ya sake ji wani daga cikinmu ya tadda zance kuɗi nan. "Duk abinda suka yi mata su da ALLAH ai Ubangiji baya bacci saboda haka na kai ƙarar su wurinsa matuƙar Jeeddah tana da hakki akansu sai ALLAH ya saka mata. Ki yi haƙuri Jeeddah nasani saki yana da matuƙar ciwo wanda misalta zafinsa sai wanda aka yi wa amma duk da haka ki ɗaure ki ɗauke shi a matsayin ƙaddararre al'amari ALLAH ya zaɓa miki abinda yafi zama alkhairi a rayuwarki. Ku tashi ku tafi zan yi magana da Mamanku. Ni da Aunty Farida muka tashi ina mai ci-gaba da sharar hawaye. Parlour Mama muka shiga yayin da muka baro Mama a can parlour Baba.
Sai misali ƙarfe 10:00pm Aunty Farida tai mana sallama da zimmar za ta dawo gobe. Mama sai lallaɓa ni take yi hatta da Aiman da ya dame ni da surutu wai na duba masa homework ɗinsa. Tsawa ta daka mishi gami da cewa ya kyaleni naji da baƙin ciki da ubansa ya ƙunsa min. Ranar a ɗakin Mama na kwana akan gadonta wani irin masifaffen ciwo kai ya saƙo ni a gaba yadda naga rana haka naga dare sai da asuba ya gabato sannan bacci ya ɗauke ni.
Tun da nayi sallar asuba Mama ta ce na koma na kwanta ina buƙatar hutu. Na koma na bi lafiyar gado yayin da ciwo kai da nake ji sai ƙara hauhawa yake yi, sai lumshe idanuwana nayi kamar mai bacci al'hali idona biyu ina jin lokaci da Mama ta shirya Aiman ya tafi school dama Abdul yaron Baba na shago ke kai shi ya ɗauko shi.
A cikin ƙura da yana Bilal Shattima ya kwana domin baya cikin natsuwar da zai nemi kyakyawan wurin kwana. Da asuban fari ya baro gidan nasu wanda har a washegari Hajja batasan cewa anan ya kwana ba. Kaitsaye hotel ya nema ya kama ɗaki sai a lokaci ya sami damar yin bacci kirki mai cike da mafalki an maida aurenshi da Jeeddah saboda haka da ya falka mafalki kawai ke mishi kai kamo a cikin ƙwaƙwalwa, har yai nasarar fara kimtsa mishi wani bakon al'amari.
Tun cikin dare Mama ta kira mommy Turai ta fesa mata mummunan labari Bilal ya sake ni saki uku, shiyasa da sassafe Mommy ta shirya tana isa parking lot Haidar Ka'oje yana fitowa daga apartment ɗinshi jikinshi sanye da sport wears white in colour da ɗan gudun shi ya nufo wajen mommy "Mommy lafiya za ki fita da sassafe nan?
Haidar ya faɗa sa'ili da ya ƙaraso gunta. Sai da mommy ta saukar da numfashi mai ƙarfi kafin ta ce "ina fa lafiya Aliyu ɗan shegiya nan tsinane mummuna tsiya mijin Jeeddah ya sake ta don yana ɗan jahila saki har uku.
   Wani irin mugun bugawa ƙirjin Haidar ya yi don sai da jiri ya kwashe shi ALLAH ya taimake shi akwai mota a gefensa yai sauri jingina jikinshi. Da ba abinda zai hana mishi faɗuwa "Innalillahi wa'inna illahim raji'un! Ita kuwa me tayi mishi da zai mata wannan sakin wulaƙanci?"
Haidar ya yi magana cikin sanyi murya.
  "Butulci ne kawai irin na ɗan Adam tun da yanzu yana gani ya yi kuɗi ya kuma auro 'yar uwarshi ai dole ya wulaƙanta ta.
"Uhmm! Mommy kada ki yi sauri yanke hukunci domin wannan bai isa ya zama gamsasshiyar hujja da zai sa ya yi mata irin wannan saki na jahilci ba.
   "To shikenan tun da ba ka yarda ba ai kai dama gaddamamme ne duk abinda aka faɗa sai ka yi gardama da kwaskwarima akanshi.
   "ALLAH ya ba ki haƙuri Mommy ni ba gardama nake miki ba kawai dai Inaso ki bari sai kin ji sahihin labari kafin ki zartar da hukunci.
  "Mtsssss! Bani wuri na wuce kada ka ɓata min lokaci da iya yinka na wofi.
Mommy ta faɗa tare da ture Haidar a fusace ta shiga ƙoƙarin shiga mota da sauri Haidar ya ce "Mommy bani key na kai ki saboda direbanki bai ƙaraso ba kuma kin daɗe ba ki yi driving da kanki ba kada ki je ki jawo mana aiki da sanyi safiya.
Ba tare da tayi magana ba ta cilla masa key ya cafe har suka iso ƙofar gidansu Jeeddah Mommy tana kwashewa Bilal da Hajja albarka.
A parlour Baba ta tadda Mama anan suka sake maimaita zance yayin da Mommy sai ɓaɓatun faɗa take ita ma ta goyi bayan mama gara Bilal ya biya ni kudina har cewa tayi idan ya yi gardama a maka shi kotu sai da Baba ya nuna mata ɓacin ranshi a fili kafin ta bar maganar amma kama daga kan Bilal, Hajja kai har ma da Aunty Bahijja sun sha zagi da tsinuwa yafi kala ɗari.
  Wani irin amai ne ya taso min a dalili mugun zazzaɓi da ya rufeni, da gudu na diro daga kan gado kafin na kai bathroom, amai ya kubce min na durƙusa ƙasan tiles na shiga kelaya shi sai kakari nake yi kamar zan amayar da hanji cikina.
  "Mama ina Jeeddah take?"
Haidar ya faɗa sai lokaci ya yi magana duk taƙaddama da ake yi bai furta uffan ya dai tallaɓe da kamatunsa, sai rarraba idanuwa yake yi shi kaɗai yasan irin yanayi da yake ciki.
Mama ta amsa mishi da cewa "Tana can ɗakina tana bacci je ka dubo ta ko ta tashi domin da zazzaɓi ta kwana shiyasa ma nace ta kwanta ta sami isasshen bacci gaba ɗaya sun hargitsa min 'ya shegu mutane kawai.
Ɗan guntun murmushi Haidar ya yi domin ya kwana da sani dama can Jeeddah hargitsatsiya ce.
Yana shiga parlourn Mama ya fara jiyo kakari amanta da sauri ya nufi ɗakin yana tura ƙofa ya hango ta durƙusawa ya yi a bayana ba tare da kyakyami ba ya rungume ni yana faɗin "Subhanalillah! Jeeddah ashe zazzaɓin ya yi tsanani har haka? Tashi na taimaka miki ki shiga bathroom ki tsaftace jikinki mu tafi asibiti.
  Da taimakon Ya Haidar na kai kaina bathroom kafin ya fita sai da ya haɗa min ruwan wanka masu zafi sosai. Da kanshi ya gyara gun da na ɓata ya fesa room freshener sannan ya fita ya faɗawa su Mama hali da ya tadda ni ciki, koda na fito su Mama na ɗakin Mommy ce ta taimaka min na shirya cikin doguwar rigar Mama saboda ban zo da kaya ko ɗaya ba. Yau na ji Mama ta kira Aunty Farida a waya ta ce da yamma ta je a kwaso kayana. Ya Haidar ya shiga kitchen ya haɗa min tea yatsine fuska nayi saboda banaso ƙarni madara cikin dusashewar murya na ce "Ya Haidar da black tea ka haɗa min.
Da sauri ya juyo ya fice da mug ɗin tea a hannu jin kaɗan ya dawo da black tea ɗin, ya miƙo min mommy ta karɓa ta dinga bani a baki nasha fiye da rabi mug kafib na ce da Mommy na ƙoshi. Tare da mommy muka fito zuwa asibiti yayin da Mama ta zauna gida.
  Nan take aka karɓe mu babu ɓata lokaci aka shiga treatment ɗina, da yake private hospital ne  kuma shine hospital ɗin family doctor ɗin su Ya Haidar. Bayan gwaje-gwaje da aka yi min bincike lafiyata ya nuna jini na ne ya ƙara hawa fiye da farkon kwanciya na asibiti. Hakan ba ƙaramin ɗagawa Ya Haidar hankali ya yi ba sai misali ƙarfe ɗaya ya baro asibiti ya zo gida ya yi wanka. Kana ya ɗauki abinci ya dawo tare da direban Mommy hakan ya ba wa mommy damar komawa gida, da yake Aunty Farida da Khairat duk sun zo.
  Sai kai da kawowa Engineer Ameer Bello Sardauna yake yi a harabar hospital ɗin da aka yi admitting ummarsa, tun safe da ya yi tozali da Haidar Ka'oje ɗauke da Jeeddah cikin halin rashin lafiya ya kasa samun kwanciyar hankali ƙarfin hali kawai yake yi domin zuciyarsa sai azalzalarsa take yi da  ya je room ɗin da take d ya ga hali da take ciki  koda zai sami natsuwa. Tun safe da ya ganta ya kasa gusawa ko nan da can sai zayar yake yi tsakani bakin ƙofar ɗakin da take zuwa wanda umma take kana kuma ya dawo harabar asibiti. Shi kanshi ya rasa gane wannan masifar da ta Kunno wa rayuwarshi na son matar aure.

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now