056

107 5 2
                                    

*💥ZAZZAFAN KISHI....!*         _{Sabon Salo}_

*FREE BOOK.*

Na Jeeddah Aliyu

Wattpad-jeedddahaliyu

©HWA

*Ga masu buƙatar a tallata musu hajar su cikin farashi mai sauƙi kindly contact me on my cell phone number 07032566172*

_*Gare ku masoyana ma'abuta karantar litattafai na ga wata dama ta same ku da za ku karanta littafai na complete documents har guda uku a cikin farashi mai sauƙi gaske dukka littattafai na guda uku akan ₦700 littafan sune kamar haka*_
*AZAAD JUNAID*
*GIDAN RINA*
*DA BANSAN ASALINTA BA*

_Ga masu buƙatar guda ɗaya tak_

Azaad junaid ₦300
Gidan Rina ₦300
Da bansan asalinta ba ₦250

*Assalamu alaikum*
Ina miƙa sauƙin gaisuwa ga masoyana mabiye wannan littafin nawa. Bayan dogon lokaci da ku ka ɗauka kuna jiran ci-gaban wannan labari sai yau ALLAH ya nufe ni da ci-gaba da kawo musu shi a dalili wasu abubuwa da suka faru dani wasu masu daɗi wasu akasin haka cikin amincewar Ubangiji da iyawarsa gashi na sake dawo muku da ƙarfina in-sha-ALLAHU babu tsayawa har sai na kai muku ƙarshen wannan labari mai ɗauke da cakwakiyya, al-ajabi, butulci, cin amana. Ku dai ku ci-gaba da haƙuri tare da jimirin bibbiya ta.
___________________________________

056.

Muryar Bilal Shattima na tsikaya yana cewa "Khamis ga Jeeddah. Kana ya juyo gare ni ya ƙara cewa "Jeeddah ga Khamis duk wani bayani da ya danganci nai masa akanki already nayi masa tun kafin haɗuwar ku. Hakazalika ke ma na faɗa miki takaitaccen tarihin sa.
   Duk maganganu da Bilal yake yi ba wanda na fahimta a dalili wani irin bugawa da ƙirjina ke yi na kuma rasa dalili faruwar hakan. Sai da khamis ya sauke boyayyen numfashi yayin da fuskarsa ke ɗauke da miskilin murmushi, ya ce "Ka yi haƙuri maigida Bilal akan tambayar da zan maka watakila ta ɓata ma rai miyasa ka ke so tayi auren kisan wuta alhali kasan ALLAH ya yi hani da yin sa?"
Tamke fuska Bilal Shattima ya yi saboda duk mutumin da ya ce zai kawo masa illar dake tattare da muradin sa haushinsa yake ji cikin daurarriyar murya ya ce "wannan ba matsalar ka bace khamis asalima wannan aiki ba kyauta za ka yi min ba biyan ka zan yi ba kuma ƙaramin amfana za ka yi da kuɗin ba musamman da za su zo ma a daidai Lokaci da ka ke da tsananin buƙatar su.
   "Haka ne Maigida Bilal tabbas ina tsanani buƙatar kuɗi shi ne ma dalili da yasa na amince da buƙatar ka saboda haka ta ɓangare na babu Matsala sai ka tambaye ita uwar gayyar idan nayi mata?"
Da sauri na ɗago da nufi na ce ba ka yi min ba sai kawai na tsikayi muryar Bilal yana faɗin babu buƙatar domin aure wuci gadi za ku yi saboda haka ba sai ka yi mata ba asalima bana buƙatar ka yi mata. Saboda haka ka shirya daga gobe za ka fara zuwa zance gidansu daga nan za tai ma iso gun mahaifinta kai kuma sai kayi gaggawar tura magabatan ka banaso a ɗauki dogon lokaci na fi so ayi komai agaugauce a wuce wurin.
   Cike da zallar mamaki Khamis yake kallon fuskar Bilal Shattima wato komai shi zai shirya masa azahirin gaskiya Jeeddah yake tausayi in ban da kwaɗayi na mata ALLAH ya raba ki da wannan mummuna mai kama da gwaggo biri, da wani burtomi hancinsa kamar ƙofar kasuwa miye na wani aure kisan wuta ki koma masa ai kamata ma yi ta haɗa gaggarumin party a tayata murna rabuwa dashi.
   "Khamis ya naji ka yi shiru ba ka ce komai ba kodai tsari nawa ne bai maka ba?"
   "Hmmm! Ba ko ɗaya maigidan Bilal ai ni banida zaɓi sai abunda ka ce.
   Murmushi Bilal Shattima ya yi tare da faɗin "shikenan za ka iya tafiya zan nemi ka daga baya sannan ka duba ta WhatsApp na tura maka number Jeeddah koda za ka je gidansu sai ku yi waya.
  "Okay maigida.
Khamis ya faɗa gami da miƙewa ya kalli Jeeddah ya ce "Ranki shida de sai anjima.
  "Humm! Ka gaida gida.
Na faɗa a sanyayye bayan tafiyar khamis na gyara zama tare da fuskantar Bilal na ce "Ni fa Love kwata-kwata ban yarda da wannan mutumin ba wallahi bai kwata min a rai ba.
   "Haba! Love don ALLAH kada ki kawo mana cikass! A cikin tafiyar nan. Da ace Khamis yana da wata matsala da ko kusa ba zan kawo miki shi ba.
"Duk da haka Love ka ƙara zurfafa bincike akan sa ruwan munafukai ne dashi.
   Dariya yasa kamar wani wawa ni kaina naji haushi dariya da yake yi ba kasafai nake so dariya ba a wasu lokuta ina sauri harzuƙa idan ana min dariya a fusace na ce "Banaso dariya love ka daina da wannan dariyar ta rashin dalili da ka ke yi dama ka natsu ka yi nazari abunda na hango a tattare da wannan mutumin mai zubin munafukai.
Ya tsagaita dariyarsa kana ya ce "Jeeddah ki yarda dani Wallahi-azim khamis bashida matsala nan da ki ke ganinsa mutumin kirki ne mai matuƙar tsoron ALLAH.
    "Mtsss! Mai tsoro ALLAH ne zai yarda ya yi auren kisan wuta ko kuma shi nashi kalar tsoron ALLAH ne haka.
"Kin ga Hajiya Jeeddah mu jingine wannan zance a gefe mu ɗauko wani.
Kafin na bashi amsa waya ta tai ringing nai sauri zuge jakkata na ɗauko sunan Mommy na gani da sauri nai picking "Assalamu alaikum Mommy Ina wuni?"
  "Wa'alaikum Salaam lafiya qalau Jeeddah na kira Mamanku a waya ta gayamin kina hanya zuwa gidana idan da akwai kuɗi hannunki ki biyo min da cabbage sai da na zo aiki dashi na tarar babu gashi kuma direba ya tafi Airport ɗaukar Haidar.
   "En! Mommy ina da kuɗi shi kaɗai ne kike da buƙata?"
"En!
Mommy ta faɗa tare da jaddada min da nayi sauri ni kaɗai take jira.
Shiyasa ina maida wayana jakka na miƙe cikin sauri Bilal Shattima ya kalle ni tare da faɗin "Ya naga kin miƙe ba dai tafiya za ki yi ba?"
  "Tafiya zan yi Love Mommy tana jira na.
   "Haba! Love bai kamata ki tafi tun yanzu ba musamman idan ki ka yi duba da tsawon lokaci da muka ɗauka ba mu haɗu ba.
  "Ni ma ba a son raina zan tafi ba na gayamaka tun farko karya na yiwa Mama na ce gidan mommy zan tafi to shine ta kira ni yanzu ta ce na siyo mata cabbage na taho mata dashi ka ga bai dace na zauna ba.
   Ambatar mommy da nayi yasa annuri kan fuskarshi ya ɓace batt! Ya yi kici-kici da wannan fuskar tashi kafin cikin muryar dake bayyanar da ɓacin ransa a fili ya ce "Ni fa Jeeddah banaso kina zuwa gidan Turai domin tuni-tuni zuciyata take kimtsa min so take ta sake cusa miki ɗanta a karo na biyu, dama can tana cikin mutane da suka tsani tarayya ta dake, shiyasa duk duniya idan da akwai mahaluki da na tsana bai wuce Haidar Ka'oje ba. Domin shi kaɗai ne mutumin da nake da yaƙini zai iya rabani dake rabuwa ta har abada.
   Yadda Bilal Shattima ya kira sunan Mommy gatsal ya yi masifar ƙona min rai ko babu komai Mommy ta cancanci girmamawa a gare shi kasancewarta ƙanwar mahaifina uwa ɗaya uba ɗaya yadda Mommy take nuna min ƙauna zan iya cewa ko 'ya'ya da ta haifa albarka. Idan har aka faɗin maganar banza akanta dole na ji ciwo saboda haka cikin ɓacin rai na kalle shi gami da faɗin "A'ah dakata malam banaso rashin kirki sunan mommy fa ka kira gatsal ba ko sakayawa kada kaga na amince da buƙatar ka, ka nemi wuce makadi da rawa muddin za ka ci-gaba da nuna rashin ɗa'a akan Mommy wallahi za mu iya ɓatawa domin Mommy Turai mahaifiya ce a gurina ba wai ƙanwa mahaifi kaɗai ba. Tun da nake da Mommy bata taɓa cusa min ra'ayi na so Ya Haidar ba saboda haka wannan ya zama karo na karshe da za ka furta mummunar kalma akanta.
    Yadda Jeeddah ta zage tana ta faɗar maganganu hakan ba ƙaramin ƙonawa Bilal Shattima rai ya yi ba dama kusan mutane naku da baƙar zuciya babu mai haƙuri a cikinsu kowanne su zuciyarsa a baki take saboda haka a hasale ya kalleta yana wani ƙanƙantar da idanuwa na tijara ya ce "Yanzu na gano ki Jeeddah idan har kin fara son Haidar Ka'oje ki fito fili ki faɗa min na daina wahalar da kaina a banza akanki.
   Nima a fusace na kalle shi from head to toe gaba ɗaya zufa ya jiƙa shaddar jikinsa kamar an masa wanka da ruwa, naman fuskarsa sai rawa yake yi kamar abinda ake girgizawa nan take haushinsa ya ƙara kama ni na ce "idan har haka zuciyarka ta kimtsa ma to ka ɗauka haka ɗin ne dama za ka ɗauki shawara ta ka je ka rage wannan uban ƙiba da ka ke kaya yafi ma wannan zargi da ka ke min.
Daga haka na juya rai ɓace na buɗe ƙofa na fice abina ina jiyo shi sai ihu da ɓamɓatu yake yi ko waigo wa ban yi ba. Bayan na siyawa Mommy aike ta akan hanyata na zuwa gidanta traffic ya tsayar dani sai na hango mai siyar da turare mota dama nawa ya ƙare na sauke gilashi mota na kira shi na siye guda biyu bayan traffic ya sake mu horn na ji ana min a bayana ni dai nasan akan hannuna nake saboda haka banga dalili a dinga yi min wannan ɗibar albarka ba. Ci-gaba da tafiya nayi ba tare da kaucewa ba ko kuma na ƙara speed kamar daga sama naga wata black Benz ta zo daff dani mamallaki motar ya zuge gilashi ya leƙo da kanshi, ta window ya kwalla min kira "Maijiddah Dan ALLAH ki tsaya ki bani taya ta.
  Lokaci da nayi arba dashi zaro idanuwa nayi a zuciyata na ce "Amma wannan mutumin an yi wawa duk don saboda taya ko taya ma take me home ba wata taya kirki ba zai nemi ya tashi hankalina akan titi mtsssss! Sabon yankar rake kawai.
Na faɗa a bayyane tare da gangara wa gefen titi nayi parking zuciyata cike da zallar haushinsa, tsabar takaici dake cina yasa na kifa kaina akan steering. Fuskarshi ɗauke da shu'umin murmushi ya ƙaraso yana zuwa babu wani excuse ya buɗe front door ya zauna kallon amma ba kada hankali nai masa kafin na taɓe baki leiƙa fuskata ya yi tamkar zai sumbace bakina nai sauri ɗauke kaina daga steering ina hararashi ƙasa-ƙasa "Maijiddah manya ganinki sai mai sa'a kullum ina sintiri haɗe da gararranba neman ki sai yau ALLAH ya haɗa ni dake.
   Har ya dasa aya ina kallonsa da baki buɗe yanzu saboda ALLAH akan wata tsinaniya taya take me home yake nema na a kufule na ce "Yallabai halan taya taka ta gold ce domin kasantuwar ta gold kaɗai zai sa ka dinga gantalli nema na?
Na ƙarashe magana ina wani yatsine fuska.
Wani irin azababben sonta ke ratsa jini jikinsa duk abinda take yi mugun burge sa take yi ji yake kamar ya jawo ta jikinsa ya yi mata kyakkyawar runguma, ya tsotse ɗan ƙaramin bakinta.
"Da alama na ɓata miki rai ko?"
    Sai da na sake galla masa harara kafin na ce "Ba iya ɓaci rai ba har haushi da takaici ka bani.
Sai kawai yasa 'yar ƙaramar dariya yana kallona yana wani lumshe idanuwa "ALLAH ya huci zuciyarki gimbiyar matan dukka duniya nayi haka ne domin shi kaɗai ne uzuri da zan kawo da zai sa ki tsaya mu gaisa.
   "Gaskiya Yallabai kai ɗin na musamman ne yanzu saboda mu gaisa zai sa ka dinga kwaɗa min kira akan titi, gaskiya banaso kar ka sake yi min haka.
Murmushi ya yi tare da faɗin "Tuba nake ranki yadade da girman kujerar ki in-sha-Allahu hakan ba zai sake faruwa ba.
  Sai lokaci na saki fuskata na ce "Ka yi haƙuri Yallabai ban san inda zan ganka ba shiyasa ban kawo maka taya ka ba. Kuma koda na dawo daga Saudiya na tarar da Yayana ya canza min mota gashi taya ɗinka yana ciki wancan mota.
   Duk abunda take faɗa daidai da second ɗaya bai ɗauke idanuwanshi daga fuskarta ba. Baisan haka yake mahaukaci sonta ba sai da yau ya haɗu da ita sai da ya saki kyakkyawar ajiyar zuciya kafin ya ɗage girar ido guda ya ce "Karki damu Maijiddah ni tuni na manta da zance wata aba taya burina shine ta wacce hanya zan bi da zan ci-gaba da gani wannan kyakkyawar fuskar taki mai hanani bacci.
    Taɓe baki nayi gami da faɗin "miyasa za ka saka wa ranka ci-gaba da son ganina alhali ka kwana da sani hakan ba daidai bane ko manta ni matar aure ce?"

#Bilal Shattima
#Egnr Ameer
#Haidar ka'oje
#Jeeddah maishadda
#team zazzafan kishi

ZAZZAFAN KISHI {Sabon Salo}Where stories live. Discover now